INUWAR WANI

Chapter 1

by @nasimat

Qofar qaton gurin ta kalla daga sama ke nan, an rubuta ‘RAIL WAY NIGERIA’ da manyan baqi. Karo na farko da za ta yi tafiya a jirgin qasa. Xan sahun da ya ke xauke da ita, ya ce, “Hajiya mun iso, a nan waje zan ajiye ki?”

Ta yi saurin cewa, “A’a, qarasa da ni ciki”.

Ba musu ya kutsa kan sahun nasa cikin harabar gurin. Ya tsaya a inda wasu adaidaitan suke tsaye. Ta fito tare da jakarta ta kaya, da kuma wadda ke riqe a hannunta, wato ‘yar qaramar (purse). Ta ajiye babbar a gefe tare da buxe qaramar ta ciro takardar kuxi ta xari biyar ta miqa masa. Ya ba ta canjin xari xaya, sannan ta kinkimi jakar ta matsa gefe inda wasu matasa suke tsaye.

“Don Allah a ina a ke hawan jirgi?” Ta tambaya tana kallonsu.

Xaya daga ciki ya ce, “Can za ki je ki sayi ticket, amma sai kin yi sauri fa, ba domin jinkirin da a ka samu ba ai da kin makara, don qarfe takwas zuwa tara na safe ya ke tashi”.

Ta ce, “Na gode”.

Ta nufi inda ya nuna mata kanta tsaye. Ta shiga xan xakin da sam bai kamata a ce nan ne wajen siyen ticket ba, saboda rashin kimtsuwarsa. Domin da farko ta xauka ba wajen ba ne, sai da ta tambayi wata mai siyar da abinci ta tabbatar mata gurin ne, ta kuma nuna mata ‘yar qaramar tagar da a ke siyen ticket xin. Ta qarasa.

Ticket za a ba ni”. Ta faxa da xaga sauti, saboda hango mai sayarwar da ta yi can nesa tana latsa waya kamar ba ta san Allah ya yi tsayuwar wani halitta a gurin ba.

Matar ta taso cikin halin ko’inkula, “Zuwa ina?”

Ta ce, “Minna”.

“Okey, xari shida da hamsin”.

Ta buxe jaka ta xauko naira dubu ta ba wa matar. Ta haxa mata ticket da canjinta, ta juya ta fito daga gurin. A inda ta bar matasan a nan ta tarar da su, ta sake tambayarsu inda jirgin ya ke. Ta bi ta ‘yar qaramar qofar da suka nuna mata, sai dai duk taragon da ke gabanta idan ta leqa sai ta hango cike ya ke da mutane maza da mata, yara da tsaffi, qabilu iri daban-daban. Tana buqatar inda babu hayaniya sosai, don haka ta yi ta tafiya ba don ta san yadda tsarin gurin ya ke ba, har ta iso tarago na farko wanda daga shi sai taragon da matuqa suke. Ta zura qafarta ciki. Babu mutane da yawa kamar sauran taragogin da ta wuto, amma abin da ya ba ta mamaki duk kujerar da ta zo zama sai waxanda ta tarar su ce, akwai masu gurin.

Tana ta bin kujeru can wani matashi wanda da alama bayerabe ne, ya kira ta. Ta dawo, ya ce. “Zauna a nan”.

Cikin rashin kuzari ta zauna a inda ya nuna mata, wato kujerar da ke fuskantarsa.

“Ki xora kayan a can sama”. Ya faxa yana nuna mata xan qarfen da a ke ajiye kaya a kai.

Ta yi qoqarin ciccivar jakar don xorawa, ya lura kamar tsawonta ba zai kai ba, ya miqe da sauri ya karba ya xora mata.

“Na gode”. Ta faxa bayan ya taimaka matan.

Ya kaxa kai ba tare da ya yi magana ba. Ya koma mazauninsa, ita kuma ta zauna a hankali tana bin mutanen da ke gefenta da kallo. Yanayin muryoyin da ke tashi ya sa ta fahinci mutanen cikin taragon ba Hausawa ba ne, domin ba ta ji an ambaci ko ‘a’ da Hausa ba. Ta saci kallon matashin da ya xora hannu kan file xin da ke kan xan qaramin teburin da ke ajiye a gabansa, ta ga ba ita ya ke kallo ba ya mayar da hankalinsa sosai ga file xin duk da ta farax xaya ba za ta tabbatar da hakan ba saboda ya sakaye idanunsa cikin tabarau mai duhuwa. Sai ta jingina bayanta da kujerar da ta ke zaune, ta lumshe idanunta, abubuwa da yawa na yawo a kwanyarta, cin amana da yaudarar da a ka shallaxa mata ya addabi zuciyarta.

A kujerar da ta ke zaune mutum biyu ke da damar zama kamar yadda ta matashin ma mutane biyu ne za su zauna, sai can hannun ne ke da sauran mutane uku da biyu, wato uku na fuskantar biyu. Muryar wata matashiya ta ji cikin harshen Turanci tana neman izinin zama a kujerar da ke bayan tata, amma fir! ‘yammatan biyu da ke zaune a gurin suka qi amincewa, wai akwai waxanda suka tanadi wajen. Mamaki ya kamata, saboda a zamanta sam ba ta ga wasu da suka tashi ba, ta dubi matashin ba tare da ta ce masa komai ba. Shi ma ita ya ke kallo, sai dai yanayin kallon da ya ga tana yi masa kamar neman izini ta ke ta zaunar da waccan matashiyar. Ya maida kallonsa ga matashiyar da ta yi duru-duru tana wurga idanunta inda ya dace ta zauna,.

“Zo ki zauna nan”. Ya ce da ita

Da sauri ta nufo gurin tana fara’a, “Na gode Bros, Allah ya saka da alkhairi”.

Ko sake kallonta bai yi ba. Ta rava gefen matashiyar ta zauna tana mita.

“Saboda tsabar munafunci irin na yarbawa, in dai za ka shigo wannan taragon ba qabilarsu ba ne kai ka shiga uku, sai ka ce don su kaxai a ka yi taragon”.

Matashiyar ta yi murmushi, “Au da ma wannan ne dalilin da ya sa suke hana mutane gurin zama?”

“Ai ko dai haka na ji wani a waje yana faxa wa wata, wai su nan hikimarsu idan an je Zaria su saka ‘yan uwansu yarbawa”.

“Tabxijan! Ai ko ba su da hali”. In ji matashiyar farko.

Sai suka yi shiru na wani lokaci, shi dai matashin ya maida hankalinsa ga tagar da ke kusa da shi.

Please, ya sunanki?” Matashiya ta biyu ta katse shirun da suka yi da faxin haka, tana xan murmushi.

“Sunana Mahashura, amma Amira a ke kirana”.

“Allah sarki, ni kuma sunana Fainusat”.

Amira ta kaxa kai, “Sunanki wani iri, ban tava jin irinsa ba. Amma ke ba bahaushiya ba ce ko?”

Fainusat ta yi dariya, “Haka ne, ni qabilar ibra ce ta jihar Kogi, amma rayuwa ta kaf! a Kano na yi ta cikin Hausawa don haka na ji hausa sosai, idan ba na faxa ba zai yi wahala ki canki qabila ta, ke fa wace qabila ce?”

Amira ta xan yi shiru kamar ba za ta amsa ba, can ta nisa ta ce.

“Ni Hausa Fulani ce”.

Ta qarashe maganar tana qoqarin buxa jakarta don ta kawar da hirar.

“Ai da ma da ganinki an san bafulatana ce, hala ke ‘yar Adamawa ce?”

A taqaice Amira ta ce, “Eh”.

Matashin ya juyo gare su ya xan zame tabarau xin fuskarsa yana kallonta, “A wace qaramar hukuma ki ke a Adamawan?” Ya tambaya.

Sai ta yi tsuru-tsuru, saboda ba ta san ko’ina ba a cikin Adamawa. Ta qi maida hankali gare su, ta wayance da faxin, “Subhanallahi”.

Ta miqe tsaye da sauri.

Fainusat ta ce, “Lafiya, me ya faru?”

Tana yamutsa fuska cikin tattaro damuwa ta ce, “Diaryna ne ban gani ba…”

Ta kalli matashin, “Don Allah taimaka ka sauko min jaka ta na duba, don shi ne maqasudin zuwa na Kano”.

Fuskarsa a xaure ya miqe ya ciro mata jakar, ta hau bincike kamar gaske. Gabaxaya suka tattara hankalinsu gare ta. Can ta sauke nannauyar ajiyar zuciya bayan ta fito da diary xin a can qasan kayanta. Ta dinga juya shi a hannunta, matashin ya xan karkato yana kallonta, Fainusat ta yi murmushi, “Kin yi ta barka”.

Ba tare da ta dube ta ba, ta ce, “Wallahi kuwa, domin da ban ganshi ba dole zan fasa zuwa Minna yau”.

Fainusat ta jinjina kai, “Wane irin muhimmin rubutu ne a cikin diary xin nan haka?”

Ta maida jakar ta rufe tana faxin, “Ke dai a yi sha’ani kawai”.

Ta dubi matashin, “Malam don Allah kada ka gaji”.

Yana qoqarin kinkimar jakar ya ce, “Sunana Uwaisu ba Malam ba”.

Su biyun suka yi dariya.

“Allah ya ba ka haquri”. Amira ta faxa yayin da ta ke komawa mazauninta.

Ya ce, “Ba fushi na yi ba, kawai hutar da bakinki kiran Malam na yi”.

Sai ta yi shiru. Ya buxa baki zai yi magana ke nan ya hango wata kyakkyawar budurwa ta shigo taragon, tana sanye da qananan kaya masu ruwan makuba, sai dai qaramin mayafin da ta yafa zai alamta musulunci a tare da ita. Bugu da qari kayan da ke jikinta masu yalwa ne, ba ta bari gashinta ya fito waje ba.

Uwaisu ya zuba mata idanu cikin wani irin kallo, Amira da Fainusat suka bi shi da kallon mamaki, yadda gabaxaya hankalinsa ya tafi ga budurwar, sai suka yi tunanin ko ya santa ne. Budurwar ta tsaya daidai kujerar da suke ta xan dubi Uwaisu, “Please can I seat here (don Allah zan iya zama a nan)”.

Da sauri ya jinjina mata kai, “Yeah, you can sit”.

Ta tattare mayafinta tana qoqarin zama a gefensa, “Hi ladies”. Ta ce da su tana kallonsu.

Fainusat ce ta amsa mata da, “Hello”.

Kai tsaye ta miqa wa Fainusat hannu don yin musabiha, “Ummahani Abduljabbar sunana”.

Okey, Fainusat Masa’oud”.

Ummahani ta kaxa kai, tare da miqa wa Amira hannu, ita ma Amiran ta miqo mata ba tare da ta kalle ta ba, “You can call me Amira”. Ta qwace hannunta.

Ummahani ta xan sunkuyar da kai tana kallon Amira ta saman gilashinta, cike da mamakin yadda ta karve ta, sai ta watsar ta maida kallonta ga Uwaisu, wanda tuni ya maqala abin kunne a kunnensa yana kallon gefe. Abin da ya fara zuwa ranta, Uwaisu da Amira tare suke idan ta yi la’akari da yadda yanayinsu ya nuna.

“Lafiya har yanzu jirgin bai tashi ba?” Ta faxa cikin harshen Hausa tana duba agogon hannunta. Lamarin da ya sa Amira ta yi saurin kallonta cike da mamaki, don ba ta yi tsammanin tana jin Hausa ba.

Fainusat ta ce, “Wallahi ga shi nan dai, wai an ce mai a ke sa masa ne”.

“Mai?” Ummahani ta maimaita, “Me ya haxa train da fetur?”

“Oho!” In ji Fainusat.

Ta ja tsaki, “Kai qasarmu muna kwankwadar madara”.

Fainusat ta yi dariya, “Allah kuwa, ki duba ki ga yadda tashar jirgin nan ta ke, abin gwanin ban haushi, wai kuma sunan Kano babbar cibiyar kasuwanci na Najeriya da a ke zuwa daga qasashe, amma babu wani ci gaba da a ka samu”.

Amira kallon Ummahani kawai ta ke, yadda ta zage tana zuba Hausa.

Sun kasance cikin shiru tsayin lokaci, kafin daga bisani Ummahani ta jingina da kujerar da ta ke zaune, ta lumshe idanu, a hankali ta furta.

“Ana canza xa ba a canza mata”.

Wannan furucin ya ja hankalin Fainusat gare ta, tana murmushi ta ce, “Haba dai, ya za a yi ido ya mutu kwalli ya tada shi?”

Ummahani ta buxe idanunta, “Ah to ke ma kin faxa, har kullum amsar da na kasa samu ke nan, ta ya za a yi a ce an sauya xa, amma ba a sauya mata ba?”

Fainusat ta ce, “Ai kuwa za ki jima ba ki samu ba, domin abin da ba zai yiwu ba ne…”

Daidai lokacin wayar Ummahani ta yi qara, ta buxa jaka ta ciro ta duba, ta kyave baki, sannan ta kara a kunne, “Hello Dad… ka yi haquri ba zan faxa maka inda nake ba… A’a ka yi haquri kawai ka qyale ni na rayu a duk inda ya yi min, ba zan iya bin umarninka ba ne shi ya sa na zavi hakan, kuma don Allah ka ci gaba da son matarka tunda ana sauya xa ba a sauya mata”.

Hakan da ta faxa ya sa Fainusat ta fahinci inda waccan maganar ta sa a gaba. Ta zuba mata idanu cike da tausayi da son jin abin da ke faruwa. Ummahani ta ci gaba da cewa, “Wallahi idan za ka zagaye tashoshin Kano kaf ba za ka gan ni ba, don yanzu haka na yi nisa da barin Arewa…”

Ta datse wayar tare da danne jan, wato ta kashe ta gabaxaya tana mita, “Tunda ka ce ka sauya ni ba shi ke nan ba?”

Fainusat ta ce, “Ya subhanallahi, haba Ummahani me ya yi zafi ki ke irin haka? Mahaifi fa ba abin wasa ba ne”.

Ummahani ta rausayar da kai, “Ai ba wani abu na yi masa ba, kawai na kauce wa ganinsa ne don ya samu nutsuwa, ni ma kin ga na huta da quncin rayuwa, na ji da maraicin da ke addabar zuciya ta”.

Fainusat ta xan yi shiru tare da kallon Amira, wadda ta jingina da kujerar ta xaga kai sama, sannan ta dawo da dubanta ga Ummahani, “Ki yi haquri Ummahani, yau na fara ganinki, amma sai na fahinci kamar mun yi tarayya a damuwa, duk da ni ba a vangarenki tawa qaddarar ta ke ba. Haka kawai tun ganin farko da na yi miki na ji kamar za mu taimaki juna a shawarwari da za mu samu mafita a kan damuwarmu”.

Ummahani ta dinga kaxa kai, “Haka fa, ni ma wallahi ganinku gabaxayan nan sai nake jinku kamar ‘yan uwana”.

Uwaisu da Amira suka kalle ta, ita ma ta kalle su.

“Duk da dai na lura kamar ba tare ku ke ba”,

Fainusat ta yi murmushi, ta ce, “Haka ne, amma su xin ma masu sauqin kai ne, a nan muka haxu sai dai kafin zuwanki yadda ki ka san mun jima da sanin juna, musamman babban Yaya Uwaisu, mai zuciyar taimako”.

Ta qarashe maganar tana kallon Uwaisu da murmushi a fuskarta.

Ummahani ta ce, “Ai na fahinci haka…”

“Ko za ki ba mu labarinki?” Fainusat ta tari numfashinta.

Ummahani ta yi dariya, “Sai dai ki fara ba ni naki”.

Ita ma Fainusat ta yi dariyar, “Wai! Ai labari na sai an tanadi hankici saboda share hawaye”.

“Duk da haka dai ki fara”. In ji Ummahani.

Daidai lokacin jirgin ya soma ham.

“Yauwa kin ga da alama ma yanzu za mu fara tafiya, labarin zai fi daxi tunda ni na fara nema, sai ki fara ba mu naki, in ya so idan kin gama na ba ki nawa”. In ji Fainusat.

Ummahani ta ce, “Ni ma labari na fa akwai ban tausayi, da motsa zuciyar mai sauraro, domin akwai wani tabo da har na mutu ba zai kankaru a zuciya ta ba, amma bari na fara ba ki”.

Jirgin ya soma tafiya.

 

UMMAHANI ABDULJABBAR.

‘Mu ‘yan asalin jihar Borno ne ta cikin Najeriya, a babban birninta Maiduguri, kamar yadda ku ka gani a zubi da tsarin halitta ta na kasance kanuri, haka abin ya ke. Dukkan mahaifa na kanurin ne. Mu bakwai ne a gurin mahaifin mu, mu biyu ne kacal mahaifiyar mu Inna Yagana ta haifa, Yaya ta Ummukulsum sai ni Ummahani. Sauran ‘ya’ya biyar sun fito ne daga xakin uwargidan mahaifin mu Hajja Fannah, maza huxu sai mace xaya Umma Jamila. A can Borno na yi firamare, ina aji biyu a sakandire guguwar sauyi ta tunkuxo da mu Kano, kasancewar mahaifi na shahararren xan kasuwa da ke siyar da suturu. Mu duka yaran gidan a makarantu masu zaman kansu (private school) muke karatunmu, don haka muna samun ingantaccen ilimi, haka islamiyya ma mai kyau a ka saka mu. Mun taso cikin kulawa daga farko ke nan kafin wata qaddara ta lulluqa da mu, wato a lokacin da na gama qaramar sakandire na shiga SS one wata ranar talata da ba zan manta da ita ba idan ina lissafin ranakun da suka zo min da munanan labarai. Na dawo ne daga makaranta na tarar da Umma ta da Yaya ta Ummukulsum a xaki dukkansu suna kuka, al’amarin da ya xaga hankali na, na yi wurgi da jaka ta a gefe, na isa gurinsu cikin damuwa nake tambayar abin da ya faru. Sai dai duk daga cikinsu ba wadda ta tanka min, sai ni ma na taya su kukan. Sai da muka xau lokaci a wannan yanayi, sannan Umma ta miqe tsaye ta fara haxa kayayyaki a cikin akwatinta. Hakan ya sa Ummukulsum ta sake rushewa da kuka, ta qanqame Umma cikin fita hayyaci ta ke cewa, “Umma kada ki tafi ki bar mu”.

Jin hakan da na yi ya sa na fahinci abin da ke faruwa, ni ma na qanqame Umman ina rusar kuka.

Daddy ya shigo cikin tsawa ya ce, “Wai me ki ke yi Yagana har yanzu ba ki bar min gida ba? Ko kina tunanin zan iya ci gaba da zama da ke bayan na yi miki saki uku? Idan ma zaman haramci ki ke so mu yi da ke to ki sani ni ba jahili ba ne, don haka maza ki zo ki fice min daga gida”.

Da gudu na isa ga Daddy ina faxin, “Don Allah ka yi haquri Daddy, kada ka raba mu da mahai…”

Kafin na qarasa ya daka min wata razananniyar tsawa kamar zai rufe ni da duka, “Ke rufe min baki sakaryar banza”.

Umma tana sharar hawaye ta ce, “Ka yi haquri yanzu zan tafi… amma kuxin hannu na ba za su ishe ni kuxin mota ba”.

Fuskarsa a turvune ya zura hannu a aljihu ya fiddo kuxi, ya qirga dubu biyar ya wurga mata, sannan ya juya yana faxin, “Wallahi ki ka qara mintina ashirin a gidan nan sai ranki ya yi mugun vaci, munafukar banza, an yi walqiya na ganki”. Ya fice abinsa.

Kasa kwashe kuxin ta yi, sai ni ce na tsuguna na kwaso na riqe su a hannu na, yayin da a gaggauce ta ci gaba da shirya kayanta. Tana gamawa ta lulluva da hijabi ta dubi Ummukulsum ta ce, “Kulsum, ga amanar ‘yar uwarki na damqa a hannunki, ki riqe ta da kyau, kada ki bari wani abu ya cutar da ita. Ku haxa kanku duk runtsi kada ku bari wani ya shiga tsakaninku, zan dinga yo muku aike, kada ku damu da rayuwar da za ku tsinci kanku a gidan nan, ku dai ku maida hankali ga karatu…”

Ta kasa ci gaba saboda kukan da muke yi kamar numfashin mu zai fita a jikinmu.

Ta janyo ni a jikinta ta rungume, tana faxin “Ummahani ke ce qarama, don Allah ki yi biyayya ga ‘yar uwarki sau da qafa, ki xauke ta tamkar ni, domin na san ba za ta cutar da ke ba”.

Cikin rishin kuka na ce, “Umma zan bi ki, ba zan iya rayuwa gidan nan babu ke ba”.

Cikin rarrashi ta ce, “Ki yi haquri Ummahani, haka rayuwa ta gada, kowanne mutum da irin qaddararsa. Idan kun kwantar da hankalinki kwanaki nawa suka rage muku a gidan nan? Kowaccenku dole ne ta tafi gidan aure, don haka ku yi haquri kun ji”.

Ta janye ni daga jikinta tana qoqarin xaukar akwatinta, Ummukulsum ta yi saurin xaukar mata muka fito daga xakin.

Daddy da Hajja Fannah suna zaune a falon, fuskarsa a murtuke yayin da ita kuma Hajja Fannah ba yabo ba fallasa. Ko da muka fito ba ta ce komai ba, haka shi ma Daddy, sai da Umma ta kai bakin qofa ta juyo tana dubansu, ta ce, “Yaya Fannah, na gode da irin sakamakon da ki ka saka min, amma duk da haka na ba ki amanar yarana, idan kin ci ke da Allah”.

Tave baki Hajja Fannah ta yi ba tare da ta ce kanzil ba, muka fice daga falon. Har bakin titi muka raka ta, ta samu abin hawa ta shiga tana kuka muna yi, don ni qanqame ta na yi a cikin motar, sai da qyar ta fiddo ni, ta ba wa mai motar umarnin su tafi. Muna ji muna gani Ummanmu ta tafi ta bar mu a gurin, sai da suka vace wa ganinmu sannan Ummukulsum ta kama hannu na muka koma ciki.

Ko kallon inda su Daddy suke ba mu yi ba muka shige xakin Ummanmu, kowaccenmu na kuka. Da qyar na daure na tambayi Ummukulsum abin da ya faru tsakanin mahaifanmu, ta sanar da ni ita ma tana dawowa makaranta ta tarar da Umman na kuka, ba ta san yadda al’amarin ya faru ba. Sai a lokacin na soma tariyo irin zaman da Umman ta yi a gidan. Tun soma wayona na fuskanci tsananin kishin da Hajja Fannah ke gwada wa Umma, kodaya ke ba ita kaxai ba, mu kanmu ‘ya’yanta ba mu tsira ba, kaxan za mu kuskure yanzu Hajja ta hau sirfa mana zagi, tamkar agololi muke a gidan. Idan kuwa wata buqata ta taso wadda Daddy zai yi mana, kai tsaye ta ke nuna hassadarta, sannan ta zuge yaranta su ma su uzzura sai an yi musu, don haka wani lokaci sai dai ya fasa dukkanmu, wai nan ma don Daddyn yana kwatanta adalci a tsakaninmu. Hatta makaranta don ya zama dole muke xaya da yaranta, amma qarara ta ke nuna wai bai kamata a dinga asarar kuxi gare mu ba, wai ba mu da qwaqwalwar gane karatu, kamata ya yi a maida mu makarantar gwamnati za mu fi maida hankali, bayan a zahiri yaranta ne a ke asarar kuxin a gare su.

Da ya ke ni na taso ba na shan miyar xanyar kuvewa saboda ‘ya’yanta, da kuma koko shi ma ba na sha, idan ranar girkinta ne sai dai na kwana da yunwa, amma ba za ta kaxa min miya ta daban ba, in ba Umma ce ta yi min ba, a cewarta gulma ce ta sa ba na shan xanyar kuvewar da koko, ba ta yi la’akari da Yaya Bakura da bai cin alala ba, wanda idan Umma ce da girki za ta yi alalar sai ta yi masa girkinsa daban, kacokam ma saboda shi ba a cika yin alala a gidan ba duk da sonta da muke yi. Sarai mun sani Hajja Fannah ta kama zuciyar Daddy ta hanyar asirce-asirce da qawayenta ke xora ta a kai, domin ni da idanuna na sha kamata tana barbaxe abincin Daddy da magani, zan iya cewa ma wannan shi ya kawo rashin jituwar nan, don zahiri ta fi tsana ta fiye da Ummukulsum kamar yadda ni ma na tsane ta.

Duk cikin ‘ya’yanta wanda ya fi xaukar halinta gabaxaya shi ne Yaya Madu, sam ba ma shan inuwa xaya da shi, haka bai jin shakkar yi wa Ummanmu rashin kunya ko da a gaban mahaifiyarsa ne, kuma ba ta cewa komai. Wani lokacin ma a gaban Daddy za su yi mata xibar albarkar da ke ransu, qarqari ya ce su kauce ko ya doke su, amma babu wani katavus da ya ke yi bayan wannan. Idan kuwa a ka yi hutu muna son zuwa Maiduguri qiri da muzu Hajja za ta shiga ta fita sai ta ga Daddy ya hana tafiyar, hankalinta ke kwanciya.

Wannan da ma sauran lamuran rayuwa da Umman ta ke fuskanta suka sa ni yanke tsammani babu shakka wani tuggu ne a ka shirya da ya datse igiyoyi uku da ke raye da zaman auren Umma a gidan tun auren lalle, auren da a ka sha gumurzu kafin a wanzar da shi, domin kafin Daddyn, tana da masoyan da suka jima suna sonta, Allah ya sa dai shi ne mijin nata.

Na ja doguwar ajiyar zuciya bayan na gama wannan nazari, sannan jiki a sanyaye na miqe na cire kayan makaranta na shiga banxaki na watso ruwa, tare da xauro alwalla na dawo xaki na gabatar da sallar azahar da la’asar da a ke gabatarwa a lokacin.

Bayan na gama ne na fito falo don neman abin da zan saka a baki na. Yaya Bakura da Yaya Madu suna zaune a falon, kowanne za ka dubi fuskarsa ka san yana cikin farin ciki. Ba abin mamaki ba ne da ma na san arina, tunda ba qaunar Umman suke ba, sun ma yi kyan kai da ban tarar da su suna cashe rawa ba, duk da a yanzu xin ma marabar kaxan ce, domin kallo suke cike da nishaxi. Kai tsaye na nufi kicin, har na kai qofa zan shige na tsinkayo muryar Yaya Madu yana faxin, “Ke Haniniya zo nan!”

In da sabo na saba, zai yi matuqar wahala Yaya Madu ya kira ni da wani suna savanin ‘haniniya’ don haka ba tare da damuwar vata min sunan da ya yi ba na juyo na dawo. Cikin girmamawa na durqusa a gabansa. Wani mugun kallo ya ke bi na da shi yayin da ya ke cewa, “Ashe baqin hali ya kori uwarku a gidan nan?”

Duk da na saba jin qasqancin da suke yi wa Umma, a wannan lokacin sai na ji raina ya yi mugun vaci na sunkuyar da kai qasa.

Ya xora da cewa, “To umma ta gaida assha, ku kuma gargaxin da zan yi muku shi ne, ku kiyaye duk abin da zai sa ku shiga gona ta, don kun san ni sarai ba ni da sauqi, yauwa! Maza ki haxo min zovo ki kawo min”.

Ban ce da shi kanzil ba na miqe tsaye.

“Ki yi sauri fa ina son na fita nan da mintina uku”. Ya sake jaddada min.

Na shige kicin. Firij na fara dubawa, amma ban tarar da haxaxxen zovo ba sai qanqara, tilas sai an haxa wani. Kai tsaye na dawo falon.

“Yaya Madu babu wanda a ka haxa”.

Ta wutsiyar ido ya ke harara ta, ya ce, “Shi ne ki ka kwaso dogayen qafafunki ki ka dawo min ko?”

Ya ja tsaki, “Oya! Maza kafin na runtse ido ki wuce ki haxa mini, in ba haka ba wallahi sai na farfasa miki jiki yau a gidan nan”.

Jiki na na rawa na juya kicin xin. A gaggauce na hau haxa zovo, abu ne da sai an dafa an tace, don haka sai ya xauki lokaci kafin na kammala. Ai kuwa kafin na gama ya qwala min kira ya fi a qirga, yana surfa min zagi ta uwa ta uba, ban damu da yunwar da ke addaba ta ba, saboda na san mai sauqi ce a kan izayar da Yaya Madu zai yi min. Abin haushi sai da na gama haxa komai har qanqara na farfasa na zuba a ciki, zovon ya xau sanyi amma wai ina shiga falon na kai masa na tarar sai Yaya Bakura kaxai a ciki. Wani kallon banza ya watsa min.

“Kina can kina dammacin naki har ya gaji da jira ya fita”. Abin da ya ce ke nan.

Na sunkuya cikin jin haushi na ajiye jug xin na miqe zan tafi.

“Ki duba a freezer idan akwai kifi ki min dambunsa. Saura ni ma ki shanya ni, wallahi ni ba tafiya zan yi ba, wanka zan yi miki da barkono ki ji a jikinki”.

Na yi rau-rau da idanu, “Don Allah ka yi haquri Yaya Bakura, yunwa nake ji”.

Kallon banzan da ya ke min shi ya ci gaba da yi.

“Don kina jin yunwa shi ne me? Ko mu ba mutane ba ne da ba a halitta jin yunwa a cikinmu ba? Get out, zan fara counting idan ki ka zarta mintina ashirin ba ki kawo min dambun kifin ba, sai na yagalgala ki a gidan nan, start!”.

Haka na wuce ina sharar hawaye, wai fa wannan duk somin tavi ne da zan kira ‘welcome back’, wato sun samu abin da suke so, babu idanun mahaifiyarmu.

Inda Allah ya taimake ni da na duba firizar babu kifin, har ajiyar zuciya na sauke ta daxi. Na dawo na sanar da shi. Bai ce min komai ba ya miqe ya nufi kicin, wai ashe manufarsa bai yarda da abin da na faxa masa ba. Ina tsaye a falon ya dawo yana jan qwafa.

“Allah ya taimake ki yarinya, da a ce na tarar da kifin na lahira sai ya fi ki samun sauqi… wuce ki ba ni guri, sai wani sunne kai ki ke ya karuwar da ta dawo yawon dandi”.

Jiki na na karkarwa na wuce kicin na xauko abinci na, na dawo xakinmu.

Har lokacin Kulsum na kife a kan gado tana kuka. Na zauna ina cin abincin ina matsar nawa qwallan. Wannan ke nan.

A haka muka tashi a gidan tamkar marayun da iyayensu duka suka rasu, domin takura da matsin rayuwa babu wanda ba mu gani ba a cikin kwanakin watanni biyu da tafiyar Ummanmu. Yadda ku ka san ‘yan aikatau haka a ka mayar da mu, kuma abin da zai ba ku mamaki, Daddy na kallo amma bai tsawatar wa kowa. Wani lokacin har makara nake a makaranta, Kulsum kuwa da ya ke ta kammala sakandire a wannan shekarar sai da ta gwammace a ce ita ma tana zuwa makarantar, domin ta faxa min idan na tafi ba wani barinta a ke ta huta ba.

Cikin xan lokacin muka zabge, muka rame duk da kasancewarmu farare, amma sai da muka yi duhu saboda ba koyaushe muke samun sararin save jikinmu da sabulu yadda ya kamata ba.

Tun tafiyar Umma ba mu samu damar magana da ita ba, tunda dukkanmu babu mai waya, sauqi-sauqinta Daddy ba mu sani ba ko tana kiransa don ya haxa mu yana qin ba mu wayar, Allah ya bar wa kanSa sani.

Duk yadda nake da karaxi da yawan surutu a wannan lokaci sai na zama tamkar kurma, baqin ciki da quncin rayuwa sun aure ni, har ya kasance na samu naqasu a karatu na. Ba baya a ka maido ni ba, amma matakin da nake xauka, wato ta xaya ko ta biyu sai ya kasance na koma xaukar ta goma sha.

Watanni uku cur! sannan Umma suka zo kwashe kaya, wani hukunci na Ubangiji a ranar dukkanmu ba ta tarar da mu ba, tun safe Daddy ya tura mu gidan wani amininsa, abin har mamaki ya ba mu saboda ba a sabar mana da hakan ba. Sai bayan magriba shi da kansa ya je xauko mu. Wata irin rama muka yi da muka tarar da ‘yan tsirarun kayayyakin da Umma ta bar mana. A bakin Umma Jamila muke samun labarin zuwan Umman, da takardar da ta bar mana, wadda kai tsaye Jamilan ta nuna ba ta so Hajja ta gani.

Bayan mun sha kukanmu mun qoshi a xakin, Kulsum ta xauko takardar ta dawo kusa da ni ta soma karantawa kamar haka.

 

Assalamu alaikun ‘ya’yana.

Na san duk inda ku ke kuna cikin sauyin rayuwa, amma kada ku damu ku miqa lamarinku ga Ubangiji, Zai kawo muku tallafinsa. Abu ne da haka Allah ya qaddara, na yi matuqar qoqari don ganin mahaifa na sun amince min na xauke ku amma sun qi goya min baya, don haka ku ci gaba da haquri. Ga lambar da za ku iya samuna a duk lokacin da ku ka samu sukuni, Allah ya yi muku albarka’.

 

Daga qasa ta rubuta lambar.

Kwanaki uku a tsakani, ranar talata ke nan na kwafi lambar a jikin wata takarda, bayan mun tashi break a makaranta nake roqon wata qawata Surayya Isma’il idan mun tashi makaranta za mu je gidansu ta roqar min Ummanta na kira Umma ta. Da ya ke Surayyah ta san dukkan halin da muke ciki, kamar yadda na faxa muku tun farko, ni haka Allah ya halicce ni, ina da yawan surutu. Qwarai ban fiye voye sirrin gidanmu ba, har haushin kaina nake ji da wannan xabi’ar tawa.

Bayan mun tashi makarantar kai tsaye gidan su Surayyah muka nufa. Maminta mai kirki, ta san ni sosai don wani lokaci har ‘yan kunne da abin hannu ta kan ba ni. Ko da Surayya ta sanar da ita buqata ta kai tsaye ta karvi lambar ta kira min, sai dai mun daki gurbi, wayar a kashe ta ke. Baqin ciki goma da ashirin kamar na rushe da kuka, wannan shi ne a ke kira, ga qoshi ga kwanan yunwa, ko kuma na ce rijiya ta ba da ruwa guga ya hana. Mami ta rarrashe ni a kan za ta ci gaba da neman lambar, in ya so gobe sai na dawo. Cikin rashin qwarin jiki na koma gida, na tarar da wani tashin hankali, Kulsum na tarar ta qone da ruwan zafi, qunar har ta tashi duk da an kai ta asibiti an ba ta magunguna. Wannan qunar ita tasa komai da Kulsum ke yi a gidan ya dawo kaina. Da ma tuni an sallami ‘yan aiki, sai ya kasance ba kullum nake samun zuwa makaranta ba. Daddy ya koma kamar ba shi ba, duk son da ya ke yaransa su yi karatu sai ga shi a kaina ya watsar, ga shi a lokacin muna zangon karatu na uku a matakin aji huxu, kuma ina vangare mai zafi, wato science. H.O.D xinmu ne watarana ya kira ni a ofishinsa yana tuhuma ta a kan dalilin da ya sa nake wasa da karatu na? Ban voye masa matsin lambar da nake fuskanta a gidanmu ba. Ya tausaya min, ya kuma qarfafa min gwiwa tare da ba ni shawarwarin yadda zan dinga rutsa karatun nawa gudun kada sauran xalibai su yi min nisa. Ya shaida min yana alfahari da ni saboda ina da qwazo.

Rana ta farko da surutu na ya ja min wata ja’ibar, domin ban san hawa ban san sauka ba watarana Daddy ya dawo ransa a vace, bai saurari komai daga gare ni ba ya sa wayar wuta ya zane ni tatas! Sai da ya farfasa min baya sannan na ji yana maida zancen abin da ya faru ga Hajja. Wai H.O.D xinmu ne ya same shi da labarin da na ba shi, yana kwantata masa a kula da ni saboda ina da qwaqwalwa kada na samu naqasu a karatu na, amma sai Daddy ya juye zancen wai na kwashi sirrin gidansa ina barbaxa wa a duniya. Bayan ya gama bambaminsa ya fita, Hajja ta hau nata ita ma ta yi ta gama na koma xaki.

Kulsum ta dube ni ta ce “Kin ga abin da nake jan kunnenki a kai kullum ko? Ki rufa wa kanki asiri Ummahani, wannan xabi’ar ta surutu ba ta dace da ke ba”.

A lokacin haushinta na ji, don me za ta sa ni a gaba tana min wannan zancen bayan an gama zane ni?

Waya dai ba ta samu tsakaninmu da Umma ba, har qunar Kulsum ta soma qanqara. Muna jarabawar qarshe da za mu yi hutu, Surayya ke sanar da ni Maminta ta samu nasarar kama wayar Umma, har sun yi magana ta ce idan mun gama jarabawar ma mu je tare. Kamar an yi min albishir xin shiga aljanna haka na ji lokacin da muryar Umma ta ratsa dodon kunne na. Na rushe da kuka na kasa ce mata komai, sai ta kashe wayar.

Mami da ke gefena ta ce, “Na sani wannan kukan da ki ke yi ne ya sa ta kashe. Idan kina son ku yi magana, sai ki danne zuciyarki, idan ba haka ba kuwa na san zai yi matuqar wahala ta iya saurarenki ko a nan gaba”.

“Na daina”. Na dinga maimaitawa cikin qoqarin shanye kukan nawa. Mamin ce ta sake kiranta. Sai da suka yi magana tukunna ta miqo min wayar.

“Umma, mun yi kewarki sosai, rayuwarmu ba daxi”. Na faxa cikin zumuxi.

“Na sani Ummahani, amma me ya sa ba kwa amfani da nasiha ta?”

Da sauri na ce, “Muna yi Umma, kowa ya tsane mu ne a gidan, duk an kori ‘yan aiki mu ke yin komai, kuma ba a ba mu abinci wadatacce, Umma…”

Ta katse ni da cewa, “Kin gani ko? Na raba ki da wannan surutun Ummahani kin qi ji, saboda Allah rayuwa za ta tafi a haka, a ce mutum ba katsari ya yi ta zuba kamar kanyar da ba daxi?”

Har ga Allah ban ga abin da za a kururuta min yawan surutu a nan ba, Umma ta ce fa nake zayyane wa matsalolin da muke ciki, kuma sai a ce na yi ba daidai ba? Ta ci gaba da cewa.

“A da ina miki kallon quruciya ne ya sa ki yawan karaxi, amma yanzu da ki ke shekaru sha shida ta cikin sha bakwai ya kamata ki nutsu. Ba a san mace da yawan surutu haka ba, yana rage mata qima a idanun mutane, duk halin da ki ka samu kanki a ciki ki zamo mai zurfin ciki. Ke ko ‘yar uwarki ba kya koyi da ita?”

Allah ya sani ba zan iya ba, ba zan iya kasancewa kamar Ummakulsum ba. Cikin sanyin murya na ce.

“Allah da gask nake Umma ana takura mana”.

Ta ce, “Ya isa haka, don Allah ki daina wannan surutun idan ba haka ba zan kashe wayar”.

“Na daina!” Na faxa da sauri.

“Ina ‘yar uwarki?”

Na ce, “Tana gida, har fa qonewa ta yi”.

“Subhanallahi, garin ya ya ta qone?”

Kai tsaye na ce, “Ruwan zafi ya zubar mata, amma ta soma warkewa… Umma yaushe za ki zo mu ganki?”

Ta xan yi shiru kafin ta ce.

“Kada ku damu. Zan zo kwanan nan, ku dai ku ci gaba da haquri kun ji, mai haquri shi yakan dafa dutse har ya sha romonsa. Kuma ku sa a ranku dukkan tsanani ba ya xorewa ba tare da ya gushe ba”.

Ta qarashe maganar cikin yanayin tausayawa.

Haka nan sai na ji zuciya ta ta yi min sanyin da na jima ban ji ba.

“Ina sonki Umma ta”. Na faxa.

“Ni ma ina sonku, kuma kullum ina yi muku addu’a, insha Allah ba za ku tave ba. Idan kin koma gidan ki ce ina gaida Ummati (sunan da ta ke kiran Kulsum)”.

Na ce, “To”.

Da haka muka yi sallama tana jaddada min na rage surutu.

Bayan na koma gida na sanar da Kulsum saqon Umma. Ta ji daxi sosai, ta kuma ce idan an kwana biyu zan raka ta gidan su Surayyah ta yi magana da Umman.

Mun ci gaba da kasancewa cikin matsin rayuwa, yayin da nake qara girma maimakon surutuna ya ragu kamar yadda koyaushe Kulsum ke yi min nasiha, sai ya kasance kamar turi, har so nake na haxu da qawayena na ba su labarin abin da ya faru a gidanmu, ta kai ta kawo Surayyah na jin haushina, da taka min burki a duk lokacin da tarar ina zuba surutu.

Wannan ya sa nake jin haushin ganinta, saboda maganar gaskiya tana shiga rayuwa ta.

Girman da na qara yi, da hankali da ya soma gauraye jiki na ya sa na gane surutu xabi’ar da Allah ya halicce ni da ita ce dimin’da’iman, ni kaina haushinta nake ji.

Duk da kasancewar Kulsum ta kai minzalin aure amma sai a ka tauye mata wannan haqqin a ka qi ba ta damar tsayawa da samari, bayan fa koyaushe cikin zaryar zuwa mata zance ake. Da farko mun zata ko za a bar ta ta ci gaba da karatu ne, amma da tafiya ta soma yin nisa muka fahinci ba karatun ne a gaban Daddy ba, karatun ne kawai ba a so ta ci gaba da yi, duk da Umma Jamila a lokacin ta shiga jami’a.

Ni kaina ban tsira ba, samari da yawa suna kawo min caffa amma babu damar tsayawa da su. A cikin lokacin Umma ta zo Kano sau xaya, mun kuma haxu duk da ba ta kwana ba saboda rashin tarbar arziqi da mutanen gidan suka yi mata, don Hajja tunda suka gaisa ta shige xaki ba ta qara fitowa ba. Na raka ta gidan su Surayya don ta yi wa Mami godiya. A can xin ma ne ta kwana, saboda Mami tana da sauqin kai da kyautatayi.

Washegari ta tafi bayan ta ba mu tsarabar kayayyaki da ta zo mana da su, tare da ‘yan kuxaxe ko da za mu buqaci wani abu ba sai mun jira Daddy ya yi mana ba.

Ina dab da shiga aji shida ne bikin su Yaya Madu ya tashi, inda za a aurar da maza biyu sai Umma Jamila. Ba qaramin daxi na ji ba, don na tabbata idan Yaya Bakura da Yaya Madu suka yi aure suka bar gidan za mu samu sassaucin takurar da muke ciki, ba kamar ma Yaya Madu sarkin sa aiki, haka nan banza ba zai barmu mu huta ba muddin yana gidan. Shi kuwa Yaya Zangina da ma bai cika shiga shirginmu ba, shi dai barshi da son girma kamar gyambo.

Ba qaramar hidima a ke ga bikin ba, musamman Daddy ya gina wa su Yaya Madu gidaje na gani a faxa, shi kansa Bello mijin da zai auri Umma Jamila ba a barshi da hidimar ginin shi kaxai ba, domin bai kai mu arziqi ba, don ma ta nace sai shi da kuma qarfin son da iyayenmu ke yi mata ya sa suka amince, amma sai da Daddy ya sayi wani kango da ke jikin ginin Bellon a ka haxe da nasa a ka tayar da gini wai a cewar Daddyn bai kamata a matsayinsa na mai arziqin da sunansa ya tumvatsa a Najeriya a saka ‘yarsa cikin wannan akurkin ba. Da ya ke shi ma Bellon xan ayi ne (xan qarya) da kuma son abin duniya bai nuna damuwarsa ba da irin cin kashin da Daddy ke yi masa ba, shi dai ta faxi gasasshiya a wajensa.

Musamman Hajja ta je Jamani ta haxo lefen Madu, Bakura da ita kanta Umma Jamila, mu dai mun zuba wa sarautar Allah ido, don ko kiranmu ba a yi mu ga lefe ba.

An fitar da ankon biki, amma da na tambayar mana Daddy fumfurus ya yi da ni, dole na bar maganar. Waxanda ma ba su kai mu gata ba sun samu damar yin ankon, Kulsum damo ce sarkin haquri, duk wani cin kashin da a ke yi mana ba ta nunawa a fuskarta, yayin da ni ba na iya voye duk abin da ke raina, kai tsaye nake sanar da ita. Al’amarin ankon nan ba qaramin tunzira ni ya yi ba, amma ita ko a kwalar rigarta, sai ma ta nuna min rashin yinsa ya fi alkhairi a gare mu. Da na ga dai lokacin biki na qara kusantowa, kuma da gaske Daddy ba zai yi mana ankon ba na sa ta a gaba da mitar ni dai ta taimaka idan ita ba ta da ra’ayi ta yi min cikin kuxin da Umma ta aiko mana da su wancan watan.

Damuwar da ta ga na nuna mata, domin kullum cikin kuka nake, ina jin wannan ya sa ta ciro dubu biyu da xari biyar ta ba ni, dubu xaya ta yi mana saura.

Na samu Umma Jamila da maganar yadda za a yi na sayi atamfar, don ita ce abokiyar yina, domin ko giyar wake na sha ban isa na tunkari Hajja da maganar ba. Umma Jamila ta daxe cikin shiru tana kallo na, kafin ta ce.

“An fa samu matsala Ummahani, waccan atamfar da a ka fara fitarwa ta dubu biyu da xari biyar ta qare, sai ta dubu uku, ya za a yi ke nan?”

Ni ma shirun na fara yi da tunanin mafita. Na yi tunanin bai kamara na qure Kulsum ba, a haka ma ba qaramin qarfin hali ta yi ba da ta ba ni kuxin, ga shi kuma ina matuqar son yin ankon. Lura da ta yi na faxa duniyar tunani ya sa ta ce.

“Amma ba komai zan cika miki xari biyar xin, sai dai kada ki bari Mama ta sani”.

Da sauri na sauke ajiyar zuciya na ce.

“Ba za ta sani ba. Na gode ‘yar uwa Allah ya saka da alkhairi”.

Ta ce, “Wata sabuwa… idan an sayi atamfar kina da kuxin xinki?”

Na ce, “A’a wallahi”.

Ta sake yin shiru na wani lokaci sannan ta ce.

“Su ma zan ba ki”.

Da wannan shawarar muka tsaya.

Bayan kwanaki biyu, ta ba ni dubu biyu cikon xari biyar na atamfa, sai dubu xayada xari biyar na xinki. Ta ba ni qyallen atamfar tare da kwatanta min inda za same ta. Na saci jiki na je kwari na sayo, ko gidan ban dawo da ita ba kai tsaye gidan su Surayyah na nufa ta raka ni wajen wata mata mai xinki a maqotansu na bayar a xinka min.

Ina dawowa gida na tarar da xan qaramin tashin hankali, Hajja na ta zazzaga masifa wai an satar mata kuxi dubu biyu. Ina jin haka jiki na ya yi sanyi, domin na san babu wanda ya xauki kuxin nan sai Umma Jamila, kuma su ne ta ba ni na yi amfani da su.

Da qyar na yaqi zuciya ta na qi tona asirin, amma ji na dinga yi kawai na faxa wa Hajja abin da ya faru. Sai da a ka yi kwanaki Hajjan ba ta daina mitar kuxinta ba, da shan alwashin duk wanda ya yi mata sata sai ya ga ba daidai ba, duk da ya ke ma har bincike xakinmu ta yi wai tana zargin mu mulka satar mata kuxi, domin duk cikin ‘ya’yanta babu varawo. Ni dai na yi muqus, ayanayina kaxai za a fahinci rashin gaskiya, Allah ne ya tarfa wa grina nono ba ta gane ba. Sai dai a lokacin da ta gama binciken sai da Kulsum ta tuhume ni, wai ta fahinci rashin gaskiya a tare da ni, kuma a yadda ta fahinci ina son yin ankon nan har satar ma zan iya yi.

Kuka na sanya mata na qarfin hali, ina qorafin ta maida ni varauniya. Da qyar ta shawo kaina na daina kukan, amma sai da ta tambaye ni ina atamfar da na saya? Na ce mata tana wajen xinki. Ta sake tuhumata ina na samu kuxin xinki, me ya sa da na sayo ban kawo na nuna mata ba? Na ba ta haquri tare da nuna mata Surayyah ce ta biya min, don na san babu yadda za a yi ta tunkari Surayyah da maganar, musamman da ya kasance ba zuwa gidan Surayyah ke yi ba, tun watarana da ta kawo min ziyara Hajja ta hana mu saqat! Tun daga ranar ta ce ba za ta sake zuwa gidan ba.

Ana saura kwanaki biyar biki na karvo xinkina, Kulsum na gani ta hau ni da faxa lallai sai na faxa mata gaskiya, a ina na samu cikon kuxin da na sayi atamfar, don tasan kuxin wannan. Ganin na ce mata Surayyah ta biya min kuxin xinkin ba ta ce komai ba, wannan karon ma sai na ce mata ita ta cika min.

Babu wanda ya ga xinkina a gidan sai ranar biki da na saka. Duk da yawan mutane da kuma hidimar da a ke hakan bai hana Hajja bina da kallo ba a duk lokacin da na gifta idonta, na sani kallon tuhuma ne ta kemin, don haka duk sai na kasa sukuni har na yi dana sanin ma yin ankon.

Ashe ban ga komai ba, an xaura aure lafiya, yammacin ranar ana shirin tafiya fatin da za a yi na Yaya Bakura, Hajja ta kira ni cikin mutanenta, na tsuguna ina sauraren abin da za ta faxa. Da buxar bakinta sai cewa ta yi.

“Baqar munafuka sai ki hanzarta cire wannan kayan na jikinki ki kawo min su, wato duk cigiyar da nake yi da ya ke ke ce almirar varauniyar da ta sace min kuxi shi ya sa ki ka yi shiru ko? To Allah ya tona asirinki muguwa, da idanu biyu gau nake bacci ba na munshari”.

Cikin rawar jiki na ce.

“Wallahi ban xaukar miki kuxi ba Mam…”

Tun kafin na qarasa ta yi wuf! Ta zabga min mari.

“Au zan yi miki qarya ne don ubanki? Idan ba sata ki ka yi min ba a gidan uban wa ki ka samu kuxin ankon? Ko kin fara bin maza ne?”

Ba ni da zavi kawai na ga dacewar na fayyace mata gaskiya, domin Allah ya sani raina ya yi mugun vaci da kalmar da ta jefe ni da ita, ni da ko kallo samari ba su ishe ni ba a danganta ni da binsu, wanda na san manufarta na nufin ina binsu suna lalata da ni. Cikin sharar hawaye na ce.

“Wallahi ba ni na xaukar miki kuxi ba, Umma Jamila ce ta cika mi…”

Ta katse ni cikin hargagi.

“Ke rufe min baki, au ta nan ki ka villo? Wato don kin ga za ta yi aure shi ne ki ke baqin ciki za ki vata mata suna? To aniyarki ta bi ki, Jamila ta fi qarfin ta yi sata domin ba ta tashi da yunwa ba. Idan ba ki sani ba tuni kowa na gidan nan ya san su waye ku, ko ba ki da labarin Alhaji ya kama uwarku tana yi masa xan hali har sau uku, sannan ta zuba masa shinkafar vera don ya ci ya mutu? Lallai ba ki yar a qasa ba, ya kumbo ya katanta. Amma wallahi kin yi kaxan ni kice za ki min halin vera a gidan nan ki zauna lafiya”.

Idan ba a lokacin ba ban san abin da ya raba Ummanmu da gidan ba, ina qoqarin nusar da Hajja ba ni da halin da ta ke zargina da shi, kawai sai miqewa ta yi ta xauko almakashi, ta kama rigata tun daga sama har qasa ta farke. Ban da Allah ya taimake ni akwai wasu kayan a jiki na da tsirara za ta yi min, domin har zanin rigar sai da ta yi masa gutsin-gutsin, mutane na ba ta haquri tana buge musu gargaxin kada wanda ya qara tsoma bakinsa a ciki. Ni kuwa ban da kuka babu abin da nake, tunda nake a rayuwa ba a tava cin zarafina irin na wannan rana ba.

Bayan ta gama gutsintsina min sutura ta ingiza ni waje tana faxin.

“Sau dubu zan ganki da sababbin kaya a gidan nan sau dubu zan farke su, don na san kuxin ata ne ba zai yiwu ban ci nanin ba nanin ta haye min, yauwa! Ai ko da nake auren ubanki ba buxe min aljihunsa ya yi ya ce na dinga zarar abin da nake so ba”.

Ina kuka na koma xaki. Kallo xaya Kulsum ta yi min ta xauke kai, na san ta ji duk abin da ke faruwa.

Ban tava sha’awar aron abin wani ba, ballantana ta kai ni ga kwaxayin xauka. Amma yau Hajja ta laqa minsatar da a zahiri ‘yarta ce ta xauka. Na yi matuqar qoqari don na shanye wannan damuwar amma abin ya gagara, musamman da na ga ‘yar uwa tana cikin zubar da hawaye wanda ko tantama babu na san tana baqin cikin ‘yar uwarta ta zama varauniya ne.

Ana gama sallar magriba Daddy ya shigo gidan, lokacin ma da qyar na samu na sallaci magribar saboda ciwon kai da ya rufe ni. Ina kishingixe a kan sallayar ina jiran a sallaci isha, na jiyo muryarsa yana qwala min kira. Yadda amon muryarsa ke tashi ya sa na sha jinin jiki na. Da hanzari na fito falo, na tarar da shi tsaye shi da su Hajja yana cika yana batsewa yadda ku ka san irin basawan nan na finafinai.

“Ashe varauniya na haifa ban sani ba?”

Da kalmar da ya fara ke nan.

“Wato kin xauko mugun halin uwarki ko? Wallahi ba dai a gidana ba, ina sake xa amma ba na sake mata don ki ji in faxa miki”.

Rana ta farko da ya fara furta min wannan kalmar. Na dai yi shiru kaina a qasa.

“Muddin ki ka ce za ki uzzura wa mata ta ki hana ta ajiye kuxaxenta ke mai dogon hannu, to wallahi zan sauya ki, tunda ba ke kaxai na haifa ba… ke ko ku nawa ne ba ku kai matsayin mata ta ba, don haka ban haxa ta da kowa ba idan ma uwarku ta koya muku wannan mugun halin to ku sani inda ta tafi ku ma za ku iya binta”.

Ya qaraci faxansa ba tare da ya ba ni damar mayar da ba’asi ba, daga qarshe ya kora ni kamar zai kwabxe ni.

Ana ta rububin kai amarya da xauko amare, amma ni da Kulsum muna xaki muna fama da baqin ciki a zuciyarmu. A wannan rana na fara tantance rayuwa nake, rayuwar ma mai tafe da maxaci. Kwana na yi cur ba tare da na runtsa ba.

Washegari na tashi kamar mujiya sam ba na son kallon da mutane ke min, domin yana sa ni tsarguwa, sai nake ganin kamar kowa ya aminta da baqin fentin da Hajja ta shafa wa rayuwa ta, wannan ya sa a qule a xaki ina koka maraicin da ya riske mu.

Ko bayan kammala hidimar bikin su Umma Jamila ba mu samu wani sassauci ba, sai abin da ya ci gaba na musgunawa.

Kowane xan Adam da irin qaddararsa, mu dai tamu qaddarar sai godiyar Allah, watarana Daddy ya shigo da wani mutum kakkaura, baqiqirin da shi, in ban da suturar da ke jikinsa babu wani abu mai kyau a tare da shi, don ni tunda na yi masa kallo xaya na xauke kai ban qara bi ta kansa na, domin a lokacin da suka shigo ina falon ina goge talabijin. Bayan na kawo musu abinci da ruwa, zan koma ciki Daddy ya ce, “Ke mai dogon hannu (sunan da ya koma kirana da shi ke nan tun bayan faruwar waccan ja’ibar) idan kin shiga ki turo min Kulsum”.

Haka nan na ji gaba na ya faxi, ina tsoron kada a ce laifi ta yi za a hukuntata shi ya sa a ka xauko hayar wannan baqin mutumin mai siffar ‘yan dambe. Nan da nan tausayinta ya kama ni, saboda tun safiyar ranar ta ke yi min mitar ciwon kai na matsa mata, har tana yanke qauna da rayuwa. Cikin rashin kuzari na sanar da ita saqon Daddy.

Da azama na ga ta zari hijabi ta fita, sai na ji kamatuwar na lave na ji abin da zai faru, idan an fara jibgarta sai kawai na nemi cetonta ko da kuwa ni ma zan samu rabona.

“Wannan mutumin da ki ke gani abokin kasuwancina ne, sunansa Alhaji Shamawilu, shi mutumin jihar Taraba ne, amma mazauni ne a Ilori. Ya ganki yana so, don haka ga shi nan za ku gaisa”.

Wani irin duka da qirji na ya yi kamar zan tsale da ihu, ina Ummakulsum za ta kai wannan xan damben? Allah na tuba ko Hajja Fannah da ta ke mummuna, kuma ta kwana biyu a duniya a ka qaqaba mata shi ai an gama cutarta, ballantana kyakkyawar mace mai xanyantakar quruciya irin Ummakulsum. Na leqa ta labule, amma sai na ga ko a jikinta, kanta dai a qasa kamar yadda ta kasance tun wanzuwarta a falon, na ji da ma ni ce, ai idan ban tsale da ihu ba, to ba shakka sai na yi suman wucin gadi.

Kai tsaye Daddy ya barsu a falon, wai su zanta, daga inda nake tsaye nake qare masa kallo da wassafa tsananin muninsa da ban tava gani wani mutum mai shi ba a duniya. Ba a iya baqi kawai ya tsaya ba, irin sangamemen mutanen nan ne masu qaton tumbi. Ji nake kamar na je na shaqe shi saboda baqin ciki, wai kyakkyawar mace da ba ta rasa manema ba ce za a nakasa mata rayuwa a haxa ta da wannan mutumin? Saboda vacin rai kasa ci gaba da kallonsu na yi na koma gefen gado na zauna tare da zuba tagumi.

Tsayin lokaci sai ga ta ta dawo, wai sai a lokacin ta samu sararin zubar da hawaye, na zuba mata idanu kawai don ban san me zan ce mata ba.

Maganar ke nan, tsananin haquri da zurfin ciki irin na Ummukulsum ta haqura da zavin Daddy. Abin da muka lura da shi auren kuxi ne ya ke shirin yi da Ummakulsum, wato kuxin da ya gani a hannun Alhaji Shamawilu ya sa idanunsa suka rufe ya kasa ganin haqqinta da ya kamata a ba ta.

Manyan motocin da yakan zo da su, da kuma hidimar da ya ke yo wa idan zai zo ya sa na gane hakan, sai dai fa duk abin da ya kawo wa Ummakulsum ba ta amfani da shi, Hajja Fannah ke karvewa, abin da ba ta sani ba daga ni har Kulsum xin ba ma maraba da duk wani abu da zai fito a hannunsa.

Wasa-wasa sai maganar sa rana ta taso, duk da har lokacin Kulsum ba ta shaqu da Alhaji Shamawilu ba, hasalima duk lokacin da zai zo sai ya haddasa mata damuwar da sai ta kai ta ga zubar da qwalla. Ba na ganin laifin kowa sai nata, tunda ba ta sonsa me zai sa ba za ta fito filo ta faxa masa ba, ko kuma kacokam idan ya zo ta qi tsayawa da shi? Shi ya sa ko na ganta tana matsar idanu ba na nuna mata damuwa, duk da a zahiri ina jin na fi ta jin tsanarsa, musamman da kallon rainin da ya ke yi min, don akwai wani zuwa da ya yi an sa na kai masa abinci, ban damu da sai na gaishe shi ba na ajiye abincin na juya zan fita na tsinkayo kakkaurar muryarsa mai kama da ta ‘yan maye, ko qauraye yana faxin, “Ke Hani ki ke ko wa? Zo nan!”

Na ba shi girma na dawo na tsaya a gabansa, idanuna a qasa saboda na kasa jure doguwar hararar da ya ke auno min da manyan idanunsa masu kama da jan gauta don kaxawar da ke cikinsu launin ja.

“Ke wace irin yarinya ce mara tarbiyya da har za ki gan ni ba za ki gaishe da ni ba?”

Na xago fuska a xaure na yi masa kallo xaya na xauke kai, “Au na manta, barka da wuni”.

Wani dogon tsaki ya ja, “Je ki da tsiyarki ba na so”.

Na maimaita kalmar ‘tsiya’ da ya ambata min, da bai kai girman da ya ke a kai ba da na mayar masa da martani, amma tilas na shanye na kwashi qafafuna na yi gaba, ina jinsa yana bina da qananan maganganu.

Tun daga wannan rana muka xaura zaren tsama tsakani na da shi, zuwa goma zai yi bai ishe ni kallo ba ballantana na gaishe shi, in ba Daddy ko Hajja ke kusa ba. Musamman da na lura rashin gaishe shi xin ya fi yi masa ciwo fiye da rashin fara’ar da ya ke gani a tare da ni.

Na dawo a gajiye ranar da muka gabatar da jarabawar biology, wadda ita ce jarabawa ta uku da muka yi cikin wadda muke yi ta Waec, ina shiga falon gidan na tarar da Kulsum tare da wani mutum, kallo xaya na yi masa na so shaida fuskar duk da a zamanin quruciyata kawo lokacin ban tava ganinsa ba sai a ranar. Na gaishe shi zan wuce xaki Kulsum ta kira ni, na dawo na zauna. A nan ta ke shaida min, wai qanin Ummanmu ne Uncle Sunusi Umman ta turo ya zo duba mu. Allah Sarki, ai sai na kasa shiga xaki, na rashe muna kwasar hira da shi. Mafi akasari tambayoyi nake masa game da ‘yan uwanmu na Maiduguri tare da Ummanmu, a nan ya ke shaida mana wai Umman ta yi aure, tana can Keffi ta jihar Nasarawa.

Jiki na ya yi sanyi, na sa a raina Umma ta manta da mu shi ya sa har ta yi aure ba mu sani ba, ga shi da ma a lokacin mun jima ba ma samun lambarta. Da wayarsa ya kira mana ita, sai dai sun kaxa sun raya a kan na karvi wayar mu yi magana na qi. Ina jin muryarta da ya sa a handsfree tana roqon na karva mu yi magana, amma na yi biris da ita wai ni fushi nake. Sai Kulsum ce suka sha hira, amma wai don zurfin ciki sam ta kasa sanar da Umman hidimar bikinta da maganar ta taso gadan-gadan don har rana an saka. Ina zungurinta da qafa alamar ta sanar da ita, ta qi.

Daddy ya dawo ya tarar da Uncle Sunusi suka gaisa, har ya bar gidan bai yi masa maganar bikin Kulsum ba, kamar yadda ni ma na kasa zantar da shi. Ya tafi bayan ya ba mu kuxi don yin hidimar yau da kullum.

Bayan tafiyarsa na hau Kulsum da mitar me ya sa ta kasa sanar da shi halin da a ke ciki, idan ta qi faxa wa Umma saboda kunyar mahaifiyar mu ce? Tana buxa baki sai ta ce min, “Ke me ya hana ki sanar da shi?”

Sai na ja baki na na yi gum.

Ranar da za mu fara jarabawar Neco ne Xausiyya matar Yaya Madu ta haihu, don zalunci irin nasa mu da muke karere wai sai ya ce na koma gidansa har a yi suna na dinga taya matarsa aikace-aikace. Allah ya sani ban so hakan ba tunda ba wani xasawa muke da Xausiyyar ba, domin ba a ba mu muhimmancin da za ta kalle mu da daraja ba. Babu yadda zan yi tilas bayan na dawo daga makaranta na haxa kaya na tafi gidan nasa.

Na zama kam tamkar baiwa, da abin da ya isa da wanda bai isa ba duk ni ce ke yi, sai dai danginta su zo su sha wuninsu su tafi, wannan ya sa ban samu sukunin karatun jarabawa ba, don ma Allah ya sa ba za mu sake yin wata ba sai bayan suna da kwana biyu, amma dai aqalla tunda jarrabawar Turanci za mu gabatar ya ci a ce na karantu sosai, ba na jin chemistry da za ta biyo baya, saboda duk cikin darussanmu ba wanda na fi qwarewa a kansa kamarsa.

Kwanana uku da zuwa gidan, da daddare ina rungume da jaririyar ina xaura mata pampers, Xausiyyah kuwa na zaune a gefen gado tana gabzar nama, kusan a nan ta fi qarfi don tunda a ka yi haihuwar kullum sai Yaya Madu ya siyo nama, har mamaki nake yadda ta koma kamar Kura. Abin ban haushi, haka za ta sa kular naman tana ci idan yawuna zai tsinke sau dubu ba ni da arziqin da za ta xauki tsoka xaya ido qarnan kai ta ba ni, da ya ke ma naman ba ma’abocina ba ne ko a farcena. Muryar Yaya Madu na jiyo a falo yana kwaxa min kira, na amsa murya qasa-qasa saboda na san Xausiyyah ba ta son hayaniya, ta ma yi min gargaxi idan ina kusa da ita na kiyaye xaga muryata. Yadda ya ci gaba da kiran nawa ne ya sa na gane bai amsawar da nake ba, jiki na kyarma na xora jaririyar a kan katifarta ba tare da na sa mata wando ba, cike da tsoron Xausiyyah za ta iya dakatar da ni saboda yawan tunzurinta, amma har na fice ba ta ta tanka min ba.

Su uku na tarar a falon, wato shi Madun da abokansa guda biyu, wanda duk ba za su wuce sa’anninsa ba. Na rusuna ina gaishe su suka amsa, yayin da shi kuma ya zarce da cewa, “Kawo musu babyn kuma ki kira Madam su gaisa”.

Na juya ke nan zan tafi na jiyo xaya a cikinsu na cewa, “Kai Madu anya ba gurinka zan lallavo na samu iri ba?

Gaba na ya yanke ya faxi, sai dai ban samu damar juyawa ba ballantana na tantance wanda ya yi maganar ba, illa iyaka sautin muryar ya zauna a kwanyata.

Na sanar da Xausiyyah saqon Yaya Madu, sannan cikin hanzari na shirya jinjirar, kafin lokacin tuni Xausiyyah ta fice daga xakin. Na fito rungume da yarinyar a hannu na, na yi tsaye sororo a nufina Ya Madu ko Xausiyyah wani ya karve ta ya miqa wa baqin don kiyaye haqqin addinina, amma sai suka yi shaqulaton vangaro da buqatar da fuska ta ta nuna. Xaya a cikinsu ne ya taso ya karvi yarinyar yana faxin, “Fara ba ni ita ni da na saba xaukar xiyan kaina, su o’eh kuwa sai a zama karere’.

Dariya xayan ya yi yana faxin, “Oho dai wataran jariri ai ango ne”.

Jin wannan furucin ya sa na gano shi ya yi wancan zanen na farko, don haka na xaga kai a hankali na saci kallonsa. Fari ne tas, mai yalwar gashin fuska (qasumba), doguwar fuska da dogon hanci tare da xan qaramin billen da ke gefen kuncinsa da ya yi baqi sidik su suka qawata kyan fasalinsa. Ta vangaren siffa kuma yana da daxin kallo, sai dai zuciyar ce ban sani ba, tunda abu ne a duhu. Qwarai duk da ban iya tantance na kai tsaikon da zan faxa komar soyayya ba, amma na yarda matashin ya burge ni a kallo xayan da na yi masa, kamar an daskarar da ni a gurin haka na tsaya, duk da kaina a qasa ya ke, amma zazzaqar muryarsa da suka tsinke hira shi da Xausiyyah tana ban qaye a zuciya ta.

A cikin taqaitacciyar hirar da suke yi xin ne na tsinkayi sunansa, wato Almustapha.

“Ikon Allah, Ummahani yaushe ki ka shigo birni ne?” Ya Madu ya jeho min tambayar da ban san inda ta dosa ba.

Na xan yi ajiyar zuciya tare da motsawa ba don zan furta wani abu ba.

Almustapha ne na ji ya ce, “Daxina da kai Madu zaurance, ga shi kai ba Bahaushe ba ballantana na ce babu mamaki… wannan zaurancen naka ai ko tsofaffi zai yi wahala su fahince ka bare Ummahani”.

Ya ce, “Ah to, idan ba wadda ta baro qauye ta zo birni ba, yaushe za ta maida mu talabijin?”

Suka yi dariya, ni kuma sai a sannan na gano manufarsa, ba wai na maida su talabijin xin ne kaxai qorafin ba, har da rashin kawo abin motsa baki. Da sauri na juya na je na shiryo drinks a babban faranti na kawo na girke musu. Kai tsaye na koma xaki na barsu suna ci gaba da hirarsu, ko da na koma xakin cikin wani sabon yanayi na tsinci kaina da ban tava kasancewa a makamancinsa ba. Almustapha ya tsaya min a rai, yadda ya dinga zaro zance lokacin da suke hira da Xausiyyah, abin burgewa ne ko ba ma haka ba, ni dai kawai na ji ya burge ni, yanayin kwalliyarsa da siffarsa sun qayatar da ni matuqa. Daga xakin ma ina jiyo sautin muryarsu suna hira, mafi akasari tsiya suke yi masa na wai ya tsofe a gida bai yi aure ba, don haka sai dai ya dinga zarya a gidan abokai yana ganin qwansu.

Can suna hirar na jiyo muryarsa yana cewa, “Madu, Allah da gaske nake na ga matar aure na a gidanka, kada ka yi min halin naka na buqulu”.

Wani daxi ya saukar min a zuciya jin shi da kansa ya taya sona. Na lumshe ido cikin jin daxi, ina kuma qara nutsuwa don jin amsar da Ya Madu zai ba shi.

“Ka ga malam, nan ba gidan neman matar aure ba ne, sai ka bari idan ta koma gidansu ka bi ta can”.

Sam ban ji daxin amsar nan ba, haka kawai sai na ji haushinsa ya kama ni, rayuwa ke nan idan a ka ce ‘yan ubanci ya ratso tsakani, to komai fa za a yi sai an sako ‘yan ubancin nan, abin da na raya a zuciya ta ke nan, domin na tabbata da Umma Jamila ce ni ba zai yi wannan furucin ba. Haushinsa da na ji ya sa ban qarasa jin hirar tasu ba, saboda dogon tunanin da na tafi, sai hayaniyar sallamarsu na ji alamar za su tafi ke nan. Sai na ji kamar na miqe na je mu yi sallama don kawai na qara kallon Almustapha, amma babu damar hakan.

Da ya ke Allah ya qadarta sai mun sake haxuwar, sai ga shi Ya Madu ya qwalo min kira, jiki na har rawa ya ke na ma manta na saka hijabina, zuruf na yi waje.

“Xauki yarinyar nan ki maida ciki”. Ya ce da ni yana nuna min yarinyar da ke kan kujera.

Sarauta! Wai Xausiyyah ba za ta iya shigowa da ita ciki ba, kodaya ke gaba ta kai ni gobarar titi a Jos, Almustapha da ke tsaye yana qare min kallo ya ce, “A’a Madu, gaskiya kada ku maida min mata baiwa”.

Daxi da faxuwar gaba suka same ni, na sunkuya da sauri na xauki yarinyar daidai lokacin da Madun ke cewa, “Au ba ka ji abin da na ce maka ba ke nan? To ni dai ba ruwana idan Daddy ya rufe ka a cel”.

Don na ji amsar da zai bayar, sai na kama tattare bargon da yarinyar ke ciki.

“Umh, ai na faxa maka ba na tsoron xauri in dai a kan yaqin neman matar aure ne, ballantana ma na san ina da hope Daddy zai ba ni aurenta… Ummahani ko ba kya sona?”

Ji na yi kamar ruwan zafi a ka kwara min a jiki. Ai ban san lokacin da na yayimi yarinyar na nufi qofa ba. Su duka dariya suke yi, xayan mutumin mai amsa sunan Auwal ya ce, “Ka gani za ka firgita ‘yar mutane”.

Madu ya ce, “Qyale mara kunya, a haka za a xauki ‘yar a ba shi bai ganin babban yayanta da qima?”

“Kai dai a yi sha’ani, watarana ma da kai za mu je zance”.

Iya nan kawai na ji na fice, sai ganin Xausiyyah na yi ta shigo xakin, alamar sun tafi ke nan.

Kwanakin da suka biyo baya sun biyo min da sassaqa min zaruruwa da yawa, babban zaren da ya fi armashi da girma a gare ni bai wuce kambaba kamalar Almustapha da zuciya ta ke yi ba, wanda ko shakka ba na yi na faxa tarkon sonsa, abin da bai tava faruwa a quliyar rayuwa ta ba. Wani abu mai shayar da mamaki da ya zamo shi ma wani zaren mai zaman kansa a cikin zaruruwan da suka ratso kwanakin haxuwa ta da Almustapha, bai wuce yadda na samu sassaucin xaure fuska da hantarar da Ya Madu ke min ba, har ita Xausiyyar ta sassauta matsa min. qarshe ma ana jibi suna suka zaunar da ni a falo suna zantar da ni saqon Almustapha na cewar yana sona. Kunya dai kam ta gama lulluve ni, wai ni ma na shiga sahun da za a kafa tarihin soyayya.

“Almustapha, xa ne ga Alhaji Faruk, su mutanen jihar Kano ne a qaramar hukumar Minjibir, amma suna zaune a cikin birnin Kano. Shi ne xa na uku a gidansu, ya yi karatu tun daga matakin firamare zuwa jami’a, a yanzu haka yana aiki da ma’aikatar tsara birane ta jihar Kano. Tsayin shekarun rayuwarsa talatin da biyar bai tava aure ba, amma dai yana da ‘yammata da yawa waxanda mafi akasari su ke wahalar sonsa”.

Yaya Madu ya ke min wannan fashin baqin game da asalin Almustapha, na yi muqus kawai ina saurarensa, ina kuma qara samun yaqinin na soma bankwana da matsalar rayuwa ta vangaren zuri’ata. Na ji qosawa mu haxu da Kulsum na fesa mata wannan albishir, ba ma ita kaxai ba, xabi’ar tawa ta surutu ta zabaro ba har qawayena irin su Surayyah da su sun daxe da shiga fagen. Kawai buri na mu haxu na zantar da su na yi saurayi.

“Almustapha, ya kamu da sonki ya shaida hakan a gabanki, ya kuma qara tabbatar min, ina da yaqini ki ka aure shi ba ke kaxai ba, mu kanmu sai mun dara, domin duk da kasancewarsa matashi ba qaramin hamshaqi ba ne, haka mahaifinsa”.

Ya qara cewa da ni yana kallo na.

“Saboda haka ina umartarki ki amince da shi, ki karve shi da hannu biyu, ba ruwana da kina sonsa ko ba kya sonsa”.

Wannan furucin ya ba ni mamaki duk da a lokacin ban fahinci inda ya dosa ba, amma a gani na har sai an ba ni umarni na karvi Almustapha? Kodaya ke don ba su san yadda na kamu da sonsa ba ne. suka gama kambaba Almustapha, suka sallame ni.

Ranar suna yarinya ta ci suna Ummulkhairi, dangi kowa ya zo, har Ummukulsum da na fi kowa farin cikin zuwanta. Ana ta shagalin suna, na janye ta muka shiga xakin da na sauka ina ta fara’a na ce, “‘Yar uwa albishirinki”.

Ta kafe ni da ido, ba tare da ta tanka ba. Ni ma sai ban damu da tankawar tata ba, na ci gaba da cewa, “Na fa yi saurayi”.

Kawai sai na hau zayyana mata yadda muka haxu da Almustapha da abin da ya gudana. Allah sarki, sai ganin qwalla na yi na bin kuncinta. Rana ta farko da ta zantar da ni wani labari game da sha’anin aurenta.

“Ke mai sa’a ce Ummahani, an ba ki damar zaven mijin da ki ke so, ya kuma cancanta ki aure shi. Amma ni an haxa ni da mutumin da ko da qwayar zarra ban tava jin sonsa a raina ba”.

Tsananin tausayinta ya kama ni, har na ga wautata na zumuxin ba ta labarin nan. Na dafa kafaxarta cikin sanyin murya, na ce, “Ki yi haquri ‘yar uwa, ba manufata na xaga miki hankali ya sa na ba ki labarin nan ba. Wallahi ba ni da wata manufa a zuciya ta…”

Ta katse ni tana girgiza kai, “Cool down ‘yar uwa, ba ke nake kallo ba, Daddy nake hange. Ya tauye min haqqi ba tare da ya duba irin rayuwar quncin da zan yi da mutumin da ba na so ba. Na sani ba ki da masaniya har Almustapha ya je sun gana da Daddy, kuma ya yi na’am da shi”.

Na zaro idanu duk da farin ciki ya kama ni, amma a jallin da muke kai tilas na sakaye farin cikina, na ce, “Yaushe a ka yi hakan?”

Ta cije baki alamar wani abu na yi mata yawo a zuciya, “Shekaran jiya suka je shi da Ya Madu, dukkan gidan sun amince da maganarsa. Da farko na yi tunanin ke ma irin tawa za a yi miki wato auren dole, amma a yadda na same ki cikin shauqi na gane da amincewarki, ni ce kaxai Daddy ba ya so shi ya sa ya zavi nakasa min rayuwa ta hanyar haxa ni zama da Sham…”

Ta kasa qarasawa sakamakon kukan da ya ci qarfinta. Na yi shiru ina kallonta tsayin lokaci, kafin na ce, “Tun farko laifinki ne Yaya Kulsum, domin da a ce da a ka yi miki maganar haxa ki aure da shi kin bijire ina ganin da yanzu an bar maganar”.

Ta ce, “Har yanzu ba ki ganewa Ummahani, kin sani Daddy mutum ne mai tsattsaurar aqida, tunda ya ce zai haxa ni da mutumin nan, to ko wane bore zan yi ba zai fasa ba… ni takaicina xaya da na fahinci ba don Allah ko don kyawawan halayensa za a aura ni gare shi ba, sai don abin hannunsa. Shi ma da ya ke ya san da hakan shi ya sa har yanzu ya kasa gani na da qima, kada ki so ki ji fa irin wulaqanci da gorin da ya ke yi min, wai kuturu da kuxinsa alkaki sai na qasan kwano, me ya ke nufi da hakan? Manufarsa fa tunda yana da kuxi mace sai wadda ya ga dama ya aura… ga shi na fahinci qaton jahili ne, bai damu da ibada ba… ke kacokam ma zan iya cewa da qyar ne idan zai iya kawo fatiha cikakkiya”.

Da sauri na ce, “A’uzu billahi, gaskiya Yaya Kulsum mu yi wani abu a kai… kawai ki kira Uncle Sunusi tunda muna da lambarsa ki faxa masa duk abin da ke faruwa in ya so sai ya sanar da Umma ta zo ta ruguza auren”.

Shiru ta fara yi, da alama ta tafi dogon tunani. Can ta sauke gwauron numfashi, ta ce, “Ko na sanar da Uncle Sunusi babu abin da hakan zai haifar illa cavewar lamari. Ni na sadaukar da rayuwa ta, da ma can haka Allah ya tsara min, farin cikina da ke za ki tsira da son da ki ke yi wa mijinki”.

Allah ya sani ba qaramin tausayinta na ji ba, a haka na yi ta rarrashinta da faxa mata maganganu masu daxi, na samu ta xan nutsu sannan muka koma cikin sha’anin sunan. Daf da magriba ta tafi gida, ta bar ni cikin alhini.

Da daddare bayan kowa ya watse sai dangin Xausiyyah na jiki-jiki, waxanda za su yi soye washegari, suna xakinta suna ta lissafin abin da ta samu, ni kuma ina falo tare da wasu qannenta ‘yammata guda biyu. Yaya Madu ya shigo falon fuskarsa a washe, muka yi masa sannu da zuwa ya amsa tare da ce min, “Ki je waje ga Almustapha can yana jiranki”.

Iya abin da ya ce ke nan ya shige xakinsa.

Duk wani qunci da nake ciki sai na ji ya gushe, haqiqa ba qaramin tasiri Almustapha ya ke da shi a gare ni ba. Na tashi na shiga xaki na xan murza mai da hoda, na sake kayan jiki na na fita.

Tsaye na hango shi jingine a motarsa, ya yi shigar farin yadi toyobo, xinkin zamani hannun mai links, ya manna qaramin farin gilashi a idonsa. Shigar ta yi masa kyau sosai, kwarjininsa ya sake fitowa, na qarasa inda ya ke tare da sallama. Ya amsa min cikin zazzaqar muryarsa.

“Ranki ya daxe, barka da hidima”.

Kaina a qasa cikin fariyar an ba ni matsayin da ban tava samu ba, na ce, “Yauwa, na gode”.

“Sai ki ka gan ni kamar daga sama ko?”

Ya ce da ni, sai na rasa bakin magana.

“Kin san komai muqaddari ne daga Allah, malama Ummahani Allah ya yi ikonsa a gare mu, Ya kimsa min qaunarki a zuciya ta ba da wasa ba daga kallo xaya, tun a rannan na sanar da ke, na kuma sanar da babban Yaya, kin dai ji irin amsar da ya ba ni. To ban yi qasa a gwiwa ba na dangano ga Daddy, kuma Allah ya ba ni sa’a ya amince min, shi ne na ce bari na yo tattaki na ji ra’ayin uwar gayyar”.

Ya yi shiru yana sauraren cewata, ni kuma sai na kasa magana, ga shi dai ni kanuri ce ballantana na ce kunyar fulani ce, amma dai a al’adance na sani zaqe wa namiji ba kyakkyawar xabi’a ba ce, shi ya sa na zavi yin shirun.

“Don Allah ki furta min wani abu, ina so mu gina kyakkyawar mu’amala ta fahintar juna don mu ji daxin kasancewa tare a inuwa xaya”.

Kai tsaye maganar Kulsum ta faxo min, da ta ce ta ji daxi da ta same ni cikin shauqin qaunarsa, bai kamata na noqe ba, ko ba komai tunda ni na samu gatancin zava min nagartaccen namiji kamarsa lto ya dace na ba da kai bori ya hau. Cikin sanyin murya na ce, “Na gode da qaunarka gare ni, Allah ya tabbatar mana da alkhairi”.

Da fara’arsa ya amsa, “Amin summa amin, wallahi har na ji daxi, saboda ba na son na takura wa mutum, wannan shi ya sa na kasa samun tsayayyiyar mace, kullum gani nake duk wadda zan tunkara da sunan soyayya to takurata zan yi ta yi min alfarma ta dinga kula ni don dole”.

Nan dai Almustapha ya kashe ni da daxaxan kalamai, na ji qwarai ni xin mai sa’a ce, Allah ya dubi maraicina da zuciya ta Ya haxa ni da mutumin da ya dace da rayuwa ta savanin Yaya Kulsum da za a yi wa auren dole da mutumin da ko da a mafarki bai kamace ta ba.

Sai dab da sallar isha’i ya yi min sallama da zummar zai sake dawowa bayan kwana biyu. Na koma cikin gida cike da nishaxi.

Washegarin da a ka yi soye na yi tunanin idan na dawo jarrabawa zan koma can gidanmu, kafin na tafi sai da na shirya komai nawa. A makarantar kafin mu shiga xakin jarrabawa cikin zumuxi na dinga ba wa qawayena labarin haxuwa ta da Almustapha, har magana ta isa kunnen Daddy. Dariya suka dinga yi min, ni kaina na fahinci suna yi min kallon gaula mara sirri, amma ya na iya? Musamman Surayyah wadda ta kasa voye maitarta sai da muka fito jarabawar muna tafiya kan hanyarmu ta komawa gida, ta dube ni tana faxin, “Ummahani, don Allah in tambaye ki?”

Na xan ba ta nutsuwa ta, “Ina jinki”.

Ta ce, “Wai ke wace irin mutum ce? Na lura kullum rayuwarki qara tavarvarewa ta ke, maimakon ki qara hankali sai ragewa ki ke…”

Na katse ta, “Da a ka yi me ke nan?”

Ta ce, “Au ba ki ma san abin da a ka yi ba?”

Da gaske ban sani ba, sai na yi mata shiru.

“Na lura ke ba ki da sirri, kuma wallahi wannan xabi’ar taki sai ta jaza miki matsala, haba me a ke da mai irin halinki, da abu ya faru har rawar baki ki ke ki fesa wa mutane ko tara ba ki yi? Ba ki la’akari da kowa yana riqe sirrinsa, ai ba a yi ciki don abinci kaxai ba, ko’ina fa da fansar Kura sai garin da ba awaki, ya kamata ki san da wannan”.

Qwarai na ji haushin Surayyah, domin sai nake ganin kamar tana cin fuska ta ne, tunda an ce a wasandare a ke gaya wa wawa magana. Ai kuwa na zumvuri baki, “Kawai ki fito fili ki ce na tsare miki guri, ba ki tsaya xan waken zagaye ba…”

Ta katse ni ta hanyar dafa kafaxuna, “Allah da gaske Ummahani ba na jin daxin yadda ki ke barbaxa sirrinki, yanzu saboda Allah ina Ramatu Shehu ta ke da sirrin da za ki kwashi sirrinki ki faxa mata?”

Na ce, “Daxin abin ba mutuwar auren mahaifa na na faxa mata ba, illa labarin Almustapha, ai ko ian da halacci abin farin ciki ne ya same ni da ya kamata na faxa wa kowa ya taya ni murna”.

Ta yi murmushi, ta ce, “Uhm, ba ki san duniya ba, kina raina sanda a hannun makaho bayan shi kaxai ya san amfaninta a gare shi. Bari ganin Almustapha saurayinki ne a yadda duniyar nan ta sauya ba wani abu ne mai wahala ba qawarki ta qwace miki shi”.

Sai kuma jiki na ya yi sanyi, na fahinci manufarta.

“Na sha karanta littattafai da irin hakan ta faru, kuma ke kanki kin san littattafan nan hannunka mai sanda ne, don haka ina ba ki shawarar ki rage faxar sirrinki”.

Cikin rashin kuzari na ce, “Wallahi haka Allah ya halicce ni, komai nake son voye wani abu da ya shafe ni ba na sanin lokacin da zuciya ta ke ingiza ni fesawa, ki taya ni da addu’a Allah ya raba ni da wannan halin”.

Ta ce, “To amin”.

Na koma gida da xokin zan koma gidanmu, amma sai na samu saqon Ya Madu wai sai nan da kwanaki biyar zan koma idan ya dawo daga Abuja. Raina ya vaci matuqa don ina son gani na kusa da Kulsum don na san ba ta cikin nutsuwarta, aqalla idan muna tare na rage mata damuwa, sai dai babu yadda zan yi, ga shi lokacin bikin na qaratowa, don bai fi sati uku masu zuwa ba. Haka na daure zuciya ta, sai dai ita kanta Xausiyyah ta fahinci ban so zaman gidan ba.

Kwanaki biyar xin nan sai suka zama kamar tsanin havaka soyayya ta da Almustapha, domin ba a kwana a wuni ba tare da ya zo gidanmu ba, inda ma abin ya rage armashi rashin waya a hannu na. Ya so ba ni ma ni ce na qi yarda saboda gudun abin da za ta ja min, na ce ya bari sai na koma gida ya tambayi Daddy idan ya amince shi ke nan.

Ranar da Ya Madu ya dawo da daddare na samu kaina cikin farin ciki da xokin gari ya waye na koma gida. Washegarin kuwa ban samu wata matsala ba, shi da kansa ya ce na shirya ya maida ni. Lokacin da muka isa mun tarar da baqi, wai an kawo lefen Kulsum, kaya na garari sai ka ce za a buxe shago. Tun a nan na qara tsinkewa da lamarin, ba shakka sayen Kulsum Alhaji Shamawilu ya yi, ban da haka yaushe zai jibgo waxannan himilin kayan?

Wani abin takaicin daga ni har amaryar kayan ba su xaxa mu da qasa ba, tunda da ma ba sonsa muke ba. Ana ta zazzagewa ana gani da surutun Kulsum ta yi goshi, mu kuwa mun qule a xaki muna kwankwaxar madarar takaici.

Hidimar biki gadan-gadan, sauran sati xaya, an fitar da anko, wai don taya vera vari sutura kala xaya ya yi mana ni da ita, amma duk a banza, don ni ko da Almustapha ya tambaye ni anko ce masa na yi ba zan yi ba, ya yi nacin, ya yi qorafin. Qarshe sai Ya Madu ya samu da maganar, ya kuwa surfe ni tsab da rashin mutunci, shi da kansa ya karvo kuxi dubu talatin da sunan anko, amma mirsisi ya lamushe, ba ankon ba kuma kuxin. Da ma abin da ya ke yi wa ke nan.

Maganar gaskiya Alhaji Shamawilu na kashe kuxi a hidimar nan, don hatta kayan xaki cewa ya yi ko cokali bai lamunce a siya ba, wai shi zai yi komai, burinsa kawai ya auri Kulsum. Baiwar Allah ta yi laushi sosai, ta zabge, jijiyar goshin nan ta fito ruxu-ruxu, na lura da ita ba ta iya bacci da daddare, sai yawan nafilfili ni ma sai nake tayata, muka haxu muna rubdugun addu’ar Allah ya kawo sanadin da bikin nan zai tarwatse.

Duk hidimar nan da a ke babu dangin mahaifiyar mu ko xaya, daga Daddy sai danginsa da matarsa, matar da a ke iqirarin ba a sake ta.

Almustapha ne ya xauke mu karvo xinkunan bikin a can unguwar su Umma Jamila, gidanta muka fara shiga. A bakinta ma muke jin wai ashe har sadaki an kawo dubu xari biyar. Riqe baki muka yi don kaxuwa, kodaya ke Kulsum ta kai darajar da za a biya waxannan kuxaxen a matsayin sadakinta, sai dai duba da lamarin zai sa mu qara aminta da maganarsa, sayenta ya yi.

Da wannan mamakin muka karvo xinkunan muka dawo gida, amma ko a fuska Hajja Fannah ba ta nuna mana an kawo sadakin ba, da ma dai ba mu zaci haka ba. Ana sauran kwanaki biyar biki a ka kawo wasu mata daga can Maiduguri suka hau gyara amarya, a vangare guda kuma ga qatuwar garwa da a ka ciko da turaren wuta xan Maidugurin na asali, wanda shi kansa ya lamushe maqudan kuxaxe kuma Alhaji Shamawilu ne ya biya kamar yadda ya ke a al’adance idan za a auri kanuri sai an yi wannan hidimar.

An shirya fatittika tun sauran kwanaki huxu biki a ka fara. Ranar farko Almustapha ne ya kai ni, shi kam yana nuna farin cikinsa da auren Kulsum bai san yadda muka xauki lamarin ba, shi ya sa idan yana koxa Alhaji Shamawilu da hidimar da ya ke yi nake masa shiru, don ni ko maganar ba na so tana haxa mu saboda ina jin nauyinsa ne da tuni na taka masa birki.

Addu’ar yi muke amma dai da alama bikin nan mai tabbatuwa ne, domin saura kwana biyu xaurin aure, zuwa lokacin gidanmu ya cika ya batse da dangin Daddy da na Hajja Fannah, mun shirya da daddare don zuwa Arabian Night da za a gudanar a Royal Tropicana, nan Surayyah ta biyo min Almustapha ya zo ya xauke mu, ana fara shagali an kira ango da amarya su taka rawa, kana ganin Kulsum ka san cikin qarfin hali ta ke yin komai, ta yi min ma ba-zata don da ni ce ita ko zuwa fatin ba zan yi ba ko da za a tsire ni da mashi, da dai na jera da wannan mumunan mutumin a ce mijina ne.

Suna fitowa filin wajen, sai ganinta na yi ta girxe jiki ta faxi, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, hidimar da ba a qarasa ba ke nan, muka kwashe ta sai asibiti, wai suma ta yi, a ka ba ta gado.

Ni na kwana a wajenta ina ta zubar da hawaye da addu’ar kada ta mutu. Sai wajen biyun dare ta farfaxo, amma sakamakon allurar bacci da a ka sa mata a ruwan da ke shiga jikinta ya sa ta koma baccin. Washegari ta farka jikin da sauqi, Hajja Fannah ta zo asibitin ni kuma na koma gida don ramakon baccin da ban samu ba.

Sai misalin sha biyun rana na farka, a gaggauce na shirya na koma asibitin, a lokacin ne na ji wai zuciyarta ce ke neman kamuwa da matsala saboda damuwar da ta sa a ranta, har jininta ma ya soma hawa. Don rashin tausayi irin na Daddy, Kulsum na gadon asibiti amma ba a fasa hidimar bikin ba, qarewa ma an xaura auren! Kuka kuwa mun sha shi kamar me.

Sai bayan xaurin aure da kwanaki biyu a ka ba mu sallama, kuma wai a ranar a ka wanke ta sai xakin mijinta inda za su yi sati biyu sannan su wuce Ilori.

Sam ban iya bacci ba a ranar, tunanin halin da ‘yar uwa ta ke ciki ya addabe ni, na qara gaskata Daddy da Alhaji Shamawilu sam ba sa qaunar Kulsum, na yi mata addu’a Allah ya saka mata zaluncin da a ka yi mata.

Washegari ina ta xokin zuwa Giginyu inda gidan ya ke, mirsisi Daddy ya hana ni zuwa. A taqaice sai da a ka kwana biyar sannan muka je ni da Hajja Fannah. Babu wani ci gaba da a ka samu, ashe tunda a ka kai ta ba ta qarasa warwarewa ba, ga tulin ayyuka domin kullum sai ya zo da abokansa wai cin girkin amarya, don haka ta qara susucewa.

Tana gani na qwalla ne ke shatata a idanunta, ni ma haka, amma Hajja Fannah sai masifa ta ke zubawa.

Mara kunyar da ya tarar da mu wai sai ga shi durqushe gaban Hajja yana faman zuba godiya, ku ji fa! Mutumin da ko a fuska an san idan bai girmi Hajja ba, to za su yi tsara a shekaru, amma shi ne zai dinga qasqantar da kai a gabanta saboda tsabar munafunci, kuma a gabanmu sai naniqe wa Kulsum ya ke, ni don haushi ma tashi na yi ina tambayarta inda banxaki ya ke.

Da muka tashi dawowa ya xauko dubu goma ya ba Hajja, ni kuma dubu biyar, amma duk ita ce ta karve. Har mamakin mutumin nake, sam ba ya jin zafin kuxi.

Bayan sun cika sati biyun kuwa suka tarkata suka koma Ilori tare da rakiyata ni da Umma Jamila, Hassana matar Yaya Bakura sai Hajja. Kwanannmu uku a can muka dawo.

Washegarin dawowarmu sai ga Umma ta dira gidan a firgice, ko bi ta kaina ba ta yi ba ta hau yi wa Daddy da ke zaune a falon qorafi.

“Wannan wulaqancin har ina, a ce in haifi ‘ya da cikina saboda tsabar zalunci ka aurar da ita ba da sanina ba? Me ka ke nufi, ko kai kaxai ke iko da ita ne?”

Tana maganar cikin xaga murya kamar numfashinta zai xauke.

Kallon da ya ke yi mata zai nuna ko a jikinsa, ya ce, “Ashe ke zan bi ba ke ce za ki bi ni ba?”

“In bi ka a kan me?” Ta faxa, “Kana tunanin ka kai matsayin da zan dauwama da kai a raina? Allah ya sauwaqe min wannan vatan basirar, cuta ce dai ka cuce ni, kuma Allah ya isa ban yafe ba. Maganar ‘yata kuwa ka faxa min inda ka kai ta”.

“An qi a faxa mikin, kuma wannan ya zamo na farko na qarshe kada ki sake tako min gida, mara mutunci kawai. Ke har kin isa ki zo gidana kina min Allah ya isa?”

Ta yatsina baki, “Gidan banza? Allah ya isa kuma ba zan daina yi maka ba har qarshen numfashina…”

Wuf! Ya tashi zai kai mata duka, Hajja Fannah ta yi saurin shiga tsakani tana faxin, “Ka rufa mana asiri Alhaji, ni kaxai nake da takaici idan ka tava wata mace ba ni ba… ke Yagana don Allah ki fita daga gidan nan”.

Wata tsawa Umma ta daka mata, tare da cewa, “Rufe min baki baqar munafuka, duk abin da ya samu shamuwa ai watan bakwai ne ya ja mata…”

Hajja Fannah ta buxe baki, “A’a’ah, yi a sannu Yagana, ni kishin mijina nake ba kuwa za ki ja masa faxa wa halaka ba”.

Haka Umma ta fice daga gidan, ina son binta mu yi magana amma Daddy ya zabga min mari tare da kora ni ciki, na shige xaki ina rusar kukan baqin ciki, ina fama da quncin zuciya, Allah ya sa ma Almustapha ba ya gari, washegarin da Umma ta zo ya zo gidan yana sanar da ni tafiyar gaggawa ta same shi zuwa Abuja, za su yi sati xaya. Sai dai duk da a uzurce ya zo min sai da ya fahinci akwai abin da ke damuna, ya tambaye ni na ce masa kawai kaina ne ke ciwo. A haka muka rabu da shi, babu wadda na tsana a duniya irin Hajja Fannah, saboda dukkan matsalolinmu ita ce sanadi. Idan na kalle ta sai na ji kamar na shaqe ta har tunanin zuba mata shinkafar vera na yi ta ci ta mutu, amma tunanin makomata ya hana.

A cikin kwanaki huxun nan da na yi cikin damuwa babu wata kalma mai taushi da ke fitowa a bakinta da Daddy don tausasa zuciya ta, hasalima tsawa suke yi min, don Daddy ma har kusan dukana ya yi.

Ranar asabar da yamma na tafi islamiyya, a can muka haxu da Surayyah, sai dai wannan karon na yi qoqarin sakaye sirrina duk da qoqarin da ta yi na tuhumar abin da ke damuna ta gan ni cikin rashin sukuni, na ce mata babu komai.

Da muka tashi islamiyyar, sai na ji ina muradin kiran Uncle Sunusi don ya ba ni lambar da zan samu Umma, a karo na farko na ji kwaxayin mallakar waya tawa ta kaina ya kama ni. Dole ba yadda zan yi na nuna wa Surayyah ina son mu je gidansu Maminsu ta kira min Uncle xina.

Muna isa gidan ta xauko wayarta da a ka siya mata cikin satin, ta ce na kira shi da ita.

Na ce, “Lallali Surayyah ba ki da kirki, ashe har kin sayi waya ba ki sanar da ni ba?”

Ta yi murmushi, “Sorry qawata zancen ne bai haxa mu ba”.

Wannan fa duk yana cikin sirrin da ta ke nusar da ni na zamo mai voyewa, haka nan na karvi wayar da ma ina da lambarsa a kaina, na zuba a wayar na kira. Ringin xaya a na biyu a ka xauka, sai dai muryar mace na ji. Na gaishe ta, ta amsa.

“Ummahani ce daga nan Kano”. Na faxa.

Ta ce, “Allah sarki, cewa za ki ‘yarmu ce, to ya Kanon?”

Na ce, “Alhamdu lillahi, Uncle Sunusi fa?”

Ta ce, “Wato ko tambayar ‘yan uwanki ba za ki yi ba sai Uncle xinki ko? Anya Ummahani kina da zumunci? Duk gidan nan babu wanda bai san labarinku ba, amma ko sau xaya ba ki tava zuwa Adamawa wajenmu ba”.

Sai a lokacin na san Uncle Sunusi ba a Maiduguri ya ke ba, qwarai ta yi qorafi mai ma’ana, sai dai ya na iya tunda ba ni ke iko da kaina ba? Sai na yi murmushi cikin wayancewa na ce, “Ki yi haquri Aunty, insha Allah ina nan zuwa watarana”.

Ta ce, “Umh Allah ya sa”.

Na ce, “Amin”.

Ta ce, “Uncle xinki ya fita, kin san suna ta kacaniya game da qarar mahaifinki da suka shigar”.

Gaba na ya faxi, ido waje tamkar a gabanta nake, “Qara kuma?”

Ta ce, “Uhum, Ummahani lamarin mahaifinku ne gaskiya yana da son rai, ta ya zai aurar da ‘yar uwarki ba tare da saninmu ba? Ai shi ma ya san bai nemi zaman lafiya ba, don haka suka kai qararsa, a gobe ma shi Uncle xin zai shigo Kano saboda za a fara sauraren qarar”.

Duk da na san komai ya faru laifin Daddy ne, sai dai sam ban ji daxi ba da lamarin ya kai har ga zaman kotu, a tunanina tunda dai hakan ta riga ta faru to kawai a haqura da tada jijiyar wuya, a yi wa Kulsum fatan zaman lafiya a gidanta.

Duk jiki na ya yi sanyi, na ce, “Allah kyauta, idan ya dawo ki faxa masa na kirawo”.

Ta ce, “Okey, lambarki ce?”

Na ce, “A’a ta qawata ce”.

Daga can qasa-qasa na jiyo muryar wata na magana, Auntyn na cewa, “Allah ba zan ba ki…”

Wayar ta katse, haka nan sai na ji ina son yin magana da wadda ke son mu gaisan, ba mamaki daga cikin yaransu ne, tunda ta ce min kowa a gidan ya san ni, sai na sake kiran wayar. Ba Auntyn ce a layi ba, muryar wata budurwa ce cikin zumuxi ta ke cewa, “Ummahani ya garin ne? Ni ce Banan babbar ‘yar Uncle xinki”.

Daga jin muryarta ko ta girme ni ko kuma ni na girme ta, ko kai tsaye ma mu kasance sa’annin juna, bayan haka yadda ta yi maganar ya sa na sanya ta cikin ‘yan karaxi irina. Cikin jin daxi na ce, “Thank you, Banan”.

Ta ce, “Qila fa na biyo Daddy a goben”.

Na ce, “Ai kuwa zan ji daxi na ganki, da ma ina kewarku sosai”.

Ta ce, “Okey, wannan lambarki ce na sa a waya ta?”

Na ce, “A’a ta qawata ce, ni ba ni da waya”.

Da sauri ta ce, “Ayyah! To zan taho miki da waya har da layi sai mu dinga gaisawa”.

“To”. Kawai na ce mata, amma idan ba da sa hannun Daddy ba ba zan tava riqe waya a hannu na ba.

Ina sauke wayar na xora idanuna ga Surayyah da ta yi tsuru-tsuru, na miqa mata, “Godiya nake aminiyata, Allah ya qara buxi”.

Ta ce, “Amin”.

Na miqe da niyyar tafiya, ta yi saurin riqo hannu na, na juyo muka haxa idanu, ta ce, “Ummahani, na sani kina cikin damuwa, kuma na ji a waya kin ambaci kotu, ga shi har za ki tafi ba ki faxa min ba”.

Na yi murmushin qarfin hali na ce, “Kada ki damu Surayyah, matsalar family ce, kuma ke da kanki ki ka shawarce ni na dinga voye sirrina”.

Ita ma murmushin qarfin halin ta yi, “Wato har ni ma na shiga ciki?”

Na girgiza kai ina dariya, “Ba ki ciki Surayyah, ke aminiyata ce ta ta sosai, zan faxa miki amma sai gobe, kin ga yanzu na tauye hannu kada na ja wa kaina duka”.

Ta ce, “To shi ke nan, Allah ya kai mu goben lafiya”.

Muka fito falo, na yi sallama da Mami, Surayyah ta raka ni har qofar gidansu.

Washegari lahadi ina ta zuba idon ganin Uncle Sunusi da Banan sun zo, amma har yammaci ban ji xuriyarsu ba, ga shi Daddy a gida ya wuni ba ballantana na ce ko sun wuce kotun ne ba tare da na yi la’akari da yau xin lahadi ce babu zaman kotu ba. Sai da na qara nutsuwa na tuna da hakan.

Da naje islamiyya na sanar da Surayyah halin da a ke ciki, ita ma ta jimanta, ta kuma yi addu’ar Allah ya kawo sassaucin lamarin.

Ranar litinin da safe na gama haxa karin kumallo, ina zaune a falo ina jiran su Daddy su fito na sallame su na koma xaki, don qa’ida ne sai na haxa musu komai sun gama ci sannan nake barin falon.

Ina zaunen suka fito, Daddy a shirye cikin shiga ta alfarma kamar wanda za shi xaurin aure. Na gaishe su, suka amsa tare da zama suka hau karin kumallon ina rakuve ina jiran su kammala, na ji Hajja na cewa, “Wai da gaske ka ke Yallavai Lagos xin za ka tafi ba za ka je kotun ba?”

Ya ce, “Kin ji ki ke ma da wani zance, to na je kotun na ce musu me? Idan ita mahaukaciya ce shi ma alqalin mahaukaci ne? ni nake iko da ‘ya’yana ko ita?”

Tabxijan! Lallai shahalar wulaqancin Daddy ya kai qololuwar mizani, na ambata hakan a raina, wato ma ba shi da lokacinsu?

“Ai gaskiya Yagana ta yi wauta, ita a tunaninta akwai mai iko da ‘ya’ya sama da ubansu? To ko ni za ka wakilta na je?”

Ina kallonsa ya kyave baki.

“Rabu da su, mun gama magana da lauyana, ko zaman kotun ba za a yi ba Alqalin zai kore su”.

Ta ce, “Yauwa, ka yi min daidai, ai da ma qimarka a garin nan ya wuce ma a saurari wata qara da ta shafe ka, in ban da wawanci irin na Yagana ke da a ka rufa miki asiri duk mugun halinki ba a kai ki kotu ba sai ke ce da samun gurin kai wani?”

Cikin qosawa ya ce, “Don Allah ki bar maganar nan”.

Sai ya miqe tsaye, da ma na qosa su gama ko na bar falon, yana ficewa a gaggauce na kwashe kayan na kai kicin, na koma xaki na ina jinjina maganar da Daddy ya faxa, lallai na yarda kamar yadda ya ce yana canza xa bai canza mata haka xin ne, domin ga shi dai ya canza mu da Hajja Fannah.

Maganar ke nan, Daddy bai je kotun ba, ban kuma ga qafars su Uncle a gidan ba, na san vacin rai ne ya hana su zuwa. Na dai kasance cikin qunar zuciya wunin ranar. Duk abin da Hajja ta sa ni na yi mata cikin qunquni nake yi, har zagina ta yi tana faxin idan na ce zan yi mata nuqufurci za ta lallasa ni a gidan. Ni dai iyakata da ita ido da kunne.

Da daddare Almustapha ya zo, Allah ya sa a shirye nake, ban vata lokaci ba kamar yadda na san ba ya son jira, na fito harabar gidan na nufe shi. Yana zaune a kan farar kujerar roba, ya sanya yadi mai ruwan madara da sanduna a jikinsa. Na lura shi dai yana son manyan kaya, zan iya cewa tsayin haxuwa ta da shi sau xaya na tava ganinsa da qananan kaya.

Na ja xayar kujerar da ke gefensa na zauna ina murmushi, “Kai zumuxi ko huce gajiya ba za ka yi ba za ka kwaso jiki ka zo min?”

Na faxa cikin faxaxa fara’ar fuska ta.

“To ya na iya da raina Gimbiya guda, ai ko ba takalma an zo a ga lafiyarta, ballantana kwanaki xaixai har bakwai ban sa ki a ido na ba”.

Ya ce da ni shi ma da fara’ar.

Na ce, “Uhum, to barka da wuni, an iso lafiya?”

Ya ce, “Alhamdu lillah, ya na tarar da ke?”

Na xan yi far da ido, “Lafiya lau sai kewarka”.

Ya kalle ni ta gefen ido, “Kamar duka ke nan?”

Na ce, “Allah kuwa”.

Ya ce, “Da wace alama zan gane hakan?”

Na ce, “Hmh, ba ka yarda ba ke nan?”

Ya langwave kai, “To ya na iya, an ce xinyar makaho ta nuna a hannunsa”.

Ina jinjina kai na ce, “Ai kuwa. Amma an ce mai kaza a hannu ba ya jimirin ass! Amma dai ka yarda da ni, na yi kewarka sosai”.

Ya ce, “Na yarda, amma fa na barki cikin wani yanayi duk da kin ce min ciwon kai ne, sai dai ban yarda ba”.

Da a baya ne zan kwashe duk abin da ya faru na faxa masa, amma a yanzu nasihar Surayyah ta yi tasiri a gare ni, da kuma mazantakar da na nuna wa zuciya ta wajen riqe sirrina, ina dariya na ce, “Ko ma wane yanayi ka bar ni tunda yanzu ba ka tarar da ni a cikinsa ba ai ya wuce ko?”

Ya ce, “Ya wuce bai wuce ba, domin masoyan juna na haqiqa ayyukansu na farawa ne daga kula da halin da ‘yan uwansu suke ciki, farin ciki ko akasinsa”.

Na yi saurin cewa, “Ga shi kuma ban sanka da mita ba…”

“Wa ya sani ko ke ki ka koya min?” Ya faxa yana dariya.

Na ce, “Ai sai dai na koya a wajenka…”

Ya tare ni cikin kawar da maganar, “Shi ke nan, Allah ya dauwamar da farin ciki a rayuwarki”.

Na amsa da, “Amin habibi”.

Wani kallo ya ke yi min wanda ya ankarar da ni dalilinsa, wato sunan da ni kaina ban san ya a ka yi na lanqaya masa shi ba.

“Au yau har wani suna mai daxi a ka saka min?”

Kunya duk ta kama ni, na sunkuyar da kai ba tare da na ce komai ba.

Well, na ji daxi sosai My Hany”.

Ni ma sai na ji daxin taqaita sunan da ya yi duk da na ji kamar zai ce ‘haniniyar’ da Ya Madu kan kira ni da shi.

“Kin san wani abu?” Ya faxa.

Na girgiza kai kawai.