PAGE 4
by @ashtar
AYDANATU π§π½
By βοΈ Malik al-Ashtar
_Sabon labari daban da sauran_ ππ½
On Wattpad : ***
PAGE 4
β
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSOπ*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
***
*[πI.W.Aπ]*
{...Ko dai wannan matar asiri ta yiwa baba na ne? Kwanaki da dama sun shude ba tare da na daina yiwa kaina wannan tambayar ba.
Ba makawa asiri tayi masa ganin canzawar dabi'un sa. Amma ta yaya? Ta yaya wannan matar ta iya aikata irin wannan danyen aikin? Idan kuwa haka ne Hassatu ba karamar muguwa ba ce. Dole zan sakawa duk wani motsi na yan gidan nan ido.
Nayi matukar mamakin ganin Hashim bai sake kula ni ko hantara ta ba. Bayan abinda ya faru a jami'a nayi jiran ganin me zai yimin shi da abokanan sa sai dai babu abinda ya faru, haka ma zuwa na gida. Idan da yaso zai iya fadawa maman shi domin ta hukunta ni ko kuma ma shi ya hukunta ni da kanshi. Akwai al'ajabi sosai, kuma shurun nan ya tsorata ni ba kadan ba.
Tunani nake wata kila saboda Faruq yace masa ya rabu da ni ne ya kyale ni.
Ko ma dai meye naji dadin yin nesa da ni da wannan shakiyin yayi da kuma kasancewar Faruq a kusa da ni.
Haka na cigaba da zuwa tallar ice cream a jami'a kamar yanda matar baba na take so domin baba na baida alamun yin wani abu akai.
Kasancewa ta a cikin jami'a da ganin dalibai suna kai kawo a cikin dakunan karatu ko cikin Amphitheater, a takaice dai ganin su suna karatu, suna tattauna tsarin goben su ba karamin saka min kunci yake ba kuma nasan abinda Hassatu take so kenan ta hanyar turo ni ina siyar da ice cream.
Soyayya ta ga karatu yasa ban iya hakuri ba, wani dan karamin lungu na samu a cikin aji da nake labewa, ba tare da kowa ya lura da ni ba, ina daukan kowanne darasi da ake koyawa. Ina rigan kowa zuwa kuma ina daukan darussa ba tare da wata matsala ba. Da zarar malam ya fita bayan gama darasi, na kan jira kowa sai ya fita, na tabbatar babu kowa, sannan na fito cikin sanda naje na siyar da ice cream dina kamar komai bai faru ba. Duk da ina tsoron kar wata rana Safiyya ta gan ni, har ta sanarwa mahaifiyar ta duk da haka na cigaba da daukan darasi. Wasu suna tunanin shiga da nake aji ba zai tsinana min komai ba, domin ba'a rubuta ni ba a jami'a haka kuma ba zana exam nake ba, bare ayi maganar uwa uba bani digiri daga karshe. Sai dai ni duk da haka ina samun wani abu, eh wani abu wanda ba wanda zai iya kwace min wato "Ilimi", ina kara samun ilimi kuma ina kara sanin wasu sabbin abubuwa.
Kuskuren da nayi wata rana shi ne, nazo aji kafin kowa kamar kullum, anan naga wani assignment na math saman table. Jarabawar lissafi ce da aka yi, wadda ban samu damar yi ba. Da tsautsayi na dauki abun rubutu na fara correcting din ta bisa allo. Ba tare da nasan da zuwan malam da dalibai ba. Duka kowa ya hallara, kallona kawai ake. Ban ankare ba sai da na karasa lissafin tare da ajiye abun rubutu, nayi kicibus da malamin wajen na juyo. Wani irin bugu zuciya ta tayi, kafafuwa na suka shiga rawa, dukar da kai nayi ina jiran hukunci.
Dalibai sai kallo na suke cike da mamaki da tulin tambayoyi a kai. Nan fa suka dau surutu. "Wannan ba ita bace mai siyar da ice cream? Toh me take yi anan?" "Ah daman na sani! Ni na taba ganin ta ta shigo class, amma ban taba kawowa tana daukan darasi ba." "Kamar ya, tana shiga aji ba tare da an rubuta ta ba?"
Nan fa kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa, babban tashin hankalin Safiyya na tsaye a gun. Ta ganni kuma nasan tabbas ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen labartawa mahaifiyar ta komai, daga karshe ta hana ni zuwa jami'a ko kuma ta hukunta ni. Ina tunanin ta yanda zan gudu, malamin ya fara magana.
"Aydanatu, haka ne ko?" Ya fada cikin sanyin murya.
"Eh malam, suna na ne." Na bashi amsa da shakakkiyar murya.
Gaban allon yaje yana duba correction din nawa, da kayataccen murmushi ya juyo ya kalle ni tare da cewa :
"Wannan assignment ne da na basu, kuma a yanda na duba aikin nasu, babban maki shi ne 14 bisa 20, alhali ke ga irin abinda kika yi yanzu, kin cancanci a baki 19! Anya kuwa kin yi wannan assignment? Domin banga taki takardar ba."
I'ina na fara ina soshe-soshe kafin Safiyya tace :
"Ta yaya zata iya zana exam, Ita da ba a yar makarantar nan ce ba? Malam, wannan yarinyar bata ko cancanci shigowa nan ba!"
"Dagaske ne abinda take fada?"
Sadda kai nayi cike da jin kunya. Yanzu yasan bayan karyar da nayi masa lokacin da muka hadu a library, gashi ina sauraran darasin sa ba tare da an rubuta ni ba a makarantar.
Dogon numfashi yaja kafin yace "Someone to clean the blackboard? Zamu fara darasin yau, bayan an gama zan ba kowa sakamakon assignment din sa, nan kowa zai ga makin sa."
Juyawa nayi da niyyar fita, amma ya tsayar da ni.
"Baki son sauraron darasin ne?"
Take karamin murmushi ya bayyana a fuskata. Mamaki da jin dadi suka mamaye ni lokaci guda.
"Amma Malam.. Kasan da cewa nayi maka karya kuma ni ba yar makarantar nan ba ce, me yasa zaka barni..."
"Zamu yi magana daga baya Aydanatu, yanzu ki nemi wuri ki zauna, kuma wannan karon ki zauna a gaba please."
"Wannan ba daidai bane, abinda kake kokarin aikatawa malam! Bakada wannan damar, kuma ya kamata ka koreta yanzu yanzu." Cewar Safiyya cikin daga murya.
"Listen young lady, ba ke zaki fada min abinda zan yi ba, kuma ina mai baki shawartar ki da ki zama da'a da kiyaye daga min murya idan ba haka ba, ba zaki sake shiga darasi na ba, is it clear?"
"Yes." Ta bashi amsa murya cen ciki.
Ranta sosai ya baci, ni kuwa ko a jiki na.
"Ku dauki example da ita, domin makin ku ba wani abun azo a gani bane." Cewar malamin kafin ya fara darasin.
Na kasa tantance abinda nake ji, farin ciki ko kuwa kunya? Ko kuwa tsoron abinda zai biyo baya? Kusan zan iya cewa duka ina ji.
Darasin yau naga tsayin sa, na matsu a ida domin na fita kuma ba zan kara dawowa ba. Bayan an fito, da sauri na fito ina son naje wajen mai gadi domin ya bani thermos na ice cream.
Godiya na yiwa malamin bayan na fito. Gyada min kai kawai yayi, yayi gaba.
"Zo nan bakar munafuka!" Cewar Safiyya dake tunkaro inda nake a zafafe.
"Safiyya.." Na fada ina sauke ajiyar zuciya. "Bana cikin yanayin yin fada da ke please."
"Hum kina tunanin zan kyale ki ne?" Ta fada tana rungume hannuwa.
"Me kike nufi? Kenan zaki fadawa mahaifiyar ki? Domin ta hana ni zuwa nan."
"Eh, me zai hana?"
"Meke faruwa ne anan?"
"Ah dear bodyguard yazo! Faruq wai kai baka da wani aiki da wuce shiga lamarin mu ne?"
"Duk abinda ya shafi Ayda, ya shafe ni. Me kuma take nema a gare ki?"
"A'a kar ka damu, ba komai."
"A'a kar ka damu, ba komai." Safiyya ta sake maimaitawa tana mai kwaikwayo na. Kafin ta kara da cewa : "Na kasa fahimtar me kake nema a gun wannan munafukar!"
"Ya isa, ban san meye ko saboda me kike takura mata ba, amma ina mai gargadin ki da ki daina zagin ta gaba na."
"Amma Faruq, bansan me yasa ka kasa fahimtar ina sonka ba? Wannan yarinyar ba wacce kake tunani bace! Baka san me taje ta aikata ba kawai dan ta dinga daukan darasi."
Sai yanzu na fahimci dalilin da yasa take shiga wannan yanayin idan ta ganni da Faruq, ashe sonshi take. Ba wai kawai dan ina zuwa kullum ta daya ba a aji kamar yanda ta fadawa maman ta, a'a har da kishin alaka ta da Faruq take yi. Bata san cewa ni da shi ba best friends ne kawai, ko kuwa wannan ne take yiwa kishi?
"Ni da kaina naje na yiwa mahaifin ta bayanin rubuta ta a wannan makarantar, kuma yayi min alkawarin yin hakan, so Safiyya ki kago wani abun ba wannan ba. Kuma bari na fada miki, ke kinyi kadan ki fada min wacece Aydanatu."
"Baka ji abinda na fada bane? Cewa fa nayi ina sonka. Amma baka iya rike komai a duk abinda na fada ba, sai abinda nace a kanta!" Cewar Safiyya tana mai saurin goge hawayen da ya digo mata a idon dama. "Ina son ka fada min duk wannan abin da kake yi mata, kana yi ne saboda abota? Aha..tsaya wai, kar dai ka cemin ka kamu da soyayyar ta?"
Kallon ta Faruq yake ba tare da ya bata amsa ba. Na san Faruq sosai, yana shiga wannan yanayin ne idan aka kure shi. Sai dai na kasa fahimtar dalilin sa na shiga wannan yanayin a yanzu. Safiyya ce ta cigaba da cewa :
"Toh ka sani, Aydanatun ka da kake alfahari kuma wata kila kake sonta ba kowa bace face, makaryaciya kuma yar canji. Ba'a rubuta ta a makarantar nan ba. Kuma saboda mahaifin ta yaki ya rubuta ta sai ta nemi taje tayi karuwanci! Taje ta yiwa Malam kwarkwasa dan ya taimaka mata ita kuma ta zama kwarkwarar shi..."
Bansan lokacin da na daka mata tsawa ba :
"Ya isa haka Safiyya! Na fara gajiya da sauraran zagi na da kike yi!"
Dariya Safiyya tayi kafin tace "Eh ai gaskiya daman daci gare ta!"
"What? Mahaifin ki bai rubuta ki ba?" Faruq ya fada yana kallo na da mamaki.
"Au bata ma fada maka ba? Of course ba zata fada ba, domin akwai plan din da take shiryawa a bayan kwanyar ta. Na fada maka makaryaciya ce kuma ba wacce kake zato bace amma ba komai zaka fahimci hakan da kan ka." Safiyya ta fada kafin ta juya tayi tafiyar ta.
"Faruq.." Na kira sunan sa a hankali, "Please kar ka saurare ta, kasan yanda take..Zan roke ka please kar ka yimin tambayoyi a yanzu domin bana cikin yanayi ko kuzarin da zan yi maka bayani."
Juyawa Faruq yayi tare da dafe kai, kafin ya sake juyowa yace "Tell me what happening Aydanatu, ki bani labari tun daga farko har karshe, kuma kar ki boye min please, ina son sanin duk abinda ke faruwa gidan ku tun daga ranar da baban ki ya auri Hassatu."
Sosai naga ransa ya baci.
"Calm down, na fada maka bana da ra'ayin yin zancen a yanzu Faruq."
"In kwantar da hankali na fa kika ce? Ayda ba zaki taba fada min komai ba! Me yasa kullum sai mun kai ruwa rana kafin ki fada min meke faruwa?"
"Faruq..." Na kira sunan sa a sanyaye.
"Eh haka ne mana Ayda, kin fi son kullum nayi ta rokon ki, ni da nake tunanin babban abokin ki ne ni, da ya kamata yasan komai game da matsalar ki! Kuma kina tunanin hakan daidai ne?"
"Aydanatu, lafiya?"
Naji muryar Malam Khabir a bayan mu.
"Malam...!" Na fada da mamakin ganin sa.
"Meke faruwa ne? Akwai matsala ne?" Malam ya tambaye ni.
"A'a.. Ba.. Ba komai malam."
Na bashi amsa murya ta na rawa.
"Please ko zan iya ganin ki office dina yanzu? Ina son muyi magana."
"Eh.. ba damuwa malam, gani nan zuwa."
"Ok, ina jiran ki, a sama ne hawa na biyu a hagun ki."
"Ok, malam."
"Me yasa yake son ganin ki?" Cewar Faruq bayan tafiyar malam Khabir.
"Ban sani ba, amma bari naje na ganshi. Faruq.. kayi hakuri zan fada maka wata kila komai ma, amma ina son ka kara hakuri kuma ka yarda da ni. Ka gane cewa akwai wasu abubuwan da ba saukin fada gare su ba."
"Ayda..." Ya kira sunana, da kokarin fadar wani abun amma ya juya yayi tafiyar sa.
Me yasa ya kasa fahimtar kalamai suna min wahalar fita a baki. Yin maganar shi ma yana tuna min da lokacin da kuma kuncin da nake ciki. Na kan ji zuciya ta na min zugi, hawaye na barazanar zubo min, ba kamar idan na tuna da alaka ta da mahaifi na, da ko in kula da yake min na kwanan da nake yi a lungu cikin sanyi. Bansan ta ina zan fara wannan maganar da Faruq ba, ta yaya zan fada masa wata kila baba na Hassatu asiri tayi masa ko akasin haka. Na kasa samun mafitar wannan al'amarin da kokarin gyara alakata da Faruq.
Kamar yanda nayi alkawari, naje ofishin malam Khabir, ya tarbe ni da murmushi da yimin bismillar kujerar zama kafin ya fara yimin tambaya da:
"Me yasa ba'a rubuta ki a makaranta ba?"
Shuru nayi ban bashi amsa ba.
"Ki yarda dani Aydanatu, ina son kawai na taimake ki ne, ke daliba ce mai hazaka, kuma ina ganin hakan kuskure ne na kin cigaban karatun ki."
Sunkuyar da kai nayi cike da jin kunya. Bansan wace amsa zan bashi ba. Shin gaskiya zan fada masa ko kuwa? Toh idan ma na fada mishi ai bazata yi amfanin komai ba, domin baba na ba yarda zai yi ba nayi karatu. Tunanin da nake yi kenan.
"Tunanin me kike? Ko tsoron me kike?"
"A'a ba komai." Na samu nasarar fada.
"Fada mini gaskiya, ko baki samu admission bane?"
"A'a, na samu admission da maki mai kyau malam, wannan ba shi bane matsalar."
"Wow congratulations! Amma me yasa baki cigaba da karatu ba? A sani na wannan makarantar gomnati ce, toh ina matsalar take?"
Shuru nayi ina kallon sa ba tare da nasan amsar da zan bashi ba. Mikewa yayi yana mai zagayen ofishin kafin yazo ya zauna a kujerar dake kusa dani. Sai da ya sauke ajiyar zuciya, yana mai fuskanta ta, kafin yace "Nasan cewa wata biyu kenan da fara karatu, kuma nasan lokacin register ya riga da ya wuce, amma idan da gaske kina so zan iya magana a sama kuma nayi kokarin shawo kan su ganin an rubuta ki."
"A'a, a'a kar kayi haka malam. Zan iya samun matsala a gida!"
"Ko kuna da matsalar kudi ne, yasa mahaifiyar ki take turo ki siyar da ice cream anan?"
Daman yasan ina siyar da ice cream? Idan kuwa haka ne yasan karya nake tun farko. Kunyar sa ce naji ta kara rufe ni. A take wata zufa ta fara zubo min, na fara da nasanin shigowa a ofishin.
"A'a..a'a ba abinda kake tunani bane. Kawai malam nagode da kokarin taimako na da kake.. amma.. ni zan tafi, nayi latti."
Naje fita ya riko hannu na a take kuma ya sake ni. Tare da shafa fuskar sa.
"Look Aydanatu, ina da.. Ina da 'ya kamar ki, kyakyawa, mai nutsuwa da kuma ilimi. Tana son yin karatu sosai kuma tana son zama lauya... Sai dai, ta rasu a hatsarin mota, a satin da aka fiddo sakamakon jarabawa, kuma taci jarabawar." Ya fada idanun sa da kwalla. "Idan na ganki sai naji kamar ita ce, ina ganin ta a tattare dake shi yasa nake son taimaka miki. Ba wani dadewa muka yi da sanin juna ba kuma na fahimce ki na rashin yarda dani, amma duk ranar da kika ji kin sake dani, zan kasance domin na taimaka miki."
"I'm sorry for your daughter, Allah ya jikan ta da rahama. Nasan kana da kyakyawan nufi a kaina, kuma naji dadin haka, amma ina son kasan wani abu malam, koda ni ina son nayi karatun, baba na ba zai barni ba, kuma kar ka tambaye ni dalili domin ko ni ban sani ba."
"Zan iya yi masa magana, na shawo kansa! Kar ki damu da wannan."
"Wani ya gwada yin hakan, amma bai nasara ba."
"Amma da kin..."
Katse shi nayi
"Kayi hakuri malam, nagode amma ka barshi."
"Ok inada wata dabara, tunda kina zuwa kullum nan, zan iya rubuta ki, kiyi karatun ki ba tare da wani na gidan ku ya sani ba. Zan yi kokari ganin na turo miki darussan da baki yi ba..."
"A'a hakan ba zata yiwu ba."
"Saboda me?"
"Akwai Safiyya anan makarantar, 'yar matar baba na ce kuma gida daya muke. A yanzun haka ma nasan har ta fadawa mahaifiyar ta da baba na abinda ya faru dazun."
"Me yasa kike jin tsoro har haka ne Aydanatu? Ko ana muzguna maki ne a gida?"
"A'a a'a, ni zan tafi." Na fada ina mai mikewa kar yasa na kara wani laifin. Ina jin yana kwalo min kira, amma ban tsaya ba, na nufi hanyar gida da sawa kaina ba zan sake sauraran sa ba. Motar farko na shiga ta kaini gida. Da zuwa na gidan, ina jiran fadan Hassatu. Sai dai koda na bata kudin ice cream da thermos bata ce min komai ba. Ko kalma daya, kuma hakan ya daure min kai.
A raina nace, akwai abinda take shirya min ne, shi yasa ta kyale ni yanzun.
"Ya aka yi ne? Me yasa kika tsare ni haka?" Ta daka min tsawa ganin har yanzu ina gaban ta bani da niyyar motsawa.
"Kar dai kice min jira kike na sallame ki, irin na sauran yan talla?" Ta fada tana min wani makirin murmushi. "Toh ba zan baki ko sule ba, kuma ke ma kin sani, dan haka ki bace min da gani."
A raina nace to ko dai Safiyya bata fada mata abinda ya faru ba a school.
"Nace ki bace min da gani, ko baki ji ne?" Ta sake daka min wata tsawar. "Ki je zan nemeki an jima, domin baki zamu yi."
Ba tare da nace kala ba, na juya nayi tafiya ta, a lungu na hadu da Safiyya. Ba tare da tayi min magana ba, ta kama hannu na zuwa dakin ta, wato dakin da a da nawa ne.
"Me kuma kike so dani yanzu?"
"Zan fadawa mama ta, ta..."
"Zaki fada mata abinda ya faru a school yau?"
Murmushi tayi "A'a zan fada ta barki ki kwana a daki na."
"Me? Toh saboda me zaki yi haka?"
Zaune tayi bakin gado tana murmushi ba tare da ta bani amsa ba, sannan ta mike ta nufi bakin drawer. Maskara ta dauka, ta shiga shafawa a girar ta.
"Zan barki ki dinga kwana a dakin nan bisa gado, kuma ba zan fadi abinda ya faru ba yau a school, amma da sharadi biyu..."
"Wane irin sharadi?" Nayi saurin tambayar ta.
"Na farko, zaki dinga taimaka min a assignment dina da duk wani abu da ya shafi karatu, nasan ke gwana ce, so zaki taimaka min dan naci exam."
Murmushi nayi. "Ok, wannan ba matsala bane, sai meye sharadin na biyu?"
"Ina son kiyi nesa da Faruq!"
"What? Me kika ce?"
"Kin ji me nace Aydanatu, ina son kiyi nesa dashi, ki barmin shi ni kadai." Ta fada tana murmushi. "Ina sonshi kuma ni kadai nake son ya dinga kulawa."
"Toh ni meye nawa? Abota ce kawai tsakanin mu. Kuma ba mai yiwuwa bane abinda kike so."
Dariya ta kyalkyace da ita, sannan ta kara fuskanta ta.
"Sakarya ce ke ko kuwa da gangan kike yi? Ke har yanzu baki gane Faruq sonki yake ba, ba wai ya dauke ki a matsayin abikiya ko yar uwa ba! Taimakon ki nake son yi, ki koma irin rayuwar ki ta baya, kar ki bata damar ki saboda wani simple guy."
"Ba simple guy bane shi gare ni, babban aboki na ne!"
"Eh blablabla! Kinsan me zan je nayi? Zan je na fadawa mama komai yanzu yanzu."
"A'a tsaya dan Allah!"
"Toh! Na gaji da jira. Kin yarda da sharudda na ko a'a?"
Jin nayi shuru, ta nufi kofar fita amma na tsayar da ita ta hanyar cewa na amince.
Murmushi tayi kafin ta fita zuwa dakin mahaifiyar ta, inda daga nan cikin daki ina jiyo maganar su.
"Kamar ya kina son ta koma dakin ki da kwana? Kin haukace ne ko me?"
"Please mama dan Allah ki yarda ta koma."
"Naga duk kin canza Safiyya, ko dai akwai wani abu dake faruwa ne wanda ban sani ba?"
"A'a mama, babu abinda ke faruwa!"
"Toh fada min dalili?"
"Kawai ina son daddyn ta yayi farin ciki ne, yaga kamar muna sonta."
"Ni ba wata fargaba da nake da game dashi, domin yana anan." Ta fada tana taba tafin hannun ta. "Kuma indai ina numfashi toh zai yimin biyayya."
"Ni fa mama kina tsora ta ni idan naji kina magana irin haka."
"Ai ke sakarya ce!"
"Mama.. Wai me kika yi har daddyn Ayda ya aure ki kuma yake miki biyayya har haka? Kama..kamar kare da mai shi." Cewar Safiyya.
"Kar ki kara yimin irin wannan tambayar kina jina?" Hassatu ta daka mata tsawa.
"Kar ki yi fushi mana mama, tambaya ce fa kawai. Amma kiyi tunani akan abinda na fada miki, domin yan anguwa sun fara sa mana ido, kar fa su gano irin muzgunawar da kike yiwa Aydanatu, dan bansan me zai faru ba."
"Bana tsoron su, ni bana tsoron komai bana tsoron kowa! Su fadi duk abinda suka yi niyya ban damu ba."
"Idan fa suka kore mu daga anguwar nan?"
Dariya Hassatu tayi. "Basu isa ba 'yata. Amma tunda kin matsa..."
"Kin amince kenan?" Safiyya ta katse ta.
"Eh, amma ki saurare ni da kyau, idan har na gano akwai abinda kike boye min ko kuma wata alaka kike son kullawa da yarinyar nan..."
"A'a mama ta yaya zaki iya irin wannan tunanin?"
"Toh shikenan tashi kije."
Fitowa tayi daga dakin mahafiyar tata, ta shigo ta tarar dani zaune bisa kujera.
"Ta amince zaki iya dawowa." Ta fada kafin tayi gaba abinta.
Ban motsa ba daga inda nake, tunanin maganganun su nake, ita da mahaifiyar ta. Tunani na ne ya koma kan Faruq, me zan ce masa kuma ta yaya zan yi ganin na kiyaye haduwa ta dashi, ta yaya zan datse alakar mu har na daina yi masa magana? Nasan ba zan iya ba, amma dole zan jaraba domin wannan ita kadai ce hanyar da zan samu yar salama a cikin gidan nan.
Da marece daidai na gama girki, sai ga bakin Hassatu sun fara zuwa daya bayan daya. Maza da mata. Mamaki nake ita kuwa Hassatu meke gamin ta da wannan mutanen. Ita da bata cika fita waje ba, bare ta yiwa mutane magana.
Bayan na shirya komai, na koma sama, na dauki Al-kur'ani mai girma ina karantawa, kafin baba na ya shigo yace min na sauko yana nema na a kasa. Hijab na saka na sauko, nan ya gabatar dani a wajen daya daga cikin bakin Hassatu, kamar yanda baba yace malami ne. Ni kuwa yafi min kama da boka! Tunani nake gabatarwa ta mecece za'a yi?
"Ayda, wannan shine Alhaji Tukur."
Sake gaishe su nayi da kakaro murmushin dole.
"Tana da kyau sosai kuma yarinya ce!" Wanda baba ya kira da Alhaji Tukur ya fada yana min kallon sama da kasa.
"Eh, tubarakallah." Cewar Baba tare da ce min "Tashi kije zamu yi magana daga baya."
Komawa nayi daki ba tare da naji kan abinda suka tattauna ba.
Bayan tafiyar baki, Hassatu ta sauya min fuska, abinci ma ta hana ni ba tare da nasan dalili ba. Haka na kwanta yunwa na addaba ta a ciki. Da tunanin me ya faru a wajen taron ita da bakin ta da har ya shafe ni na samu wannan horon na yunwa? A raina nace ko ba komai yau zan kwanta a daki ba a lungu ba.
Wajejen karfe ukun dare, Koke-koken da ciki na ke min ne ya tayar dani tsabar yunwa da nake ji. Saukowa nayi na nufi kitchen domin nasha ruwa ko hakan zai rage gurnanin da ciki na ke yi.
Kan hanya ta ta dawowa daga kitchen, na hango wani haske yana fitowa daga dakin baba na. Yau nasan baba yana wajen aiki, baya kwana a gida sai wajen biyar na safe yake dawowa. Ban ankara ba, kafafuwa na suka kai ni bakin kofar dakin da bata rufu ba da kyau.
Bugun zuciya ta ne ya karu, jiki na ya fara rawa, wata zufa ta fara zubo min tamkar ana watsa min ruwa, a gaba na Hassatu ce da kwarangal din kan tsuntsu a gabanta, ga wasu abubuwa barkatai a wurin, sai sambatu take da alama tsafi ne take. Hannu biyu nasa na toshe baki na, ganin ta fiddo hoton baba na ta saka a wani dan karamin akwati, sannan ta kawo wani katon kwado ta rufe akwatin tare da laulaye shi da wani bakin zare. Tsorata nayi sosai, da gudu na fita daga gidan na zauna bisa dakali hankali na a tashe. Yanzu na fahimci komai.
Hassatu asiri take yiwa baba na, kuma yau insha Allahu sai na fallasa ta. Zan fadawa baba na duk abinda ya faru da ya dawo.
Da wannan tunanin, na cigaba da zama bakin kofar gidan ina jiran baba na. Yana zuwa na fada jikin sa ina kuka ina bashi labarin abinda na gani. Sai dai ban ga alamun ya kama magana ta ba.
"Tsaya da wannan shirmen naki, kuma ki fada min abinda kike yi waje a wannan lokacin!" Ya daka min tsawa. "Kenan da gaske ne kina fita da dare?"
"Me kake cewa ne baba? Baka lura da iya gaskiya ta nake magana ba! Baba Hassatu matsafiya ce, baba muna zaune da matsafiya bamu sani ba!" Nima bansan lokacin da nayi maganar ba a tsawace.
Sallallami muka jiwo Hassatu nayi a bayan mu.
"Me kike cewa?"
Tsoro ne ya kama ni, nayi tsit.
"Bukar ni 'yarka take cewa matsafiya?" Cewar Hassatu da muryar kuka.
"Dan Allah kiyi hakuri my love, bata san me take fada ba."
"A'a baba! Wallahi da gaske nake, na ganta da idanu na!"
"Yimin shuru, ya isa haka Aydanatu!"
"Idan baka yarda da abinda na fada ba baba, kazo muje dakin ka na nuna maka." Na fada ina mai jan hannun baba na zuwa dakin sa.
Hassatu na biya mu a baya tana kukan munafunci.
Da zuwan mu dakin, kayan sun yi kasa ko bisa. Bude wardrobe nayi ko zan ga yar akwatin amma shuru. Nayi nema nayi nema amma babu alamar kayan tsafin Hassatu.
"Toh zaki fada mana abinda kike kitsawa ko kuwa?" Cewar Hassatu. "Bukar kaga irin rainin da 'yarka tayi min, tsabar rashin tarbiya ni zata kira da matsafiya, kuma bayan haka har ta iya zuwa dakin baccin mu tana yi mana bincike amma kai ba zaka ce komai ba!"
"Baba, na rantse maka da Allah abinda na fada maka gaskiya ne. Ka kara min lokaci na sake dubawa." Na fada ina kokarin cigaba da bincikawa.
Janyo ni baba yayi da karfi, tare da sakar min wani zazzafan mari. Tuni naga ya canza ba a babana da na sani ba. Dafe kunci nayi ina kuka.
"Ke har kin isa ki yiwa Hassatu kazafi!" Ya fada yana nuna ni da yatsa. "Ke kin isa? To daga yau idan kika sake irin wannan kuskuren zan yi waje dake, zaki bar min gida!"
"Baba, dan Allah ka saurare ni..."
"Bace min da gani!" Ya daka min tsawa.
.....]
Rufe littafin Maryam tayi, a ranta tace "A duk lokacin da nake karanta wannan littafin, bacin raina karuwa yake, tausayin Aydanatu na kara lullube ni. Ya kamata na nemo ta, na nemo inda take.
Ina kike ne Aydanatu?"