6
by @sadikgg26
Sadik Abubakar
Lafazi Writers
Wattpad @sadikgg
*SAHURA 06*
Kimanin sati daya ke nan cir! Umma ba ta yi wa Faruk magana, koma ya gaishe ta ba ta amsawa, fishi take da shi sosai. To abin tun yana jurewa har ya fara damun sa, ya zaci bacin rai ne na kwana biyu idan ta huce ta sauko shike nan! Amma abin ya ci tura. Don haka ran nan sai ya shirya ya tafi cikin gari unguwar Galadanci, gidan kakarsa wato wajen mahaifiyar Umman, ana kiranta Baba Abu.
Sallama ya yi tana zaune a tsakar gida tana sauraren rediyo, cikin fara'a ta amsa, "A a a ah, yau muna da babban bako! Maigidan sai yau ka tuna da ni, ai ni fishi nake da kai."
Faruk dariya ya rika yi yana cewa, "Haba amaryarta ai ba za a yi haka ba, ban manta da ke ba, babu mai raba mu da ke."
"Ya kuke ya Baban naku da sauran 'yan uwanka, da fatan duk kuna lafiya."
Ya amsa, "Lafiya lau wallahi."
Bayan sun gaisa ne yake sheda mata duk abin da yake faruwa a gidan nasu har da raunukan da aka yi wa Sahura da yadda Umma ba ta tausaya mata, kai har ma da gabar da take da shi, wacce ita ce babbar damuwarsa a halin yanzu.
Baba Abu ta nisa sannan ta ce, "Yanzu ita Saratun ce da wannan aikin? Wace amsa ta tanada da za ta fada wa Ubangiji idan ta tsaya gabanSa ranar gobe Kiyama? Lallai tana neman hallaka kanta a aikin banza. Shin Sahura kishiyarta ce ko me? Wannan ai sakarci ne. Ka je gidan In Sha Allahu jibi zan zo.
"To shike nan Baba Abu ni zan koma, ga wannan kudin ko ruwa kin saya." Ya mike mata ya fice, ya barta tana fada a zuciyarta, "Saratu ba ki kyauta ba ko kadan, don yaro ya nuna miki gaskiya sai ki tsane shi har ki daina masa magana, gaba da 'dan cikinki, wannan ai shashanci ne, Allah ya kai mu jibin."
To al'amarin Salim fa sai kara gaba yake, a halin da ake ciki ba ga shaye-shaye kadai ya tsaya ba, a yanzu kam har ya fara bibiyar matan banza. Wani cikin abokan shaye-shayen ana kiran sa Man, asalin sunan sa Mannir, shi. ne ya hada Salim da wata fitsararriyar yarinya bakatafiya mai suna Rabeca.
Tun a ranar farko da suka fara haduwa da Salim din a dakin abokin nashi, babu abin da Salim bai yi da ita ba in ban da saduwa. Ta sakar masa jikinta ya yi romancing din ta sosai. Ya tabe ta, ya shafe jikinta kaf hade da 'yan tsotse -tsotse. Da yake gogaggiya ce a harkar, ta fi shi kwarewa kallon shi kawai take kyar! Wani abin ma bai taba sani ba sai a ranar ta koya masa.
Ta yi farinciki da samun Salim, a zuciyarta take cewa, "Kai gaskiya na yi babban kamu wannan guy din za a samu dollars a hannunsa."
Tun yammaci suke a dakin ba su bukaci komai ba, domin babu abin da ba su nema ba kafin su shiga. Shi ma Man din da tasa yarinyar, Zubee shi ne sunan da take amsawa. Don haka wadannan yanmata su ne suka shiya musu abinci. Misalin karfe 11:45pm, Salim ya tuna ba a gida yake ba, kuma ya zarta lokacin da ya saba komawa gida. Bai wani tada hankalinsa ba, domin ya san Abban su baya gari, shi kadai yake shakka.
Ya mike ya fara shirin tafiya gida, Man ya ce, "My guy kawai ka kwanta a nan mana, ga babies nan."
Rebeca ce ta mike tsaye tare da rungumo shi ta baya tana cewa, "Haba dear yanzu tafiya za ka yi ka bar ni, I'm really need you at this moment, pls stay with me, I love you." Ta juyo da fuskarsa ta yi masa irin kiss din nan na tsotsar tongue.
Gabadaya jikin Salim ya yi sanyi, yarinyar ta kashe masa zuciya, wasi-wasi ya fara a zuciyarsa, shin ya tsaya su kwana tare ko kuma dai ya dawo gida abinsa? A karshe wata zuciyar ta ce masa ka dai koma gidan tunda wannan shi ne karon farko, idan ka yi garaje sai ka rasa damar yin yawon ma gabadaya.
Yayin da ya gamsu da wannan shawara da zuciyarsa ta ba shi, sai ya ce da babyn tasa, "Ki yi hakuri sweetyna! Tomorrow as early as possible zan zo. Yanzu idan na kwana a nan hankalin Mum zai tashi." Yana fadar haka ya saka rigarsa ya fice.
A ranar dai Salim bai dawo gida ba sai bayan karfe 12:00am na dare, yana shigowa ya raba ya shige dakinsa, Faruk da ke harabar gidan yana karatun Qurani kallon sa kawai ya yi bai ce masa komai ba. Sai ya tashi ya rufe gate din gidan ya komo ya ci gaba da karatunsa. Daga bisani kuma ya tashi ya fara sallar nafilar dare, da ma ya saba haka kullun idan ya gama karatun Qurani sai ya rufe gate, bayan ya yi sallolin nafila kuma sai ya shige dakinsa.
Shigar Salim daki keda wuya sai ya zaro wata kwalbar magani mai kama da maganin tari irin syrup din nan, ya balle murfin ya daga ya kai bakinsa ya kwankwadi kusan rabin kwalbar, ya mayar da murfin ya rufe. Nan ya cire rigarsa da wandonsa ya bar singlet da short nicker, sai ya fada gado, nan take barci ya yi awon gaba da shi.
Washegari da safe kowa ya tashi lokacin breakfast ya yi, Umma da kanta ta hada abincin breakfast din ta shirya komai, sai ta ce, "Wai ina Salim ne, har yanzu bai tashi ba ne? Hafsat je ki tashe shi haka."
Dakinsa Hafsat ta nufa, ta kwankwasa kofa shiru bai amsa ba, ta sake kwankwasawa shiru dai ta ji, sai ta kira sunansa, "Yaya Salim ka tashi."
Shirun dai ta sake ji, komowa ta yi, "Umma ya ki tashi" Ta fada cikin shagwaba.
Umma da kanta ta nufi dakin, ita ma kwankwasawar ta fara yi bai amsa ba bare ya bude. Tura kofar ta yi, kofa ta bude da yake ya manta bai kulle ba. Tana shiga ta iske shi warwas a kan gado sai sharar barcinsa yake kamar wanda bai fi awa daya da kwanciya ba. Kiran sunansa ta yi,"Salim Salim tashi mana gari ya waye." Amma inaa ko motsi bai yi ba.