SAHURA 💖

11

by @sadikgg26

Sadik Abubakar

Lafazi Writers

Wattpad @sadikgg

*SAHURA 11*

Aka kammala taro lafiya kowa yana fara'a da farinciki. Abin mamaki daya tak! Da ya tsaye wa kowa a ransa daga kan mahalarta taron har malamai da shugaban makarantar shi ne, tunda aka bude makarantar ake gudanar da irin wannan bikin karramawa da ba da kyaututtuka, ba a taba samun dalibi walau a maza ko a cikin mata da ya taba samun kyauta a bangarori har uku lokaci guda irin Sahura. Wannan dalili yasa mamallakin makarantar, Alhaji Isah ya umarci Principal da ya dakatar da su, kada su tafi yana son ganawa da su. Haka kuwa aka yi Principal ya fada wa Faruk su dan jira kadan a watse kana su tafi.

   

Da aka dan ragu sai Principal ya kira Faruk da su Sahura ofis dinsa. Alhaji Isah ne a ciki wanda ya samu rakiyar mai dakinsa Hajiya Fatima, da babban dansa ana kiran sa Is'haq sai kuma shugaban P.T.A na makarantar duk suna cikin ofis din.

   

Faruk ya shiga ya zauna kan kujera yayin da Sahura da Hafsat suka durkusa kan gwiwowinsu. Faruk ya gaisa da mutanen da ke ofis din, sannan Principal ya gabatar da shi ga mamallakin makarantar kamar haka, "Yallabai wannan shivne Faruk dan gidan Alhaji Mustapha, shi ke wakiltar wannan dalibar, kazalika shike halartar duk wani taro da ake bukatar iyayen yaran, sakamakon mahaifin nasu ba ya zama a gari sosai."

   

Alhaji Isah ya kalli Faruk tare da cewa, "Ma Sha Allah, ya yi kyau. Abin da yasa na ce a kira mini kai shi ne, na yi matukar farinciki da ganin wannan daliba a wannan makaranta tawa. Hakika wannan yarinya ta samu cikakkiyar tarbiya da kyakyawar kulawar da yaro yake bukata a wajen iyayensa. Baya ga kyaututtukan da makaranta ta bai wa wannan yarinya, ni ma da kaina ya cancanci na ba da tawa kyautar domin karfafa mata gwiwa ta ci gaba da kokari tare da mayar da hankali a wajen karatu. Saboda haka na ba ta kyautar computer laptop, ranar litinin ka zo ka karba mata a wajen Principal. Allah ya yi miki albarka Allah ya kara basira."

   

Faruk ya yi masa godiya sosai, ita ma Sahura godiya ta yi masa, daga nan Principal ya sallame su suka nufo gida fuskokinsu cike da annuri da fara'a in ban da Hafsat da ta dan hade rai kadan. Bayan sun fita ne Principal yake fada wa Alhaji Isah labarin Sahura, ya yi matukar tausaya mata tare da yi wa iyayen nata addu'a da roka musu rahamar Allah Subhanahu Wata'lah!

   

A kan hanyarsu ta dawowa gida Faruk da Sahura wata chapter suka bude ta hira, fuskokinsu cike da walwala da annuri, murmushi kawai suke ta musaya a junansu, yayin da ita ma Hafsat ke ta murmushi amma fa ita nata na dole ne, domin cikin zuciyarta tamkar gidan burodi, kamar za ta fashe saboda tsananin zafin da take ji. Kamar ta fasa kuka don bakin ciki, kana kallon fuskar ta da kyau za ka fahimci akwai wani sako da yake son bayyana daga zuciyarta, amma ta hana shi bayyanar. Ba wani abu ba ne illa kishi da bakin ciki.

   

A zuciyarta kam yanzu babu wanda tafi jin haushi sama da yaya Faruk, duk shi ne silar faruwar wannan abin da yake neman tona mata asiri, da a ce bai yi shisshigin kai Sahura makarantar ba, da haka ma ba ta faru ba balle har a zo wannan matsayin. "Yaya Faruk ka cuce ni wallahi, ban yafe ba." Ta fada a zuciyarta.

   

Suna cikin tafiya, Faruk ya dubi Sahura da wani irin asirtaccen kallon mai dauke da wasu sakonni na musamman ya ce, "Ai ni ma ba za a bar ni a baya ba wajen ba uwa gwarzuwar shekara lambar yabo da kyaututtukan ba, ya kamata ni ma na shiga sahun masu ba da gudummawa ga dalibai masu hazaka da biyayya da girmamawa."

   

Sahura wacce har yanzu fuskarta ke cike da fara'a, wani siririn murmushi ta sake sakar masa sannan ta ce, "Yaya Faruk ke nan! Ina masu hazakar da biyayyar suke?"

"Ga ki nan kuwa." Faruk ya fada yana ta sakin murmushi, yayin da wani abu ya taso ya zo ya tokare wa Hafsat a kirji, yaki fitowa waje kuma ya ki komawa inda yake a cikin. Wani zuzzurfan tunanin ta afka, "Shin to me yaya Faruk yake nufi da haka? Me kuma zai ba wa Sahura? Kuma ita kadai ma ya ce zai ba wa? Wannan ai cin fuska ne, a gabana yake yabon Sahura ita kadai, ba ya tunanin nivce kanwarsa ciki daya, wannan wane irin wawa ne?"

   

Wannan tunani da Hafsat ta tafi ya dan yi nisa har su Sahura suka fahimci lallai hankalinta na wani wajen daban, ba ta san ina ma suke tafiya ba. "Lafiya kuwa Hafsat, me ke damun ki na ga kin yi shiru?" Tambayar da Sahura ta jefa mata ke nan yayin da ta dawo hayyacinta, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ba komai, barci ne yake son ya dauke ni."

Faruk ya karbe zancen da cewa, "To sarkin barci, ke ke nan barci, barci barci ba karewa, kila ma barcin kike a aji shi yasa ga shi nan kin zama 'yar rakiya."

   

Sahura dariya ta dan yi har sai da sauti ya fito sannan tabce, "Haba yaya Faruk! Ita ma fa tana da kokari sosai, kawai dai kavsan abin sa'a ne kuma komai rabo ne, idan rabonta yavzo sai kavga ita ma ta samu."

   

Hafsat rai ta hada sosai ta sha kunu, fuskar nan ta yi murtuk babu annuri kamar za ta fasa ihu. Maganar da Faruk ya fada mata ta yi mata zafi, ta taba mata zuciya sosai. Tsananin haushin sa take ji, da a ce za ta iya, da ta mayar masa da martanin bakar magana me zafi koda sau daya ne, watakila zuciyarta tavyi mata dan sanyi, amma tana shakkar sa, don haka ta daure ta cije tare da shan alwashin sai ta fada wa Umma duk abin da suka yi mata, "Wannan ai cin mutunci ne, sai zolaya ta kuke." Ta fada a zuciyarta.

Suna cikin tafiya Faruk yana tuki sannu a hankali, ba wani sauri yake ba, dududu malejin motar bai wuce 30-40, ba ya so su iso gida da wuri domin yana jin dadin hirar da suke da Sahura, yanayin ya yi masa dadi sosai nishadi kawai yake ji da farinciki a ransa. Sun iso daidai shatale-talen Dangi kan titin Zaria road, ya dauke kan motar ya nufi yamma titin Gidan Zoo, bai zame ko ina ba sai Ado Bayero Mall, Shoprite.