RUHI BIYU!

EPISODE 05

by @abdull10k

πŸ§Ÿβ€β™‚οΈπŸ§Ÿβ€β™€οΈπŸ§Ÿβ€β™‚οΈπŸ§Ÿβ€β™€οΈ

   

    *RUHI BIYU*

 _[a gaangar jiki daya]_


            πŸ§Ÿβ€β™€οΈπŸ§Ÿβ€β™‚οΈπŸ§Ÿβ€β™€οΈ πŸ§Ÿβ€β™‚οΈ   β€


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

   _Kungiya d'aya tamkar da dubu._



    *_SPECIAL EDIT 2021/2022_*


*Written*

Abdul Alhaji musa 10k

*Phone no:*

***


     *REPORTS*


 *FREE BOOKπŸ’―βœ…*

*EPISODE_0️⃣5️⃣*




*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*


*FRIDAY UPDATE*

*_March_27_2020_*


*_BIRTHDAY WISHES_*


πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽ

*HAPPY BIRTHDAY YAYA HAYAT[THE ADMIN OF ADMINS]*


I wish you continuous dreaming, planning and achieving your biggest dreams; may you find fulfilment in your endeavour. Happy Birthday..

On this special day, may your life be renewed with crackles of laughter and the great feelings of affection; I wish you the best of your dreams.


*HAPPY BIRTHDAY YAYA HAYAT[THE ADMIN OF ADMINS]*

πŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽπŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰


*RECAP ON EPISODE 5*

 _PAGE 20 TO 24_


Hakan yake furtawa yayin da yake kokarin shigewa *shop* din....

Nanfa yayi karo da safraz da kuma Rihana....inda takardun dake hannun safraz ta zube.....kasa


Ba tare da yaga fuskar safraz ba ya tsunkuya ya kwaso takardun.....

Saifa daya kammala wayarsa.....yakuma saka a aljihu kafin nan ya Mike....


"I'm sorry wallahi ban ganku bane......"

Furta hakan yayi a lokacin da yake....kakkade kurar dake jikin books din...

But a lokacin daya d'ago ido sukayi arba da safraz....saiyayi murmushi...hade da Mika ma sarfaz littattafen....


Ajiyar zuji safraz yayi sannan ya Miko hannu da niyar ansan littattafen...

But supresily sai Harun ya sake littattafen suka zube kasa.....

πŸ†•

Parking yayi a gefe guda.....

Inda ya sauko daga motar..ya kuma taka ahankali izuwa wajen friend nasa....


"What took you so long.....Harun,shin kasan kuwa tun d'azu nake zaman jiran ka anan.....gurin?"


"Oh God taya zansan da hakan.....tunda bana gurin...

Anyway za'a shiga aji yanzu....idan kuma muka Bari malamin ya shiga gabadamu toh pha mun banu...."

Haka ya basa ansa...abokin nasa ko ya sake cewa dashi...


"Yeah hakane.....but You look so worried....Harum,what happen to you?"


"actually wanine ya 'bata min rai...,awajen sayan abinci"

Haka ya basa ansa...abokin nasa ko cikin bacin rai yace...


"What!! Waye wannan? Mai yake takama dashi?"


"Oh daad'i na dakai saurin fushi.....anyway I'm enjoying fighting....with him

Domin Yana burge ni yaro.......I always like to teste his filling.....cause yin hakar na nishadantar dani" 


"What do you mean.......by saying,Kana jin dadin fad'a dashi....

And idan ma kana enjoying...mayasaka ka kasance cikin bacin rai toh"

Haka abokin nasa yace dashi..shiko yace 


"Yep because I did something rubbish.....and I really regret it"


"What?.....😁

are you serious?,daman wannan sad face din....Dan ka 'bata ma wani rai ne?

Hmm okay bani Labarin what happened then....

Domin naji mai kayi da kakasance cikin bacin rai"

Abokin nashine ya furta hakan.....


"Maybe bayan mun shiga lecture zan baka labarin....komi

But now we are late...so mu wuce cikin ajin kawai"


Nanfa suka wuce aji....inda suka tarar da malamin already acikin ajin....

Sunawa wannan malamin lakani da *No nonsense* domin yadda sukaga ya dauki komai nasa da daraja.....

Tunda ya soma koyarwa a wannan school din baifah taba barin *late comers* sun shiga aji ba....

Daga zarar ya shigo aji,toh fa babu wanda zai sake shiga a ranar...kodan waye shi.


"Excuse.....Sir"

Haka Harun ya furta.....

But ko waigowa malamin bai yiba....nanfa suka soma raukon alfarma dukda sunga baya kulasu,sunyi tamai magiya....amma babu respond daga gurin sa...

Sun cinye akalla 20minutes suna gurin a tsaye....

Nan saiga *Safras da kuma Raihana* sun zo cikin rushing....


Bayan sun karasa wajen....suka tsaya guri guda.....harun ko bayan sun hada ido da safras.....ya wani murmusa kamar ansakashi yi dole....😁


"Excuse me sir" safras ne ya furta haka.....

"Please sir can we come in?"......furta hakan keda wuya sai malamin ya juyo hade da murmusawa....


Takawa yayi a slow izuwa wajen nasu......sannan yace da safras din..


"Malam safras....sabida kai,sabida kai zan baku damar shiga....."

Nan ya juya ya kalli sauran yace da su.....

"Last warning....."


Nanfa yayi allowed nasu suka shige.....ajin

Bayan sun shige ajin kuma Safras da Rahina suka zauna guri daya....

Da ganin haka Harun ya riko hannun...abokin nasa yajashi izuwa kujerar da su safras suke zaune....


"πŸ™„πŸ™„what the hell...are you doing" haka Rihana ta furta bayan Harun da abokin nasa sun zauna.......


Hada fuska safras da rihana sukayi,harma sunyi yunkuri tashi subar gurin...

Sai suka jiyo muryar malamin na cewa....


"What wrong with you guys....?,it's just because I let you in....

Shiya saka kuke takurawa ajin da surutu ko?......

Toh I don't want to hear your voice again"


"Okay sir"


Bayan malamin ya koma koyarwar sai abokin Harun yace....


"Yauwa yauwa I remember.....bani labarin"


Harun alama yayi ma abokin nasa da baki....inda ya gane cewa wannan na gefen sa... shine wanda yake son fad'a dashi......


"Oh Great..he look so beauty....bani labari"


"Wai mayya saka bazakuyi shiru bane....duk kunbi kun cikamana kunne da surutu...

Ko damar sauraran lecture bamu da shi"

Safras ne ya furta hakan...Suko basu ma kula shiba...


Harun ciro waya yayi inda ya shige....WhatsApp...ya soma typing ma abokin nasa..

Yana bashi labarin abinda ya faru a Ice cream places din kamar yadda ya bukata.....


Nanfa ya zaiyana ma abokin nasa komi.......asa'in zo wajen daya zubar da littaffen safras......

Sai abokin nasa ya fashe da muguwar dariya....


Inda dukkan student din dake cikin ajin suka juyo ganin su izuwa wajen dayake zaune....


"Sorry sorry....."

Haka ya furta yayin da yake sosa kai....malamin girgiza kai yayi sannan ya cigaba da koyarwa...

Haka shima ya cigaba da karanto labarin kamar haka....  


Ajiyar zuji safraz yayi sannan ya Miko hannu da niyar ansan littattafen...

But supresily sai na sake littattafen suka zube kasa.....


"Oops Dan gaye....littattafen sake zubewa..."


"Alright....it's okay ka wuce kawai zamu tsinto su"

Haka safras din ya bani ansa...yayinda suka tsunkuya dashi dakuma rihana..

Suka soma tsinto books din.....


Sadly na taka daya daga cikin books din yayin da safras na kokarin daukowa saita tage...

Wanda wannan book din ta kasance assignment ne aciki....


"Oops sorry again,"

Bayan na furta hakan na taka izuwa wajen masu sayar da Ice cream din...ya tsaya


Safras ko Hada rai yayi yayin dayaga assignment nashi a yage....


"Safras dear... what happened? are you alright?"

Haka tayi mai tambayan danko bataga lokacin da na taka assignment din ba...


"I'm fine...muyi sauri mu wuce lecture"......


Nanfa abokin Harun...yakawo karshen labarin......

Inda ya dago kai ya kalli fuskar Harun....


"Gaskiya Harun....kanada naiman rikici....anyway labarin ya nishadantar dani......"

😁😁😁


*nan ya ajiye hankali ya soma sauraran lectures*


*5:42PM*

Safras da Raihana....sukayi sallama,inda ta shige adaidaita ta wuce gida..Saida ta karbi number safras kafin ta wuce......


Tsaye safras din yake inda yaji alarm na bugawa a wayar sa....

*5:50Pm* ya gani inda ya zuro idanu ya soma sauri.....

Ya wuce dakin sa....kamar yadda ta faru a yammacin jiya,haka ma yau din...ta faru.


Bayan ya shige dakin ne ya rufe kofa, sannan wata farar haske mai dauke ganin mutum....ta bayyana....na yan wasu dakiku.


*Bagaren gidan su Harun kuma*


Ramlah ce ke tsaye a kitchen....tana cooking....yayin da take sauraran wani new song na *Dj ab* tana kuma mamin kamar ita ta raira wakar.

Bayan ta gama hada komi na abinci ta daura a kan *gas cooker* sannan ta wuce falo ta zauna...a kusa da mahaifiyar ta..


"Ramlah...shin *Harun* yauma zai dawo gida late ne...."


"Uhmm haka ya fadamin,dazu da mukayi waya,yace yanada aikin da zaiyi a gurin

Maybe 9:00 ko 10:00 zai dawo gida"

Haka ta bawa umman nata ansa....umman natanko tace da ita.


"Okay ki kula da abincin,bari na shiga na watsa ruwa...

Sannan mind me,ya kamata ki daina sauraran wake wake a irin wannan lokacin..."


"Oh Mom,shin wai yaushe zaki daina wannan surutan ne...kullum a daina sauraran kid'a

Kullum ace abu daya..."

Haka ta bata ansa yayin da take kokarin saka iyafis a kunne....


"Hmm shikenan nidai na wuce"


Bayan mahaifiyar tasu ta wuce....sai ta dauko masarrafi ta kunna...TV ta soma kallo...yayin da kuma ta aje wayar tata a gefe guda...

Shiga *Zee world* chennal tayi yayin da ake nuna *bolly tone* ma'ana wakoki akeyi a lokaci...

Nan ta soma gyada kai tana mai murmusawa...bata dauki 30minutes tana wannan kallon ba sai taji an kashe Tv aka sake kunnawa.....


"Oh naipa yah haka......"


Cigaba tayi da kallon bayan Tv ta gama loading...


Nanfa taji anzo da gudu ta baya aka shake mata wuya.....

Ihu ta buga,maimakon tayi addu'a....

Ayayin dataji duk gashine ta mamaye mata wiya....

Ma'ana hannun wannan abun na lullube da gashi....

Kokari take taga ta kwato kanta.....daga hannun wannan abun....but sai ta gagara yin haka...

Daga karshe abin ya sake mata wiya,bayan tasha bakar azaba.....jikinta na rawa ta waiga baya inda tayi ido biyu da wannan abun mai muni...

da ganin fuskar wannan abinko ta sake uban ihu...danko idanun wannan abun sunfi a irga....


A firgice ta farka daga barcin da take......inda tayi saurin ciccire iyafis din dake kunnuwan nata....

Nishi take yayinda zuciyar ta ke bugawa kim kim kim.....sannan ta kuma jike shakaf da zufa....


Dafa goshi tayi...sannan ta ambata cewa....


"Oops ashe ma mafarkine..."....hmm maimakon tayi addu'a...a'a sai ta ambata oops


Tashi tayi ta wuce izuwa....kitchen inda ta sake arba da wani abin mamakin....

Ba komai bane wannan illa taga babu komai a wannan kitchen...kama daga kan *PANCAKE* πŸ₯ž data hada da su *yellow rice* dadai sauran su dukka babu komi....

Duk anbi an kwashe....


Sheka uban ihu tayi.....akaro na biyu yayin data ga haka...nanfa ta farka daga barcin dominko still daman tana wannan barcin....

Farkawar datayi a fari itanma ta kasance part na wannan. mafarkin ..


Tarar da umman nata tayi a zaune gefen ta tana kuma shafa man jiki...


"Sai shegiyar san barci.....wai yaushe nema na shige bayi....

Amma har kin wani yi barci...."


Haka umman tana ta furta....itako ta zara idanu...

Afusace ta yunkura ta wuce kitchens inda ta tarar da komi normal.....

Zuro idanu tayi yayin data tarar da hakan......domin tayi matukar mamaki...


Idan kuma kuka leka dakin *Harun* zaku tarar da wannan zanen da zana na kyakyatawa....da dariya

Sannan bayan tayi hakan ta hade fuska at last....


*cikin university*


Wata santaleliyar yarinyace ta bayyana a *male hostel* a hankali take takawa sannan ta kasance babu ko talkami a kafar ta....


Bakin kayane a jikin ta....sannan takasnce farar fatace ita....

Siririyace mai kyan gani da kuma yalwar gashi....


Takasance tana hayewa wannan upstairs....saifa datakai last floor ta dakata....


Tsayen take yayin data haye samar wannan gini....sannan ta saukar dakai kasa ta soma kallon kasan gurin.


Kasar wannan ginin ko Harun ne ke tsaye yana kokarin kiran abokin sa...awaya

Wasu bakaken haluttune suka kewaye sa....yayin da ya kasance baya iyya ganin wannan laliktun...


Amma wannan yarinyar dake saman ginin na kallon komi.....

Wannan haluttun ko sun kasance suna kokarin suga sun taba jikinsa....harma suna taba kayan jikinsa.

Nanfa sai wannan yariyar ta diro daga saman wannan ginin......ta diro a gaban Harun....


Bakaken aljanun da ma shi kansa Harun din saida suka razana....


A rakkwafe take yarinyar......tana kuma nishi kamar wata bakar mesa.....


Harun din kuma ya gagar ganin fuskar wannan yarinyar....ta sanadiyar gashi kanta ta lullube fuskar tata.... 

A fusace ta yunkura,bayan tadan dibe wasu dakikun....bakanen aljanun ko da ganin fuskar wannan y'ar suka ruga a guje suka bar gurin...


Dashike Harun din baya ganin komi baima ji ajikin saba...


"Yar uwah......kina lahiya kuwa"

Gadon bayanta yake fuskantan....shine dalilin daya saka jikinsa ke 'bari yayinda yake tambayar ta...


Gaskiya abin mamakine sabida gashin kanta har kugu....


"Hello"


."yar uwah......shin kina sauraro na kuwa"


........πŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺπŸŒͺ.......

KUDAKACE MU........MUHADU A NEXT EP