SOYAYYA CE

EPISODE 02

by @abdull10k

*SOYAYYAH CE*©®2020

     *MINI SERIES*

*✍STRONG PEN WRITERS ASSO.🖋🖊*

  _aiki da nazari domin farin cikin makaranta(readers)_



  *DAGA ALKALAMIN MARUBUCIN*


MEENAH SERIES

RAEES AND NAJMAH

AWANNI CESA'IN

WAYE SILA


*AND NOW*


*🌹🌸SOYAYYAH CE🌸🌹*


*Written*

Abdul Alhaji musa 10k

*Wattpad*

@Abdul10k

*WhatsApp no:*

@***

*Facebook acc*

Abdul Alhaji musa

*YouTube chennal*

Rahama TV




*DEDICATED TO MY FANZ ONLY,LOVE YOU ALL*



*EPISODE. 2*









"Ummah barka da safiya...."


Tace dani "barka ya hannun"

Nuna mata nayi maimakon nace lahiya.

.

Saita duba sannan tace

."waiyo hannun ya kumbura,kaga dole ka fasa zuwa school domin muje asibiti a duba ka.


Amince mata nayi muka wuce asibitin sannan mun yini a wajen,saboda zunzurutun layi......


  *3:00o'clock Shep*

Naji wayata na ringing,Ciro ta nayi daga aljihu na....

Kiran qudsiyyah na gani,inda nayi receive...


Sannan nayo Sallama,ansamin tayi

Sannan tace dani


"*friend*yau yahdai,........ban ganka a lecture bah?"


Ansa mata nayi cewar wallahi ummah ce ta kaini asibiti ga kuma layi......

"Harfa yanzun da muke maganan ina kan bin layin....

Muna. kan wannan maganar saiga kiran *Hussein*.


Inda nace da qudsiyyah ta dan rike waya na dauki kiran Hussein

Sai tace dani


"Ah hadamu *confriends* mana....."

Ni ko na amince Mata.


Nanfa na hadamu confriends din....inda Suka soma bani labarin abinda ya faru a school din yau........


Haka muka ta fira har lokacin ganin likitana yayi...

Na shige aka duba hannun nawa sannan aka taran magunguna birjik..

..


Nan muka koma gida,nako jeni side din su *Eysha*muka soma fira hade da wasanni kamar yadda muka Saba......kullum




*WASHE GARI*

na tashi babu sauran kuzari a jiki na.

Inda na tako a hankali har na shige falo....


Tadda *qudsiyyah,Hussein,ummah da kuma Eysha*

zaune suna fira inda nai mamaki kwarai da gaske,domin bansan tayadda suka naimo gidan namu ba.......


Karasawa nayi wajen su inda na tambaye su cikin sauri...


"Friends......wai taya kuka naimo gidan namu...?

.Gaskiya kunyimin bazata sosai."


Dajin haka kuwa suka murmusa,umman tawan ko ta bani ansan cewar..


*"Imraan* saurin mai kake kuma,ko sannu da zuwa bakai musu ba...... ka soma cika su da tambayoyi".


Murmushi nayi sannan nace da ita..


"Aiko wannan abin mamaki ne....kinga ko dole na tambaya.....irin wannan bazatar haka"


"Hmm gaskiya mutanen kirkine.....

aiko banyi zaton haka zan gansu ba....gasu da saukin kai...."


*Eysha*ce tayi wannan batu niko nace da ita


"Sis bar wannan zancen ki samo musu abinsha"...


Nan ummah tayi murmushi sannan tace dani


"Abin dariya,kaida yanzu ka tashi daga barci suko da suke nan tun 5:00am, zaman jiranka fa suke”.....


Nanfa na zuro idanu nace da ita


"Haba.....toh maiyasaka baku tashe niba....."


*eysha* ta bani ansar cewa


"Toh ai su suka hana a tashe ka shiyasa,wai sunce babu kyau yanke wa mutum barci....".


Nan *Hussein* yadan murmusa sannan yace dani


"Toh ba gashi yanzun ka tashi ba.....aiko kawai ka manta da baya......

shiga ciki Kawai ka sauya mu wucce school...."


✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔

Hmmm Yau kwata kwata babu kwari jikina nafi son na huta....

But zuwan nasu sai naji kwarin gwiwa nayi dakina cikin sauri na shirya sannan na fitoh......


Bayan na fito sannan nakuma karya kumallo, sai sukayi sallama da umma sannan muka taka izuwa farfajiyar gidan namu....


Inda naga jibgegiyar mota mai launin ruwan toka....

Nanko nayi mamaki sannan kuma na kasa cewa komi.


Domin banyi zato yan masu kudi bane su...

Nan muka karasa wajen motar sai Hussein ya bude but,ya ciro kiret kiret na moltina da kuma pik milk sannan da kayan d'anye ya jibgesu gaban *Eysha* sannan yce da ita..


"Sis kikai ciki...... inda mun ka wuce...


Nanko na cike da farin ciki nace dashi


"Hadda wahala haka....gaskiya na gode Sosai.."


"Aiko yiwa kayine...."

*Qudsy*ce tayi wannan batu


Nanfa muka shige motan sannan muka wuce school....din


🔛

haka kundin rayuwata....ta cike da shafukan farin ciki babu addadi......

haka zalika madubin rayuwa ta, ta cike da hasken ni'ima daga uban giji...

Kowace rana na zuwa min da ni'imar sa iri daban daban.....


Haka muka shafe watanni uku tare...Cikin soyayya irin ta friends...

Kullum mukan yini a school sannan muyi firar da daddare a *"WhatsApp group...."*


*Abotan tamu haka tayi tsanani....*

Dankon shakuwa tayi tsananin kaifi tsakanin mu,kai in fayyace muku,ranar da ban gansu ba har jinake kamar bani da lahiya......


*RANAR ALHAMIS DA MISALIN KARFE SHADAYA RANA, RANAR DATA ZAMANTO MINI UNFORGETTABLE*


lokacin muna cikin school,a wannan watan muna pripration nayin exam........

Shine dalilin da yasa testsis sukayi mana yawa....


Wannan ranar,a daidai kuma wannan lokacin muna shirin shiga wani test.

Wacce aka saka dokar saida laptop za'ayi ta.


Tun 2days back aka sanar damu,niko dana kasance bani da laptop saina shige naima a unguwar mu...

Nan shafe kwanki biyun nan ba tare da na samu laptop din ba...


Nan saina sanar da *qudsy*kafin wayewar gari, cewar banfa sami aron laptop ba itako tace dani...


"karka damu zan dan kokarta na samo maka a side na mu...."

Dajin hakako na saki jiki na daina naiman masu laptop din a unguwar mu...tunani na *qudsy* zata samo min.


Yau alhamis,kuma da muka hadu a school din saita bani hakuri akan rashin samomin laptop din datayi......


Tsaye muke guri daya *Ni,Qudsy da kuma Hussein*


Nanko "Hussein" yahau surutan cewa.


"Wannan wace iriyar gangacine....

Tunfa kwanaki biyu dasuka wuce aka sanar mana da cewa saida laptop zamu yi wannan test din, amma baka dashi shine baka sanar dani ba.....aiko da ko laptop din umman tawa saina dauko kayi using...but yanzu its to late uhmm"


Cikin nuna bacin rai ya furta hakan..

*qudsy* tace dashi


"Came down.....wannan kuskure nane,domin ya sanar dani tunda jimawa na kasa samowa....sannan ban fada mishi cewar na kasa samowa ba."


"Duk wannan maganar bata taso ba....5minute to start the test,kunga kawai ku shige ciki ku soma test din niko zan biyo ku daga baya".......

Hakan ko na furta cikin kasaita *qudsy* tace dani


"no we can't Left you behind.......idan fadiwace tazo,toh kasani tare zamu fadi sannan.... don't worry about us...."


"Yeah gaskiya ta fadi,kawai shawarar da akwai shine mu naimi aro anan.....

Idan kun amince da batun nawa ya kamata mu soma naimah kunga saura 4minute Left....."


Amince masa mukayi da cewar "yeah we have agree" cikin hadin baki.

Nanko muka bazama naiman laptop..

inda nayi ta wajen hutawa domin acenne zan iya samon mutane da yawa....


Nanko naita tambayar mutane iri daban daban but ansar su duk iri dayace

"Gaskiya kayi hakuri".


Nanfa na tsaya domin ko na gaji gashi kuma duk zufa ta mamaye sassar jiki na...


Ina tsayen nanko na hango wani wanda yake zaune sannan gefen sa kuma da wata siririyar yarinya mai kyawun gaske......


Dannadannen cumputer yake abin sa baya mind din kowa.

Niko da ganin haka sai na murmusa na nufi wurin da sauri.

Abinda ban sani kuma ba shine wannan yarinyar dake gefen sa ta kasance budurwar sace.....

Sannan kuma ta wahala tana rokon kan sa cewar ya bata Aron cumputer na minti guda tasai wani abu a online....amma saiya hanata.


Domin yace da ita abu mai muhimmanci yake da laptop din.


Bayanko danajeni gurin sa saina ce dashi..


"Broz....dan allah ka taimakamin da aron laptop dinnan naka mana,wallahi test nake dashi yanzun kuma sun saka dokar sai da laptop zamuyi.......gashi zan iyya rasa maki idan har ban samu laptop din ba....."


Dajin haka ko ya sauka dga abinda yake cikin laptop din sannan ya dagokai ya kalli fuskata....

  

Shiru yayi na yan dakiku sannan yayi Murmushi,niko na saukar dakai kasa alamar kunya..sannan sai yace dani....


"Dan kyaukkyawan saurayi,Bayan ka kammala test din ka mayarmin kaji......"

Wannan saurayin ne ya furta haka.....


Nan na murmusa sannan na anshi laptop din kaina na kasa.

karo daya ko naga fuskar mutuniyar tasa ta sauya...

Danko tawani hada fuka kamar wacce aka sanar da ita labari marar dadi ji.


Niko bandauki abin serious ba kawai na kara Gaba....


😱😱


Hmm Idan da ko nasan abinda zata biyo baya dako bazan yadda na anshi wannan laptop din daga hannun wannan saurayin ba.😢


Amma..

Kaddarar mutum takan riga fata.....


Haka na wuce da laptop banko tambayi sunan sa ba..

Shima kuma bai tamabayi sunan nawa ba.


Bayan na karaso gaban *hold* din, wacce ake test din aciki sai na tabo su qudsy a waya suka taho....cikin Sauri......


zuwan su keda wuya*Hussein* ya tambayeni cewar...

"Yahdai *imraan* naga ka kirawo mu ka samo laptop dinne"


Maimakon nace *eh* a'a saina daga nayi sheking nashi domin su gani..


Hussein ko yayi murna sosai sannan ya sake tambaya ta karo na biyu..


"Wani dan albarkan ne ya baka,sannan kuma ya sunan sa"?

..

"Ooops wallahi na manta ban tambayi sunan saba....".

Na furta hakan ne yayin dana dafa goshina da tafin hannuna.


"Uhmm toh tayaya zaka mayar masa da laptop din....?"

*Qudsy* ce tayi wannan tambayan..


Niko nace da ita


"Insha Allah ko zai jirani a wajen,kungafa mun bata lokaci....wannan tattaunawar zamuyi ta bayan mun fito...... dan Yanzun an soma test din kuxo kawai mu shige ciki".


Nanfa muka kashe maganar a gurin sannan muka shige test......


Bayan mun kammala sai muka naimi bawan allah bamu same shi ba........

Nan muka yanke shawaran na tafi gida dashi,gobe inda muka dawo sai mu cigaba da naiman nasa......

Domin munga dare ta soma...


Tafiya gida nayi da laptop din

Washe gari ko na koma dashi...

Inda muka sake yini muna naiman sa amma ba result..


Ahaka muka safe kwanaki uku da d'oriya kafin nan muka hadu da wannan budurwa tasa ina na tabbatarwa *qudsy* itace nagansu tare..


Tace dani


"Toh in banda abinka aisu yanzu suna 400level...

Shekarar su ta karshe a wannan school..

Aiko bazamu taba samun sa anan cikin tarun yan part1ba"


"Aiko dole ka gajiyar damu *imraan* tunda kaki tambayar sunan sa"..

Hussein ne yayi wannan batu


Niko nace

"anyway muje dai karta bace mana ..


Takawa mukayi izuwa wajen ta yayin da takasance tare take da friend Nata...


Sai nace da ita

"Barka dai sister...."


Nako ta juya da murmushi fuskar ta amma a sa'in da tayi arba da fuskata saita hada rai....


"Sunana *imraan* dan Allah zaki sanar dani,inda zan sami wannan abokin naki dana ganku tare rannan na ari laptop a wajen sa.."


Tashi tayi daga zaman datake sai ta kalli cikin idanuna tace dani..


"Shin kama nayi maka dame tantace mutane ne ko kuma kaka....tun wuri ka bace min da gani tun kafin nai maka illah....."


Dajin haka ko na juya sai na jiyo tana fadawa kawarta cewar


"Toh ai shine wanda nake baki labari......zumuzumu da shi"."


Nako na juya na basu guri jikina sanyaye..

Sai na karasa wajen abokan nawa.....


Sai qudsy tace dani

"Duk haka manyan school dinnan suke da ra'ayi...karka damu domin ko zamu samo shi...

Haka na sake wuce da na'uran gida....


*WEDNESDAY*

ranar Allah yahada mu,ta hanyar taimakon wata yarinya..

Sannan ta bamu labarin wannan yarinyar mai takamar tsiya.....


Cewar ta "aiko haka halayen ta suke tunfa ranar da akai musu baiko ta hanashi sakat....

Ta kasance Mai kishin tsiya sannan kishin nata ba kan mata kawai ta tsaya ba,harma mazan domin tabi ta rabashi da friends nashi....kuma sannan ta hani yanmatan schools din zuwa wajensa."


Dajin haka ko saina gyada kai alamar mamaki sannan nace kut...

Qudsy ko tace da ita


"Wannan wace iriyar kishine haka.....gaskiya wannan yarinyar bataji dadi ba"


Kiko band'auki maganan serious ba domin baji ko ajiki naba...

Nan na naimi daata mana rakiya izuwa wajen da zamu same shi..

Amma saita ki amincewa tace tana da Math class yanzu...


"Okay babu damuwa yi mana kwatancen wurin....

Qudsy ce tayi wannan batu

Inda wannan yarinyar tayi mana kwatance inda zamu same sa muka wucce sannan mah ta sanar damu sunan sa...


a lokacin ko muka wucce,muka kuma samesa a labary yana karatu....bayan mun karasa wajen sa

Sai nace dashi...

"Yahya daman computer ka muka kawo maka,wallahi tun wancen ranar nake naiman ka,Sannan kuma na mayar maka da laptop, but abin ya citura,kuma hakan ya farune a sanadiyar rashin sanin sunan ka danayi".


Da jiyo wannan batu sai yayi gajeriyar murmushi sannan yace Dani......


"Don't worry,ai nama sami wani tunda jimawa.......

Nasan zakai ta nemahna domin mun manta bamu sanarda juna.....sunayen mu ba.


Murmushi nayi sannan nace dashi


"Nagode d'an uwa........


Mika mini hannu yayi yayin da yake furta cewar

"I'm *Mubarak* ,na kasance....... ina shekara ta ta karshe a wannan unimaid"


Dajin haka nayo murmushi.....sannan nace dashi


"Imraan nake wannan kuma kawatace qudsy........muna part 1.


"Oh Nice to meet you guys,at any time idan kuna bukatar taimako ku sanar Dani.....kunji


Mubarak ne yayi wannan batu yayin da yake mika mana card Nasa..


*HAKA MUKA ZAMANTO ABOKAI CIKIN KANKANIN LOKACI*

sannan muka shaku sosai,haka ya shigo cikin tawagar tamu....

Amma ko sunfi shakuwa da *qudsy* domin koda yaushe saita yi masa magana ta WhatsApp....

Sannan tayi hanyar da aka sakashi cikin department group namu....


Kullum tare muke da juna,wajen shan coffee,labary....resting place dadai sauran wajajen....


Dukkan abubuwan dake faruwa babu wanda ke da sanin cewa wannan shakuwar tamu na bakantawa *may ah* rai


Tuni muka manta da ita.......haka Mubarak ma yayi mata rata....

Sannan wasu lokutan idan tana naimansa sai ta naimesa ta wayan mu domin mu hadasu.....


Bayan kwanaki kalilan y'an ajinsu *Mubarak* suka soma hada shagulgula sannan kuma kowace shagalin sai sun gayyace mu...domin mune close friend na Mubarak....


Haka muka hallauci shagulgula iri daban daban tare kuma da Mubarak din.....

Haka ma yau muna tare wajen shagali inda na soma jin barci tun 9:00 saina wuce na kyale su qudsy a wajen......


Karasawa nayi gida 9:30 inda ban tsaya ko inaba sai kan katifa ta...

Nan na fadin kan shunfudar na soma mishari.......


  *TWO DAYS LATER*

  

  

  farkawa nayi daga barci,6:59 inda nayi saurin mikewa na nufi bayi.....sannan na Watsa ruwa

   nan nafito...cikin kankanin lokaci na shirya sannan na taka izuwa falo..

Inda na tadda abba na zaune yana karanta *news paper*


Gaidashi nayi sai yace dani......


"Imraan,yana ganka cikin rushing?


"Chem 101 muke da shi yaushiyasa nake saurin.....

Haka na basa ansa shiko yace dani


"Kennan bazamu karya kummallo tare ba....?


"Eh dad,ina da poket money zanyi using......na karya a school din..


"Ok wish you the best......


Nanfa na taka izuwa bakin titi inda na tsaya....inda na tsaya din kuma takasance wurine da mutane ke tsayawa domin hawa daidaita.....


Tsayen nake sai ga wasu samari biyu sun zo wajen da muke tsayen.....

Tsayawa gefen namu sukayi,bayan wasu yan dakiku sainaga sun zaro waya daga aljuhunsu sannan suka soma duba wani abu ciki wayan....

Suna duba cikin wayan hade da nuna ni da yatsa suna cewa


"shine....wallahi shine fa ku duba kugani.......

Nan kaina ta dagule na kasa sanin meke faruwa...


Haka duk gurin dana ratsa saina ga wasu na nunani suna "shine,gashinan.....


Hakama cikin school din sukai ta nuna ni

Niko bansan meye silar faruwar haka ba.....


Duk inda na jeni saina ga kowa ya tashi ya wuce......





*GAJERAN LABARI,YAKAMATA KUSAN DA HAKA*

*DAGANI ABDUL ALHAJI MUSA*

*MASU BADA SHAWARA,KO KUMA GYARA KOFA A BUDE TAKE*

.


*KU TUNTUNBE WANNAN LAYIN*.


.


*🌹🌸SOYAYYAH CE🌸🌹*

    *MINI SERIES*