Page 13
*Fito na fito*
*A KAN SOYAYYA TA*
Labari da tsarawa RAHAMA MUH'MD RUFA'I NALELE
Wattpad @rahamanalele
*Haske writer's association*
Shafi na 13
Ban yarda wani ko wata ya d'ora min labari na akan shafinsa ba, ban amince ba, duk Wanda yamin hakan ya d'ora haramun tunda ba amincewa ta.
Sannan makaranta na, z na baku dama zaku iya tura labarin nan duk Inda kukaga dama, Ku Kan na yarje muku Dan nasan karanwata ne kawai naku bazaku Dora min Shi dan kasuwanci ba, babu hakan a tsarina.
Cikin sanyin jiki Seeyama tace "Nayi mamakin faruwar wannan lamari, banyi tunanin hakan a tsakaninku ba, why meyasa ReeYAH ta aikata haka, RaHinAT tace "ai manufar a bayyane take, gaskiya ne mutum ba abin yarda bane, Shamsiya tace "Ni kuma haka kawai naji shakku ina ganin ReeYAH bazata aikatama SafiYAH haka ba, ina ganin akwai dai abin daya faru.
Shuru RaHinAT d'in tayi,
SafiYYAH dai batave musu qala ba
Haka shamsiya tayi parking a kofar gidansu, nan ita da Seeyama suka fitto SafiYAH ta koma mazaunin direba su Shamsiya suka musu sallama nan SafiYYAN taja motar, basu wani dad'e ba suka iso kofar gidansu RaHinAT, bayan RaHinAT d'in ta ibi kayanta kallan SafiYAN tayi da cewa, "kiyi hakuri Qawata nayi miki mummunar fahimta Insha Allah hakan bazata qara faruwa, cikin rashin bama zancen nata muhimmanci taja motar ta tanace Mata "karki damu.. shuru RaHinAT tayi, sai zuwa can ta Shiga gidan nasu..
SafiYYAH direct gidansu tayi, bataga Momynsu a falo ba hakan ya bata damar shigewa room d'inta, Zama tayi agefan gadanta tana tuno abin daya faru, ba abin da take gani a idanta sai fuskar ReeYAH, ta tuna lokacin da abin ya faru hawaye na zuba a idanta taga itama ReeYAN hawayen ya zubo mata, duk wajen tafi kowa Shiga damuwa da halin da taganta a ciki, sannan lokacin da akayi maganar Camera taga lokacin da ReeYAN itama ta sauke a mjiyar zuciya kamar yanda ta sauke, tabbas akwai abin daya faru ta kasa yarda ReeYAH ce ta aikata mata hakan, maganar gaskiya kuma taji mamakin RaHinAT taji haushin yanda atun farko ta yarda zata iya yin sata..
Nan ta dinga tunani iri iri Amma tunanin nata ya tsaya ne a ila wa k'ala, a haka Momynsu ta shigo d'akin tasameta, tace da ita "Me yake faruwa naganki haka cikin tunani, tace "Yau Naga abin mamaki Momy, nan ta kashe komai ta gaya Mata, Momyn nasu tayi shuru, can ta dafa kafad'arta tace, "Kar wannan ya dameki yarinyar kirki, ina San ki kasance akowane lokaci kidinga yima kowa kyakkyawan zato, kisa a zuciyarki ReeYAH baza ta tab'a aikata miki haka ba, haka RaHinAT Shamsiya Seeyama Suma bazasu aikata miki hakan ba, Saboda haka ki miqama ALLAH komai ki roqesa ya warware komai cikin sauqi, wannan shi zai baki nutsuwa da kwanciyar hankali, Amma karki fara kuskuran zargin kowa acikinsu, Danni har a zuciyata bani da shakku akan ReeYAH, Naga lokacin sallah yayi gashi ana Kira maza ki tashi ki gabatar da sallar ki roqi ALLAH akan Lamarin zakiga ikwansa akan hakan, sannan akwai abinci akan dirning idan kina buqata, tace "toh momy.. daga hakan Momyn nata tabar d'akin ita kuma tayi toilet da niyar San gaisar da ALLAH...
Haka da HaYdaR ya dawo da ReeYAH gida kallansa tayi cikin sanyi da cewa "Brother kaina ciwo yake min, ya kalleta tabbas alama ta nuna bata jin daɗi, nan yasa mata filo a bayanta ta gingina da jikin kujera, ya bud'e box din maganinsu ya dauko maganin ciwan Kan da ruwa ya kawo mata, nan ta karb'a tasha, yace ko zakije room dinki ki d'an kwanta ne, tace yanzu "za'a Kira sallah Yaya, kawai kaje Yaya Karka damu idan nayi sallar saina kwanta.. yace yauwa tom ALLAH ya baki lafiya ki Kula da kanki kinji, to tace mai
Har ya kusa fitta tace "I luv u honey, juyowa yayi da sakar mata murmushi yace "luv u 2..
Daga haka ya ficce ita kuma tatashi tayi room d'inta, tana tunanin ina Laila tayi Dan daga dukkan alamu bata nan.
RaHinAT ma anan ta idar da salla Kenan Momynsu ta shigo da wani kayan Mata data had'a mata, tace mata duk yanda zatayi tayi qoqari ta shanye ayau, Dan na kwana uku ne, "toh tace Mata, tana fitta hawaye ya zubo Mata, Habiba ba mahaifiyarta bace Amma ta nuna Mata dukkan qauna kamar itace ta haifeta, Dan tunda take hannunta bata tab'a nuna mata bambanci tsakaninta da ummi ba, ita Kam dame zata sakama Wannan bayin ALLAHN, idan ta tuna cewa basu San tasan su ba iyayenta bane qaunarsu qara kamata yake, tana godema ALLAH daya bayyana Mata HaYdaR alokacin daya dace, tabbas data b'ata rayuwarta zasuji ciwon hakan mara misaltuwa..
HaYdaR gidansu SafiYYAH yayi, anan bayan ya gaida Momynta Kira masa SafiYYAN tayi da basu waje, kallanta yayi cikin nutsuwa yace "Ya kikaji aranki, kina ganin ReeYAH zata iya aikata miki hakan?
Tace "Wallahi Luv ko yanzu danayi sallah na roqi ALLAH akan Lamarin na samu tunani me kyau, kwata kwata naqi yarda ReeYAH zata aikata min hakan.
Yace "Gud, nima ban yarda ba, please Bana San ki kullaceta, ina san kici gaba da d'aukarta kamar yanda kuke da..
Tace "ba damuwa yanzu idan naci abinci ma zan kirata.
Yace "Dako kin faranta min, naji dad'in yanda kike da sauqin Kai haka.
Murmushi tasakar Mai shima ya mayar mata, kana yayi Mata sallama Dan Yana san komawa ya had'u da Dadynsu a office..
Aiko SafiYYAN tana idar da cin abincinta tahau kiran layin ReeYAN, lokacin bacci ya kama ReeYAN, amma ringing d'in wayar ya tasheta, sanda gabanta ya fad'i da taga SafiYYAH ce me Kiran nata, nan ta dauka tana cewa "Hello..
Tace "Karfa wannan abun ya dameki, nasan bazaki aikata min hakan ba, dole akwai abin daya faru, Dan haka Kar wani Abu ya dameki please.
Sauke ajiyar ZUCHIYA tayi sanda SafiYYAN taji, nan tace "wallahi SafiYYAH ko a mafarki banta tunanin cutar daku ba, haka bantab'a tunanin in had'a muku wani makirci ba, Dan ALLAH kiyarda dani wallahi ba nice na aikata miki hakan ba, tace "na yarda, kinga komai ya wucce karki damu da hakan..
Tace "nagode Y'ar uwata, kuma Qawata Allah ya barmu tare, tace "amiin ya ALLAH sai mun had'u a online, tace "ok bye.. "bye
Daga haka suka sauke wayar suna masu tunanin juna..
Koda dare da HaYdaR ya kasance da RaHinAT suna hira ta d'auko masa hirar nan yake tabbatar Mata bai yarda ReeYAH zata aikatama SafiYAH haka ba...
Cikin mamaki ta kallesa da cewa, "ikon ALLAH abin mamaki baya qarewa, Dan Allah meya baka qarfin gwiwar cewa ReeYAH bazata aikata hakan ba, ita Y'ar Adam ce fa, zata iya canjawa akowane lokaci, mutum ba abin yarda bane, yakan iya canjawa kamar hawainiya, nikam na yarda zata iya aikata hakan saboda ni bayan Kai ban yarda da kowa ba..
Kallanta yayi cikin nutsuwa can ya saki murmushi da cewa, "mubar wannan hirar Dan ba itace ta kawoni ba, soyayya itace ta kawoni...
Murmushin itama ta sakar Mai cikin rashin Jin dad'i tace " Baka da madadi acikin zuciyata Ya ALIYU Dan soyayyata takace, kuma ina fatan takama ta Zama mallakina ni d'aya..
Yace "zahiri ina jinki a raina fiye da kowa, Dan haka soyayyata takice dan sai kinyi sake wasu zasu kwace miki ita, tace "AI bani ba wannan Saken, yanzu dai bani labarin yanda kake San matar Auranka ta kasance wajen yima hidima..
Murmushi yayi da cewa, me yasa kike so ki sa'ni yanzu, tace "saboda ina so na Zama ta musamman awajenka ba iya yanzu kawai ba har abada nake fata..
Yace "hmmm ina San matata ta kasance me ibada, me ladabi da biyayya wacce zatabi umarnina sannan me gaskiya wacce zata tafiyar da rayuwarta bisa gaskiya da amana, me tsafta wacce take da San ado da kwalliya, uwa uba wacce ta iya girki Dan bana wasa da cikina, sauran kuma ya rage naki ki qirqira way'annan dai sune masu mahimmanci..
Dace "Insha Allah kuwa zanzo maka dasu, zakayi alfahari dani yace Allah yasa, daga nan cigaba sukayi da hirarsu, bayan Rabin awa ya dawo gida, lokacin tara ma batayi ba, hakan ya bashi damar yin hira da ReeYAH, wacce taqi yin bacci da wurri Dan tana San Bama Dadynta hakuri da tabbatar masa itafa bata aikata lefin komai ba, Amma koda ya dawo baibi ta kanta ba, wannan ya qara jefata cikin damuwa, Amma yanzu hirarsu da HaYdaR yasa ta nemi Rabin damuwar tata ta rasa....
Saidai har yau da ake gobe d'aurin Auran nasu Dadyn nata baya kulata, HaYdaR Baya Jin dad'in hakan, hakan yasa yau yaje supermarket d'in da abin ya faru, Yana parking d'in motarsa a harabar wajen yaga wannan Budurwa daya karb'i numbarta ranar, wacce yayi ma layin nata Kiran duniya Amma yaqi Shiga..
Nan ya fitto daga cikin motar tasa ya nufi wajensu, Dan tare suke ita da qawarta..
Yace "haba mana Y'an Mata, nayi kama da mugu ko mayaudari ne da aka ban jabon number, kallansa take cikin Jin dad'in ganinsa tace "Kai haba Kar kace haka mana, ko kusa baka kama dasu ba, kawai an samu wani akasi ne, wayar tawa ce tasamu matsala tun ranar har yau tana wajen me gyara Amma ya Kiran d'azu wai ta gyaru, murmushi yayi da fad'in, "minti biyar yamin yawa idan zaki bani damar yin magana dake ayanzu, Kallan qawar tata tayi da cewa "Bani lokaci kad'an Dan Allah.. nan ta gyad'a mata kai alamar ba damuwa, Dan haka Zama sukayi nesa da qawar kad'an haka Kan wani dandamali Wanda da alama anyishi ne dan Zama irin hakan, nan ya kalleta cikin nutsuwa yace "har yanzu wannan yarinyar da aka qalama wannan shirrin mahaifinta baya Shiga harkarta, Yana fushi da ita fushi me tsanani, gashi sun kusa rabuwa da juna, Dan gobe d'aurin auranta, kinsan waye zata Aura?, nan ta girgiza masa Kai, sai yaci gaba da cewa, Nine Wanda zata Aura, shin kina ganin yadace taje gidan auranta ba rabuwa tajin dad'i tsakaninta da mahaifinta, tace "ko kad'an hakan bazaiyi dad'i ba, na tausaya mata matuqa, yace "ina rokwanki da ALLAH sannan naci darajar manzan Allah, tace "Sallallahu'alaiyiwassallam, yace "ki gaya min gaskiyar abin d'aya faru awannan ranar, Dan nasan kinsan komai daya faru, ki temaki wannan marainiyar yarinyar wacce bata da uwa ki fitto ki wanketa daga kallan da mahaifinta yake Mata ko tasamu sassauci...
Tace "maganar gaskiya ba itace ta aikata ba, acikin su biyar din ne d'aya daga cikinsu itace duk da aikata hakan, saidai bazan iya ganar dakai ita ba, Dan bansan kwatancen da Zan maka ka ganeta ba, nan ya zaro wayarsa daga cikin ajjihunsa ya nuna Mata hotan SafiYYAH da cewa, "sunanta SafiYYAH itace wacce abin ya faru akanta ko ba haka ba, d'aga masa Kai tayi, Saiya nuna Mata hotan ReeYAH yaci gaba da cewa, Sunanta ReeYAH kuma itace wacce yanzu muke magana akanta ba, tace "Haka ne, hotan Seeyama da Shamsiya ya nuna mata da cewa, "wacece acikin su biyun nan, tace "bata cikinsu, gabansa ne yayi mummunan fad'uwa daya tuna hotan RaHinAT shine na qarshe dazai nuna mata, cikin sanyi ya fitto da hotan RaHinAT d'in Yana nuna mata da fad'in "sunanta RaHinAT itace ta aikata komai d'in, cikin sauri tace "Yes, babu ko tantama wannan itace ta aikata komai, da fari muna tare da wacce abin ya fara faruwa da ita sai Naga tasaka mata turaran acikin jakarta dake jakar lokacin abude take, abin yaban mamaki amma da nayi wani tunani saina share hakan, duk tunani na irin b'arayin y'an matan nan ne, saidai bazasu iya sata agurin ba, Dan Naga ko ina Camera ne, nasan dole masu Kula da tsaro zasu kamasu, abin daya ban mamaki shine ganin da nayi tana kuka tana cewa wallahi bata Satan musu turare ba nan ya tabbatar min tarko akesan a had'a Mata, domin haka sai naji ina San temakonta amma ina tare da tsoro dan ban san yanda wasan zai Kaya ba, sai nayi tunanin Karna fitto na nuna wacce ta aikata Mata hakan gwara dai masa tsaron wajen su fitto su bayyanata da Kansu, Dan ance idan baka iya kama b'arawo ba Shi Saiya Kamaka, bayan na bada shedar banga lokacin da ita SafiYYAH ta d'aukar musu turaran ba, nayi mamakin yanda ma'aikacin wajen me Kula da camera ya fitto yace ReeYAH ce ta sakama SafiYYAN turaran acikin jakarta, alokacin tambayar kaina nayi me yasa bai juna RaHinAT ba, bayan yasan itace ta aikata hakan!
Kasan mecece amsar tambayata?, girgiza mata kai yayi alamar aa, sai taci gaba da cewa, amsar tambayata itace wannan, saita nuna masa Zoben dake hannunta, Wanda RaHinAT ya sa'ni da Zoben, Zoben zinare ne, tunda ya dawo daga England suka had'u yasan RaHinAT d'in da Zoben.....
Budurwar katse Mai tunani tayi wajen ci gaba da cewa, itace tasaka min Zoben a hannuna, cikin murya qasa qasa tace min, nasan kinsan nice na aikata komai, Inasan kiyi shuru da bakin ki, Dan darajar wannan Zoben agunki kimanin dubu d'ari uku ne, nasan zai share Miki wasu matsalolin ki
Bawan Allah bansan sunanka, ni dai tunda naji wannan Zoben a hannuna na kallesa na tabbatar zinare ne, nan na fahimci kamar yanda ta biyani akan nayi shuru da bakina haka Shima ma'aikacin wajen me Kula da kemerorin tabiyasa ne shiyasa yazo yake bada shedar qarya akan ReeYAH, haka sunan nata yake ko, d'aga Mata Kai yayi cikin mutuwar jiki, sai tayi murmushi daci gaba da cewa, a wannan lokacin da muke ciki kasan ba kowa bane zai iya dauke Kai daga barin kudi kimanin dubu d'ari uku, wannan yasa nayi shuru da bakina, Amma maganar gaskiya ReeYAN taban tausayi, har yanzu maganar da nake maka da tausayinta araina..
Murmushi yayi da cewa, "wato duniya sai qara lalacewa take, ga gaskiya Amma wasu MUTANAN Basu iya fad'arta saboda abin duniya, kamar yanda ta baki wannan Zoben kikayi Shuru da bakin ki, Nima Inasan na Baki kudi linkin kudin Zoben kimin wani aiki, cikin farin ciki tace "wane aiki ne wannan Zan maka Shi bisa gaskiya da amana, na d'aukar maka alkawarin hakan, yace "Gud, Zan gaya komai kuma ina San komai d'in ya tafi a dai dai, tace, "baka da matsala, Sunana Balkisu kai fa, Yace "ALIYU, yanzu akwai numbar da zaki ban ko babu, tace "wayar ta gyaru yanzu haka wajen karb'owa zamuje Dan haka zaka sameni idan Ka qara Kira na, yace "ok muje na rage muku hanya, tace "godiya muke
Washe gari da misalin qarfe takwas na safe, suna breakfast dukkansu saiga Balkisu tayi sallama, Laila tabata izinin shigowa, bayan ta shigo durkusawa tayi kusa da ReeYAH cikin zubar hawaye tace "Na aikata miki babban kuskure baiwar ALLAH, nasha wahala kafin nasamu Inda kike, wani mummunan mafarki nayi akan idan banzo na nemi yafiyar ki ba akwai abin dazai faru dani, maganar gaskiya nice na saka ma SafiYYAH turaran nan acikin jakarta, nice na biya wannan ma'aikacin wajen me Kula da Camera Akan yace kece kika saka Mata, duk nayi hakan ne saboda kud'i, wata ce ta biyani kudi akan na shirya miki hakan, kuma ni bansanta ba, bansan dalilinta nayin hakan ba, nidai tabiyani kudina atake hakan yasa ban tambayeta dalili ba, kuma koda komai ya kammala ban qara sakata a idona ba bare na iya sanar dake ko itad'in wacece.
Amma saidai tunda abin ya faru haka naketa mafarkai kala kala na ban tsoro, wanda hakan nuni ne akan lalle saina nemoki na nemi yafiyar ki akan hakan..
Cikin farin ciki ReeYAH ta kalli Dadynta, hawaye na zubar mata tace, "kaji ko Dady, yanzu Ka yarda ba nice na aikata bako, wallahi Dady bazan tab'a aikatama SafiYYAH haka ba, Dan ALLAH Dady kadena fushi dani yarka bazata aikata lefi irin wannan ba, cikin Jin dad'i da murmushi yace "ALLAH yayi miki albarka naji komai...
Cikin Jin HaYdaR yace "Masha Allah, yanzu dai taci arziqin manzan Allah kiyafe mata qanwata tunda kinga Allah ma muna masa lefi ya kuma yafe mana.. Dadyn yace "wannan haka yake... Cikin sanyi ta kalli Balkisun tace, "Na yafe miki amma Dan Allah kimin alqawarin bazaki qara aikata irin hakan ba anan gaba.. tace "Insha ALLAH na d'aukar Miki wannan alqawarin bazan sake ba nagode sosai.. tana fad'in hakan tatashi tana yi musu sallama ta ficce daga falan.
Laila tace "dama nasan akwai abin daya saka uba ya dena kula Y'arsa, Usman yace "Nima nasan aikwai abin daya faru Amma ReeYAN taqi gaya min komai, Lailan tace "toya kamata yanzu su Gaya mana abin daya faru, HaYdaR yace "Momy komai ya wucce yanzu ai koba haka ba Dady, murmushi ReeYAH da Dadyn sukayi Dadyn yace, "haka ne HaYdaR, ba wani labarin da zasuji..
Murmushi kowa yayi, daga haka sukaci gaba da breakfast d'insu...
Can HaYdaR daya kammala ya tashi yayi room d'insa, anan ya Kira Balkisun Yana cewa, "naji dad'in kafcenki, tace "Dole na cika maka aikinka tunda kana da alqawari, idan Ka manta na tunatar dakai Ka biyani tunkan komai ya wakana, yace "kawai nidai naji dad'in hakan, tace "Nima naji dad'i, yace "tom sai wata Rana idan Allah ya qara had'umu, tace "Allah ya qara had'a mun, daga haka suka ajiye waya...
Dama ya d'auki videon maganar da Balkisun take fad'a d'azun, kaf d'insu Dady ReeYAH Laila Usman ba Wanda ya lura Yana d'aukar videon, Dan haka turama RaHinAT da SafiYAH dasu Seeyama yayi, Yana Gaya musu ga wacce ta aikata lefin...
SafiYYAH ce ta fara ganin videon kafin su Shamsiya, nan ta bud'e aiko taga abin mamaki, nan take Suma da suka gani mamakin ya kamasu, nan gabaki d'ayansu hankalinsu ya qara kwanciya, suka qara tabbatarwa ReeYAN bata aikata hakan ba...
Shamsiya ta Kira SafiYYAH a waya danta sanar da ita, anan take gaya Mata yanzu itama tagama gani da alama dukkansu ne ya turoma videon, dama ita bata yarda ReeYAH zata aikata Mata hakan ba...
RaHinAT ce ta qarshensu wajen ganin videon, hakan baqara min mamaki ya bata ba, cikin matuqar mamakin ta kira numbar HaYdaR d'in, yako d'auka cikin Nishad'i, yace "Ya akayi ne sweetheart, tace "nayi mamakin ganin videon daka turamin ne, yace "Haka ne, Nima nayi mamakin hakan matuqa, muna breakfast sai gata ta shigo, tunda naganta na ganeta, nan na fara d'aukar videon Dan jikina ya bani tana tafe da abu me mahimmanci, to gashi Ku bakwa wajen, wannan yasa na fara d'aukar videon dan bana San ta furta kalma d'aya wacce zakuyi missing d'inta.
Cikin sanyin jiki tace Bayan hakan bata qara cewa komai ba, yace "kinafa gani har fitarta daga falan sanda videon yakai nan, daga haka ba wata maganar data qara yi da wani...
Sauke ajiyar ZUCHIYA RaHinAT d'in tayi, Wanda sanda yajita..
Murmushi ya sake da cewa, "wato HEENAT Bana San makirci nakan ji natsani me aikata Shi, a lokacin da abin ya faru da nagane duk itace ta shirya hakan da abin dazan mata kare bazai iya d'auka ba, saboda naji zafin hakan har fata nake asiri ya tonu a lokacin Kuga yanda Zan nuna tsanata GA Wanda ya aikata hakan, yanzu dai ta nemi yafiya kuma ko nine Zan yafe mata, Amma Inda zata qara aikata hakan ban san wata irin tsana Zan Mata ba..
Sauke ajiyar ZUCHIYA RaHinAT d'in taqara yi..
Tace "sweetheart mu manta da wannan zancen tunda kowa yasan gaskiya yanzu, kawai Ka gaya min yanzu Saura awa nawa muzama matanka.. murmushi yayi da cewa "Awa uku, me kike shiryamin ne, tace "aiko na shirya maka bazan zo a uwar gida ba bare nasamu damar nuna maka komai, yace "kinsan menene, tace "aa, yaci gaba, "duk wacce aka fara kawomin adakinta zan Fara kwana, cikin sauri tace "insha ALLAH nice, yace "idan kuma hakan yazo bake bace zanji miki babu dad'i fa, Dan ban tab'a tunanin Zan fara Shiga d'akin wata mace wacce bakece ba, tace "Nima haka, yanzu meye mafitta, yace, "mafitta d'aya ce shine addu'a, Kita addu'a afara kawoki, tace "toh shikenan.. yace "sannan Dan Allah karki bari shed'an ya Shiga zuciyarki ki aikatama ReeYAH ko SafiYYAH wani abu... Cikin fad'uwar gaba tace "me yasa kacemin haka, yace abin dazan gayama ReeYAH da SafiYYAN ne shine na fara gaya miki, please ku riqe juna da Amana, dukkanmu Amanar juna ne, sauke ajiyar zuciya tayi da cewa, "indai ta fanni nane baka da matsala da hakan, yace ina miki fatan alkairi, yanzu saiki barni nayi tunanin irin gayun da zanyi Wanda zanfi kowa kyau a wajen d'aurin Auran, tace "AI kaima kasan zakafi kowa kyau, kaifa me tsada ne, Samun kyakkyawa kamarka Wanda yake kyau da kowace irin sutura sai an tona, yace godiya sarauniya ta, bye bye, tace "bye..
Suna ajiye wayar RaHinAT ta qara sakin ajiyar ZUCHIYA, ita dai tunaninta ya bata kawai Balkisu taje ta wanke ReeYAH ne saboda ta bata tautsayi, yin wannan tunanin yasa hankalinta kwanciya, Amma taji rashin jin dad'i da hakan ta faru, taso abar ReeYAH cikin zargi, nan take ta tuno da yanda ta Kaya dame Kula da kemarorin supermarket d'in, bayan ta sakama SafiYYAN turaran acikin jakarta nan idanta ya sauka akan cameran wajen, gabanta ya fad'i nan tatambayi wani ma'aikacin wajen ina ne Inda zata gana dame Kula da cameran supermarket d'in, nan ya kwatanta Mata, shine tana zuwa yace Mata ai yaga abin da tayi, anan tace zata bashi 100k Akan ya temaka ya yarda da shirinta, Jin hakan yasa suka shirya makircin ya sauka Akan ReeYAH Amma taso SafiYYAH ta fad'a tarkwan tayanda za'a kallanta a matsayin me sata, Amma dole ta canja shiri ya fad'a Kan ReeYAN, anan take ta karb'i account number d'insa ta tura mai kudin...
Wannan shine abin daya faru...
Tuno da hakan yasa ta saki murmushi ayanzu, abayyane take cewa, "nayi asarar zuben dana karb'a agun SafiYYAH kuma ina sanshi sosai, gashi harda kudina Amma burina bai cika ba...
Kasancewar tun kwana biyar data wucce akaje akama amare jere agidan mijin nasu daya amsa sunansa, hakan yasa yanzu da Aure ya d'auru dukkansu gidajen uku suke kici kicin shirya amare Dan za'aje walima daga nan suna fatan suna dawowa akai amare gidansu..
ALIYU Ahmad da SafiYYAH Muhammad
ALIYU Ahmad da RaHinAT Zakkari
ALIYU Ahmad da JuwaiReeYAH Ahmad Aure ya kullu akan sadaki dubu d'ari d'ari...
Babban waje ne Wanda ya amsa sunansa anan aka gabatar da walimar, wacce akaci akasha akaji aziri Kala kala na lamai, tabbas amare da duk Wanda yaje wajen ya qara jin tsoran Allah, amare suna fatan bin mijinsu sau da qafa, ammafa ance musu Banda duba wayar miji Banda bincikarsa akan Yan mata😃
Ana kammala walimar su HaYdaR ma suka gabatar da tasu walimar, kud'i ne dai yayi kuka Dan wajen ci da sha ba qaramin lada aka samu ba tun daga Kan walimar amaran data angon an kashe kud'i Bana wasa ba, harta iyaye Maza sanda sukaje walimar, abin yayi kyau sosai, sai fatan alkairi ga mijin da amaransa.🙏🏻
Zanso naga wacce za'a Fara kawowa cikin gidan, shin ReeYAH ce ko SafiYYAH ko RaHinAT wakuke tunani zata fara wuf da HaYdaR