AYDANATU

PAGE 1

by @ashtar

  AYDANATU 🧕🏽 

 By ✒️ Malik al-Ashtar

_Sabon labari daban da sauran_ 👌🏽

 PAGE 1

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~

(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:***

      7:30 AM

Firgigit Maryam tayi ta tashi, ganin agogon dake kusan kanta ya nuna karfe bakwai da rabi.

"Hasbunallahu ai kuwa nayi latti!" ta fada tana kokarin saukowa daga bisa gadon, ji taji an riko hannun ta ta baya.

"Ina kike kokarin zuwa?"

Da mamaki ta kallesa lura da shi tuni ya dade da shiryawa zuwa wajen aiki.

"Wai har ka shirya? Amma Mahmud me yasa baka tashe ni ba? Gashi yanzu nayi latti. Ta fada cikin damuwa. Ya ilahi Yara! My dear, ban tashe su ba, kuma ban hada musu breakfast ba, su ma yau zasu yi lattin zuwa school! Ya aka yi nayi wannan baccin mai nauyi haka. Ta fada cike da damuwa ta dalilin baccin ta gashi yaranta ma zasu yi latti.

Murmushi wanda ta kira da Mahmud yayi tare da cewa "Kwantar da hankalin ki my dear. Naki tashe ki saboda naga kina baccin ki cikin kwanciyar hankali, gashi dama kin jima rabon da ki samu irin haka."

"Dear, wannan ba hujja..." Katseta yayi da cewa "A'a, kin cancanci ki samu hutu dan haka koma kiyi kwanciyar ki, zaki iya aikin daga baya, kuma kar ki damu da yara da abun breakfast dinsu, tuni na hada masu komai kuma yanzu zan je na kai su school."

"Amma my heart..."

"Kar kice komai my love, yau hutu zaki yi. Ya fada yana mai rufe mata baki tare da yi mata kiss a goshi, yana mai ce mata "love you".

Dogon numfashi taja kafin ita ma tace masa "love you too". Ta fada tana mai lunshe idanu.

Gajiya da bacci ne sosai a jikinta. Tsawon kwanaki kenan take fama da aikin wani project a office. Kula da yara da mijinta, ga kuma aiki ba karamin gajiyar da ita ba suke, ba'a ma maganar rashin yin bacci da take. Domin bai wuce sa'o'i hudu na bacci take samu ba a rana.

Sallama tayi da mijin nata, tun bai karasa fita ba, ta sake komawa ta cigaba da baccin ta. Sai da tayi mai isarta, sannan ta tashi ta nufi ban daki. Bayan ta fito ta gama shiri, ta sauko kasa ta nufi kitchen domin hadawa kanta breakfast. Tana tsaka da karyawa kira ya shigo wayarta. Murmushi tayi tare da daga kiran, tana mai yin sallama.

"Wa alaikum salam 'yata, ya kike?"

"Lafiya lau dad, ka tashi lafiya?"

"Lafiya lau alhamdulillahi, jiya zuwa karfe biyu na dare na dawo kuma yanzun nan na fito daga wajen meeting, mun daidaita dasu komai ya kammala. Ke fa ya bangaren naki komai lafiya?"

"Oh abokanan kasuwancin mu na kasar China, yau ne aka yi metting din, kayi hakuri daddy na manta da zaka dawo kuma zamu zauna meeting."

"Kar ki damu 'yata, nayi magana da Mahmud da safen nan kuma yayi min bayanin komai."

"Gaskiya dad nayi takaicin rashin halartar meeting din nan da ban yi ba..."

"Ai ba yau farau ba my daughter, contracts da kusan kullum ana samu sai ki tari gaba, kuma dama bana son ki dinga gajiyar da kanki wajen aiki har ya kai ga kin kwanta rashin lafiya."

Dariya tayi tare da cewa "Kai Dad!"

"Dagaske my princess, dan haka na baki 2 days na hutu kuma ki dawo mun cikin koshin lafiya."

"Kwana biyu? Dad ai sunyi yawa..."

"What? Ni ai da zan ce 2 weeks."

"A'a dad shikenan zan yi 2 days din."

"Wise decision... Bare dama bakida zabi da ya wuce yin biyayya. Toh ni zan barki my princess."

"Ok dad, zan zo na ganka insha Allah."

Sallama suka yi, daga dayan bangaren aka katse kiran.

Gajiya da kadaicin da take ciki tayi, ta yanke shawarar fita waje domin shan iska. Tunani ne yazo mata da hakan me zai hana ta ziyarci mahaifiyar ta. Domin yau tsawon kwanaki hudu kenan bata sanya ta a ido ba.

Kamar da rabin sa'a sai gata a gaban kamfanin mahaifiyar tata. Sosai tayi kewar kamfanin.

Lokacin da ta shiga daga cikin kamfanin, tsaye tayi tana tuna rana ta farko da ta saka kafafuwanta cikin kamfanin. Ta kasa yarda cewa shekaru da dama sun shude tun ranar...

Katse mata tunani wani matashin saurayi yayi ta hanyar gaishe ta. Sanin ko ita wacece bai sa ta tsaya yi masa wani dogon jawabi ba, ta nufi hanyar ofishin Mahaifiyar ta.

Ba tare da ta konkwasa kofar ba ta murda ta shiga tana mai rada sallama, domin yiwa momyn tata suprise.

"Assalamu alaikum Mommy... Oh i'm sorry bansan kina da bako ba." cewar Maryam da kokarin juyawa ta fita ganin mommyn nata na da bako.

Dakatar da ita mom tayi, "Shigo my daughter, baki gane shi ba, barista Usman ne."

Gaisawa Maryam tayi da baristan tare da tambayar juna kwana biyu da iyali. Sannan ta gaisa da mahaifiyar tata.

"Ni zan wuce Hajiya, aiki na jirana a kotu." Cewar barista yana mai tattare takardun sa.

"Ka gaishe min da dan uwana Ibrahim idan kun hadu." Cewar Maryam.

"Ba zan manta ba insha Allahu, sai an jimanku." Barista ya fada kafin ya rufe kofa bayan ya fita.

"Tunda danki ya zama lauya, ganinsa ke mana wahala. Cewar Maryam tana mai zaunawa bisa kujerar dake kallon ta mommy. Sam ya daina neman mu ni da Amina."

"Ku dinga masa uzuri, ayyuka ne suka yi masa yawa, ya fada min wani case ne mai rudu ya sanyo su a gaba. Duk da bai min wani karin bayani ba amma na fahimce shi."

"Hum haka dai ya tsara miki mom."

"Bani labarin gida, cewar mom tana mai kama hannayen Maryam, yaya mai gidan ki da jikoki na?"

"Ai bari kawai mom, Maryam ta fada tana mai dafe kanta jin yana sara mata. Jikokin ki ba kananan shakiyai ba ne."

Dariya mom tayi "Not so much har haka!"

Murmushi Maryam tayi kafin tace "No they are adorable, but suna wahalar dani, kuma su hakan na masu dadi. Wadda keda dan hankali cikin su Nuriya ce."

"Twins ma sunada nutsuwa."

"Eh idan basu a tare ba. Zan kawo miki su na 1 month please."

"Hannuwa bude kuwa sai kin kawo su."

"Amma fa kar ki maido min su ko nan da sati daya ne. Maryam ta fada tana dariya. Muna maganar su ma, bari naje na dauko su daga school domin bani komai dad ya ban hutu."

"Gaskiya kam ya kamata ki huta."

"Wai kowa sai yace ya kamata na huta!"

Murmushi mom tayi kafin tace "Saboda kina aiki sosai kuma kema kin sani. Well, ki gaishe min da yaran."

"Ok, my mom zasu ji." Maryam ta fada tana mai daukan jakanta zata fita. Mom ce ta dakatar da ita "Kinga barista ya manta wani file dinsa mai muhimmanci da zai je dashi kotu, ki biya dan Allah ki kai masa." Cewar mom tana mai kallon agogon hannun ta.

"Wannan ne?" Maryam ta fada tana mai nunawa mom file din.

"Eh, ki biya dan Allah ta kotun ki bashi." Amsar file din Maryam tayi ta nufi hanyar fita.

(....)

"Fatan dai ban zo a latti ba?" Cewar Maryam lokacin da ta karaso kotun.

"A'a kin zo daidai kan lokaci kuwa! Yi hakuri da bata miki lokaci da nayi. Bansan ta yaya zan gode miki ba."

"Ah kar ka damu, wannan ba wani abu bane."

Murmushi Usman yayi kafin yace "Dan uwanki bai dade da tafiya."

"Ayya bamuda rabon haduwa. Ta fada a dan dame. Zan ganshi wani lokacin insha Allah."

Bankwana suka yi, Usman ya koma cikin kotun ita kuwa ta juya tana cikin tafiya zuwa wajen motar ta. Tayi arba da wani littafi a kasa.

"Wannan kamar novel! Ta fada lokacin da ta duka ta dauke shi. Wata kil mai shi ya yadashi ne ba tare da ya sani ba."

A jikin bangon littafin an rubuta AYDANATU. Littafin kyakyawa idan ka ganshi daga waje. Saidai abinda ya bata mamaki lokacin da ta bude littafin ta lura rubutun ciki da hannu aka yishi.

"Abin mamaki!" Ta fada tana mai waige-waige ko taga mai shi.

Ganin babu kowa a wajen ta yanke shawarar rike littafin ta hanyar zura shi a jakarta. Da tunanin zata duba cikin littafin ko Allah yasa akwai adreshin mai shi a ciki, amma yanzu zata je ta dauko yara a school.

Tazo daidai an taso yaran, da murna suka nufeta suka rungumeta.

Dariya take tana fadin "a hankali kar ku kayar dani."

"Mama naji dadi sosai da kika zo daukar mu, saboda an dade baki zo daukan mu ba." Cewar Nuriya.

"Eh an dade sosai sosai mama." Arish ya maimata.

Murmushi Maryam tayi sannan tace "Nayi muku alkawari daga yanzu zan dinga zuwa daukan ku akai-akai daga yau. Kai fa Arfan dage kan na meye?"

"Saboda malamar su tace sai ya rubuto “ba zan sake yin laifi ba” har sau 50 kuma sai iyaye sun sa hannu a takardar."

"Arfan!" Maryama ta fada da sigar nunawa Arfan din bai kyauta ba.

Cikin muryar sa ta yara da nuna iya gaskiyar sa Arfan yace "Mama na rantse miki bani bane, na kusa dani ne amma malama taki yarda!"

"Saboda kullum kana yin laifi shi yasa bata yarda ba kai kayi laifin ba."

Kara zunce baki Arfan yayi tare da rungume yan kananan hannayen sa.

"Toh yanzu dai ku shige muje, mun yi magana idan muka isa gida tare da baban ku." Cewar Maryam tana mai budewa yaran kofar mota.

"Fushi zai yi da ni." Arfan ya fada a hankali.

"A'a ba zai yi fushi da kai ba, amma kai ma ka daina rashin ji. Cewar Maryam tana mai daura damarar kujerar ta domin tsaro. Kai kuma Arish ka daina yin dariya da yiwa dan uwanka gwalo."

"Bani bane mama, Nuriya ce!"

Dariya Maryam tayi sannan tace "Me? Ka dauka ban ganin ka ne, maza bashi hakuri."

"Yi hakuri." Ya fada yana yiwa dan uwan nasa wani makirin murmushi.

A mota, suke bata labarin duk abinda ya faru a school. Nuriya kamar kullum tana daga cikin masu kokari na ajin. Tana samun maki mai kyau, haka ma Arfan duk da rashin jinsa akwai kwazo kamar batagwayen sa Arish.

Suna karasawa gida bayan sun huta, Maryam ta shiga kitchen. A yau har da yaran suka tayata aikin girki.

Sai wajen karfe biyun rana Mahmud ya shigo, ya tarar da ita tana zuba abinci, yaran sun shimfida babbar tabarma, sun kawo duk wani abu da za'a bukata.

Sun ci sun sha cikin nishadi, sosai Maryam tayi kewar irin wannan ranar. Domin kwanakin nan duk ta bata su ne wajen aiki, hutun da baban ta ya bata ba karamin dadi yayi mata ba, domin kuwa tana bukatar hutun. Mahmud bai gushe ba yana yiwa Arfan fada akan laifin da yayi school, ina tunanin ba zai sake ba a yanzun, sai dai kuma kaji ance gobe dan uwan ne yayi wani laifin dan idan ba Daushe ba toh Bosho ne da yan biyun nan.

Kowa ya nemi wuri ya kwanta domin hutawa banda Maryam da ta wuce lambu domin shan iska da kuma duba ko me littafin da ta tsinta ya kunsa, domin tun dazun tunanin sa take.

Buda shi tayi tana mai kara yin mamakin ganin da hannu aka rubuta shi, wata kil ba novel bane kamar yanda tayi tunani. Fara karanta littafin tayi kamar haka :

Sunana Aydanatu Bukar, ni yar asalin kasar Mali ce kuma cikin shekara ta 18 nake shirin shiga.

Nayi rayuwar yarinta ta mai dadi da ban sha'awa a gaban iyayena (Bilkisu da Bukar). Mun zauna a kasar Germany, a garin Munich inda a nan aka haifeni kuma anan na girma. Babana bai yi kasa gwiwa ba wajen zabar min makarantar boko mafi kyau a kasar, haka shi da kansa yake koyar dani karatun alkur'ani mai girma duk da karancin addinin musulunci a kasar. Iyayena suna alfahari dani na irin kwazon dake gareni a ilimin boko, ga uwa uba kuma iya kira'ar alkur'ani dake gareni.

Haka ba zan manta da ranar da mama ta tayi min kyautar wannan kyakyawan littafin ba, yayin da na cika shekaru sha bakwai (17). Fankon littafi? Eh, nayi mamaki rana ta farko da na buda littafin. Ina dariya nace wa mahaifiya ta:

Littafin da baida komai mama, shi ne zaki ban a matsayin kyautar ranar haihuwa ta?

"Eh my dear." Ta bani amsa tana mai yimin kayataccen murmushin ta.

"Ban gane ba mama, me yasa sunana ke rubuce a jikin bangon littafin?" Na fada ina mai kara duba wannan kayataccen littafi.

"kina yawan bata lokaci a cikin library wajen karanta littafai tun lokacin da muka dawo Mali, shi yasa nace me zai hana ba zan miki kyautar wannan littafin ba."

"Eh amma kuma babu komai a ciki!"

"Ki cika shi." ta bani amsa.

"Ban gane ba, kina nufin ni zan yi rubutu a ciki?"

"Eh me zai hana?"

Sai da nayi dariya kafin na bata amsa :

"Mama wani abu ne zama makaranci, haka shi ma zama marubuci wani abun ne daban."

"Eh na sani, amma zaki iya rubuta wasu abubuwan masu ma'ana a ciki, ban sani ba misali ko irin kananan quotes haka."

Sosai na gani a idanun mahaifiya ta, maganar da take fada min da gaske take. Amma ban taba tunanin zan fara rubutu ba, kuma ban taba yarda cewa wata rana zan dauki alkalami domin rubuta labarin rayuwata ba domin yaye kuncin da nake ciki na dan wani lokaci.

Ka dawo tamkar wani littafin sirri a gareni, idan ina rubutu kan shafukan ka na kan ji tamkar ina magana ne da mama ta. Ina jin tamkar ina bata labarin abinda ke faruwa da tilon 'yarta da ta tafi ta barta ita daya, tafiyar da ba zata taba dawowa ba...

«Mama ina ma zaki san irin kewar da nake miki...»

Ya kai wannan littafi, a yau zan rubuta bisa wannan fankon fegin naka abinda nauyayyar zuciyata ta kasa dauka kuma na kasa rikeshi ni kadai.

Inada shekaru 17 lokacin da komai ya fara faruwa. Mahaifina yayi wata asara, ya rasa kamfanin sa, hakan ta sanya dole muka dawo gida Mali. Ban taba zuwa Mali ba sai wannan karon, na kan ce ni kasar bata min ba, bana son zuwa domin zan rasa abokaina dake cen Munich kuma zan sake school. Sai dai wannan karon bana da zabi.

Kutiala, babban birni ne kasar Mali, da mazaunan cikin sa akasarin su Fulani ne kamar mu, akwai rikon al'ada da yin sha'anin gaban su. Cikin kwanakin da basu wuce sati ba, muka tare a wani madaidaicin gida amma kyakyawa ne sosai, Mamata ta kulla kawance da wata makociyar mu mai suna Hassatu da gidanta ke kusa da namu, ban sani ba amma akwai wani abu wanda bai min ba ga wannan matar, kuma bansan ta yaya zan kwatanta shi ba, haka kuma baida alaka da babban danta mai suna Hashim mai shekaru 23 dake da son mata. Sai kuma 'yarta mai suna Safiyya mai shekaru 20 mai shegen iyayi da son karya! A'a kawai dai wannan matar bana tunanin akwai alkhairi a tattare da ita, a koda yaushe a tsorace nake idan ta kalle ni, sai naji gabana yana faduwa. Ba'a jima ba, na koma school, ina ajin karshe wanda daga shi sai jami'a.

Banda aboki ko daya, hakan yasa kullum nake yin hijira zuwa library kamar yanda na saba, har zuwa ranar da na hadu da Faruq. Matashi ne kyakyawa kuma ga hankali. Nayi mamaki rana ta farko da ya tarar dani cikin library, domin wuri ne da mata kawai nake gani wurin. Kwanaki sun shude, Baba ya samu aiki, mama kuwa na kula da gida, exam din mu ta karshe na kara matsowa, tuni muka yi sabo ni da Faruq. Ya zamo babban abokina, kullum muna tare bayan school. Muna zuwa bakin ruwa, ko gidan zoo ko kuma kamar kullum muje cikin library muyi ta karatu. Ya kan ce yana jin dadin muryata idan ina karatun kur'ani, ni kuwa hakan na min dadi.

Komai na tafiya daidai cikin rayuwar mu har zuwa...

Cikin watan June, wajen karfe shidda da rabi na safe (6:30 AM), na fito daga ban daki, na nade jikina da tawul, na taho ina kokarin wucewa zuwa dakina. Cikin falo, naji maganar mama ta kasa-kasa, dan taku biyu nayi zuwa baya domin ganinta. Bayan sallar asuba mama bata komawa bacci zaunawa take tayi ta salati har sai garin Allah ya waye. Wannan karon ganin nayi ta daga hannaye sama tana fadar kalaman da ba zan taba mantawa dasu ba :

"Ya Allah, kai ne madaukakin sarki, ina jin wani abu zai faru, wani abu da zai ruguza wannan ahali, ya Allah kada ka taba bari 'yata ta dulmiye cikin wannan kazamtar ta duniya, ka bata juriya da yalwar imani. Ka biya mata mafi tsada daga cikin bukatun ta. Ya Allah." Ta karasa addu'ar ta tana shafa fuskarta dake da alamun gajiya da son bacci.

Bayan ta idar ta nade sallayar, ni kuwa da gudu na wuce dakina. Haka na yini ranar kaina cike da tambayoyi. Me yasa mama ta roki Allah da kar ya barni na dulmiye cikin kazantar wannan duniya, ya kuma saka min juriya? Me taji yana shirin faruwa? Shin ko kuwa nan gaba wani abu zai faru dani? Duk lokacin da irin wannan tambayoyin suka zo min sai na watsar dasu ta hanyar girgiza kaina.

"A'a babu abinda zai faru dani marar kyau, kawai mama ta dan damu ne da exam din nake, kuma nasan insha Allahu zan cinye ta yanda zan zo na fada mata da bakina kuma tayi murna." Na fada cikin zuciyata.

Murmushi a fuskata na fita daga cikin dakina, cikin shigata mai kyau, na nufi wurin iyayena na gaishe su. Baba ne ya tambaye ni, ko nayi tsuntuwa ne ganin walwalar dake kan fuskata. Bashi amsa nayi akan yau sakamakon exam din mu yake fitowa. Nan suka min Allah ya sanya alkhairi da fatan sa'a.

(....)

Cike da murna nake fadawa Faruq naci exam. Yana wurin lokacin fadar sakamakon dan haka bai gushe ba yana taya ni murna, naso na wuce gida domin sanar wa da mama wannan kyakyawan labari, saidai Faruq ya kange akan zai kaini bakin ruwa da kuma shan ice cream, sosai ranar na nishadantu kuma ban yi tunanin wannan murmushin zai gushe a fuskata ba idan naje gida.

Na dawo gida cike da farin ciki domin labari mai dadin da na kawowa iyayena. Saidai koda na dora kafata kwanar gidan mu, naga cincirindon al'umma a kofar gidan mu. Da ka kalli fuskokin su zaka ga alamar damuwa, koda na karasa suna ganina wasu suka shiga girgiza kai wasu kuma suka sadda kai kasa. Nan na shiga tambayar su abinda ke faruwa jikina na rawa «Me yasa kuke cikin damuwa haka? Me yasa kuka taru a kofar gidan mu?», ganin basu da niyyar bani amsa nayi cikin gida da gudu hawaye na bin fuskata. A nan na hangi babana ya jingina da bango yana hawaye. «Baba meke faruwa? Ina mama?» na shiga tambayar sa da muryar dake tsoron jiran jin mummunan labari.

Kallona yayi da idanunsa da suka yi jajir suna zubar da hawaye, sai kuma ya kalli hagunsa. Ji nayi tamkar an yakice min zuciya daga kirjina lokacin da naga mama ta kwance a kasa. «Me mama take yi kwance anan baba, sanyi zai iya kamata, taimaka min na tasheta ta koma daki.» Rungume ni yayi sosai sannan yace min : «Maman ki ta rasu 'yata. Tarin hukan ta ne ya tashi, kuma lokacin ita kadai ce cikin gidan.»

Ba zan iya tuna me ya sake faruwa ba, domin sai da na kwashe kwanaki uku ni ba a mace ba ni ba a raye ba, ba wanda nake yiwa magana, bana cin komai kuma babban tashin hankalin na kasa yin kuka. Naji tamkar daga wannan ranar na daina rayuwa, kuma ban gushe ba ina maimaita «da duk hakan bata faru ba, idan da ranar ban bi Faruq ba, na dawo gida da wuri...»

Wannan shine lokaci mafi wahala a gareni, nazo da niyyar fadawa iyayena kyakyawan labari, amma ni an tare ni da mafi munin labari, cewar mama ta, wadda banda tamkarta ta rasu...

Rufe littafin Maryam tayi, tana jimamin wannan labarin.

Tunani take, anya kuwa ta kyauta da ta buda wannan littafi ta karanta. Bata sani ba ko zata iya cigaba da karanta wannan labari.

   Karshen wannan babi kenan.

Toh ya kuka ga wannan labari?

  Shin na cigaba ko kuwa?

Ra'ayoyin ku plzz, sannan kar ku manta da share shi zuwa abokan ku idan labarin ya kayatar daku.