FITO NA FITO AKAN SOYAYYA TA

Page 4

by @rahamanalele

*Fito na fito*

*A KAN SOYAYYA TA*

Labari da tsarawa RAHAMA MUH'MD RUFA'I NALELE

Wattpad @rahamanalele

*Haske writer's association*


Shafi na hud'u 04


Ban yarda wani ko wata ya d'ora min labari na akan shafinsa ba, ban amince ba, duk Wanda yamin hakan ya d'ora haramun tunda ba amincewa ta.


Sannan makaranta na, na baku dama zaku iya tura labarin nan duk Inda kukaga dama, Ku Kan na yarje muku Dan nasan karanwata ne kawai naku bazaku Dora min Shi dan kasuwanci ba, babu hakan a tsarina.







HaYdaR ko lokacin dame gadi ya bud'e musu get din gidan nasu bayan direba yayi parking zaro wayarsa yayi a ajjihu ya Kira numbar Dad dinsa...


Lokacin Dadyn Yana dining Yana cin abinci, Yana ganin Kiran ya dauka da hello, nan HaYdaR ya sauke ajiyar ZUCIYA cikin matuqar kaunar Dadyn nasa yace "Bazata...

Cikin mamaki Dadyn yace "my HaYdaR bazata kuma, sannan da numbarmu tanan gida Naga ka kira ni fah, yace "Yes Dad, idan Kana gida ina san ka leqo haraba Inasan Ka fara ganina kafin Momy Usman & ReeYAH..


Tashi kawai Dadyn nasa yayi cikin matuqar farin ciki yayo harabar gidan Laila nacemai "Alhaji dawa kake waya, Amma ko kusa bai kulata ba...


Saurin fittowa HaYdaR yayi daga motar dai-dai lokacin kuma Dadyn nasa ya fitto, nan yaje da gudu ya rungumarsa Yana cewa cewa "I miss u Dady, nayi kewanku dukka, cikin murna da farin ciki Dadyn nasa yace, "qewa ta qare daga yau my HaYdaR, nayi murna nayi farin ciki da zuwanka D'ana..

"Nagode sosai Dady..

Nan Dadyn yajasa suka Shiga ciki..

Laila na ganin HaYdaR gabanta ya tsinke ya fad'i, ta kallesa a furgice, nan ta rikice, Tatashi tana qaremai kallo, Suko zuba Mata Ido sukayi, murya tsarke tace HaYdaR wannan bazata haka, cikin nutsuwa ya qarasa gareta, ya durkusa yace nayi missing dinki Momy, yau ga d'anki ya dawo gareki, kullum kina fad'in Baki San mu dinga gaisawa saboda bakyajin dad'i tunda naqi dawowa, wannan yasa nasaka Dadyn NajEEB agaba kan lalle ina San nadawo gareku a cikin satin nan, gashi kuma Allah ya yarda.


Cikin murmushi tace nayi murna na kumayi farin ciki da hakan, Allah yay maka albarka...

Yace "Amiin.


Nan suka zauna Akan kujera, Dadynsa ya kama hannunsa, yace "HaYdaR damuta ta qare tunda Allah ya dawo min dakai, gaskiya nayi murna sosai da hakan.. Cikin murna yace, "ina Usman ne da ReeYAH ban gansu ba, Laila tace "ReeYAH tana ciki can wajen shaqatawa tana karatu, Usman kuma Ya fitta da alama Yana can wajen abokinsa Anas, yace "Masha Allah bara naje Naga ReeYAH tukunna, kullum batunta brother kaqi dawowa, Dady yace "ok kafin Ku gama ganin juna bara yanzu a gyara maka shashin naka...

Kan yayi magana saiga Me bama fulayoyi ruwa yazo cikin girmamawa yace da Dady, "Yallab'ai ga wasu sun kawo wasu kaya wai na HaYdaR ne..

Nan HaYdaR din yace, "eh Dady kayayyaki ne na tsarabarku, na turosu tun jiya, dama sunce min iyanzu kayan zasuzo gida, Ashe ni zan rigasu zuwa..


Dady yace "Ok ashugo Mai dasu shashinsa yanzu maza..

"Toh me bama fulayoyin ruwa yace Mai cikin girmamawa..

Yayin da HaYdaR yayi wajen shaqatawar gidan, anan ko yaga ReeYAH cikin Shigar qananun Kaya, Riga da Wando, rigar tazo Mata har gwiwa, wandan ko har qasa yakai Mata, ta daure Kanta da wani gyale tana karatun novel, gaskiya ne yarinyar tana kyau, ba da wacce ya had'ata sai SaffiYYA suna Dan kama ta Ido, Amma sanyin kyau SafiYAH tafitta, Amma zubin halittarsu kusan daya ne, gaskiya yarinyar tayimai mai kyau sosai, nan yaje bayanta a hankali ya zare littafin da take karantawar me suna RAYUWA TA na RAHMA MUH'MD RUFA'I NALELE...

Aiko girgiza Kai tayi, tace kaga Usman Bana so kaban littafina, wai me yasa kake min haka, badama Ka ganni ina karatu sai kawani zo Kana dauke min littafin, idan na tashi zan hukuntaka..


Shuru taji ammata, sai taja numfashi, daci gaba da cewa, qamshin turaran naka nayau yayi dad'i sosai, gayamin me tunan turaran.... Ta fad'i hakan tana me juyowa, aiko nan sukayi Ido hudu, gabansu ya fad'i, tayi saurin tashi daga Kan kwantacciyar kujerar, hannunta na rawa tahau nunasa cikin matuqar farin ciki, zatayi magana ya riga ta da cewa, "Yau Big brothern ki HaYdaR ne ya zare Miki littafin, dan haka sai'a hukuntanin.


  Cikin murna da farin ciki tace, "Wayyo Allahna brother, K'anwa bazata iya hukunta Babban Yayanta ba, kamin afuwa nayi badaidai ba, Dan Allah Brother ka yafemin Kar kayi fushi dani.


Yace "wane ni nayi fushi da Y'ar Auta, yanzu gaya min kinyi farin ciki da ganina..

D'an b'ata fuska tayi da cewa, "nayi farin ciki kad'an haka, saboda naci buri Kan cewa duk ran da zaka dawo nizan gyara maka part dinka, zan shirya maka abin da zakaci, gashi yanzu kamin zuwan bazata, yace "sorry nayi lefi bazan qara ba, sannan zaki iya had'a min lemun kwakwa ina so sosai, idan nasha zanyi farin ciki sosai da hakan, tace "Alhamdulillah, ina tabbatar maka da cewa kafin kayi sallah kayi wanka zan had'a maka, zaka tarar dashi anan gefe wajen abincin ka Yana jiranka, yace "shiko zan Fara sha, tace "wallahi Babban Yaya nayi farin ciki da zuwanka, yace "Nima nayi farin ciki da ganinki, ki kira min Usman awaya kice yadawo gida na gansa naji dad'i, tace "tom brother Insha Allah yanzu kuwa.


Nan yayi shashinsa itako farin ciki ya cika zuciyarsa, gaskiya tana mutuqar San Yayan nasu HaYdaR..

Nan tayi ciki da sauri zuwa kitchen dan aiwatar da lemun kwakwan nasa..


Shiko part din nasa yayi, yaga wasu ma'aikatan gidan biyu maza masu yima Usman gyara suna mai gyaran, nan suka zube suka gaishesa ya amsa cikin kulawa Kana yayi badroom dinsa, nan sun gama gyarasa tsaf har toilet sun wanke.. hakan yasa ya fad'a gadonsa da bismillah Yana godema Allah daya had'asa rayuwa da wannan family, can ya fad'a tunanin RaHinAT dinsa, tunda yasa kafa yabar Nigeria bai rabu da tunanin yarinyar ba, Yana Santa Yana Jin tausayin Kansu, kullum addu'a yake Mata akan Allah ya dorata akan sababbin iyayen nata su sota su qaunaceta kamar yanda yayi dacen samun su Alhaji Ahmad da Laila matsayin mahaifansa.


"Tabbas tunda har nakai wannan matsayin ban rabu da tunaninki da qaunarki ba HEENAT tabbas akwai wani Abu tsakanina dake, nakasa mantawa dake, Shin soyayyar Yaya da qanwa nake Miki Koko soyayyar Aure?... tabbas saina ganki zan tantance hakan, YA RABBU YA RABBU YA RABBU YA RABBU YA RABBU, na rok'eka daka sadani da ita cikin qanqanin lokaci... Ya fad'i hakan da tofa addu'ar tasa a tafukan hannayensa da shafawa, tabbas duk me neman wani Abu agun Allah ya fara kiransa da wannan suna nasa sau biyar Insha Allah zaiga biyan buqata..


Tashi yayi da niyar shiga toilet saiga Usman ya shigo room ya rungumesa ta baya Yana cewa welcome Yaya Sunna da dawowar bazata, nayi farin ciki da hakan sosai.

Nan HaYdaR ya juyo da qara rungumarsa cikin farin ciki shima yace "nayi murna da ganinka qanina, da fatan na sameku lafiya..

Yace Lau Lau muke Yaya, Yaya kaga yanda ka qara kyau kuwa, yace, "Kai zance kayi kyau qanina, yace "Yaya wane kyau ne anan, Ya Yaya NajEEB yake Yana lafiya ko, "Lau yake Usman yace na gaishe ka sosai, yace "masha Allah bara na barka Ka fitto naga zaka Shiga toilet ko, yace ”haka ne zan dan watsa ruwa ne nayi salla naga ana Kira yanzu, yace eh, Nima bara naje nayi mu had'u a daining naga Momy can ta shirya maka Shi. Yace "Masha Allah..

Nan Usman din ya fitta Shi kuma ya Shiga toilet din....



ReeYAH ta kira SafiYYA Amma bata d'aga ba, saita Kira RaHinAT data fitto tana shagon Saida giya, nan taga kiran ReeYAH ya shigo mata, nan ta dauka tana cewa "Yane, tace "Ke wannan Big brothern namu ya dawo fa, yau zaku gansa na muku bazata, cikin murna RaHinAT tace "Wow yaushe.. 

"Yanzu bai dad'e ba, ai har na kira SafiYYA bata dauka ba, nayi tunanin ma ko kuna tare ne, tace "qila ko wayan bata kusa da ita ne, Amma d'azu muka rabu ki qara kiranta, ni nan nazo siyan abu ne idan na siya zan biyo gidan naku dama ina San biyuwa dan zan karb'arma momyna sak'o, tace "tom ina jiranki.. "ok Saina iso.


Daga haka suka ajiye waya...



SafiYAH ko tana isa gidansu nan ta fad'a jikin momynta tana ce mata "Momy ki tayani murna, tace "dota me ya faru, tace "Momy yau nayi saurayi, sunansa HaYdaR, tace "Masha Allah, Amma my daughter bana gaya Miki cewa na Miki miji ba, cikin sauri ta raba Kanta da jikin mahaifiyar tata tare da waro ido tace, "Momy nasan wasa kikemin, shiyasa duk lokacin da kika gaya min bana damuwa, bakiga ko tambayarki sunansa bana yi ba, nikam ina San wannan Wanda nake baki labari yanzu, Wallahi kallo d'aya zaki mai kisan mundace da juna.

Tace "toh Allah ya zab'a miki abin dayafi alkairi SaffiYYAH, ki dage da neman zab'in Allah...

"Toh Momy nagode sosai, ina sanki momyna, tace Nima ina sanki yarinya ta..

Qanwar SafiYYAN dake Kwan kujera tana karatun Al'Qur'ani tace "Nifa Momy, tace "kema ina sanki Muhibba Allah ya rayaku gabaki dayanku bisa tarbiyar addinin muslinci.. Amin sukace da ita..


Khadija Kenan taja yaranta a jiki Sam basa b'oye Mata komai da yake wakana tsakaninsu, duk abin da zasuyi sai sun gaya mata, duk hakan ya faru ne sanadin jansu da tayi a jiki kamar qawayenta.





RaHinAT tasai giyarta kwalba d'aya tayo gidansu ReeYAH, bayan sun gaisa da Momyn su Laila nan ta gaya mata zata bata sak'o takaima momyn nasu, tace mata dama Shi tazo karb'i Amma bara taje gun ReeYAH idan tatashi tafiya zata karb'a tace mata toh.


Nan tabar room din Lailan ta fitto waje, can wajen bayan part din HaYdaR daidai window dinsa anan ta tsaya dama nan ne wajen Shanta...


Sai aka taki sa'a daidai lokacin HaYdaR ya idar da sallah ya tashi Kenan zai dauki wayarsa akan firiji kamar ance kalli window, nan ya hango RaHinAT ta zaro kwalbar giyar daga baqar Leda da zaro wata wata goran lacasera ta ajiye a gefe kana ta bude giyan nan sanda ta shinshina taja numfashin jin dad'i Kana ta zuba giyan a cikin goran lacakaseran sanda tayi rabi, Kana ta d'aga sauran zata kwankwad'e sai HaYdaR yayi saurin bod'e glass d'in windan, nan ta kalli windan a furgice, suka had'a Ido, gabansu ya bada wani dam, tsoro ya bayyana a fuskanta sosai, nan cikin basarwa tace, ”kai miye haka miye haka da zaka bude window da qarfi haka har kaban tsoro, cikin mamakinta, Yace "wacece ke, tace "hmmm "amm ina ruwanka, yace "mene, tace "cewa nayi ina ruwanka dani, Kan yayi wata magana ta qara d'aga sauran giyar data Saura a kwalbar giyan nan ta seta bakinta tahau kwankwad'ewa, cikin sauri yace "ke...! Kinyi hauka ne, giya kike sha fa, Sam bata kulasa ba, sanda ta shanye tsaf kana ta kallesa da cewa "Saura naji Ka gayama wani cewa Ka ganni ina Shan giya wallahi saika sani.. shuru yayi mata Yana kallo ta maida kwalbar gidan cikin baqar ledar Kana ta saka ta lacaseran itama a wata ledar daban, har zata tafi saita kallesa taci gaba da fad'in, na making fuskarka wallahi Karka kuskura Ka tona min asiri anan gidan idan har Ka tona min saina kulla maka shirrin da har Ka mutu bazaka tab'a mantawa dani ba, sannan ma wai Kai waye ne haka kamar balarabe amma kuma Kana Jin hausa, shuru yayi mata ransa ya gama b'aci da ita, ganin da tayi ransa kamar ya b'aci da ita hakan yasa tayi gaba abinta, dama karfin hali tayi wajen yimai magana haka, dan kwarjininsa sai maketa yakeyi haka kawai taji wani yar yar yana fitta daga jikinta, ita Sam bata tab'a Jin hakan akan wani d'a namiji ba, kai koma dai waye Shi ya had'u ya mata kyau sosai..


Dama idan ta zuba giyar a goran lacakaseran ta shanye sauran Yar da kwalbar take a kwatan can waje, Dan haka yanzu ma yarwan tayi a kwatan Kana tadawo gidan da Shiga d'akin ReeYAH tana jin Kanta Yana mata wani dim haka, nan ta kwanta akan gadan riya dama Yana mata haka Amma da zaran tayi baccin rabin awa nan yake saketa sai ta jita sakayau haka, dama abin da take so Kenan.




Daidai lokacin ko HaYdaR ya fitto zuwa daining jikinsa yayi sanyi haka, Amma Dan Kar Dadyn da ya tambayesa dalili nan ya sake, aiko lemun kwakwan ReeYA ya fara sha, anan Dadyn nasu yake tambayarsa jikin Dadynsu NajEEB duk da yasan ya samu sauqi sosai, Samun sauqin ne ma yasa HaYdaR din tawowa, banda haka baisan ranar dawowan HaYdaR din ba...


Dan abin daya faru shine, cikin shekaru qalilin HaYdaR ya gama karatunsa, Amma saidai Yana gamawa, hatsari ya afku da NajEEB, Wanda ya samu mugun rauni a kafafunsa biyu, badamar takawa, ganin hakan yasa Dadyn NajEEB din ya yanke jiki ya fad'i saboda ya tsorata da ganin NajEEB din cikin wannan hali, Sam ya dauka ma kutuwa yayi, cikin rashin sa'a kuwa ya samu shanyewar jiki, ba abin dake motsi a jikinsa sai hannunsa, maganarsa ma bata fitta sosai..

Shi kansa Dadyn HaYdaR din da yazo Shi da mahaifinsu dan dubasu sun Shiga tashin hankali akan hakan, Mahaifinsu yace dole su tattaro su dawo Nigeria ayi jiryarsu anan, nan Dadyn HaYdaR yace aa zasufi Samun kulawa anan din, tunda a babban asibiti suke, kawai dai dole Abar wanda zai Kula dasu na d'an wani lokaci aga yanda jikin nasu zai Kaya, cikin wani hali Dadyn NajEEB din yace yasan bamai Kula Mai da dukiyarsa wajen kasuwancinsa irin HaYdaR tunda kasuwancin ya karanta, akwai wani abokin kasuwancinsa anan bature zai dorasa Akan komai, ya zab'i HaYdaR ne Dan yasan shine zai riqemai amana.

Danka haka Allah D'an uwan nasa ya basa HaYdaR din na d'an wani lokaci, Jin hakan yasa Dadyn HaYdaR cewa ba damuwa Allah ya Basu lafiya...



Tabbas HaYdaR me rukwan amana ne, kuma Yana da albarkar hannu, tunda abokin kasuwancin Dadyn su NajEEB din ya dorasa Akan kasuwancin nasu shikenan komai ya qara cigaba.. akwalla HaYdaR da mahaifiyar NajEEB summa NajEEB da Dadyn NajEEB din jinya na kusan shekara shidda kafin su samu sauki su dawo kamar da Dan NajEEB shine ma ya fara Samun lafiya.

Koda Dadyn NajEEB din yaga sun dawo normal qin yarda yayi HaYdaR ya koma Nigeria haka ya dinga bawa Yayan nasa hakuri wai ya bar masa Shi ya qara Zama dashi nadan wani lokaci sai yadawo, Sarai Dadyn HaYdaR din ya gane k'anin nasa baya San rabuwa da HaYdaR dinne, hakan yasa yay masa kawaici ya zuba mai ido yaga ikwan Allah.


Wata Rana Dadyn nasa yakawo musu ziyara sai HaYdaR ya fahimci Dadyn nass Yana San ya dawo garesa, bayan tafiyar dadyn nasa hakan yasa HaYdaR din cikin wayo da dabara ya dinga maidama da NajEEB komai na kasuwancin mahaifin nasa, sanda komai ya koma hannun NajEEB sannan HaYdaR din ya nuna ma Dadyn NajEEB din Yana San zuwa duba Dadyn nasa Amma Insha Allah zai dawo, nan ma daqer Dadyn NajEEB din ya yarda, sai HaYdaR din yace Mai baya San Dadyn nasa yasan da zuwansa yafi San yamai zuwan bazata, yace mai Dan wannan ba damuwa, Yana sauka a jirgi akwai Wanda Saisa yazo ya dauke zuwa gidan nasu...


NajEEB Sam baiji dad'in tafiyar HaYdaR din ba, haka mahaifiyarsa ma tana qaunar HaYdaR din saboda rikwan amanarsa, da kuma yanda ya bama mijin nata da D'an nata NajEEB kulawa lokacin da suka fad'a wannan jinya..

Gashi bisa gaskiya da amana ya kula da tarbiyan yaranta matan wato qannan NajEEB din, ga wajen kasuwa arziqinsu qara Habb'aka yayi.

Gaskiya ne zasuyi kewarsa sosai...


Har a ZUCIYAR HaYdaR Bai dawo Nigeria Dan ya koma England wata Rana ba, yasa a ransa ya dawo kenan zai bama Dadynsa kulawarsa ko kad'an ne..


Wannan shine dalilin dadewar HaYdaR a England 





HaYdaR ya kalli Dadyn nasa yace "Jikin nasa da sauqi sosai Dady, yace "Masha Allah, amma da fatan Ka dawo kenan, yace "ai Dady na dawo kenan bani ba barinka, yace "nako gode sosai..

ReeYAH tace brother qawata RaHinAT tazo gaisheka fa, yace "oh kamar na hangota d'azu a haraba, itace tasa doguwar riga pink colour ko, tace "Yes itace, kullum zai ja musu aji nake ita da SaffiYYAH, Sam Basu cin sa'a lokacin da kake Kira ko muke video call su ganka, musamman SaffiYYAH har fushi tayi dani Kan ban tab'a nuna mata hotanka ba, ni Kam bansan ya zanyi ba, Dan ko na kiraka lokacin da muke tare Kai kuma ba dauka kike ba, wani ikwan sai mun rabu saika kira, gashi bana da hotunanka, abin kamar wasa kuma naki turawa a wayan Dady da wayan Momy, yace "Ai yanzu zasu ganni, Usman yace "Yanzu kam dole zamuyi hotuna Wanda zamu kakkafasu, Dady yace wannan shine abin daya dace..


Haka suka dinga hira cikin farin ciki da qaunar juna


Suna a haka ne abokan HaYdaR din wayanda yayi rayuwa dasu a skull can England din wayanda dama su y'an Nigerian ne nan suzazo mai sannu da dawowa..


Hakan yasa yabar daining din sukayi part dinsa, anan suka dinga hirar yaushe gamo.




ReeYA ko fad'awa tunanin HaYdaR din tayi, ita dai ba Wanda yake Burgeta kamarsa, bata tab'a ganin Namiji me tsafta kamarsa ba, ga kyau, ita Kam Yana Burgeta..



Dadyn nata yana lura da farin cikin dake tare da ita na ganin HaYdaR din, murmushi yayi da tashi yayi part dinsa Laila tabi bayansa..


Bayan sun kasance su biyun yake ce mata kina ganin HaYdaR da ReeYA Basu dace da juna wajen Zama ma'aurata ba, gaban Laila ya fad'i tace kwarai sun dace da juna, yace Allah ya tabbatar da alkairi.. amiin tace aciki ciki, can kuma tace mishi tana zuwa, tayi part dinta da sauri...


Tana zuwa ta rufo kofar badroom dinta da k'arfi, hawaye ya zubo Mata, bata San me yasa ayanzu zuwan HaYdaR tafi tsanarsa akan ReeYAH da Usman ba, lokacin da tasamu ciki tayi tunanin damuwarta ta Kau, Saidai abin daya faru cikin nata na cika wata bakwai ya fitta sakamakwan fad'uwa da tayi a toilet bayan sunje asibiti, anan aka gane gudan jinin nata ya mutu kuma da wiya ta qara Samun ciki, wannan bayanin daga bakin mijin nata ya fitto danshi ya dubata, ya kuma tabbatar mata da hakan.. bayan an cire cikin ta samu lafiya sai taji a duniya ba wayanda ta tsana irin ReeYAH da Usman, tasha alwashin bazasu tab'a gadar mahaifinsu a dukiya ba.. Saiya kasance bata ta HaYdaR a wannan lokacin, tunda tasan Shi dama bazai gaji dukiyar mijin nata ba..



To yanzu kuma mijin nata Yana San had'a Auran ReeYAH da HaYdaR din, dole zatayi wani abu akai, Sam bazata tab'a barin hakan ta faru ba, yanzu zata San nayi dole zata Nemo qawarta Hajara wacce tasan zata bata gudun mawa akan hakan, gwara tayi duk abin da zatayi yanzu tunda ita dai ba Haihuwan take ba..


Nan ta share hawayenta ta gyara Kanta kana ta koma d'akin mijin nata 






ReeYAH ko tana shigowa d'akin nata RaHinAT na farkawa, tace Mata "ankira sallah ni ina mamakin wannan bacci naki da kika tsiri yinsa yanzu, murmushi tayi dace mata, kisan Allah in banyi baccin rana a dakin nan naki ba bana jin dad'i..


Tace "lalle naga kan alama, kin dai yi missing ganin Big Brothern mu yau, Dan yanzu ya koma part dinsa Shi da abokansa, Amma idan kina so muje can ki gaishesa, tace "La karki damu zan gansa badai Yana gidan nan ba. Kinga bara naje gida kar momy ta nemeni, tace to SafiYYA ma ta kirani, wai Kanta na ciwo sai gobe zata zo, tace yauwa shikenan ma hade goben, nan ta dauki goran lacakaseran ta ReeYAH tace "bansan yaushe kika fara San Lacasera har haka ba, tace haka dai Nima na tsinci kaina dasanta, gashi keko Sam kin tsaneta, tace "Wallahi kuwa, Bana San Lacasera dan zaqinta yayi yawa.. tace tom nikam bara na tafi, zan karb'i sakon Momy a gun Momyn Ku, kawai sai mun had'u a online tace, to ki gaishe min da Momyn tace zata ji...