EPISODE 06
by @abdull10k
π§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈ
*RUHI BIYU*
_[a gaangar jiki daya]_
π§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈ π§ββοΈ β
*πMANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πποΈ*
_Kungiya d'aya tamkar da dubu._
*_SPECIAL EDIT 2021/2022_*
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Phone no:*
***
*REPORTS*
*FREE BOOKπ―β *
*EPISODE_0οΈβ£6οΈβ£*
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*UPDATE*
*_APRIL_3ST_2020_*
*Ramlah* zaune take a falo.......tana kallon tashar *Starlife*
10:45Pm ita kadai,ke zaune cikin falon....nanfa sai taji an kwankwasa kofar daki....
Cikin sauri ta yunkura ta taka izuwa bakin kofar ta bude.....
Inda tayi arba da *Harun* a tsaye bakin kofar......
"Au daman kaine?.......shigo daga ciki"
Nanfa suka shige dakin inda ta bashi abinci yaci yadan tayata fira kafin nan ya wuce dakin sa....
Hmm abin al'ajabi a nan gurin ko shine.....cikin university Nainah ce ke zaune...gefenta kuma Harun ne ke kwance....
Alamar a sume yake......
π²π²π²π²π²
Toh abin mamaki idan har yanzu *Harun* yana cikin makarantar toh waye wannan wanda yaje gidan a suffarsa?
π²π²π²π²π²
Cikin kasala *Harun* ya bude idanu inda yayi ido hudu da *Nainah* zaune gefensa....
Abinda ya soma fitowa daga bakinsa ko shine.....
"Nasan zamu ga juna......Nainah"
Cikin kasaita Nainah tace dashi.....
"taya kasan sunana?.....sannan waye kai"
Dajiyo haka yayi yunkurin cewa wani abu amma daga baya ya janye.....
Itako ta sake tambayarsa a karo nabiyu....
"Baka cedani komi ba....taya kasan sunana"
"uhmmmmmmm Kawai naji tazomin ne"
Bayan ya furta hakanne ya soma waige waige.....alamar bai gane gun da yake ba.
Da ganin yadda yake ta jujjuyawar yasa ta tace dashi....
"Dan saurayi.....karka zurfafa tunani,nasan kana mamakin ganin kanka dakayi a nan gurin......
Bari na sanar dakai abinda ya faru....na tarar da kai kwance ko nace asume bakin hanya shine na dan taimaka maka"
Da jiyo hakan fa *Harun* ya tuno da wannan farar abin daya diro masa a gaba....
Cikin sauri ya yunkura...inda *Nainah* tace dashi.......
"Kayi a hankali.....Kuma tunda ka farka ni zan wuce"
Da jiyo haka sai ya juyo ya tambayeta cewar...
"Shin baki tarar da wata...wacce take sanye da farar kaya a gurin ba....?"
"A'a babu wanda na gani....amma lahiya kuwa? Mayya saka ka tambaya?"
Haka ta bashi ansa shiko ya sake da cewa....
"Sanye fa take da farar kaya,gashin kanta kuma har kugunta ya tsaya....."
"Nidai babu wanda na tarar a gurin"
Dajiyo haka ya dafa goshi hade kuma dayin wani batu kasar zuci.....
"Shin ko mafarki nake ne ne ne?".....
Hakan ya furta cikin kasar zuci,amma ko cikin karfi irin ta tsatsuba Nainah ta saurari komi.......
Gajeriyar murmushi tayi,daga karshe ta hade fuska......nanfa ta soma tunano abinda ya faru a wancen lokacin.....da kuma abinda yayi sanadin sumewar Harun.
β¬
A yayin da Harun ke Yunkurin taba kafadar wannan halittar data diro masa a gaba..... sai bakaken aljanun nan suka sake bayyana inda suka aika sakon tsafi....wacce tayi sama da Harun din ta kuma bugasa da kasa.....
Cikin kankanin lokaci ya sume....Nainah da ganin haka ta hade rai hade da cewa....
"Kai kananun masharranta mai kuke takama dashi da har zaku sumar da wanda nake karewa...."??
*Karku shige rudani _readers_ dan wannan wanda ta diro gaban harun ba kowa bace illa Nainah....*
Dajiyo batun nata ko daya daga cikin bakaken aljanun ya koma bayan babban nasu yace dashi......
"Yaya Gafur.....ninasan hatsarin wannan Yarinyan....
Itace fa wannan gimbiya danake baka labarin wato Nainah.........ita tayi sanadiyar mutuwar Gwarzon mayakan Bakaken aljanun na saman tsauni...."
Dajiyo hakan ko Gafur ya fashe da muguwar dariya hade kuma da kyakyatawa....yayinda muryarsa ke fita uku uku
Sannan yace da dan uwan nasa........
"ba gimbiya take ba...ko itace sarauniyar aljanun duniya ce,tunda dai ta shigo gonata saina koya mata hankali"
Haka kannen nasa sukayi ta kokarin tsayar dashi amma yaki sauraron su...
Dukda mawa kannen nasa akayima laifin amma hakan ta matukar hassala shi...
Nainah ko....motsawa batayi ba,ta wani bushe kim guri guda...
Nanfa gafur ya umurci kannen nasa da su basa guri....
Sannan yaja layi ya soma aika sakon tsafi iri iri.....
Tohfa dayasan abinda zai biyo bayan hakan da bazaiyi yunkurin hakan ba....
Danko Nainah..zaro wata zabgegiyar bulala tayi a tsakankanin yatsun ta mai kama da harshen uta...
Ta soma zabgan sa dashi.....bayan yayi laushi ta kama kunne sa ta soma hajijiya dashi a kai.....
Da ganin haka kannen gafur suka rusina hade kuma da cewa...
"Fatan tsahon rai ga gimbiya Nainah.....mun yadda mun kuma amince kece aljana daya mai karfin sadaukai dubu...."
Nanfa sukayi mata sujjada...itako ta hade rai sannan tace dasu...
"Karku bari na sake ganin ku kuna shiga rayuwan yan adam....a yanking masarauta ta .......
Ku bacemin da gani"
Nanfa wannan bulala ta bace.....
Cikin kankanin lokaci suka ja dan uwan nasu suka wuce dashi....
Itako ta wani rukkufa kawai saiga Fukaafukai suna bayyana a gadon bayan ta....
Nan ta ciccibi harun ta tashi sama dashi suka wuce....zuwa gurin da Harun ya tsinci kansa bayan ya farka daga suman
β¬
Nanfa ta karashe tunan nin nata....sannan ta mike tsaye tace da Harun...
"Take care......ni zan wuce"
Dajin haka Harun ya soma nazarin yadda zayyi ya hanata tafiyar.. Bayan ta juya baya alamar zata wuce...
Wasu yan dakiku ya dibe yana kikkiro plan....
Bayan Nainah tajuya ta kuma soma takawa sai yayi ihu sannan ya soma d'ingishi....alamar bazai iyya takawa ba
Nainah ko dukda tasan karya yake yi...amma saita koma ta dan dafeshi....suka soma tafiyar tare. .
Nanfa sukayi ta fira...harma Harun ya sanar da ita karatun da yake hade kuma da raukon layin waya ta "phone number".....
Amma saita ce dashii ...........
"Gobe a irin wannan lokacin zan kasance a labary domin zanyi karatu...
Idan kana da bukatar ganina zaka same ni a gurin......"
Hakafa Harun ya koma gida da murmushi a fuskar sa....
Danko yasami abinda ya jima yana muradi.. wato Nainah
Zuwansa gidan ya kwankwasa kofa....still Ramlah na zaune tana wannan kallon....
Bayan an kwankwasa kofar taga Harun dake dakin ya kashe fitular cikin dakinsa.....nanfa ta tashi tana mai Magana cikin makogoro alamar an takura Mata....
Buge kofar keda wuya ta tarar da Harun a tsaye....
Buga ihu tayi........nanfa ta sume...harun ko ya dauke ta izuwa cikin daki
Inda iyyayen nasu suka fito sukayi mata addu'a takoma bacci....
*WASHE GARI* da sassafe Harun ya farka inda kuma ya shirya ya wuce ...school
Zuwansa school din ya tarar ana marna wata sanarwa wacce ya karasa gurin ya karanta kamar haka.....
*CIKIN KWANAKIN NAN AKA NAIMI WASU MUTANE UKU AKA RASA INDA SUKA SHIGA.......*
*SANNAN AN GAGARA GANEWA SHIN SACESU AKAYI KO KUWA...*
*MUTANEN SUN HADA DA BABBAN LIKITA NA WANNAN MAKARANTA DA KUMA MAI TAYASA AIKI WATO NURSE SANNAN KUMA DAN SANDA DAYA.....WANDA YAKE AIKINSA A WAJEN MAKARANTAR AMMA HARYANZU ANAKAN BINCIKE SANNAN DUK WANDA YAGA WANI ABINDA BAI YADDA DA ITABA KO HANKALINSA BA KWANTA DA ABINBA YA HANZARTA KAWO MANA BAYANI*
"Oh abin mamaki....."
Harun ne ya furta hakan yayinda ya juyo ko sai yayi arba da safras da kuma Rihana...
Kamar kullum yauma sai dayayi tama safras wasa da hankali....
Hakama lokacin daukar lecture ya hanasu sakata.....
*BAYAN KWANAKI UKU*
cikin kwanaki ukun nan yansanda suka zurfafa bincike akan batan...likitocin.
Sannan kuma sun soma bin diddigin CC Camara ...
Inda sukayi arba da wata Video mai abin mamaki wacce ta kasance ranar da acid ta kona safras CC camara ta gagara daukar hoton safras din a lokacin da suka kaisa domin ai masa magani ......sannan kuma su da kansu sun kasa gane waye wannan wanda ya kone a ranar domin sun manta komi.....
CC cemara ta gagara daukar safras...saidai gani suke anata hajijiya da likitocin asama....daga karce cemara ta daina daukar su baki daya.....
Wani Dan sandane ke wannan binciken kadai sunansa Faruq.....sannan ya kasance dogo mai faffadar kirji....
Bangaren gidansu Raihana cikin kawanaki ukun yayan nata ya soma attending gasar........sannan kuma still yana koya mata girki kowace safiya.....
*Harun* ko cikin gidan nasu aka naimi malamai suka soma yiwa Ramlah Rukiya........
Domin samun kubuta daga shafar aljanu.....
*Safras* kamar kullum bayan 5:55 tayi saiya ruga izuwa damin sa haka wannan farar haske ta sake bayyana bayan ya rife kofar.....
Haka al'amarinsa da Raihana......kullum suna tare sannan bayan ta koma gida tana yawan kirasa a waya......amma kuma bai taba ambatar yana santa ba,sannan bai tabayin Mata wani alamaba......But Raihana na tsammanin so daga gare sa.
*HARUN* DA *NAINAH* kullum basu da lokacin haduwa sai 10:00pm shep suke hadduwa sannan kuma soyayya ta ginu tsakanin su.....Mai kaifin gaske
Dukdadai shimadin bai sanar mata ba amma suna mu'amala kamar masoya....
Like always...Yau Monday sannan kuma5:50pm inda safras ya takawa Raihana....ya sakata a adaidaita....cewa tayi dashi...
"Zan sanar dakai bayan na kai gida....."
"Okay bye"haka ya bata ansa....wucewar ta keda wuya yajuya ya ruga aguje izuwa dakin nasa.....
Sako karfar dayayi cikin dakin sai ya tarar da wani tsaye cikin dakin fuskarsa kuma lullube take da kellen sihiri....wanda tasa ya gagara gane waye...... dukda cewar dakin a kulle ya yini....amma sai ya tarar dashi a ciki.
Da ganin haka ya Daaki kasa da tafin kafar sa inda yayi ta jikin bango da niyar nitsewa ciki....harma ya soma nitsewa cikin bangon amma sai wannan mutumin ya miko hannu sulululu hannun sai dad'a tsawo yake......
Saidafa ya jawo safras ya kawosa tsakiyar dakin ya hadasa da kasa....
Cikin gajiyawa Safras din ya mike sannan bayan ya mike ya hade tafukan hannayen sa......gurin daya....sannan ya lumshe idanu...nanfa mutumin ya aika sakon tsafi kamar kiftawar ido....safras ya koma gefe guda hade da lullube kansa cikin wata farar kelle....nanfa wannan farar hasken mai dauke ganin mutum ta bayyana a jikin nasa a yayin da agogo ya lasa kan 6pm shep...shiko ya kasance lulluben yake da kellen....
Bushewa safras yayi da dariya bayan hasken ta yaye sannan yace.....
"I'm back"
π²π²π²π²π²
*KUYI HAKURI DA LATE UPDATE DAN ALLAH AM SORRY.....*