15
by @sadikgg26
Sadik Abubakar
Lafazi Writers
Wattpad @sadikgg
*SAHURA 15*
Sahura da Hafsat na can ɗakinsu, tana ƙara koya wa Hafsat karatun hadisi na Islamiyyarsu domin malamin nasu zai karɓi hadda, ga shi kuma ba ta iya ba. Su ma dai ba su ga giccin Salim ba, suna cikin karatun Umma ta iske su, “Ashe karatu kuke? Ai na zaci kuna nan kuna latsa computer.”
Sahura ta yi dariya ta ce, “A'a, ai mun ji faɗan da yaya Faruk ya yi mana. Wani abin za a yi ne?”
Umma tace, “Ki je ki gyara mini ɗaki ki yi mopping ko'ina da ina, kuma ki kunna mini turaren hayaƙin nan.”
Sahura ta amsa, “To Umma.” Nan ta bar Hafsat ta nufi ɗakin Umman, yayin da ita kuma ta koma kitchen ta ci gaba da aikin girkin.
Sahura ta kama aiki dandanan ta gyare ɗakin ya yi kyau sosai, tacyi mopping ko'ina, kyalli kawai kayan ɗakin suke, ga wani daddaɗan ƙamshin turaren hayaƙi ɗan Maiduguri yana tashi wanda har falo ana jiyo ƙamshinsa, kai ka ce a falon aka kunna turaren. Tana gamawa ta faɗo cikin falon shi ma ta gyare shi. Tana kammalawa toilet ta nufa shi ma ta wanke shi tas!
Sahura ke nan! Agogo sarkin aiki, yarinya mai son aiki ba ta gajiya sannan ba ta da san jiki. In dai ta san wannan aikin nata ne, kai koma ba nata ba ne muddin za ta iya shi, to ba ta jira, yanzu ne za ta kama ba bata lokaci kuma ba ha'inci, ta gama cikin farinciki da walwala. Sahura 'yar albarka, Allah ya azurta mu da 'ya'ya masu irin halin Sahura.
Da yake yamma ta yi sosai, tana gama wannan aikace-aikacen, sai ta shiga toilet ta yi wanka ta yi kwalliya sosai, wata shadda light blue ta saka ɗinkin doguwar riga ta sha aiki sosai. Kwalliyar ta yi mata kyau sosai. Ashe da ma Sahura kyakkyawar yarinya ce haka? Kawai rashin kwanciyar hankali ne da ta shiga a baya ya sa ba ma a ganin kyanta, amma ga shi yanzu ta murje ta yi kyau, haskenta na asali ya fara fitowa.
Tana gama kwalliyar ta juyo ga Hafsat wacce take ta latsa computer ta ce, “Wai ke Hafsat ba za ki tashi ba ne, ko sallah fa ma ba ki yi ba, ya kamata ki haƙura da game ɗin nan haka ki je kivyi sallah ki yi wanka mana kafin Magriba ta yi, kin san wankan Magriba ba kyau fa.”
Hafsat ta kashe laptop ɗin, suka fito tare, Hafsat ta yi toilet yayin da Sahura ta nufo falo riƙe da littafin azkar na *HISNUL MUSLIM,* kan kujera ta zauna ta fara dubawa.
Tana nan zaune tana karanta azkar din da ake yi da yammaci, kiran Umma ne daga kitchen ya katse mata karatun, “Sahura, Sahura.”
Ta amsa “Na'am!” tare da miƙewa ta nufi kitchen din. “Umma gani.”
Umma ta ce, “Kin gama aikin da na saki?” “E na gama.”
“To ɗauki abincin nan ki shirya su a kan dining table.”
Ta kwashe komai kamar yadda Umma ta umarce ta, ta shirya su tsaf a kan table ɗin, ta komo falo ta ci gaba da karatunta, yayin da Umma kuma ta nufi dakinta daidai lokacin da Hafsat take fitowa daga toilet, Umman ma fitowa ta yi ta shiga wankan.
Sahura na zaune, Faruk ya shigo ya yi sallama, ta amsa tare da cewa, “Sannu da zuwa yaya Faruk, ya kasuwa an dawo lafiya?”
Ya amsa, “Yauwa ƙanwata, kasuwa AlhamduLillahi.”
Ya miƙa mata wata leda, ta karɓa, ya ce, “Ke da sister ɗinki Hafsat.”
Kilishin tsokar ƙaramar dabba ne, mai shegen daɗi ɗauri biyu a cikin ledar. Ya kuma miƙa mata wata ledar daban ya ce, “Wannan kuma na Umma ne ajiye mata.”
Ta karɓa tare da cewa, “Oh! yaya Faruk kai dai ba ka gajiya da kashe kuɗi wallahi, to mun gode, Allah ya6 saka da alkairi.”
Faruk kallonta kawai yake yana sakin murmushi, shi ma dai ya lura sannu a hankali kyan Sahura sai ƙara fitowa yake. Tana burge shi sosai musamman kyawawan ɗabi'unta.
Nan ya wuce ɗakinsa ya canjo kaya, jallabiya golden colour ya sako ya komo falon daidai lokacin Umma da Hafsat sun gama shiryawa su ma suna falon. Faruk ya gai da Umma, ta amsa masa gaisuwar cikin fara'a har da tambayar sa yaya kasuwa. Sahura ta miƙa wa Umma ledar kilishin da Faruk ya ba ta ta aje mata, sannan ta buɗe tasu ledar ta miƙa wa Hafsat ɗauri ɗaya ita ma ta buɗe suka fara ci, sai santi suke yi.
Sahura ta ce, “Yaya Faruk na ga kai ba ka ci, ina naka?”
Ya ce, “Ni ai na ci nawa a kasuwa.”
Ta miƙa masa nata ta ce, “ka ci wannan, ni ya ishe ni.”
Ya ƙi karɓa, ya ɓata rai, tare da cewa, “Ko dai kin rena ne, ya yi miki kaɗan ko?”
Ta ce, “Koɗaya, to ai na ga ba ka ci, ta yaya zamu riƙa ci mu kaɗai kai kuma kana kallon mu, kawai ka karɓa.”
Faruk yasa hannu ya ɗauki wani ɗan ƙanƙane ya ce, “To ga shi na ci shike nan?”
Hafsat sai faman tauna kawai take kamar akuya ta samu harawa.😂
Ita kuwa Umma mamakin wannan kinibibi na Sahura take yi, kallon ta take kawai, a zuciyarta tana faɗin "Dubi yarinya ƴar ƙarama da ita sai iyayi, ta wani damu ya ci ya ci sai ka ce irin uwa da ɗanta ɗin nan".
Haka dai suka yi ta hirarsu har lokacin sallar Magriba, Faruk ya miƙe ya yi alwala ya fice Masallaci, Sahura ta tashi ta ɗauro alwala haka Umma ma, suka gabatar da sallar, ita kuwa Hafsat zamanta ta yi kasancewar tana cikin kwanakin hutu yin sallah.
To Salim kuwa fitarsa keda wuya daga gidan, yana barin layin nasu, ya tari mai ɗan sahu drop ko ciniki ba su yi ba, ya ce, “Ka kai ni Yahuza Suya ko na ina ne.”
Ba da ɓata lokaci ba mai ɗan sahu ya ja mashin suka tafi, ba su yi burki ko'ina ba sai titin State Road, babban reshen Yahuza Suya. Salim ya ce da me ɗan sahu,
“Ka jira ni kaɗan in sayo sai ka kai ni gida, ba jimawa zan yi ba.”
“Babu matsala.” Mai ɗan sahu ya faɗa tare da kashe mashin ɗin.
Salim ya nufi cikin Yahuza Suya ya sayo banƙararrun daƙwalen kaji guda biyu, ya fito ya shiga ɗan sahu. Sun fara tafiya ke nan ya ce da mai ɗan sahu, “Yanzu mu je Alu Avenue zan sayi madarar L & Z, sai ka wuce da ni Badawa layout.” Me ɗan sahu ya girgiza kai tare da cewa, “To ba matsala.”
Nan da nan sai ga su a Alu Avenue, Salim ya shiga ya sayo yaghout ɗin L & Z babbar jarka guda biyu, ya fito, mai ɗan sahu ya ja sai Badawa layout. Suna isowa daidai ƙofar gidan abokinsa Man, Salim ya dan taɓa kafaɗar mai ɗan sahu alamar ya isa, an zo wajen da zai sauka, ya fito ya zaro dubu biyu ya miƙawa mai ɗan sahu.
Zaro idanu 👀 ya yi yana mamakin Salim, naira dubu biyu zafafa haka, a tafiyar da ba ta wuce mintuna talatin ba? Shi a tunaninsa bai wuce ya ba shi naira ɗari biyar ba (N500) a ya kyautata masa ke nan. Ya yi wa Salim godiya ya ja mashin ɗinsa ya yi gaba, yayin da Salim kuma ya shige gida.
Unguwar Badawa layout unguwa ce ta masu masu hannu da shuni da kuma ƙabilu daban-daban, babu wanda ya damu da me wani yake aikatawa, kowa sha'anin gabansa yake, ba kasafai ma za ka ga mutane a waje ba balle ma har su kafa majalisar cin naman junansu.
Wannan gida da Salim ya shiga suke sheƙe ayarsu mallakar mahaifiyar Man ne. Dayake ba a nan gida Nigeria take zaune ba, tana can ƙasar Saudiya, Man ne kaɗai a cikin gidan, kasancewar shi kaɗai ta haifa. Babu tsiyar da Man yake sai kawo matan banza tare da abokanansa suna aikata abin da suka yi niyya.
Uwar ita ta ɗaure masa gindi ta hanyar turo masa da kuɗi ko nawa yake buƙata kuma a kowanne lokaci, baya aikin fari bare na baƙi. Man ɗan gata ne sosai, mummyn tasa tana bala'in son sa ba ta son abin da zai taɓa masa zuciya, tun yana ƙarami ta ɗora sa a kan wannan sangartaccen tafarki mai kai mutum ga kogin nadama. Wannan ne dalilin da yasa Man ya sangarce ya zama tantirin ɗan duniya.
Mahaifinsa kuwa ya rasu ne tun lokacin Man bai wuce shekara ɗaya ba da haihuwa, daga nan kuma mummyn tasa ba ta sake yin wani auren ba. Bayan ya girma ya kammala Secondary School ya wuce School of Management Studies, kafin ya gama mummyn ta tafi Saudiya har kawo Yanzu. Sai dai kawai waya da suke yi da ita kusan kullum.