Book 1 (BIYU IDANUN DABBA)
by @nasimat
BIYU IDANUN DABBA...
Tsayesuke su biyu, xaya da goyo, xaya riqe da qaramar jaka. Kowaccensu na sanye da baqin leshi iri xaya, sun yafa farin gyale, qafafunsu da kunnuwansu duk fararen ababe ne, wato takalma da ‘yan kunne. Kallo xaya zaka yi musu ba za ka bambance su ba saboda matuqar kamar da suka yi da juna, hatta yanayin jikinsu xaya ne, wato dogaye, masu matsakaicin jiki da matsakaicin haske, kyawawa masu dogon hanci, da yalwar gashin gira.
Yanayinsu na nuna qosawa da gajiya da tsayuwar da suke, duk da dai a gefen titi ne suke qarqashin itaciyar darbejiya, akwai yalwar inuwa, don haka zafin ranar da a ke qalawa bai samu nasarar damunsu kamar yadda ya ke damun mutanen da ke kai kawo a kan titin keke, mashin, mota, ko matafiya kacokam kan diga-digai.
Wadda ke riqe da jakar ta ja tsaki tare da duban mai goyon ta ce.
“Anya kuwa ba tasi za mu hau ba? Na ga alamar El-Mansoor ba shi da niyyar zuwa”.
Maigoyon ta dube ta, ta ce.
“Ko ki qara kiransa tunda ya ce yana tafe kar mu tafi kuma ya zo”.
Haka xin kuwa ta yi, ta ciro wayarta a cikin jaka, ta sake kiran lambar El-Mansoor. Yana xauka cikin zafin rai ta ce.
“Idan ka san ba ka da lokacinmu don me zaka vata mana lokaci... Ka ga kar ka yi min surutun banza ai ka san na fi qarfin tsayuwa a bakin titi ko? Mts...”
Ta ja tsaki tare da kashe wayar, ta ce.
“Kin ga zo mu tafi”.
Ta soma takawa mai goyon na biye da ita cikin sanyin jiki, sam bata son su tafi gudun kada ya zo bai tarar da su ba. Bawan Allah yana bakin qoqarinsa, don dai ita sam bata gani bare ta raga masa.
Kiyy! Wata mota ta ja birki yayin da ta kusa kaxe mara goyon, su duka hankalinsu ya kaxu, da ya ke ita mai zafin rai ce, yana fitowa don ba ta haquri sai ta hau shi da masifa... Shi kuwa sororo ya yi yana kallonta cike da mamakin maganganun da ta ke furtawa a gare shi, laifinta fa ne, saboda ta afkewa titi ba tare da ta duba ba, Allah ya taqaita maimakon ta gode wa Allah sai ta vige da yarfa masa rashin mutunci? Maganarta ta qarshe ta fi kaxa masa zuciya.
“Wawa kawai, xan qauye”.
Ta qarashe tana jan tsaki. Mai goyon da ta san laifinta ne sai ta matso kusa da shi tana faxin.
“Ka yi haquri don Allah, haba SANAH laifinki fa ne...”
“Da Allah rufe min baki, sakara in za ki zo mu tafi ki taho”.
Ta yi gaba, idanun mai goyon ya kawo ruwa, ta sake raunana murya ta ce.
“Ka yi haquri”.
Ya yi murmishin qarfin hali ya ce.
“Ba komai, haquri da ma na fito na ba ta duk da laifinta ne, to amma a matsayinta na musulma da kuma mace ya kamata a yi mata uzuri”.
Ya buxe motarsa yana satar kallon mai goyon, duk da alamun da ya gani na cewar matar aure ce ta burge shi da ta kasance mai ba wa kowa haqqinsa.
Da sauri ta isa ga Sanah tana faxin.
“Don Allah Sanah ki sassauta wannan zafin ran naki, saboda rayuwa...” .
“Kin ga ba na son dogon surutu, Allah na tsani waxannan kalaman naki, ke kullum wa’azi ko gajiya ba kya yi ganin ba na xauka”.
Sai ta yi gum suna tafiya Sanah ta tsayar da mai tasin da ya fito daga wani layi, suka hau bayan ta faxa masa inda zai kai su
Yana sauke su ta biya shi kuxinsa, sannan ta buxe musu gidan da makullin hannunta suka shiga kai tsaye, ita bedroom ta nufa, mai goyon ce ta tsaya a falo, ta cire wa jaririyar ‘yar wata huxu nafkin ta xora ruwan zafi a kettle. Yana ximamuwa ta yi mata wanka, tare da shafa mata mai.
Nan kuma yarinyar ta hau kuka dole ta nufi bedroom xin, ta tarar da Sanah har ta soma bacci tana shiga Sanah ta tashi da masifa.
“Ke don Allah rufewa mutane baki, kin bi kin cika mana gida da kuka”.
Cewar Sanah kenan.
“Yunwa ta ke ji, ai ta yi juriya ma... karve ta”.
Wata muguwar harara ta auna mata ta ce.
“Ina baccin zan datse na tsaya ba ta nono? Ai sai dai kar ta yi shirun”.
Jinjirar tana tsanyara kuka ta miqa mata ita.
“Don Allah ki karve ta Sanah ki bata ta sha...”.
Cikin zain rai Sanah ta ce.
“Wallahi ba zan ba ta ba... ke ni fa SANAH kin ishe ni, na rasa yadda zan yakice ki a rayuwata na huta... wannan wane irin bala’i ne?”
Qwalla suka zubo mata da ya ke ita sarkin kuka ce ta ce.
“Ki yi haquri ba don ni ba ki ba ta ta sha, wallahi idan Little Sanah ta rasu ke ce sanadi...”
Da sauri Sanah A ta ce.
“Ta rasu mana, sai me? Idan kin yi zuciya ki bata naki ta sha, ai ke ma ‘yarki ce”.
Tana faxar haka ta juya ta kwanta.
Sanah B ta jinjina kai cike da tsananin vacin rai, ta koma falo ta ajiye Little Sanah a kan kujera, da sauri ta dama mata madara, ta xora yarinyar a cinyarta tana ba ta madarar har ta qoshi, ta vingire bacci.
Sanah B ta zuba mata idanu, tausayin yarinyar na qara shigarta, ta yadda ta samu UWA marar adalci.
Tana nan zaune El-Mansoor ya shigo falon fuskarsa a xaure, hannunsa riqe da leda.
Sanah B ta xago kai ta dube shi, tare da amsa sallamarsa. Ya xan washe fuskarsa kaxan, ya ce.
“Kun kyauta”.
Cikin girmamawa kamar yadda ya ke al’adarta, ta ce da shi.
“Afuwan, ba laifina ba ne”.
Ya ce, “Na sani, amma dole na xora miki laifi tunda duk xaya ne ku... Haba bacin rashin adalci ba za a yi min uzurin go slow ba, kawai sai ku kama hanya ku taho?”
Ta yi muqus, sarai ta sanshi da baqar zuciya, yanzu za ta yi magana ya rufe ta da faxa, ga ta ita kuma da raunin zuciya ba ta jurar tashin hankali ba ta koka ba.
Ya ja gajeran tsaki ya ajiye ledar hannunsa a kan kujera, sannan ya shige ciki.
Tana kwance a kan gadon hankalinta a kwance. Ya yi tsaye yana qare mata kallo, shi kam qaunar da yake yi mata ta yi yawa, bai san dalili ba duk lokacin da ta vata masa rai komai ya yunquro don nuna mata vacin ransa, da ya yi tozali da kyakkyawar fuskarta sai komai ya kunce masa. Yanzu ma hakan ce ta faru da shi, amma duk da haka zai tauni tsakuwa don Aya ta ji tsoro.
Qarasawa ya yi kusa da ita yana kiran sunanta. Tana jinsa, amma ta yi masa shiru. Ya kai hannu ya tafki cinyarta. Zumbur! Ta miqe cike da masifa ta ce.
“Wannan wane irin wulaqanci ne ina bacci za ka kama dukana sai ka ce baiwarka?”
Ya ce, “An dake ki, ko za ki rama ne?”
Ta ce, “Ka san zan iya!”
Ya xora qafarsa xaya a kan gadon yana kallonta ido cikin ido, ya ce.
“Wallahi kin raina ni Sanah, amma ba komai na san maganinki. In bacin wulaqanci kin san ba za ku jira ni ba, me ya sa kika sa na zo xaukarku?”
Ta ce, “Oh, wannan shi ne ya sa ka dake ni?”
Ya ce, “Eh, saboda kin gama qular da ni”.
Ta ja wani dogon tsaki, ta ce.
“Ai da ma sai da na faxa maka a waya, ba ka kai ajin da za ka shanya mu a bakin titi ba kamar karnuka, idan ba ka shirya cin zarafina ba me ya sa ka qwace min mota?”
Zama ya yi a kan gadon cikin kwantar da murya ya ce.
“To na ji, yanzu zauna kar ki fashe min”.
Ba ta musa ba, ta koma ta zauna.
Ya ce, “Ko da na qwace motarki ai na faxa miki dalili ko? Har yanzu ba a kawo waccan ba ne... Kuma Allah ba zan voye miki ba raina ya vaci da na zo ban tarar da ku ba”.
Ta ce, “Naka ran bai kai nawa vaci ba, tunda kai a mota ka ke, mu kuwa fa? A kan titi muke kowane karabiti ya zo wucewa sai ya zuba mana na mujiya sai ka ce baqin kallon mata”.
Ya ce, “To yi haquri, haka kike so ko?”
Ta yi shiru ba ta tanka ba.
Ya ce, “Kun yo kitson ne?”
Ba ta amsa da baki ba, sai xankwali da ta cire masa. Ya kalli kitson da ya sha qyalqyali, ga gashinta da ma baqi mai santsi sai kitson ya haskata sosai. Ya yi murmushi, ya ce.
“Wau! Gaskiya mai kitson nan qwararriya ce, sai ka ce da inji ta ke yi?”
Ta gane nufinsa, so yake ya shashantar da fushinta, don haka ba ta maida kai gare shi ba. ya gama subaxinsa ya xora da cewa.
“Gobe ne fa bikin Rosy, za ki samu zuwa dinner kuwa?”
Wani mugun kallo ta auna masa, ta ce.
“Kai ma ka san wutsiyar raqumi ta yi nesa da qasa... da dai sarauniyar marasa zuciya ce ka faxawa wannan na san ko ba goron gayyata ta je tunda sarkin neman suna ce”.
Tana nufin Sanah B. Ya yi dariya ya ce.
“Ke kam ban san irin zuciyarki ba, mutumin nan fa ya baki haquri, ya ce dama rashin fahimta ne, saboda me ba za ki huce haka ba?”
Ta ce, “Saboda tsattsauran ra’ayi irin nawa da ba a isa a tankwara ni don qoqarin tauye min haqqina ba”.
Ya ce, “Mhm! Idan kina maganar haqqi wallahi kunya kike ba ni, saboda yadda ke kike tauye haqqin wasu ba ki damu ba, amma sai haqilon naki haqqin kike”.
A nutse ta ke kallon shi, ta ce.
“Haqqin su wa na tauye? Ban son sharri fa El-Mansoor”.
Ya ce, “Au sharri ma ne ba ki san haqqoqin da kika tauye ba?”
Ta ce, “Eh mana, in bacin mugun sharri wa na tauye wa haqqi?”
Kai tsaye ya amsa mata.
“Sanah da little Sanah su kika tauye wa haqqi, saboda kina kallonsu a matsayin duwatsu ba su motsi bare su san haqqoqin rayuwarsu har idan an tauye su yi haqilon karvo shi”.
Ta haxe fuska sosai, ta ce.
“Ni kuma shiga sharo ba shanu ne ba na so, saboda matsalar da ta shafe mu ba ta shafe ka ba, don haka in ka so zaka iya jinginar da maganar, idan kuma ba ka so ba zaka iya ci gaba, illa dai ina maka albishir tamkar kana vavatu ne a Sabon Gari ko Singa”.
Ya ce, “Eh tun da ba kya son gaskiya dole ki faxi haka... ya kamata ke ma tunda kin kasa sauke haqqin wasu idan ba a sauke naki ba, ki gum...”
Ta katse shi da cewa.
“Don ina tukunyar dambu? Mhm! Kowa ya yi shiru kansa ya yiwa, ni kam ina ji ina gani ba za a tauye ni na qi tankawa ba”.
Ya buxe baki zai yi magana ta xaga masa hannu.
“Idan dai ka san wannan hirar ce za ka ishe ni da ita bana buqata”.
Ya yi murmushi ya ce.
“To shike nan sarkin iko, ke sai dai ai miki yadda ki ke so ba dai ki wa wani ba”.
Ta ce, “Ya son ranka?”
Ya ce, “A’a ba komai... amma ina roqon alfarma goben ki riqe little Sanah a wajenki tunda kin ga taro ne na biki, bai kamata ta je da goyo a gurin ba”.
Kamar za ta rufe shi da duka ta taso masa da faxin.
“Ai sai dai ku fasa zuwa, ‘yata ce ko tata?”
Ya karyar da murya cikin sigar rarrashi ya ce.
“Tata ce, amma alfarma ce na roqa, na san kuma a matsayina gurinki da ban tava neman alfarma ba yanzu za ki yi min ita”.
Ta ce, “Da na amince da soyayyarka ba alfarma ce na yi maka ba”?
Ya jinjina kai ya ce.
“Eh to za a iya cewa ita ce kuma za a iya cewa ba ita ba ce, saboda ke xin ma alfarma na yi miki na saka sonki a ruhina...”
“Iye! Lallai da sauran lale an bawa mai kaza kai... ashe ni ka yiwa alfarma? To sha kuruminka ni bana son alfarmar kowane xa namiji in dai a kan sona ne”.
Ya ce, “Na ji, amma don Allah a taimake ni ai min wannan alfarmar”.
Ta yi jim na wani lokaci sannan ta ce.
“Zan duba idan ba ni da wurin zuwa”.
Ya gimtse fara’ar dake fuskarsa ya ce.
“Me kike nufi?”
Ta ce, “Ka fi kowa sani!”
Ya ce, “To mu zuba ni da ke...”
Ta amsa masa, “Shege ka fasa”.
Sai ya riqe baki, “Ni ne shegen?”
Yadda ya yi maganar ya kaxar mata da gaba, ta ce.
“Ni ban ce ba, karin magana ce mu zuba shege ka fasa, na ga ba ka qarashe ba ne shi yasa na cikashe maka, don kasan ni bani barin a ci mutumcin karin magana ko da kuwa harafi xaya za a cire a ciki”.
Ya ja tsaki ya ce.
“Kura ga tsoro ga ban tsoro”.
Ba ta tanka ba ya miqe ya ce.
“To ni zan fita ga Pizza xin can na kawo miki, sai na shigo da daddare”.
Ta ce, “Da ka hutar da kanka zuwan, don yau ina buqatar shan iska”.
Ya yi tsai da idanunsa a kanta, tukunna ya ce.
“Wai ke wace irin mace ce mai son kanta da yawa?”
Ta ce, “A’a wace iri kake so na kasance? Ko kuwa so kake na tauye haqqina?”
Ya ce, “Kar ki tauye, amma kin iya tauye na wasu”.
Ya qarashe maganar cike da gundura ya fice, ta bi shi da kallo tana murmushi.
A falon ya sake tarar da Sanah B ya zauna kan kujera ya ce.
“Na dawo gare ki”.
Ta dube shi ta ce.
“Tunda ka shawo kanta ko?”
Ya ce, “Au haka ma zaki ce? To mu ture wannan. Gobe a ke dinner xin Rosy da misalin qarfe takwas na dare, ko zaki sami zuwa?”
“Ashe har bikin ya zo ba mu sani ba sai daren xaurin aure?”
Ya ce, “Afuwan, wallahi hidimomi ne suka yi yawa, kuma bikin ne ya zo da tangarxa, da sai sati biyu masu zuwa za a yi, to amma daga baya a ka maido shi gobe”.
Ta ce, “Allah ya kai mu lafiya”.
*** *** ***
Qarfe tara na dare Sanah A ta fito daga wanka, ta tarar da Sanah B zaune a gefen gado tana sanyawa little Sanah pampers. Kai tsaye ta isa ga dressing mirrow, ta murza kwalliya ta xaukar hankali, sannan ta nufi wardrob ta zavo wasu qananan kaya riga da wando pink colour waxan da suka kama mata jiki sosai.
Ta sake dawowa gaban madubin, ta xauki masharci {cumb} ta sharce gashinta ta raba shi biyu, rabi ta watsa shi a baya, rabin kuma ta sake raba shi biyu, ta xora xaya akan wancan, ya zama hawa kan hawa, xayan kuma ta zubo shi a gefen fuskarta wajan kunne kenan, tabi da mai ta lunde shi.
Ta yi tsai da idanunta ga taswirarta da ta bayyana a jikin madubin, ta yi murmushin yabawa da haxuwar da ta yi, sannan ta miqe ta xora qaramin mayafi a kafaxarta, ta feshe jikinta da turare kala-kala.
Daidai lokacin Sanah B ta gama sakawa little Sanah pampers ta xago kai ta dubeta, tausayi ya sake kwaranya a zuciyarta. Muryarta a raunane ta ce.
“Ina za ki je ne?”
Sanah A ta juyo ta dube ta, yayin da take zura cingum xin da ta vare a bakita, ta ce.
“Wani abu ne?”
Ta ce, “Eh to kamar kullum yauma nasiha ce zan yi miki ‘yar uwata, jinin jikina, ko da ba za ki xauka ba ina neman alfarma ki saurara kamar yadda wasu lokutam ki ke saurara”.
Sanah A ta haxe fuska sosai ta ce.
“Idan kuma qurarren lokaci gare ni fa, sai na sarayar da shi ga mas’alar da ke ta shafa?”
Ta ce, “A’a ba a yi haka ba, sai dai minti biyu ma ya wadatar. A matsayinki na ‘yar uwata ina tunasar da ke wannan rayuwar da ki ke yi ba ta dace da ke ba, haka ba rayuwa ce mai xorewar jin daxi ba, ki yi haquri ki tsare mutuncinki domin shi madara ne idam ya zube baya kwasuwa. Bayam haka ma a matsayin little Sanah na ‘yar watanni uku ya kamata ki tsare kanki idam har komawa wannan rayuwar ya zama dole a gare ki, gudun kada ki gurvata mata nono...”
Da sauri Sanah a ta katse ta da cewa.
“Na yi tunanin ba ni kaxai na haifi little Sanah ba?”
Sanah B ta amsa mata da cewa.
“Haka ne, ammam kin san abin da likita ya ce kar na kuskura na shayar da ita nonona saboda qarfin dafin da ke tare da shi zai iya yi mata lahani ko? Ba don haka ba ke kanki kin san daga ranar da muka haifeta zan janye ta daga gare ki. To amma tun da babu yadda zan yi na shayar da ita ya dace ke a matsayin ki na wadda nononki ba zai mata lahani ba ki shayar da ita, ki kuma kiyaye duk abin da zai gurvata shi”.
Sanah A ta ja tsaki ta ce.
“Kinga Sanah don Allah ki saurara min da wannan fatawar ta ki, wallahi da za ki buxa zuciyata ki ji yadda na ke jin qunci a duk lokacin da kika tsare ni da irin waxannan kalaman da kin daina tunkara ta da su. Ni fa ina da hankali da tunani ba sai anyi min dolen cusa min su ba. rayuwa ce ban hana kowa zavar wadda ya ke son yi ba, don me za ki uzzura min ki dame ni? Na yi- nayi da ke ki koma gida ki kyale ni kin qi, har cewa nayi ni na haqura da little Sanah kamar yadda yake kowanne yana da haqqi kanta tun da mu biyu muka haifeta ki tafi da ita ki barni na yi rayuwata kin qiya. Kullum sai ki bi ki dame ni... to ina miki albishir na kusan barin duniyar gaba xaya”.
Sanah B ta yi murmushin takaici ta ce.
“Wallahi da zan iya rayuwa ba tare da ke ba da tun farko ba a tubalin wadda muke yanzu ba. mutuwar kuwa da kike ikirarin za ta raba mu, ita xin ma ba raba mu za ta yi ba, domin har kullum ina ji a jikina sanadi xaya zai raba mu da duniya kamar yadda muka zo a tare haka za mu koma... idan ko ba mu tafi tare ba ba na fatan ki riga ni tafiya, domin ban san yadda rayuwa za ta kasance a gare ni ba. sanah ke kanki da kike wannan ikirarin da ke nuni a bayyane ba ki qaunata na tabbata ba za ki iya rabuwa da ni ba. Mhm kina xaukar qaunar da mu ke wa jina iyakacinta a fuska ne?”
Cikin dakewa Sanah A ta ce.
“Ke ce ke wannan wahalar, amman ni tsaf zan iya rayuwa babu ke! Idan ma kina wa kanki gata ki yi ki koma gida, ni kam daga nan ma gaba na qara”.
Ta qarashe maganar tana latsa wayarta. Sanah B ta ce.
“Idan Allah ya yarda kafin ki qara gaban za ki ganki a tsaftataccen gidan da kika tsana”.
Ba ta kuma magana ba ta kara wayarta a kunne, tana faxin.
“Kai fa na ke jira...”
Ta xan saurara, sannan ta cu gaba da cewa.
“To gani nan fitowa”.
Ta sauke wayar ta dubi Sanah B ta ce.
“Saura idan ‘yarki ta fitine ki da fitinarta ki biyo ni falo, wallahi a sai na sauke miki rashin mutuncin da ban tava yi miki ba, don ba za ki kunyata ni gaban baqona ba”.
Tana kai aya ta muxa qifa ta fice. Sanah B ta qi yarda hawayen da ke qoqarin zubo mata zubowar, saboda ta soma gajiya da asarar da su da ta ke a banza.
Sanah A ta fita waje ta hango mota mai ruwan toka tsaye a nesa da ita, ba ko tantama ta san shi ne, don haka daga nan inda ta ke ta kira shi a waya ta sanar da shi ya matso ga ta nan tsaye, ta buxe masa get ya shigo da motar, ya yi mata muhalli a inda ya dace, sannan ya bixe ya fito yana murmushi.
Sanah ta yi dariya ta ce.
“Barka da zuwa sabon wata”.
Ya sake haske ta da yalwataccen murmushinsa ya ce.
“Wow fine girl! Dama ni nasan sai kin fi kyau da dare”.
Ta narke idanunta cikin salon kissar da ta ke xaure hankalin duk namijin da ya faxa komarta, sannan ta ce.
“Muna iya shiga daga ciki”.
Ya maida murfin motar ya rufe sannan ya bi bayanta zuwa cikin gidan. Suka zauna a kujerun da ke falon. Sanah ta gaida shi, sannan ta xauko masa pizza xin da ta sa Elmoonsir ya si yo mata ta girke a gabansa. Ta buxa firij ta xauko lemon Shani da kofuna guda biyu suma ta ajiye. Ta ce.
“Ranka ya daxe a soma da wannan”.
Ya ce, “Ai ganinki ya qosar da ni Sanah, domin kin cancanta kashe yunwar mai yunwa a dik lokacin da zai yi tozali da ke”.
Ta ce, “Duk da haka bai kyautu baqo ya zo wuri ya kasa cin abin da aka tanadar domin sa ba”.
Ya ce, “Kuma fa haka ne”.
Sai ya ja pizzar a gabansa, ta ce.
“Nazeer kenan”.
Ya soma cin pizzar kenan Sanah B ta fito daga bedroom da niyyar xaukar littafin addu’o’in da ta manta a kan firij, ganin baqin ya sa taga rashin kyautuwar ta wuce ba ta gaishe hsi ba, don haka bayan ta xauki littafin ta gaida shi, ya amsa a mutunce yana binta da idanu.
Sanah A ta auna mata harara ba tare da ta ce da ita komai ba, duk sai ta ji ta tsargu kamar ta yi wani gungumemen laifi.
Haka a kallo xaya da ta yi wa fuskar baqon ta ji wani abu da ba ta san mene ne ba ya ziyarce ta, kamar ta san fuskar, amma ta kasa tantancewa.
Har ta kai qofa za ta shige xakin ta sake juyowa, idanunsa tsaf a kanta, ta kuma shaida lallai ta tava sanin fuskar nan.
Tana shigewa Nazeer ya dubi Sanah A ya ce.
“Wani abu ya xaure min kai, na ga kuna matuqar kama da wannan, shin ku ‘yan biyu ne?”
Ta gano dalilin nacewa kallon da ya yi wa Sanah B, don haka sai ta yi murmushi, ta ce.
“Qwarai”.
Ya jinjina kai da alama yana son sake cewa wani abu, amma ya share ya xauki kofin lemon zai kai bakinsa kenan, kamar an wurgo shi ya faxo falon wurjanjan!
Turus ya tsaya fuska a tamqe kamar zai ci babu. EL-MOONSIR ne!
Sanah ta xaga kai da sauri ta dube shi, duk da ta xan tsorata saboda ba ta kawo ganinsa ba, kasancewar da ma ta ce masa kar ya zo, amma sai ta share ta sha kunu sosai, ta kawar da fuska.
Nazeer kuwa da bai san dawan garin ba, ko xar bai ji ba bare tunanin wani abu. A haka suka wanzu tsayin mintoci niyu sannan El-Moonsir ya isa tsakiyar falon, idanunsa qyam a kan Sanah ya ce.
“Yau kika tabbatar min da ba ki da mutumci!”
Duk da ta tsammaci jin haka daga gare shi maganar ta yi qololuwar qona mata rai. Ta xago da kai da sauri ta ce.
“El-Moonsir ni ce marar mutum...”
Kafin ta qarasa ya daka mata tsawa, ya ce.
“Idan akwai matsayin da ya fi wannan muni kin cancanta hawansa a gare ni. Da ma saboda wannan banzar bazaran kika wahalar da ni nemi miki pizza, kuma kika ce kar na zo yau?”
Maimakon ta ci gaba da xaure fuska kamar yadda maganganunsa suke xaure jijiyoyin jikinta, sai ta yi murmushi mai tura haushi, ta ce.
“Ashe yau ka san sharrin mace? Ai na xauka a matsayinka na wanda yake iqirarin babu halin mace da bai sani ba ka san wannan babin?”
Nazeer wanda ke ta kallonsu ba tare da ya san inda suka dosa ba, ya ce.
“Wai Sanah me ke faruwa ne?”
A matuqar tunzure El-Moonsir ya ce.
“Da ma ya za a yi ka fahimta tun da qwalwar kifi gare ka wayonka a ruwa ne, da ka fito waje ka tashi aiki? To gargaxi na ke maka da babbar murya, ka yi maza ka bar gidan nan, ko a hanya ka ga Sanah kada ka nuna ka santa bare wata magana ta biyo baya a tsakaninku. Sanah matata ce!”
Dariya ta yi, ta ce.
“Ashe an xaura auren? To kai ka ji Nazeer tsaya sanya rival ya yi maka buqulu”.
Nazeer yanzu ya gane zancen, sai kuwa ya sa dariya abin da ya qular da El-Moonsir kenan, ya shaqo wuyan Nazeer.
Rigima ta kaure a tsakaninsu, hankalin Sanah ya yi qololuwar tashi, ta rasa yadda za ta raba su.
Sanah B da ke kwance a gado ranta vace na halayyar jaye-jaye da ‘yar uwarta ke yi ta jiyo wannan hayaniya, cikin azama ta fito falon ta tarar El-Moonsir na kokawa da baqon, da ma ta san arina, yadda El-Moonsir ya ke da tsananin kishi a kan Sanah zai yi wahala ya ganta da wani hakan ba ta faru ba.
Da qarfin murya ta ambaci sunansa tana cewa.
“Don girma Allah El-Moonsir ka yi haquri ka qyale shi”.
Ko da ma can Sanah B mai matsayi ce a gare shi, don haka Nazeer ya ci albarkacinta ya sake shi, su duka suna huci. Ya xora da cewa.
“In bacin wulaqanci Sanah har ta isa ta kawo mana qato a gidan nan? To wallahi idan ba ta kiyaye ba sai ta fi kowa nadama!”
Sanah A ta yi saurin cewa.
“Nazeer ka yi haquri, ni dai na ce ina sonka, wani kuma bai isa ya raba mu ba. ka je gobe ma haxu”.
Nazeer yana gyara botiran rigarsa ya ce.
“Kada ki damu, idan da sabo na saba da irin waxannan qadangarun...”
El-Moonsir ya yunqura zai kifa wa Nazeer mari, da sauri Sanah B ta shiga tsakani tana roqonsa kar ya tava shi. Haka Nazeer ya fita ransa fari don ya tura wa El-Moonsir haushi sai dariya ya ke.
Bayan ya fita, El-Moonsir ya sauke dubansa ga Sanah A ya ce.
“Wallahi kin ji haushin halinki, kina iqirarin sanin haqqi, amma ba ki san kare haqqin wanda ya ke da haqqi a kanki ba”.
Wani dogon tsaki ta ja, ta nufi qofar bedroom za ta shiga ta juyo ta ce.
“Taqamarka ba ka da shamaki a gidan nan ko? Wallahi daga yau na yi maka shamaki da kusantar inda nake, idan kuma ka musa ka biyo ni xakin nan, wallahi sai dai a xauki gawarka.. banza kawai!”.
Daram! Maganar ta bugara masa zuciya, ya yunqura zai bi ta xakin, Sanah B ta sha gabansa, ta ce.
“Don Allah kada ka bi ta, wallahi za ta iya aikatawa... Ka taimaki rayuwata kayi haquri”.
Ya ja turus ya tsaya yanahuci, Sanah A ta sake auna masa harara, ta ja tsaki ta shige xakin.
Sharaf El-Moonsir ya zube a kan kujera, ya ce.
“Sanah kin zame min bala’i, na rasa yadda zan yakice ki nasamusassauci daga wannan azababben son da nake miki”.
Sanah B ta zuba masa idanu cike datsananin tausayinsa. Duk da a da tana ganin Abdulhalim ya fi kowa son Sanah, amma yadda salon soyayyar El-Moonsir ta ke ya nunamata ya fi Abdulhalim son Sanah, kuma haqiqa shi xin ya cancanta ta nuna masa kulawa kamar yadda yua ke nunawa a gare ta, sai dai ruxin shaixan na ruxar kwanyarta, har ta ke sa qafa tana shure xumbin qaunar da El-Moonsir ke nuna mata. Cikin kwantar da muryata ce.
“El-Moonsir don Allah ka ci gaba da haquri da halin Sanah, wallahi duk abin da ka ga tana yi maka qarfin hali ne kawai, amma ita ma tana qaunarka, tana muradin ka zamo abokin rayuwarta”.
Ya ce, “Haba Sanah, wannan ba hujja ba ce, a ce kana son mutum kuma kana wulaqanta shi. Ni na sani ni kaxai ke wahala da ciwon son Sanah, ita ba ta sona. Ba ta qaunar ta ganni cikin farin ciki, ta fi so koyaushe ta cusa min vacin ran da zan yi zuciya na ce ba na sonta. Zuciya kam talna son mai kyautata mata, amma ni tawa zuciyar raguwa ce, ba ta iya qin Sanah duk da rashin kyautatawar da ta ke wa rayuwata.
Ba na tunanin nman kusa zan iya daina son Sanah ko da kuwa kullum za ta sa reza tana rexar fatar jikina”.
Sanah ta ce, “To tunda har ka tabbatar da ba za ka iya rabuwa da ita ba, kuma ka gano matsalarta ina ganin abu mafi dacewa ka ci gaba da juriya da ma soyayya ta gaji haka, mu xin ma duk doron soyayyar ne ya zaunar da mu a nan inda ba mu da kowa, ba mu san kowa ba, ba mu da wata hanya da za ta kare mu duk wani abin jimantawa da zai same mu, sai Lillahi”.
Qwallah suka zubo mata, ta ci gaba da cewa.
“Kullum cikin baqin ciki nake na wannan rayuwa da muka samu kanmu, ina tausayin rayuwarmu a ce mun qare ta a wannan vigire”.
Jin yadda muryarta ta raunana ya san yanzu nan za ta fashe da kuka sosai, fiye da yanzu da hawaye ta ke sharewa, ya sa ya miqe ya ce.
“Don Allah ki ci gaba da taya ni da addu’a Allah ya ba ni sa’a a kan Sanah, Allah ya sa ni ne sanadin da zan kawo muku farin cikin da ku ka rasa”.
Ta ce, “Allah ya sa, na gode”.
Daidai lokacin da ita ma ta ke miqewa tsayen. Ya kai qofa ya juyo yana faxin.
“Ki zamo cikin shiri goben zan zo bayan magriba mu tafi gurin dinner xin Rosy”.
Ta ce, “Allah ya kai mu”.
*** *** ***
Misalin qarfe shidda na yammaci Sanah B ta gama shan ado cikin material lace mai ruwan qwai, ya yi matuqar yi mata kyau, ta saka baqar hijabi da baqin takalmi gami da baqaqen ‘yan kunne da sarqa.
Tunda ta fito wanka ta ke cikin fargaba kada El-Moonsir ya zo xaukarta Sanah A ta ce ba za ta riqe Little Sanah ba, har ta gama kwalliyar ba ta fita daga halin fargabar ba, yayin da Sanah A ke zaune a falo tana kallo, ita kuma Little Sanah tana kan gadonta tana kalle-kalle da aka san mafi akasarin jinjirai na yi.
Da ta gama kwalliya sai ta fito falo, ta xosana a kan kujera kamar mai tsoron zama a kan qaya. Shiru na ‘yan mintoci ba wanda ya ce wani abu, zuwa can Sanah B ta sauke gwauron numfashi murya a sanyaye ta ce.
“Sanah idan El-Moonsir ya za mu tafi”.
Sanah A ta juyo kaxan ta dube ta, ta ce.
“To, Allah ya kawo shi lafiya”.
Sanah B ta ji daxin faxar haka, don ta xauka a zafafe za ta amsamatya. Ta ci gaba da cewa da ita,.
“Da ma game da Little Sanah ne, don Allah kar ki barta ta yi takuka”.
A taqaice ta ce mata.
“Ba damuwa”.
Shiru ya sake gilmawa a tsakaninsu, aka kira sallar magriba da yake Sanah B na fashin sallah sai ba ta tashi ba, ta ce.
“An kira sallah, ya kamata ki tashi ki sauke farali”.
Wani mugun kallo ta auna mata, ta ce.
“Da can ke ke sani na yi? Ni fa kin ga abin da yake haxa ni da ke, shisshigin bala’i”.
Sanah B ta rusunar da kai ta ce.
“Allah ya ba ki haquri, tunatarwa ce”.
Tsaki ta ja ta shige xaki, Sanah ta bi ta da kallo tana murmushi. Duk tsiya dai ta yi wani abu a kai.
Ana gama sallar magriba El-Moonsir na shigowa harabar gidan. Ya shigo falo ya tarar da Sanah B a shirye, ya yi murmushin jin daxi ya ce.
“Yauwa, haka nake so sarkin cika alqawari, mu je ko?”
Ta dube shi da fara’a ta ce.
“Ai ban kai ka ba, tunda ga shi ka zo daidai lokacin da ka ce za ka zo. Amma ya kamata ku gaisa da mutuniyar kafin mu fita”.
Ya ce, “Kin manta abin da ta ce jiya?”
Ta girgiza kai, ta ce.
“Ai jiya ba yau ba ce, kai ya kamata ka ba da labarin Sanah mace ce mai saurin hawa da kuma saurin sauka”.
Ya ce, “Haka ne, amma na ba ta hutu na wani lokaci idan ta sace sosai don kanta ma koma daidai”.
Kamar an jehota ta faxo falon tana faxin.
“Qwarai ka taimaki kanka da ka kiyaye dokata, domin kuwa idan ban janye shamakin da na shata tsakaninmu ba ka shigo inda nake sai na keta mutumcinka”.
Ya dube ta da wani irin duba, ya ce.
“Ashe kina muradin ganin fuskata tunda kika kasa haquri, daga jiyo muryata kin fito, ko kin xauka ban san tabarmar kunya ce ki ke naxewa da hauka ba?”
Ta ja tsaki ta ce.
“Kanka ake ji”.
Ya ce, “Ko kuma ke ba...”.
Ya maida dubansa ga Sanah B ya ce.
“Taso mu je”.
Ta dubi Sanah A ta ce.
“Mun tafi sai mun dawo”.
Ba ta ce mata komai ba, ta koma xaki, su kuma suka fice El-Moonsir na dariyar mugunta.
Bayan sun fita daga gidan ya ce.
“Na yarda da maganarki, wallahi Sanah na sona, yawo da hankali ne kawai irin nata”.
Sanah ta yi dariya ta ce.
“Ai da ma ya kyautu ka san haka, don dai zuciya ce da ba ta da qashi”.
Ya jinjina kai yana murmushi ya ce.
“Kin san wani abu?”
Ta ce, “Sai ka faxa”.
Ya ce, “Mahaifana sun dame ni da maganar na yi aure, ita kuma mutuniyar har yanzu ta qi ba ni fuska”.
Sanah ta ce, “Ka ci gba da rarrashinsu insha Allah za a dace”.
Ya ce, “Ai ba ki san inda gizo ke saqar ba, har yanzu ba su san wacce zan aura ba, kuma Ummina kullum naci ta ke na kawo mata ita ta ganta”.
Sanah ta ce, “Me zai hana ka kaita xin na san ba za ta qi amincewa ba”.
Ya ce, “Kayya Sanah, kin san fa halin Sanah murxaxxiya ce, na snai idan na roqe ta za ta je, amma matsalar xaya ce, ba za ta amince ta yi shiga irin wadda nake so ba. idan kuwa Ummina ta ganta a shigar da ba ta yi mata ba, wallahi za a samu matsala. Ni kuwa a duniya ban ga ‘ya macen da nake so kamar Sanah ba”.
Shiru Sanah ta yi tana nazari, yayin da shi kuma ya ci gaba da cewa.
“Yau xin nan muka yi da Ummi idan ban kawo mata wadda nake iqirarin ina so ba, za ta bayyanar da qudirinta ga Abbana, wato za ta faxa masa xiyar qanwarta na sona, wanda idan ta faxa masa babu makawa tawa damar ta rogaje, don shi mutum ne mai son qulla zumunci”.
Sanah ta dube shi, ta ce.
“Tabxijan! Ni kaina wallahi ina wa BIYU sha’awar aurenka, don ka cancanta da ita. Ga shi kuma kuna ‘yar tsama da ita, ya kenan?”
Ya ce, “Abin da ya dame ni ke nan, tunda na baro gidan. Da farko na yi niyyar tunkarar Sanah da maganar, amma sai na kawar da hakan tunda ga abin da ke gudana a tsakaninmu. To kuma sai wata shawara ta zo min, duk wanda zai kalle ku ke da Sanah ba zai iya tantance ku ba saboda tsananin kamar da kuka yi da juna. Farinku xaya, gashinku xaya, tsayinku xaya... komai dai na halitta xaya kuke da juna.
Abu biyu suka bambantaku, na farko Sanah ta fi ki wayewa, ke kuma kin fi ta haquri da sanyin zuciya. Sai maganarku da taki ta fi sanyi, yayin da tata ta ke kai tsaye babu tausasawa. Waxannan abubuwan kaxai ne za su bambanta ku, har wanda yake zaune da ku yau da kullum ya iya shaida wannan da waccan. Shi ne na ga tunda hakan ta faru mai zai hana na kai ki ga Ummina a matsayin Sanah...”
Da sauri ta girgiza kai ta ce.
“Idan muka yi haka mun yi yaudara a sha’anin aure, wanda yin hakan ya haramta”.
Shi ma ya girgiza kai, ya ce.
“Ko xaya babu abin da ya haramta, domin fata na gari lamiri, ina son Sanah matuqa, kin isa ki zamo shaida a kan haka. Kuma kullum ina qoqarin maido ta kan turba madaidaiciya, ina fatan ta koma kamar ke ko finki ma, kin ga ke nan da sannu haqana za ta cimma ruwa”.
Sanah ta ce, “Son zuciyarka ne ke qawata maka samun nasara mai girma wadda kan danne karin maganar nan tun ran gini ran zane, ku...
Ya katse ta da cewa.
“Idan har karin maganar tun ran gini ran zane za ta taka rawa a wannan vigire mai zai kawo qaddara irin wannan? Haba Sanah sai ka ce ba ke ba da na sani da zurfin tunani da hangen nesa? Fata fa nake Sanah ta shiryu ba cewa na yi dole ta shiryu ba”.
Ta gamsu da bayanansa, sai ta girgiza kai, ta ce.
“To misali sai ka kai ni ga Ummin a yanzu, nan gaba kuma sai ka kai mata Snah ta je musu da yanayi savanin nawa ya kake gani?”
Ya ce, “Albishirinki? Kallo xaya na tsara za a yi wa matata, daga haka babu wanda zai kuma ganinta sai ta zamo matata lakadan. Saboda haka idan har ta ganki yau bani da shkku za ta yaba da zavina, har ta xokantu a xaura aure”.
Sanah ta yi dariya ta ce.
“Allah kai kam ba ka da dama, wato har ka gama shirya yadda fim xin zai kasance?”
Ya ce, “Wa ya ce miki fim ne? Gaske ne, idan muka bi wannan siraxin mun gama da lamarin”.
Ta ce, “To shi kenan, amma fa ka sani, duk abin da ya biyo baya ba ni a ciki”.
Ya ce, “Har ladar?”
Ta ce, “A’a, lada ai da ma idan lamarin aurenku ya tabbata zan same ta, matsala dai nake nufi”.
Ya ce, “Insha Allahu ba mu tare da matsala”.
Ta ce, “Haka ake fata”.
Daga haka babu wanda ya qara magana a cikinsu har suka iso Xorayi unguwar su El-Moonsir. Maigadi ya buxe musu tangamemen get ya shiga da motar.
Sanah ta jinjina tarin kayan alatun da gidan yake xauke da su, don ba ta tava tunanin El-Moonsir xan gwaska ne haka ba. ba ta tsinke da lamarin haxuwar gidan ba, sai da suka shiga cikin qayataccen falon da ya gama haxuwa.
Su kansu kujerun falon idan mutum ya hau su sai ya rantse kanm zallar auduga yake ba soson karifa ba, saboda tsananin laushi”.
Ta zauna tana qarewa falon kallo, shi kuma ya shiga wata qofa. Jim kaxan suka fito shi da Ummin tasa da Safiyya qanwarsa. Da sauri Sanah ta sunnar da kanta qasa saboda kwarjinin da suka yi mata. Da ma tusa hali, duk wanda ya san Sanah ya santa da kawaici da alkunya, ba ta cika kallo ba, ba ta kuma damu da a nace mata da kallo ba.
Wannan tsarin sai manya (Sanah A) wadda idan ka yi mata kallo xaya za ta qyale ka saboda baqunta. Amma kana kuma na biyu za ta tambaye ka ba’asi.
Hajiya Maimuna babbar mace hakima, ta hakimce a kan kujera, Safiyya ta zauna kusa da ita, dukkansu idanunsu a kan Sanah. Yanayin yadda Hajiya Maimuna ta ga Sanah ya burge ta, ba ta yi tsammanin yadda El-Moonsir yake xan rayuwa zai zavo ‘yar gidan manyan mutane kamar wannan ba, shi ya sa kullum ta ke matsa masa ya kawo ta don ta gani idan ba ta kai Kubra ingancin tarbiyya ba tai wa tufkar hanci.
To amma ga dukkan alamu wannan za ta fi Kubran, saboda haka ta jinjina masa matuqa a ranta. Cike da jin daxi ta ce.
“Yau Allah ya yi El-Moonsir ya kawo ki, sannu da zuwa”.
Sanah ba ta amsa ba, illa zamowa da ta yi daga kujerar ta zauna a kan kafet, cikin launin muryarta mai sanyi ta gaishe da Hajiya Maimuna. Ta amsa, yayin da Safiyya ke faxin.
“Saura ni”.
El-Moonsir ya aunamata harara, ya ce.
“Da yake gaba kike da ni dole ta gaida ki”.
Kafin ta yi magana, Sanah ta yi saurin cewa.
“Ina wuni?”
Ai kuwa Hajiya Maimuna da Safiyya suka tuntsire da dfariya, Safiyya ta ce.
“Ka gani ita ta san daidai, ai ita ta tarar da mu dole ta gaida ni”.
Ya ce, “Wallahi ko ki rufe min baki ko na bubbuge ki”.
Ta qara lafewa jikin Ummin ta ce.
“Daxin abin Ummi na kusa, kuma ka san dai wasanka na hannuna, idan ka ce kulle zan ce cas, shi kenan sai dai wani sabon wasan”.
Ummin ta ce, “To suda mai bakin magana ya isa haka, a kira Lamimiya ta kawo wa baquwa abin motsa baki”.
Safiyya ta miqe, Ummin ta maida dubanta ga Sanah ta ce.
“Ya sunanki?”
El-Moonsir ya yi karaf ya ce.
“Kai Ummi, na fa faxa miki sunanta Sanah”.
Ta ce, “Waqa a bakin mai ita ta fi daxi, kuma ai ba cikakken sunan ka faxa min ba, saboda haka ka bar ta ta faxa min da kanta”.
Zai kuma magana Ummin ta xaga masa hannu dole ya yi shiru, sai dai ba ta samu amsar tambayar daga Sanah ba, saboda ta yi xuf bakin ya mutu murus, kunya ta ke ji sosai sai ka ce ita ce asalin budurwar tasa.
Ummi ba ta tsawaita lallai sai Sanah ta yi magana ba, saboda sarai ta fuskance ta tana jin nauyi ne. Da Lamimiya ta wadata gaban Sanah da kayan lashe-lashe tashi suka yi ita da Safiyya suka shige xaki don ba ta damar cin abin da aka kawo mata.
Amma Safiyya tsayawa ta yi bakin qofa tana leqe ta ga Sanah za ta iya cin abincin a gaban El-Moonsir. A vangaren Sanah ko kallon kayan ba ta yi ba, saboda ba ta tare da yunwa, ko ba don haka ba a ganinta bai kyautu ta kama abu kayayam-kayayam tana ci kamar mara katsari ba.
El-Moonsir ya hau yi mata magiya ko ya ya ne ta daure ta ci wani abu, amma ko xaga kai ta kalle shi ba ta yi ba, ganin haka sai ya ja spring rool cake ya ci yana faxin.
“Bari na taimake ki na xan ci miki”.
Safiyya da ke kallon duk abin da ke faruwa ta juya ta dubi Ummi, ta ce.
“Wallahi Ummi Yaya ya yi dace da mace ta gari, ki dubi shigarta ta kamala, sannan duk abin da aka kai mata ta kasa tava ko da ruwa ne”.
Ummi ta sake jin farin ciki ya kwaranya aranta, ta ce.
“Masha Allahu, addu’ata ba ta faxi”.
Bayan mintoci biyar su Ummin suka dawo falo, El-Moonsir ya ce.
“Ummi kin ga cake kawai ta ci”.
Sdafiyya ta kanne ido, ta ce.
“Kai Yaya mai mai... xan wuta!”
Ya kimtse fuska, “Ni ne mai qaryan? Da ma lave kike mana? To ba ta ci ba, ni na ci sai me?”
Su biyun suka kama dariya, ita kanta Sanah abin ya ba ta dariya, sai dai ba ta dara ba, murmushi kawai ta yi cikin sunnar da kai. Ummi ta ce.
“Sanah ina farin ciki da Allah ya sa za ki zamo surukata, don na kula akwai nutsuwa a tare da ke, ina fatan za ki xore da halayyarki”.
El-Moonsir ya yi saurin cewa.
“Insha Allah”.
Safiyya ta ce, “Oh Yaya kunya ta yi balaguro ko?”
Ya yi wuf zai kai mata duka, ta sake shigewa jikin Ummi tana tsuwwar zai buge ta. Ummi ta ce.
“Ai ta tsira tunda ta vuya a bayana...”
Ya ce, “Tafiya za mu yi, minti ashirin aka ba ta a gidansu”.
Hakan ma ya qara faranta wa Ummi rai, ta ce.
“Hakan yana da kyau... Ke Safiyya xauko min ledar nan”.
Safiyya ta je ta xauko, suka rako su har harabar gidan, Safiyya ta buxe wa Sanah mota ta ce.
“Shiga Aunty mai sunan Larabawa, in Allah ya yarda zan kawo miki ziyara”.
Sanah ta shiga cikin motar tana faxin.
“To sai kin zo”.
Safiyya ta saka ledar a bayan mota, sannan El-Moonsir ya tayar suka tafi.
“Kai Sanah kin gama min komai, ladarki na ga Allah”.
Ta ce, “Da aka yi me?”
Ya ce, “Da kika shirya abin da kika kira shirin fim ya qayatar da ‘yan kallo”.
Ta yi murmushi, ta ce.
“Ashe ka yarda shirin fim muke, tunda har muka burge ‘yan kallon?”
Yana duban hanya ya ce.
“No, kawai ke xin ta daban ce, ina fatan Biyu ma ta zama haka”.
Ta ce,. “Allah ya sa... Gida za mu koma?”
Ya ce, “A’a, wajen dinner xin za mu je”.
Ta ce, “Ga isha’i ana kira”.
Ya ce, “Au, to ko na maida ki gida sai bayan isha’in na dawo na xauke ki”.
Ta ce, “Idan muka koma Sanah ba za ta bari mu sake fitowa ba, idan na dawo na yi (ba ta so ya gane tana fashin sallah)”.
Ya ce, “To me zai hana na kai ki gidan Rosy inda za a fara kai amaryar, inyaso daga can sai na xauke ki mu tafi da su gaba xaya?”
Ta ce, “Yauwa, hakan zai fi”.
Kai tsaye ya wuce gidan Rosy. Mutane cike da gidan, har an kawo amarya. Ta shiga cikin matan da ba ta sani ba ta yi tsamo-tsamo kamar kazar da aka tsamo a ruwa.
Da yake sha’ani ne na biki ba wanda ya damu da ita bare ya magantu ganin ta yi tsamo-tsamo a cikinsu tana muzurai. Bayan sallar isha’i aka soma jidar ‘yammatan amarya, El-Moonsir ya kira Sanah a waya ta fito ya xauke ta suka nufi Daula Hotel inda za a gabatar da dinner xin. Guri ya haxu iya haxuwa, duk wadda za ka gani a gurin ka san ta gama jiquwa da naira, domin dai biki ne na ‘ya’yan gata, ‘ya’yan garari ba angon ba, ita kanta amaryar mahaifinta hamshaqin mai kuxi ne, don haka za mu ce ta tadda mu je.
Duk da haxuwar Sanah sai ta raina kanta, domin hatta da amaryar gyale ne a jikinta, Sanah ita kaxai ce mai hijabi, don ma Allah ya sa ba zumbuleliyar hijabi ta sa ba ma da abin sai ya fi damunta, da sai ta fi zama mujiya a cikinsu.
Kasancewar El-Moonsir abokin ango sosai ya sa yana higher table, ita kuma Sanah tana rakuve cikin jerin matan da ke gurin. Da farko ta tsaya sunne kai amma ganin kowa yana sha’anin gabansa, sai ta ga kyautuwar ta ba wa idanunta haqqinsu. Saboda haka ta xago kai tana dube-dube.
Karaf idanunsu suka haxu da na juna, yana zaune a jerin kujerun da maza ke zaune cikin dogayen kaya shar da shi, ya matuqar haxuwa kamar yadda ya haxu a waccan haxuwar da suka yi.
Tsai ya yi sosai a kan fuskarta, ko tantama ba ya yi ita ce, sai dai me ya kawo ta wannan gurin? Ina goyon da ya ganta da shi a ranar da suka haxu a bakin titi? Ko da ma ‘yar uwarta da suke kama sak da juna ita ke da jaririyar ne? Tambayoyi barkatai suka dinga zuwar masa ba tare da ya samu amsar xaya daga ciki ba.
Abin da ya sani, an tsara wannan dinner samari da ‘yammata ba mace ko xaya mai aure da aka ce za a gayyata, ko ta zo gurin ba da izini ba, hasalima gaba xaya an ce an haramtawa matan aure wannan shagalin, idan haka ne ko tantama babu ita xin ma ba mai auren ba ce? Haqiqa idan haka ta tabbata ya fi kowa farin ciki, domin tun ranar da suka haxu ta jefa zuciyarsa cikin tsananin qaunarta, musamman yadda ta ke ba shi haquri cikin sanyin murya.
Koyaushe yana tunanin ranar, taswirarta ta zame masa abar qawata masa zuciya, har ya cire rai da sake haxuwa da ita, ashe da rabon ganawa? Shin yanzu me ya kamata ya yi, tunkararta zai yi ko kuwa binta zai yi idan an tashi daga dinner xin ya ga inda za ta nufa, inyaso daga baya sai ya same ta?
To idan kuma aka samu akasai akwai shamaki a tsakaninsu (aure) ya kenan?
Zuciyarsa ta qarfafe shi babu wani shamaki da zai haramta masa kasancewa da ita tunda dai an tabbatar ba a gayyaci matan aure a gurin ba, kuma ko a yanayin shigar matan da ke gurin ya isa ya tabbatar da haka, ita kaxai ce za ka cire mai sanye da hijabi, ita xin ma ba wani tsayi hijabin ta ke da shi ba.
Iya juriya ya jure, amma zuciyarsa azalzalarsa ta ke, qaunarta na tsiruwa a cikin gurbin qaunar da ke zuciyarsa wanda ya yi wa matar aurensa tanadi. Haqiqa ta cancanta zamowa a wannan muhallin.
A vangaren Sanah xin ma ta shiga wasu-wasi, anya ba shi ne suka haxu ba da suka je kitso, jiya kenan lokacin da ya kusa kaxe Sanah? Tabbas shi ne, domin daga inda ta ke zaune tana hango billen da ya zauna daram a gefen kuncinsa, da yake fari ne shi sol sai baqin billen ya qayatar da fuskar tasa.
Su duka biyun haka suka kasance cikin tunane-tunane har aka soma gudanar da casu ba kama hannun yaro, daga qarshe Sanah ta duba agogon hannunta, ta ga qarfe goma saura. Ta lalubi lambar El-Moonsir ta yi masa flashing. Tsam ya taso daga inda yake ya iso gabanta fuskarsa cike da murmushi, ya ce.
“Ya ya dai?”
Ta narke murya kamar mai shirin kuka, ta ce.
“Duba lokaci fa, don Allah ka mayar da ni gida haka nan, bana so Little Sanah ta yi rigima”.
Shi ma ya narke murya cikin salon kwaikwayonta, ya ce.
“Shakuruminki, nan da minti goma za mu koma”.
Wannan abu da ke faruwa a kan idanun matashin saurayin yake fahruwa, yayin da ya ga El-Moonsir ya isa gaban Sanah ya ga kuma yadda ta ke magana, sai hankalinsa ya tashi qwarai, saboda tunani biyu da ya zo masa a lokaci guda, ko dai mijinta ne, ko kuma saurayinta. Saboda haka zuciyarsa ta karye idxan mijinta ne bai kyauta ba da ya xauko matarsa ta sunnah ya zo da ita wannan gurin, domin maza irinsa za su kalle ta har su yi sha’awar qulla mu’amala da ita. Idan kuma saurayinta ne, ya yi wa kansa katovara, domin za a iya yi masa qwacenta kamar yadda shi ma ya qudiri niyyar hakan.
Yana hango El-Moonsir ya isa gaban M.C ya karvi abin maganar ya ce.
“A matsayina na abokin ango ina mai ba su haquri kasancewar zan xauki qanwata na mayar a gida, idan hali ya ba ni zan dawo a qarasa shagali da ni. Ina yi musu fatan alkhairi da xorewar zamansu, sannan ina miqa godiyata ga al’ummar da suka zo taya mu murnar wannan rana”.
Jin haka da matashin ya yi ba qaramin farin ciki ya sa shi ba, don ya samu damar da yake ganin zai samu nasarar shigar da kansa. Yana ganin Sanah da El-Moonsir sun fita daga hall xin, sai shi ma ya miqe ya shiga motarsa ya bi bayan tasu ba tare da sun lura yana biye da su ba.
Har qofar gida El-Moonsir ya sauke Sanah, yayin da matashin ya tsaya daga nesa da su, yana hango Sanah ta shiga cikin gida ya fito da sauri ya tari El-Moonsir da ke qoqarin tayar da motarsa, suka yi musabiha cikin aminci, sannan matashin ya ce.
“Sunana MUFTAHU JABEER, kwanaki biyu da suka wuce na haxu da qannenka wanda na lura tagwaye ne saboda kamar da suke da juna. A taqaice dai wannan wadda ka ajiye Allah ya jarrabe ni da qaunarta, ban sani ba ko kun yi mata miji”.
El-Moonsir ya tsura wa Muftahu idanu cikin nazari kafin daga bisani ya ce.
“Haqiqa ba mu yi mata miji ba, sai dai akwai ra’ayi. Idan tana sonka ai shi kenan”.
Muftahu ya ce, “Wannan damar nake nema, wato izinin neman soyayyarta”.
El-Moonsir ya ce, “Shi kenan, kana iya zuwa gobe da yamma”.
Suka yi sallama, suka rabu.
*** *** ***
Washegari da safe misalin qarfe goma Sanah B ta samu Sanah A a falo kwance a kan doguwar kujera. Ta zauna a gefenta cikin raunanniyar murya ta ce.
“Sanah, magana nake so mu yi da ke ta fahimta”.
Sanah A ta xago kai kadaran-kadahan ta ce.
“Kin saba qaqale-qaqale, faxa in ji”.
Sanah B ta yi taqaitaccen murmushi, ta ce.
“Ki gode wa Allah da ya yi miki gamo da katar. Jiya na sadu da surukarki mace mai yakana, haka qanwar mijinki ma. Wallahi kin yi dace da samun miji mai qaunarki...”
Sanah A ta tare ta.
“Ashe kin xaura min aure ban sani ba?”
Sanah B ta girgiza kai, ta ce.
“Ban xaura miki aure ba, sai dai ina sanar da ke El-Moonsir ya cancanta, ya kuma dace ya zamo miji a gare ki, saboda shi kyautar Allah ne a gare ki. Ki duba yadda kike gasa shi, amma hakan bai sa ya daina muradin ki zamo uwar ‘ya’yansa ba”.
Sanah A ta tashi zaune, amma ba ta yi magana ba illa bin ta da kallo kawai da ta yi.
“Saboda son da yake yi miki jiya ya kai ni gurin mahaifiyarsa a matsayin ke ce, kuma sun ji daxi, har soyayyarsu ta kasa voyuwa a gare ni. Abin da nake shawartarki shi ne, ki rabu da qyale-qyalen rayuwa, ki kama El-Moonsir ya zamo mijin.ki, ina yi miki kyakkyawan zato muddin kika aure shi kin gama dace a rayuwarki”.
Sanah A ta yi dariya da tafi, ta ce.
“Allah mai iko, ai kin ga tsiyar shirmenki. Har ki je gaida surukarki ba ki sani ba”.
Sanah B ta yi jagale da baki cikin rashin fahimtar inda ta juya maganar. Ta ci gaba da cewa.
“Idan kina da hankali da tunani ya kyautu ki gane manufar El-Moonsir, ni yana sona da shashanci, ke kuma yana sonki da aure shi ya sa bai xauke ni ya kai wa mahaifiyarsa ba sai ya xauke ki”.
Da sauri Sanah B ta girgiza kanta, ta ce.
“Kada ki yi masa bahaguwar fahimta, shi ya kai ni ga mahaifiyarsa ne saboda yana tsoron ya ce ki yi shiga ta kamala ki qi. Ya tabbatar min da muddin kika je a irin shigar da kike yi ta qananun kaya mahaifiyarsa ba za ta goyi bayan lamarin ba, shi kuwa a yadda ya ke sonki ba ya fatan a raba shi da ke. Wannan ita ce manufarsa, kuma ko da abin da kike tunani shi ne, kina ganin ya dace na auri mutumin da wata mu’amala ta haxa ku?”
Cikin tabbatarwa Sanah A ta ce.
“Yo me zai hana? Ai ba haramun ba ne don kin auri wanda na yi shashanci da shi ba, bare kuma El-Moonsir wanda mu’amalarmu ba ta qazantar da kunya za ta hana halak samun muhalli ba. idan kuna son juna ai abu ne mai sauqi”.
Sanah B ta sake girgiza kai.
“Wallahi ko da wani ne can daban ba El-Moonsir da na san yana mutuwar sonki ba, ba zan iya aurensa ba, duk da kuwa alqawarinmu na rayuwa tare ai ba mu manta haqqin Allah da hukuncin da ya shimfixa na hana auren ya da qanwa...”
Sanah A ta katse ta.
“Ai ni ba aurensa na yi ba bare ki kawo qaharun hana aurenki da shi”.
Sanah B ta amsa mata.
“Don Allah ki daina ma wannan maganar, El-Moonsir yana sonki, idan kika rasa shi bana jin za ki samu namijin da zai so ki kamarsa”.
Da sauri Sanah A ta ce.
“To albishirinki! Ba shi ba da kike qawar na aura ba, saboda wani banzan hasashenki. Ko wanda ya fi shi lalacewa da rashin dacewar mu’amala auratayya ne ba zan aura ba. Ni ba zan yi aure ba har abada! Ba na son aure! Ba na son ko maganarsa, don haka kullum nake so ki koma gida ki yi aure kin qi tunda kina qawarsa”.
Sanah B ta dinga gyaxa kai, ta ce.
“Subhanallah! Don Allah Sanah yaushe za ki daina wannan mummunan furucin na kin tsani aure?”
Kai tsaye Sanah A ta amsa mata.
“Ranar da numfashina ya xauke, gangar jikina ta daina motsi! Bari kuma El-Moonsir ya zo, zan faxa masa hukuncin da na yanke kamar yadda na sanar da shi jiya na haramta masa zuwa inda nake har abada, na haramta!”
Tana qarashe faxar haka ta yunqura za ta shige xaki, sai ga El-Moonsir, don haka ta dawo ta zauna tana hura hanci.
Sanah B ta gaishe da shi, ya amsa tare da cewa.
“Jiya fa kin yi kasuwa, wani saurayi ya biyo mu wai yana sonki, ya nemi izinin zuwa gurinki”.
Wani sanyin daxi ya shige ta ba don farin cikin ta samu masoyi ba, sai don farin cikin ya yi riga malam masallaci kafin Sanah A ta furta shirmenta, a qalla dai da kunya ko da ta furta shirmen ya yi tasiri a gare shi, musamman ganin shi ya fara karvar zancen saurayin.
Kafin Sanah A ta yi magana sai ta yi saurin faxaxa fuskarta da murmushi, ta ce.
“Kai amma na yi farin ciki, ka ba shi izinin?”
Ya ce, “Eh na ce ya zo yau da yamma”.
Sanah A ta tsomo baki.
“El-Moonsir wata ya qare, ‘yan nefa za su iya zuwa kowane lokaci karvar kuxin wuta. Haka masu ruwan famfo, sannan kayan abincinmu sun yi low”.
Farin ciki ya shige shi jin ta tanka masa har ta soma lissafo hidimomin da yake musu, yana ganin tunda har ta tunasar da shi wata ya qare zai samu nasarar sanyaya mata zuciya.
Cike da karsashi ya ce.
“Ina sane, anjima zan fiddo kuxi a ban...”
Bai qarasa ba ta katse shi.
“Ban lissafo ba don ka yi xawainiya ba. na lissafo ne don ka sani, kamar yadda na ce na nesanta kaina daga gare ka, qarewar watan yana nufin qarewar duk wata xawainiya da ka ke min. Ni ba na so, kar ka qara kashe kobonka a domin ni! Wadda ka xauka ka kai wa mahaifiyarka a matsayin matar aurenka za ka iya ci gaba da yi mata xawainiya, ni zaman kaina nake ba zaman wani qaton ma’ahu ba. Kuma ina sanar da kai na ba ka ita, ka ci gaba da neman aurenta”.
Duk da tuquqin da furucin nata ya haifar masa, maganarta ta qarshe sai ta sa shi dariya, don ya gano zafin kishi ne ya motsa, bai barta ba har sai da ya dangano da ‘yar uwarta, kai mata masu sha’ani, kishi ba wasa! Ya yi dariya sosai, sannan ya ce.
“Ai kin makaro, domin bakin alqalami ya riga ya bushe, ke idanuna suka fara gani, zuciyata ta amince da qaunarki ba Sanah ba! da a ce ita na fara so wallahi ko kallo ba za ki ishe ni ba, don haka lissafinki ya zamo shirme! Ke nake so, kuma...”
Zumbur ta miqe tsaye, ta iso gabansa.
“Wallahi ba na sonka! Ba zan aure ka ba, idan ka isa ka sa dole na so ka”.
Ya miqe shi ma yana faxin.
“Na isa mana, tunda ga shi har kin taqarqare kina nuna soyayya. Ai sarai na gano ki naki salon soyayyar kenan na ture abin da kike so don kada a zarge ki kin cika rashin kunya”.
Ta ce, “Gargaxi na qarshe da zan yi maka a kan gidan nan ne, Little Sanah ba ‘yarka ba ce, ba ka da gadonta, wannan gidan kuma mallakinta ne don haka kada ka qara shigo shi”.
Ya ce, “Ko da ba na amsa sunan ubanta na haqiqa da na bogi, ubanta aminina ne, uwarta aminiyata ce, haka xayar uwar da ba ta cancanta zamowa uwarta ba matar da nake burin aure ce”.
Ai wannan furuci nasa ya tunzura Sanah A, kawai sai ta cakumi wuyansa ta fashe da kuka.
“Ka fitine ni, ka fitini rayuwata El-Moonsir, me na tsare maka da ka ke son ganin bayana?”
Bai damu da riqe wuyansa da ta yi ba, ya ce.
“Ke kika fitini kanki Sanah, ke kike haifar wa kanki matsalolinki, amma ni alkhairi ne a gare ki”.
Ta sha majina, sannan ta ce.
“Alkhairin banza? Na ce ba na yi, ba na yi. Ka qyale ni”.
Murmushi kawai ya ci gaba da yi, yayin da Sanah B ta zuba musu idanu tana kallon ikon Allah. Ta yi hargaginta ta gama sam bai qara cewa da ita ko uffan ba, dole ta koma kan kujera ragwaf ta zauna.
Bai kulata ba, sai ya maida dubansa ga Sanah B ya ce.
“Anjima da yamma sai ki zamo cikin shiri zai zo ku gana”.
Ta ce, “To”.
Misalin qarfe uku da mintuna arba’in da biyar El-Moonsir ya fito daga masallacin da ke layin su Sanah, kai tsaye gidan ya nufa. Ransa ya yi fari yadda ya ga Sanah B ta shirya abin tarar baqon, ta kuma kimtsa kanta cikin shigar da ta saba, wato shigar mutumci, ya yi murmushin jin daxi ya ce.
“Da ma kura na sauya launi kamar yadda hawainiya ke sauyawa, da ta kama dabbobi da yawa cikin ruwan sanyi”.
Sanah B ta yi dariya ta ce.
“Kai kuma da azancin magana kamar ba likijta ba”.
Ya zauna a kan kujera sannan ya ce.
“To a sammin abin tarar baqon na xanxana na ji idan ya yi daxi”.
Ba musu ta durqusa gaban kayan ta zuba masa a faranti, ta ajiye a gabansa.
Kamar an jehota kawai sai gani ya yi ta xau farantin abincin ta kife masa a jiki.
Tsananin mamaki da vacin rai ya hana shi magana, illa bin ta da kallo kawai da ya yi, ita kanta Sanah B kusan daskarewa ta yi a gurin, wulaqancin ya kai mizanin da ya wuce mamaki illa takaici, yau ko da a ce El-Moonsir ba mai kyakkyawar niyya ba ne a gare ta bai dace ta yi masa haka ba. Kai gaba xaya abin da ta yi ba ya daga cikin hankali, shirme da wauta ne suka yi mata jagorancin sakar wa shaixan linzamin tunani da dacewarta.
Kafin xaya daga cikin Sanah B da El-Moonsir ya tanka, sai Sanah A ta yi yalwatacciyar dariya idanunta tar a kan El-Moonsir, haka muryarta sam babu damuwa ta soma cewa.
“El-Moonsir ka san dalilin da ya sa na yi maka haka?”
Ba ta jira amsarsa ba, don ba ta buqata, ta xora.
“Na yi maka haka ne don na tabbatar da qiyayyata a gare ka, ina fatan wannan hukunci da na yi maka zai sa ka cire ni daga zuciyarka”.
Da ya ji abin da ta faxa, ya kuma tausashi zuciyarsa daga tsanantaccen hukuncin da ta shirya masa ya yanke mata, sai ya yi irin murmushin nan nasa mai tura mata haushi, ya ce.
“Ki nuna min tsantsar qiyayya ko dai ki nuna xokantuwarki a kan soyayyar da kike min? Wai ina tunaninki yake zuwa ne da kike manta farin sanin da na yi miki? Tun fil’azal fa na san ke mace ce mai nuna kulawa ga abin da kike so ta hanyoyi mabambanta, me ya sa kike tunanin zan gaza sanya wannan abin da kike min a matsayin kulawa ta tsananin soyayya?
To bari ki ji karatun kurma mai sauqin fahimta ne ga mutum mai hankali. Duk abin da za ki yi min babu abin da zai sanya na cire soyayyarki a zuciyata”.
Ya miqe tsaye ya dunqule hannunsa na dama yana dukan tafin hannunsa na hagu, cikin raunanniyar murya ya ci gaba da cewa.
“Kaico! Kaico da zuciyar da ke manta alkhairi, zuciyar da zafin rashi ba ya sa ta nadama sai dai tunzurawa, kaico... kaico... kaico!!!”
Ya dinga nanata wannan kalma a bakinsa, idanunsa na qoqarin kasa juriyar da ya aro don hana zubar qwallansa, sai dai kallo xaya za ka yi wa idanun ka san sun gama jiquwa da tsananin tashin hankali, domin sun rine.
Sanah A ta samu guri ta zauna fuskarta ba ta nuna karaya ba, sai dai zuciyar fa ta gama narkewa da tsananin nadama. Rashi ya dilmiyar da ita tashin hankali, ya sanya ta shiga taskar qure tandun tozarta, koyaushe ta kan yi kuka da rashi, ta kan kuma saka shi cikin lissafinta na rashin komai na alfanu a rayuwarta.
Ba don rashi ba haqiqa da samu ya baibaye ta, ya baibaye duk wani gurbi da rashi kan iya samun masaqa ko da ta allura ce. Ta sani tana son El-Moonsir, sai dai kalmar aure ce ba ta son ta shiga tsakaninsu, wanda ita kanta ba za ta iya canko illar da ta zamo jigon hana ta jin sha’awar auren nasa ba, illa za ta iya xorar da cewa abadan da’iman ba ta jin aure zai zamo malafa a rayuwar jin daxinta, dolen da ta sa ba za ta kuma dawo da hannun agogo baya ba tunda rashi ya baibaye ta.
Yayin da vangaren Sanah B ta ke kuma jinjina qarfin son da El-Moonsir ke wa ‘yar uwarta wanda ta ke rufe ido ta qi gani. Shiru na mintoci ya shiga tsakaninsu, sannan El-Moonsir ya girgiza kai, ya ce.
“Haqiqa da kina tuna mafara da maqara da qarfin tauhidi ya kuma shigarki har ki duba cancantar abin da ake kwaxaita miki... amma ba komai Sanah, ina taya ki addu’a Allah ya karkato da ke hanya madaidaiciya”.
Ya qarashe maganar cikin qara raunanar da murya.
Sanah A ta yi qarfin halin cewa.
“El-Moonsir, ni fa ba aurenka zan yi ba, duk wannan dogon sharhin da kake babu abin da yake amfanar da ni, don haka ka daina wahalar da kanka”.
Ta nuna Sanah B ta ci gaba da cewa.
“Waccan ita ta fi cancanta da zamowa matar aure, saboda dalilai masu qarfi. Na farko ita ce tsarkakkiyar uwar da ya dace ta haifo xan da za a yi alfahari da abin da ta haifa. Na biyu, abar tausayi ce kasancewarta marainiya, ba uwa ba uba, ba dangi ba gata... to kuma cikin hukuncin Allah sai ya haxa BALA da BALARABIYA, me ya yi saura? Aure!”
Ta dire maganar tata, idanunta na juyawa vangare biyu wato vangaren Sanah B da vangaren El-Moonsir, da kuma manufar kallon da ta ke musu qarara da bai wuce na su ne ta ke nufi harshent ya cafko a furucinta.
El-Moonsir ya shiga tsananin fushi saboda maimaita wannan qudiri da ta ke, amma sai ya share ta, ya qi kulata ita kuma sai ta yi shiru kamar an katse jijiyoyin jikinta.
Wayar El-Moonsir ta yi qara, tun kafin ya duba ya fara kissima mai kiran, saboda sanin akwai alqawarin haxuwarsu, ilai kuwa Muftahu ne a kan wayar.
Sai da ya dubi Sanah B sannan ya kara wayar a kunne yana faxin.
“Ya aka yi ne Mufty? Ka iso ne... to ga ni nan fitowa”.
Ya kashe wayar tukunna ya xora idanunsa ga Sanah A, ya ce.
“Don Allah ina roqonki alfarma ki koma xaki idan har kin san ba za ki taya mu karvar baqonmu cikin aminci ba, shaixan shi ne yake hana haxa alkhairi...”
Kafin ya qarasa ta taso masa da cewa.
“Okey, ni ce shaixan xin kenan?”
Sam fuskarsa babu damuwa ya ce.
“Ni ban ce ba, alfarma dai ce na roqa, na sankuma ko ba a sona na roqa za a yi min”.
Ya miqe tsaye ya fice zuwa wajen gidan.
Ya hango Muftahu cikin motarsa, ya isa tare da ce masa ya qaraso. Suka shiga cikin falon suna masu fara’a.
Sanah A ta koma xaki don haka Sanah B kaxai suka tarar.
Babu dogon surutu bayan Muftahu ya kammala ci da shan abin da aka tare shi da su, El-Moonsir ya sake bayyana wa Sanah abin da ya kawo Muftahu.
Ta kuma nuna masa amincewarta tare da fatan Allah Ubangiji ya tabbatar da lamarin nasu.
*** *** ***
Tun daga ranar kuma El-Moonsir ya xauke wa gidan qafa don ba wa Sanah A sarari kamar yadda ta buqata, abu xaya ya yi, wato washegarin zuwan Muftahun ya aiko direbansa da kayan masarufi kamar yadda ya saba yi musu, sai kuxin ruwa da na wutar lantarki da ya je ya biya.
Bayan kwana goma Muftahu ya zo wajen Sanah, yau kam ya turke ta da tambayoyi, bayan da suna zaune ya ga Sanah A ta fito cikin shigar qananun kaya kanta ya sha gashin doki babu xankwali, ga kayan sun matse ta tsam ta zo ta dire Little Sanah a jikin Sanah B, sannan ba tare da ta maida kai ga Muftahu bare ya samu arziqin gaisuwa ta sa kai ta fice, wanda a lokacin qarfe takwas da minti goma na dare.
Abin da ya ja hankalinsa yi wa Sanah B tambayoyin kenan, ina iyayensu da za su bar Sanah A ta yi wannan shigar ta fita a daidai wannan lokacin? Sannan ina mahaifiyar Little Sanah ne?
Ba ta amsa masa tambaya ta farko ba, sai ta biyu da tana duban yarinyar ta ce.
“Ba zan voye maka ba Muftahu, maganar gaskiya ta fi nagarta a kan maganar ado. Wannan yarinyar da kake gani mu biyu muka haife ta”.
Ya yi murmushi ya ce.
“To in ba cin abinki da ma mutum xaya na haihuwa ne? Ina nufin ‘yarki ce da kika haifa a cikinki?”
Ta xaga kai da cewa.
“Qwarai ‘yata ce, kuma xiyar ‘yar uwata da ta fita yanzu, ya zamo mu biyu ni da ita kenan muka haifi yarinyar”.
Wannan karon kallon mamaki yake mata, muryarsa na nuna shakku ya ce.
“Ku biyu ku ka haife ta? Mace da mace suna samar da xa? Da mamaki! Amma don Allah idan ba za ki damu ba ina so ki yi min gamsasshen bayani”.
Ta girgiza kai, ta ce.
“Bayanin kenan Muty, ni da ‘yar uwata muka haifi ‘yarmu".
Sai ya yi shiru bai ce komai ba tsayin mintoci, ya shiga ruxani matuqa, tabbas bai tava jin kwatankwacin wannan labarin mai kama da almara ba, don haka ya kasa yardar wa kansa gaskiyar da ta ke nufi...
“Bari na kwantar da Little Sanah”.
Ta katse masa dogon tunanin da yake ta hanyar miqewa tsaye. Bai tanka ba ta shige bedroom, jim kaxan ta dawo.
“Sanah haqiqa yau ce ranar farko da na tava riskar labarin da ya rikita min tunani ya sa ni damuwa mai yawa. To amma shi lamarin Ubangiji girma ne da shi, yana saukar da ayoyinsa a lokacin da wata halitta ba ta sani ba... Idan zai yiwu zan so ki faxa min yadda aka yi kuka xauki ciki har kuka haife shi ku biyu... a taqaice dai ina nufin ki ba ni tarihin rayuwarki”.
Abin da Muftahu ya faxa kenan, idanunsa a kanta. Ta ce.
“Labarin yadda muka haifi Little Sanah labari ne da rashi ya baibaye shi, saboda haka ba shi da amfanin tayarwa, illa iyaka duk wanda zai aure ni akwai sharuxxa guda biyu kawai da za su shiga tsakaninmu, su suka fi muhimmanci fiye da jin labarin samuwar Little Sanah”.
Bai tanka ba, kallonta kawai ya ke. Ta risinar da kanta qasa, sannan ta ci gaba da cewa.
“Muftahu, a ‘yan kwanakin da muka yi da haxuwa na gamsu da irin son da kake min na gaskikya, kuma na yi amanna ka cancanta zamo wa miji a gare ni. Sai dai bisa sharuxxan da na faxa, na farko za ka aure ni a matsayin bazawara! Na biyu ba iyayena ne za su xaura mana aure ba...”
Jin haka da ta faxa ya gane tana son ta auna mizanin son da yake mata, don haka cikin nuna rashin kula ya ce.
“Na ji, mu bar maganar yanzu, zan yi shawara da zuciyata”.
Haka xin kuwa, daga wannan rana ba su qara tada magana makamanciyar wannan ba, sai dai shi a gare shi ya zuba idanu, ya kuma buxe qofofin nazari da ke cikin kwanyarsa don gano wace ce Sanah?
Cikin hukuncin Ubangiji ya fuskanci abubuwa da yawa daga ciki har da ganowa zaman kansu suke, ma’ana ba a gaban iyayensu suke ba, kuma ya gano Sanah A karuwa ce, yayin da xayar ya rasa matsayin da zai ajiye ta a kai. Bai dai tava rutsa ta da shigar banza ko ya tarar da wani namiji tare da ita ba, koyaushe zai ganta cikin kamala ta ke, sannan uwa uba ga riqo da addini.
Abu xaya yanzu ya tsaya a ransa shi ne, ta faxa masa abin da ya rabo ta da iyayenta, wanda har ya sa ba ta son jivanta lamarin aurenta da su, ga shi dai ba ta yi masa kama da kirista ba bare ya ce ko don ta musulunta ne suka rabu da mahaifanta.
Abin da ke qara xaure masa kai da sanya shi ruxani shi ne maganar Little Sanah wanda ta ce ita da ‘yar uwarta suka haife ta, shin mene ne gaskiyar lamarin?
A vangarensu kuwa rashin zuwan El-Moonsir a gidan ya dame su su duka biyun, sai dai qarfin hali irin na Sanah A ta qi nunawa sai ma nunawa da ta ke rashin zuwan nasa ya sama mata kwanciyar hankali, ya kuma ba ta damar watayawa, don maza ta ke kawo wa a gidan sosai, ga Nazeer da suka yi wata irin xinkewa ta ban mamaki, sai dai matsalar bai tava nuna kishinsa a kan mazan da ta ke tare da su ba, zai dai nuna mata soyayya, ya kuma yi mata duk abin da ta ke so.
Wannan rashin nuna kishin nasa na tuno mata da El-Moonsir, har yake sanya ta kewarsa.
Haqiqa yanzu ta ke gano abin da yake nunar da ita, wato shi masoyi ne a gare ta na haqiqa, duba da cewa, so na gaskiya na tafiya da kishin abin da ake so, idan kuwa babu kishin to kuwa son ba na gaskiya ba ne sai dai sha’awa.
An kwarari mako biyu shiru babu wani labarinsa, ga shi idan Sanah B ta kira wayarsa a kashe ta ke samunta.
Wata zuciyar na ba ta shawara ta je gidansu ta gani ko lafiya? Sai kuma ta yi tunanin idan ta je ta tarar da shi lafiya abu biyu ne zai faru, wato shi ya xauka maganar Sanah A ta tabbata, tana son ya aure ta, ko kuma iyayensa su ga rashin kunyarta ta vata tsarin da yake muradin tsarawa na iyayensa su yaba da zavin da ya yo na ‘yar gidan qwarai.
Ai rashin mutumcin da Sanah A ke masa ya ci ya yi fushin da ya fi haka ma, to amma idan rashin lafiya ce ta voye shi ya zai xauke su, ko kuma ya zai xauke ta tunda ya san abin da Sanah A ke muradi kenan ta daina ganinsa? Zai xaukew ta a matsayin wadda ba ta yaba alheri bare ta kula da rashin mai alherin.
Ta shiga cikin raba hankali biyu a wannan vigire, sai kuma ga soyayyar Muftahu da ke mata dukan kawo wuqa. Tana jinsa sosai a ranta, ya kuma cancanta ya zamo miji a gare ta, sai dai duk da soyayyar da yake nuna mata hakan bai mantar daita qalubalen da kan iya bibiyar yiyuwar aurensu. Wato tunanin anya mahaifansa za su amince da sharaxinta, a ce limamin masallaci zai zamo waliyinta, ina hujjar yin haka? Ai wannan makamar wata tatsuniya ce da ake yi wa yara don faxaxa kaifin qwalwarsu.
Ba su da matsalar abinci, ko wani abin amfani na yau da kullum, amma kallo xaya za ka yi musu ka gane suna cikin halin razani, domin su duka biyun sun rame, tamkar waxanda suka yi rashin lafiya.
A ranar da aka cika kwanaki ashirin Sanah A ta kasa jure yanayin da ta ke ciki na qunci da fargaba, ta risko Sanah B a xaki tana lunke kayan Little Sanah da ta kawo daga shanya.
Ta zauna a gefen gadon ta xau wata riga tana valle mavallin sannan murya a raunane kamar mai tsoron furta abin da ta ke son furtawa, ta ce.
“Wai Sanah, kina da labarin El-Moonsir kuwa?”
Sanah B da ke qoqarin linke wani wando ta kasa qarasawa, ta xago kai ta dubi Sanah A cike da tsananin mamaki, duk da a wani vangaren bai kamata ta yi mamakin ba, idan ta yi la’akari da yanayin quncin da ta ke ciki, da kuma ramar da ta ke yi, ta yi kama da wadda ta yi rashi irin rashin da ya zama sababben abu a gare su.
Kamar za ta yi mata tambihi a kan tambayarta, sai ta ga yin hakan mayar da hannun agogo baya ne, abokin kuka ai ba a voye masa mutuwa, ko ma ba don haka ba, ita da ma ta san in ta rina za ta yi shuxi, ma’ana ta san Sanah tana son El-Moonsir kawai miskilanci da halin nata na tsiwa ke mata jagoranci. Saboda haka muryarta a sanyaye ta ce.
“Wallahi ba ni da labarinsa”.
Sanah A ta yi tsam da ransa, can ta ce.
“Kin kira shi a waya?”
Ta ce, “Na kira duka layukansa a kashe”.
Ta ci gaba da abin da ta ke, ita kuma ta qara jeho mata wata tambayar.
“Ai kin san gidansu, me zai hana ki je ki gani?”
Girgiza kai ta yi, ta ce.
“Babu amfanin zuwa, da ma ke ya ke so, kin kuma ce ba kya yi, ina ganin ya haqura ne”.
Kamar maganar ba ta yi mata daxi ba, don gaba xaya annurin fuskarta gushewa ya yi. Daga qarshe ma sai ta fice daga xakin.
*** *** ***
A hankali ta xaga kai ta dubi agogon da ke manne a jikin bangon falon, wadda ta nuna qarfe biyar na yammaci. Ta maido kan nata saitin akwatin talabijin, sannan murya a cushe ta ce.
“Sanah wannan shirin fim xin ya yi min kyau, me kika fahimta a saqon da yake isarwa?”
Sanah B ta yi murmushi ta ce.
“Ai saqo ne kai tsaye ga rayuwa ta zahiri, ki duba yadda Laila ta saqa zaruruwan yaudara mazan na ruftawa. Kin ga kenan duk wanda zai kalli shirin zai gane ba kowace soyayya da ke bayyane ta ke ta gaskiya ba”.
Sanah A ta jinjina kai, ta ce.
“Da kyau, ni ma abin da na fahimta ke nan, sai dai ba ki ga labarin shirin ya yi shige da rayuwata ba?”
Sanah B ta yi shiru tana nazari, ita kam ta ko’ina ba ta ga inda za a alaqanta shirin da rayuwar ‘yar uwarta ba, domin yadda ake nuna wa tauraruwar shirin wato Laila tana kula mazaje da yawa, kowanne kuma da sunan tana sonsa. Da mutum ya sakankance sai ta xibga masa damfarar da zai daxe bai cike gurbinta ba, ya neme ta sama ko qasa. To ta ya za a jivanta shirin da rayuwar ‘yar uwarta? Ta girgiza kai, ta ce.
“Ko kusa wannan shirin bai yi shige da rayuwarki ba”.
Sanah A ta yi malalacin murmushi, ta ce.
“Da ma na san zai yi wahala ki gane, amma bari na yi miki fashin baqi”.
Ta gyara zama tare da latsa pause a jikin remote, ta xora idanunta a kan Sanah B, ta ci gaba da cewa.
“Idan furen fulawa ya fito za ki ga ya zama abin burgewa ga kowa, saboda qamshin da yake da shi da kuma qyallin da ke xaukar hankalin ma’abota kallonsa. Amma da zarar rana ta bugi furen zai soma yin yaushi, zuwa yamma ki ga ya sauya kala. Da an qara kwana xaya rana ta sake dukansa sai ya bushe yana murmurewa...”
Ta yi shiru tana ci gaba da duban Sanah B yayin da farin ciki ya lulluve Sana B saboda tana tunanin wannan misali da ta kawo ita ya shafam, wato ta fara gano mazan da ke sinsinarta ba alfanu ba ne a gare ta.
Shiru na wani lokaci ya gilma a tsakaninsu, sannan daga bisani ta ci gaba da cewa.
“Yadda furen fulawa ya zama abin burgewa ga ma’abota kallonsa, ya kuma zama abin kawar da idanu lokacin da ya dusashe daga qyallin da yake, to haka mace ma ta ke a gurin maza.
Xauki misali a kaina, dubi yadda Abdulhalim ya nuna min so, qauna, da gata. Amma lokaci xaya ya guje ni!”
Da sauri Sanah B ta ce.
“Ban gane ya guje ki bayan mutuwa ce ta raba ku?”
Sanah A ta yi murmushi mai bayyanar da xumbin takaici, ta ce.
“A ganinki mutuwa ce ta raba mu, amma a lissafina da kuma nazarina na gano kura da fatar akuya ce, shiryayyen abu ne da ke ba za ki gane ba, saboda raunin tunani da wayewarki a halayyar mutane ‘yan bariki... Kada ki tsinka ni, bari na qarasa miki bayanina wata qila ki haskaka daga duhun da ba ki gane ba”.
Ta gyara zama, ta ci gaba da cewa.
“Bayan shuxewar Abdulhalim sai aka kawo El-Moonsir wanda ya taka rawa kwatankwacin ta Abdulhalim, yanzu kuma ya shuxe ba tare da an yi amfani da wancan salon ba, wata qila yau, gobe, jibi... ko mako mai zuwa a villo da wancan salon... Amma daxin abin wannan karon xan koli bai ci riba ba...”
Tana qarashe faxar haka sai ta miqe tsaye tana tafa hannaye.
“Abdulhalim da El-Moonsir suna qullin da suke tunanin raunina na kasancewata ‘ya mace ba zan gane ba”.
Sam Sanah B ta kasa fahimtar zantukan, hasalima sai ta yi mata duban wadda zafin so ya soma tavuwa a kwanyarta.
Ba ta tanka ba, sai da ta zauna sannan ta ce.
“Idan har kina nufin Abdulhalim bai mutu ba aka kawo mana labarin mutuwarsa, me ya sa ya yi haka? Sannan a matsayin El-Moonsir na abokinsa kina ganin zai rungumi Little Sanah a matsayin ‘yarsa ba tare da ya sadata ga El-Moonsir ba? Kada ki ruxa kanki mana saboda zafin son da ki ke wa El-Moonsir, maimakon haka me zai hana ki je gidansu ki gani?”
Sanah A ta ce, “Yan barikin ake wa wannan karar? Shi ya sa na ce miki ba za ki gane ba, rayuwar bariki ba irin taki ba ce, ba ki san shu’umancin da ke cikinta ba.
An sha kashe mutum da ransa a cikin rayuwar bariki saboda wasu dalilai, wata qila gundura da rashin rabo! Amma idan har zan yarda wannan hasashen ba gaskiya ba ne zan sake ganin El-Moonsir a rayu...”
Wayarta ta yi qara, don haka ta dakata daga maganar da ta ke, tana murmushi ta jkara wayar a kunnenta.
“Ina ciki”.
Abin da ta ce kenan ta kashe wayar, ta maida dubanta ga Sanah B tana cewa.
“Na yi tuya na manta da albasa, wato na manta na sanar da ke Nazeer zai zo, ga shi nan ya iso, don haka kina iya komawa ciki”.
Tun ma kafin ta qarasa faxa Sanah B ta shige bedroom ta kwanta a kan gado tana kissima abubuwa da dama.
Lallai ‘yar uwarta tana gab da zautuwa a kan rashin El-Moonsir, tunda har ta ke son kawo rashin tauhidi (yarda da qaddara) a rayuwarta, tabbas akwai buqatar ta nemo El-Moonsir idan fushi ya yi ta ba shi haquri ya dawo, idan kuma rashin lafiya ce ma duk ba zai gagara ba.
Washegari da safe ta isa asibitin da yake aiki, amma sai ta taki rashin sa’a, wai ba ya ma qasar gaba xaya, sun je wani kwas na wata shida a qasar Singpore. Ta dawo wa Sanah A da wannan bayani.
Ba ta gamsu ba, domin tana ganin kamar ta faxa mata haka ne don kada ita daga hasashenta.
Kwatsam ranar juma’a da yamma sai ga El-Moonsir ya iso gidan, lokacin ma Sanah A ba ta nan. Ya zauna suka tattauna da Sanah B, inda ta shaida masa duk halin da Sanah A ta ke ciki, ya yi farin cikin faruwar haka, da ma yana da yaqinin hakan za ta iya faruwa a lokacin da ba wa Sanah sarari, rashin ganinsa kusa da ita zai iya juya akalarta, sai ga shi hakan ta tabbata.
Kasa barin gidan ya yi saboda farin ciki, ya zauna zaman jiran dawowarta.
Ashe dawon bai kirvu ba, lokacin da Sanah A ta tashi dawowa gidan ba ta zo ita kaxai ba, sai da rakiyar Nazeer, kuma ko da ta shigo ta tarar da El-Moonsir duk da begen ganinsa da ta ke, amma sai ta basar kai tsaye suka zube falon ita da Nazeer.
El-Moonsir ya yi kicin-kicin da fuskarsa, wato mai hali ba ya fasa halinsa, haka gargaxin da ya yi wa Nazeer bai shige shi ba kenan?
Ba qaramin artabu ya yi da zuciyarsa ba ya danne vacin ransa don kada ta ga wallensa. Sai ma ya xauke kai kamar bai san da wanzuwarsu ba.
Su kuwa kamar da gayya sai suka buxe wani babin hirar suna shewa da dariya har da tafawa.
Sanah B da tsananin vacin rai ya gama turnuqe ta, sai ta tashi tana duban El-Moonsir ta ce.
“To El-Moonsir, Allah huta gajiya”.
Shi ma ya miqe cikin tave baki ya ce.
“Allah ya kai mu, ni ma tafiya zan yi don kaina ya matsa min da ciwo”.
Haka ya sa kai ya fice bai ko dubi inda suke ba, abin da ya matuqar tunzurar da ita kenan, domin ta so ya tanka a tuna baya, duk da cewa ko da ta shigo falon suka yi tozali da juna sai da gabanta ya faxi, da ma sarai ta san ita ya yi wa qaura, kuma da sanin Sanah B shi ya sa ta yi waxancan zantukan, kuma sai ga shi sun yi amfani.
Sai dai ta xauka yana nan a El-Moonsir xinsa na da mai nuna kishi a kanta, ashe ta kai shi gejin da ko duba ba ta ishe shi ba? Wayyo Allah ai ji ta yi tamkar ta bi shi ta hana shi fitar.
To dai hakan ta ci gaba da faruwa a tsakaninsu, zai zo gidan ya yini cur ba tare da ya matsu ya yi mata magana ba, kamar yadda ita ma ta qi yi masa maganar, sai dai kallo da neman abin da zai kusanta su da juna. Yayin da Sanah B ta zama ‘yar kallo a tsakaninsu suna kuma burge ta, saboda matakin da kowanne ya xauka na dojewa da juna ga shi dai yanayinsu na nuna buqatuwarsu da son ci gaba da mu’amalarsu, girman kai ko kuma a ce miskilanci da kowa ya sa wa ransa ya hana su kula juna.
To amma dawowar El-Moonsir a rayuwarsu ko ba komai ya taka wata rawar, domin Sanah A ta rage kawo tarkacen samarin nata, wata qila hikimar hakan ba za ta wuce ta nuna masa salon nata son ba.
Shi kansa Nazeer da ke kara-kaina ya rage zuwa gidan, ba kuma don ya samu umarnin daina zuwa daga vangarorin biyu (Sanah da El-Moonsir) ba.
A haka aka kwashe watanni biyu wanda a lokacin Little Sanah ta cika watanni takwas da haihuwa har ta fara koyon tsayuwa. A wannan lokaci El-Moonsir ya soma zubar da makamansa ganin yadda Sanah A ke shisshige wa lamuransa.
Muftahu ya zo gidan ya tarar da El-Moonsir inda suka tattauna game da lamarin aurensa da Sanah B, ya kora masa bayanin duk yadda suka yi, daga qarshe ya xora da faxin.
“To maganar gaskiya ni ina son Sanah, amma ysarin da ta biyo da shi ne tarnaqin da zai lulluve yiyuwar aurenmu. A taqaice dai ina so ka ba ni tabbacin wace ce Sanah?”
El-Moonsir ya yi jim na wani lokaci, sannan ya ce.
“Babu abin da zan ce da kai a yanzu, sai dai ka ba ni sati xaya, insha Allah za ka samu amsarka”.
A haka suka rabu, El-Moonsir ya rasa yadda zai hudo wa lamarin, tabbas ya fahimci Muftahu yana son Sanah fisabilillah, to amma ta ya za a yi aurensu ya tabbata ba tare da iyayen Sanah sun jagoranci lamarin ba? shi kansa damuwar da yake da ita kena, wato yadda zai shawo kan mahaifansa har ya auri Sanah, koda yake yana tunanin samo wasu mutanen ya xora su a matsayin su ne mahaifanta, duk da cewa har yanzu tana kan bakanta na cewar, babu ita babu aure!
*** *** ***
Ranar juma’a da yamma Sanah A ta shigo gidan ta tarar da Sanah B a kicin tana qoqarin yin girkin dare, ta ce.
“Don Allah idan kin gama yanka kabejin ina son magana da ke”.
Sanah B ta juyo ta dube ta, ta ce, “To”.
Bayan ta gama ta nufi bedroom ta tarar da ita zaune a gefen gado tana shirya kaya a jaka. Ta nemi guri ta zauna ba tare da ta ce komai ba, Sanah A ta juyo ta dube ta da murmushi a fuskarta ta ce.
“Wata tafiya ce ta same ni zuwa Abuja, zan yi kwanaki uku zuwa huxu, shi ne nake son yin sallama da ke”.
Sanah B ta kafe ta da idanu, ta ce.
“Y aza a yi da Little Sanah?”
Wani duba ta yi mata.
“Kamar ya za a yi da ita? Ni kaxai zan tafi mana”.
Shiru Sanah B ta yi, ita kuma ta xora.
“Yarinyar da ta iya cin abinci mene ne abin damuwa don ta yi kwana uku ba ta sha nono ba? To ni da ma yaye ta zan yi, don ina da juna biyu!”
Daram! Maganar ta daki zuciyarta, ta maimaita juna biyu a ranta, sannan ta ce.
“Yanzu abin da kika yi kina ganin kin kyauta...?”
Kafin ta qarasa ta xaga mata hannu.
“Kada ki maida hannun agogo baya... ba huruminki ba ne titsiye ni maganar juna biyu, kuma ina mai sanar da ke ina son kayana, zan kuma haife abina... Ina so mu yi rabuwar arziqi da ke muna ganin juna da mutumci, don wata qila sai a darussalam mu sake haxuwa, saboda koyaushe mutuwa za ta iya giftawa”.
Sanah B ta gyara zamanta ta ce.
“Tunda kina tuna mutuwa me zai rufe miki idanu ki kasa hango makomarki?”
Ta ce, “Ba wannan ne abin duba ba, ke dai ki zamto mai yafiya a gare ni, ko da mutuwar za ta gifta. Sannan na san Little Sanah ‘yarki ce halak malak babu buqatar na ce ki riqe ta amana, dukiyarta na hannunki, komai nata ma dai kin sani...”
Ta qarashe maganar tare da ci gaba da haxa kayanta, Sanah B ta girgiza kai ta ce
“Ke da wa za ku tafi Abujan?”
“Ina ruwanki?” In ji ta, “Idan ma da mazan duniya zan tafi duka akwai abin da ya shalle ki?”
Jin yadda ta maido mata maganar ta ga rashin amfanin tsaywa ci gaba da sauraronta, kawai sai ta miqe ta koma kicin ranta na yi mata suya.
Sallamar tasu kenan, domin bayan ta gama haxa tarkacenta kai tsaye ta fice daga gidan, yayin da Sanah B ta bi ta da kallon rashin adalci irin nata, ai ko ba komai yadda Little Sanah ke fama da kwaikwai ya dace ta tsaya, amma shaixan ya buga mata gangarsa ta tsallake wai har kwana uku ko huxu ta ke kira za ta yi.
Wannan abu ya fi komai ci mata rai, ta qarashe daren ranar a cikin quncin zuciya da tsananin vacin rai.
Washegari El-Moonsir ya zo gidan da farin cikinsa, amma sai farin cikin ya juye masa zuwa baqin ciki sakamakon labarin da ya samu na tafiyar da Sanah ta yi.
Ya yi shiru cikin tagumi yana kissima abubuwa da yawa a ransa, ta tabbata dai Sanah ba za ta dawo yadda yake so ba, rabuwa da sha’aninta ya fi cancanta, sai dai zuciyarsa ta kasa wannan jarumtar, domin ji yake wannan bai zamo hujjar da zai rabu da ita xin ba, ya daure dai ya ci gaba da bibiyarta da yi mata fatan shiriya idan mai shiryuwar ce.
A nan ya ke faxa wa Sanah B yadda suka yi da Muftahu, ya kuma so ta ba shi tarihin rayuwar tasu a karo na barkatai da yake neman sanin hakan. Amma jiya iyau,domin kada baki ta yi ta ce.
“Ka yi haquri El-Moonsir, abin da kake son ji ba zai samu ba kamar yadda tun farko na sanar da kai. Labarin rayuwarmu wani irin bahagon labari ne da rashin jinsa zai fi fa’ida fiye da jinsa”.
Ya ce, “Abin da nake so na sani shi ne, iyayenku na raye? Wace jiha ko qasa ku ke? Idan kika faxa min wannan ya wadatar”.
Ta yi shiru na wani lokaci, sannan ta xago kai suka haxa idanu, ta ce.
“Na ji zan faxa maka labarinmu, amma ka yi haquri har Sanah ta dawo na nemi izini daga gare ta”.
Ransa ya xan vaci, amma ya jure ya qi bari ta gane, ya ce.
“Saboda kina tsoron kada ta yanka ki?”
Ta girgiza kai da faxin.
“Ba tsoron ta yanka ni nake ba, alqawari ne tsakaninmu babu wanda za mu buxe wa sirrinmu ba tare da amincewar xaya daga cikinmu ba”.
Ya ce, “Kin san adadin mutanen da ita ta buxe wa sirrin naki?”
Ta ce, “Ai da ta buxe lallai da kana cikin waxanda ba su buqatar ji daga gare ni. Ka yi haquri jibi ko gatan ta dawol, kada ka tursasani, domin ranka ne kawai zai vaci ba tare da ka ji ba”.
Ya yarda da ita xari bisa xari, ita mai ganin girmansa ce, ba ta son abin da zai vata ransa, misali idan Sanah A na masa xibar albarka wani lokaci har qwalla ta ke, wannan dalili ya sa ya haqure sai ta dawo xin.
“Kin san me?” Ya ce da ita.
Ta ce, “Sai ka faxa”.
Ya ce, “Tun jiya Safiyya ke damuna wai tana son na kawo ta gurin Sanah, to tunda ‘yar dabin ba ta nan, me zai hana na kawo ta anjima?”
Shiru ta yi tana nazari, sannan ta ce.
“Ni fa wallahi ina tsoratar maka wannan lamari, kana haxa ni da zuri’arku a matsayin ‘yar uwata, shin ba ka gudun ranar da balli zai tashi?”
Yana murmushi ya ce.
“Bna wani balli, insha Allah Biyu za ta dawo yadda muke tsammatar mata kafin mu yi aure”.
Ta ce, “To, shi kenan. Ni a gare ni abin farin ciki ne na taimaki ‘yar uwata samun sa’ar auren managarcin miji irinka, kai dai ne nake tausayawa domin...”
Ya yi saurin katse ta.
“Ni ma ya zamo abin farin ciki a gare ku na yi jihadi, ko kin fi son na zare hannuna a lamarin Biyu mu bar ta cikin wannan gurvatacciyar rayuwa?”
Ta amsa masa.
“A’a, ba zan so ta dauwama haka ba, zan so matuqa ta zamo uwa ta gari ga ‘ya’yan da za ta haifa a nan gaba”.
Ya ce, “To fatan da za mu ci gaba da yi kenan... bari na tafi anjima da yamma zan zo da ita xin, idan mun zo sai ki nuna mahaifiyarku ta tafi unguwa”.
Da sauri ta girgiza kai.
“Nan fa xaya, abin sai ya yi yawa, ga voyon wadda za ka aura, sannan kuma a shigo da wannan?”
Ya ce, “Ke dai ki yi yadda na ce”.
Ta tuvure da faxin.
“Ba fa zai yiwu ba, yaudarar ta yi yawa El-Moonsir, ka faxa musu gaskiya gudun samun tangarxa a gaba.... ka san dai ba mu da kowa a nan, don me za a nuna akwai mahaifiyarmu? Ba ka tunanin yau da gobe?”
Ya yarfa hannu.
“Oh shet! Shi ya sa aka ce zama da maxaukin kanwa na sa farin kai, wato ke ma kin fara koyon musu ko?”
Ta ce, “Allah ba maganar musu ba ne, ina tausayin soyayyarku ne, na tabbata duk ranar da mahaifanka suka gano yaudarar da ka yi musu sai an samu tangarxa”.
Ya ce, “Wannan kada ya dame ki, ba kin ce idan Biyu ta dawo za ki sanar da ni labarinku ba?”
Ta ce, “Ai ce maka na yi zan nemi izininta, ka ga idan ba ta amince ba ba za ka ji ba”.
Ya xan harare ta cikin wasa ya ce,.
“Ku dai kuna da matsala, xaya dama, xaya hagu...”
Ta katse shi.
“Ai BIYU KYAUTAR ALLAH kenan, dama da hauni rayuwar ta gada”.
Bai gane qarashen maganarta ba, don haka ya nemi fashin baqi, amma mursisi ta qi, sai dariya da ta ke masa.
A haka suka rabu zxai dawo da yamma, bayan tafiyarsa ta sake nutsawa duniyar tunani, haqiqa idan Sanah A ta rasa El-Moonsir ta yi BABBAN RASHI!
Ai kuwa da yammaci ya kawo Safiyya, ta kuwa ishi Sanah da tambayoyi cikin hikima kamar yadda ta ke mai yawan magana, sai kuma aka ci sa’a jininsu ya zo xaya da Sanar shi yasa ta biye mata tana amsa mata wasu tambayoyin. Cikin haka ne Safiyya ta ce.
“Wai ina uwar yarinyar nan ne na ga kina ba ta madara? Ko qanwarku ce?”
Sanah ta yi shiru tana satar kallon El-Moonsir wanda farax xaya ya gane me ta ke nufi, don haka ya yi saurin cewa.
“Qanwarta ce”.
Sai kuma ta qara jeho wata tambayar.
“Na so mu gaisa da Mummynku, ga shi ba ta nan, ko yaushe za ta dawo?”
Nan ma El-Moonsir ne ya ba ta amsa.
“Sai bayan kwana biyu”.
Ta fiddo idanu waje.
“Yanzu sai Mummyn ta yi kwana biyu ta bar yarinya qarama kamar wannan ana ba ta madara?”
El-Moonsir ya yi tsuru-tsuru saboda saurin ranfo shi da Safiyya ta yi, sai kuma wata dabara ta sake zuwar masa.
“Wasa nake miki, anjima da daddare za su dawo”.
Haka dai jefi-jefi ta dinga jeho mata tambayoyin, har gab magriba sannan El-Moonsir ya ce ta taso su tafi. Ta tuvure lallai sai ya bari Mummyn Sanah ta dawo su gaisa, sai da ya yi mata jan ido sannman ta tashi.
Sanah ta raka su har gurin mota, sannan ta dawo bayan sun tafi.
*** *** ***
Tun da safe Sanah B ta kira wayar El-Moonsir hankalinta a tashe. Yana xauka bayan sallama da ta yi masa ko gaishe shi ba ta tsaya yi ba ta ce.
“El-Moonsir, don Allah ka taimaka ka zo ka duba Little Sanah”.
Shi ma hankalinsa ya tashi ya ce.
“Lafiya kuwa?”
Ta ce, “Tun jiya da daddare ta ke kwance ba ta da lafiya, koda yake a tsaitsaye ta ke rashin lafiyar, jiya da yau ne abin ya tsananta”.
Ya ce, “Ok, ina nan zuwa”.
Cikin mintoci ya iso gidan, ya duba yarinyar sannan ya dawo da dubansa ga Sanah ya ce.
“Haqora ne ke wahalar da ita, na yi mamaki ma da har ta kawo yanzu ba ta yi ko xaya ba... Anjima idan zan dawo aiki zan taho mata da magunguna... ko kuma zan turo a kawo miki, insha Allahu za ta yi su da sauqi”.
Sai yanzu hankalinta ya kwanta, ta ce.
“To, na gode”.
Ya ce, “Ba damuwa... Kun yi waya da Sanah kuwa?”
Ta ce, “Ba ta kira ni ba, haka ni ma ban kira ta ba”.
Ya yi shiru na wani lokaci, sannan ya ce.
“Kin san me?”
Ta ce, “Sai ka faxa”.
Ya ce, “Kirawo ta yanzu a wayarki ki ji yaushe za ta dawo”.
Ta yi shiru, ta kuma tssare shi da idanu da son samunta ne ba za ta kirata ba ganin ita tunda ta tafi ba ta kira ta ba kuma ta san Little Sanah ba ta jin daxi, amma matsayin da El-Moonsir yake da shi a gare ta ya wuce ta musa masa, ko ba ma don haka ba yadda ya ke son Sanah ya dace ta tallafa masa, musamman idan ta yi la’akari da manufarsa, yana son Sanah ta dawo amma ba zai iya kiran wayarta ba gudun kada ta yi masa sababben halin nata.
Wannan ya sa ta tashi zuwa bedroom ta xauko wayarta ta dawo falon ta zauna, ta kira layin.
Ta yi ringin har ta katse ba a xauka ba. ta sake kira a karo na biyu, sannan ta xauka muryarta na nuna yanayin daga baci ta farka.
“Ya aka yi ne?”
Ta tambaya. Sanah B ta ce.
“Da ma na kira don na ji yaushe za ki dawo?”
Kamar ba za ta amsa ba, sai kuma ta amsa xin.
“Qila da azahar zan dawo, qila kuma sai la’asar. Amma tabbas yau zan dawo”.
Sanah B ta sauke gwauron numfashi bayan ta xauke wayar daga kunnenta, ta dubi El-Moonsir ta ce.
“Wai yau za ta dawo”.
Ya ce, “To Allah ya dawo da ita lafiya. Bari na je, zan aiko da magunguna”.
Ta ce, “An gode”.
Ya fice, bayan awa xaya da fitarsa Rabi’u yaronsa ya kawo mata magungunan. Ta karva ta zauna a falo tana ba wa Little Sanah.
Bayan ta gama ba ta, ta miqe zuwa bedroom ta xauko qaramar rediyonta da ta ke saurare kafin zuwan Rabi’u, ta dawo falo ta zauna tana sauraren radiyon, yayin da tashar freedom ke yekuwar wani haxari da aka samu na wata farar mota da tayarta ta fashe, motar ta dinga qundunbala, kafin wani lokaci ta kama da wuta.
Duk qoqarin dfa aka yi don kawo agaji hakan bai samu ba, nan da nan motar da duk wanda ke ciki suka qone qurmus, saboda haka ake sanarwar duk da ba a samu tabbacin su waye a ciki ba, sai dai an tabbatar mutanen guda uku ne, maza biyu mace xaya.
Subhanallah! Wannan sanarwa ta kaxa wa Sanah hanji, ba don komai ba sai don tausayin majivatan gawarwakin, rashin samun tartibin su waye haka masu gawarwakin za su kasance cikin fargaba.
Kai Allah ya tsare musulmi daga faxawa irin wannan mummunan haxari, wanda ba za a samu damar yi maka sutura ba sai dai a tattara qasusuwan a rufe.
Da wannan alhinin ta ci gaba da raya yinin, haka nan zancen haxarin sai ya tsaye mata a rai har ta dinga jin kamar ita aka yi wa haxarin.
Qarfe xaya da minti goma Muftahu ya kira ta a waya, tana xauka ya sanar da ita yana nan zuwa qarfe uku, don haka ta tashi bayan ta yi sallar azahar ta haxa Pineapple Lassi, da ma ta yi girki tun sha biyu. Ta yi wanka ta sanya farar atamfarta mai ratsin zanen duwatsu jajaye, don haka xankunne da abin hannunta duk jajaye ne.
Tana zama a falon El-Moonsir na shigowa, ta yi murmushi, ta ce.
“Har ka taso?”
Ya ce, “Eh, ta iso ne?”
Ta ce, “Har yanzu ba ta qaraso ba”.
Ya zauna a kan kujera yana faxin.
“Tun da na je ofis nake jina wani iri kamar mara lafiya… wallahi na qosa na ga Biyu, ni kam yau na sauke duk makamaina, idan ta dawo zan kai ta ga mahaifana idan sun amince da ita shi kenan…”
Sanah ta katse shi.
“Idan kuma ba su amince ba fa?”
Cikin karyayyar murya ya ce.
“Shi kenan sai na haqura da ma haka Allah ya tsaro”.
Cikin tsananin tausayi ta ce.
“Tun farko haka ya kamata ka yi ka tsaya…”
Wayarta ta yi qara, tana dubawa ta ce.
“Muftahu ne ya zo”.
Ya ce, “Ban so ya tarar da ni ba, saboda alqawarin da na yi masa, koda yake sati xaya na ba shi”.
Ba ta maida masa raddi ba sakamakon kara wayar da ta yi a kunne, ta ce.
“Ka shigo falo”.
Ta kashe wayar, sannan ta dawo da dubanta ga El-Moonsir ta ce.
“Ina zuwa”.
Ta miqe zuwa bedroom ta xauko Little Sanah, wadda ta ta shi a lokacin. Ta dawo, ta tarar da Muftahu suna gaisawa da El-Moonsir. Ta zauna cikin nutsattsiyar murya ta gaishe da shi, ya karvi Little Sanah daga hannunta, ita kuma ta gabato musu da abinci, daidai lokacin da ta ke qoqarin ajiye jug xin da ke hannunta, wayarta ta yi qara.
Ta ajiye jug xin, sannan ta xauko wayar. Ganin murmushi a fuskarta ya sa El-Moonsir ya yi saurin cewa.
“Biyu ce?”
Ta ce, “Ita ce!”
Sannan ta kara wayar a kunne, tare da sallama. Muryar namiji ta ji yana faxin.
“Sunana Faisal Abubakar, saurayin Sanah, xazun da za ta taho Kano ta manta wayarta a xakina… To dama wani abokina ne ya xauko ta kuma sai tsautsayi ya rutsa da su, sun sami haxari gaba xaya sun qone qurmus! Na ga…”
Kafin ya qarasa faxar abin da zai faxa, wasu taurari suka dinga walainiya a idanun Sanah, jiri ya xebe ta ta faxi qasa warwas ba numfashi a tare da ita.
Matuqa hankalin su Muftahu ya tashi, su duka biyun suka yi kanta, Muftahu na faxin.
“Mu kai ta asibiti”.
El-Moonsir ya yi saurin xaukar wayar ya ga lallai da lambar Sanah A aka yi kiran, jikinsa uya ba shi duk abin da aka faxa wa Sanah B ba mai daxi ba ne, don haka bai tsaya vata lokaci ba ya kira lambar Sanah A xin, yayin da shi kuma Muftahu ya kixime ya rasa ma abin da zai yi wa Sanah, addu’a kawai ya ke jerowa, Allah ya sa kada ta mutu, don in ta mutu bai san yadda zai yi da soyayyarta da ta gama mamaye masa zuciya ba.
Wayar ta shiga tana ta ringin ba a xauka ba, har sai da ta kusa katsewa, sannan aka xaga. Maimakon ya ji muryar Sanah sai muryar wani qato ya ji, duk da tsananin kishinsa yau sai ya shanye, ya san ba lafiya .
“Ina mai wayar?”
Ya ce, “Sun taho Kano ita da abokina sun samu haxari sun qone qurmus!”
El-Moonsir ya ji kamar jiri na niyyar xaukarsa, ya ce.
“Ta qone fa ka ce? Ya aka yi wayarta kuma ta zo hannunka?”
Ya ce, “A xakina ta barta… Yanzu haka ina kan hanyar Zuru zan je wa mahaifan abokin nawa da labari…”
Xif wayar ta xauke, da sauri El-Moonsir ya sake kira amma sai ya tarar da ita a kashe. Yana qoqarin sake nema ne Muftahu ya ce.
“Haba El-Moonsir waccan fa tata ta qare, wannan kuma tana cikin mawuyacin hali, ya kamata mu yi wani abu a kai…”
El-Moonsir ya yi saurin ajiye wayar a matsayinsa na qwararren likita, ya shiga duba Sanah. Cikin tsananin tashin hankali ya xago kai idanunwa jawur ya ce.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, ita ma ta rasu!”.
Muftahu ya girgiza kai da sauri ya ce.
“Ba ta rasu ba! Kamata mu je asibiti”.
El-Moonsir bai damu da abin da Muftahu ke faxa ba, ya zaro wayarsa a aljihu, tuni qwalla sun samu damar zubo masa, ya kara wayar a kunne yana faxin.
“Safiyya, yi sauri ki zo gidan su Sanah ina jiranki”.
Za ta yi masa tambayoyi, ya ce.
“Ki xauko mota na ce miki ki same ni gidan su Sanah, ko da yake ba ni Ummi idan tana kusa… Ummi ina cikin tashin hankali, Sanah ta mutu… ta rasu! Ta rasu Ummi!! Don Allah ku taho yanzu”.
Ya kashe wayar tare da zaunawa xabas a kan kafet ya kafe shimfixaxxiyar gawar Sanah da idanu. Wasu kalamai suka soma dawo masa a rai.
“Kada ka zaqe ga lamuran duniya, har kullum dinga zatar wa kanka alkhairi sai alkhairin ya riske ka, idan ka zatar wa kanka sharri, to fa sharrin zai riske ka”.
Wata rana Sanah B ta furta masa haka, lokacin da ya ke faxa mata tsananin damuwar da yake ciki a kan Sanah A, har yana nuna gazawarsa, ashe kuwa abin da yake hangowa a wancan lokacin na RASHIN RABO zai tabbata, yau ga shi ya rasa BIYU KYAUTAR ALLAH.
Abin da ya fi xaga masa hankali shi ne, bai san su waye Sanah da Sanah ba, ballantana ya kai wa mahaifansu labarin mutuwarsu, ga Little Sanah da ta zama cikakkiyar marainiya, ba uwa ba uba, ya zai yi da yarinyar?
“Na sani El-Moonsir kai mai amana ne, mun haxu da kai ba tare da ka damu da sanin asalina ba, ka zauna da ni bisa aminci da yarda har Allah ya kawo mu wannan rana, ina gode maka taimakon da ka yi min.
Har kullum yanzu ma amanar Sanah zan damqa maka, ga shi Allah ya cika mana burinmu mun zamo ma’aurata, yau kuma tsautsayi ya rutsa da ni, wanda ba na tunanin zan tashi saboda yadda nake jin tsananin ciwo a jikina… na ba ka amanar Sanah duniya da qiyama, ba ta da gata sai ni sai Allah, ka kula min da ita…”
Wannan wasiyyar ce Abdulhalim ya bar masa a daren da ajali zai riske shi. Yau ga qwan da ya samu ta jikin Abdulhalim da Sanah da Sanah, su kuma sun bar duniyar, kenan shi ne uwa da uba ga Little Sanah!
A hankali El-Moonsir ya sa hannu ya share hawayensa, zuciyarsa na ci gaba da raxaxi, yana kuma tuna irin jumurxar da aka sha a tsakaninsu duka huxun, amma yau ga shi sai shi kaxai ne ya yi free, wayyo Allah duniya kenan, kana taka Allah na tasa!
Qwarai ya so Sanah, ya so ta gyara gurbin da ta vata kafin mutuwarta, amma Allah bai hukunta ba, don haka tsakaninsa da ita doguwar addu’a ce, Allah ya kai haske da rahama a kabarinta. Ita ma nutsattsiyar yana yi mata kyakkyawar fata zuwa ga makwancinta!