Book 4 (Karshe)
by @nasimat
BIYAR NA YATSUN HANNU
Dole ta sa El-Moonsir ya bar Sanah ya tafi Zuru shi kaxai, saboda ta samu damar zuwa Katsina ta duba mahaifiyarta, ta kuma samu albarkarsu. Washegarin da ya tafi Zuru direban da ya wakilta ya xauke ta zuwa Katsina. Ba qaramin kaxuwa ta yi ba da ganin halin da mahaifiyarta ke ciki, ta yi kuka har idanunta suka kasa buxuwa a lokacin, ta dinga tuna lokacin da Umman tasu ta dawo daga Saudi gwanin sha'awa tana ta gwalli, amma yau duniya ta juya mata baya, ita ma ta riski yanayin qaddara da ke bibiyar rayuwar xan Adam, lallai DUNIYA BA ALJANNA BA CE (In ji qawata Rabi'atu Adamu Shitu).
Sai da ta yi kwanaki biyar a Katsinan kafin lokacin Rahinat ta samu rangwame, har raba dare suka yi suna hira da Sanah a daren da za ta koma Kano. Babu abin da ya burge Alhaji Adam, sai ganin yadda sam Sanah ba ta nuna qyamatar mahaifiyarta ba, hidima ta ke yi mata kamar wadda ke jinyar rashin lafiyar da ba ta haifar da fargabar kada a xauka.
Kwanakin El-Moonsir goma sha biyu, ranar juma'a ya dawo hutun qarshen mako, inda suka qarasa shirya kayan da za su tafi da su, ranar lahadi da sanyin safiya suka xau hanyar Zuru. Sun isa lafiya, komai Sanah ta ke buqata El-Moonsir ya tanadar da shi a gidan, babu abin da ke burge ta irin qaunar da ya ke nuna mata a aikace da baxinance, ta yarda ta amince linzamin zuciya na karkata ga wanda ya yi wa linzamin kyakkyawan riqo.
Sun samu tsawon makonni uku a garin na Zuru suna saune lafiya da kyautata wa juna. Tunda suka tare a gidan, a washegarin ranar El-Moonsir ya umarce ta da ta shiga maqotansu su gaisa ta kuma gabatar da kanta gare su. Ta bi umarninsa, duk gidan da ke layin sai da ta shiga, a gida na huxu da ke varin da ma da ta shiga akwai wata matashiyar budurwa mai suna Salamatu, ta kan shigo gidan Sanah su gaisa ta haka ne suka saba da juna, shi ya sa ko El-Moonsir yana wajen aiki ba ta da kewa, domin zai yi wahala Salamatu ba ta shigo gidan ba, wani lokacin sanadin Little Sanah ta ke shigowa, saboda a cewarta tana matuqar qaunar Little Sanah, yarinyar na burge ta a dalilin qiriniyarta da qoshin lafiyar da ta ke da ita.
Yau laraba, misalin sha xaya na rana, El-Moonsir yana wajen aiki, Sanah na hidima tsakanin falo da kicin, a qoqarinta na kammala girki kafin maigidan ya dawo. Haka nan ta ji zuciyarta ta tashi, kafin ta yi wani yunquri sai amai ya qwace mata, ta fito daga kicin za ta nufi banxaki, a falo ta yi kacivus da Salamatu da suke shigowa ita da wata mata. Sanah ba ta tsaya saurarensu ba, saboda aman da ya sake taho mata, ta wuce banxaki da gudu.
Salamatu ta bi ta hankali a tashe tana faxin, "Subhanallahi, Mommy Little, lafiya?"
Sai da ta gama sheqa aman tukunna ta kurkure baki, ta juyo tana yatsina fuska, ta ce, "Wallahi zuciyata ce ta tashi..."
Ta qarashe maganar suna dawowa falo. Matar da suka shigo gidan tare da Salamatu tana zaune a kan kujera, sanye da doguwar hijabi da niqabi a fuskarta, ban da idanunta babu abin da ya ke a bayyane. Little Sanah tana gefenta tana kiciniyar fasa ledar alewar da matar ta ba ta.
Sanah da Salamatu suka zauna a kan kujera suka gaisa, Sanah ta dubi matar, ta ga sai kallonta ta ke yi, amma ta kasa gaishe da ita, cikin basarwa ta ce, "Salamatu, baquwa muka yi?"
Salamatu ta xan yatsina fuska, kafin ta ce, "Eh wallahi, wata 'yar uwarmu ce ta zo, duk gidanmu da ni ta fi shaquwa, to ta zo ni kuma zan shigo na ga Little Sanah shi ya sa muka shigo tare".
Sanah ta xan washe fuska, ta ce, "Ayya".
Ta mayar da dubanta ga matar tan faxin, "Sannu baiwar Allah, kun zo lafiya?"
Dariya Salamatu ta yi ta ce, "Ai kurma ce, ba ta ji, ba ta magana".
Sanah ta xan zaro idnu cike da mamaki ta ce,, "Tofa, ikon Allah".
Salamatu ta ce, "Amma ta iya rubutu, duk hirar da muke yi da ita rubutu mu ke yi".
Ta nuna wa matar hannu alamar su gaisa. Jakar da ke hannunta ta buxa ta zaro joter da biro ta yi rubutu, sannan ta miqo wa Sanah. Ta karva cike da al'ajabi ga mata har mata duk da ba ta ganin fuskarta a zahiri, amma babu kunne ba baki. Gabanta ya yi wani irin yankewa ya faxi sakamakon rubutun da ta gani a jikin takardar. Kamar ta tava sanin rubutun, amma ta kasa tunawa. Ta xago kai ta dubi matar kafin ta karanta abin da ta rubuta kamar haka.
'Barka da rana ya ukhti, sunana SA'UMA AHMAD'.
Sanah ta sake kallon Sa'uma fuskarta da murmushin yaqe, ta jinjina kai alamar ta amsa, sannan ta dawo da dubanta ga Salamatu, ta ce, "Wallahi na yi matuqar mamaki, ashe kurame ma na da ilimi?"
Dariya sosai Salamatu ta yi, ta ce, "Abin da su ma suna da makaranta musamman domin su... Ke wasu kuramen ma sun fi masu kunne da baki ilimi da hankali".
Sanah ta saci kallon Sa'uma da ke raba kallo tsakaninsu, ta ce, "Budurwa ce ko matar aure?"
Salamatu ta ce, "Wallahi ba matar aure ba ce, sai dai an yi mata baiko da wani xan uwanta Mubasshir. To shi ne mai tsananin kishi shi ya sanya ta yin irin wannan shigar. Ki bari ai za mu je bikinta".
Sanah ta ce, "A wane gari suke?"
Salamatu ta ce, "A nan Zurun su ke, suna can Tudun Wada".
Sa'uma ta miqo hannu ta xauki joter xinta ta yi rubutu, ta miqa wa Salamatu ta karanta, sannan ta ce, "Wai cewa ta yi hala maganarta muke yi, kin san kurame akwai tsarguwa".
Su biyun suka yi dariya, Sanah ta karvi joter xin ta rubuta mata.
"Allah ya huci zuciyarki Sa'uma, abin ne ya burge ni, ga ki kurma amma kina da xumbin ilimi".
Bayan Sa'uma ta karanta, sai ta rubuta.
"Haka lamarin ubangiji ya ke, ki ga wannan fari wancan baqi, wannan na gari wancan xan banza, wannan kyakkyawa wancan mummuna. Don Allah 'ya'yanki nawa...?'
Da Sanah ta karanta sai da ta yi murmushi, sannan ta ba ta amsa.
'Ita ke nan 'yata Little Sanah'.
Sa'uma ta sake rubuta mata.
'Allah sarki, to Allah ya inganta wanda gare ki yanzu, ya raba ku lafiya, Ya qara so da qauna tsakaninki da mijinki'.
Cike da jin daxin addu'arta Sanah ta rubuta mata.
'Amin summa amin, ke ma Allah ya kai mu ranar naki auren'.
Bayan ta miqa wa Sa'uma takardar ta dubi Salamatu, ta ce, "Don Allah ku xan yi min haquri, girki na ke yi, ga shi Daddyn Little ya kusa dawowa".
Salamatu ta ce, "Ba komai".
Cikin lokaci qanqani ta kammala girkin, ta zubo musu. Suna tsaka da ci ne El-Moonsir ya dawo. Sanah ta tashi cikin girmamawa da ladabi ta yi masa sannu da zuwa, tare da karvar jakar hannunsa, ya tsaya suka gaisa da Salamatu sannan ya wuce xakinsa. Sanah ta roqe su alfarmar minti biyar, ta bi bayansa. Bayan ta gama shirya masa abinci, ta ce, "Ka ga wannan matar mai niqabi ko?"
Ya juyo yana dubanta, ya ce, "Me ya faru?"
Tana murmushi ta ce, "Wai fa nan kurma ce, ba ta ji ba ta magana, amma ta iya rubutu da karatu".
Ya yi dariya, ya ce, "Mene ne abin mamaki a ciki?"
Ta ce, "Wallahi dole na yi mamaki, don ban tava ganin kurma mai gatan wannan ba".
Ya ce, "Ai akwai su da yawa, don dai ba su samun kulawa daga gwamnati da su kansu iyayensu shi ya sa ki ke ganin kurame ba su da ilimi, amma har waxanda ba su jin Hausa sai Turanci ma akwai".
Ya qarashe maganar yana dosar qofar banxaki. Sai ta yi amfani da wannan damar ta koma wajen su Salamatu. Suna ganinta suka miqe tsaye, ta ce, "Har kun yi me?"
Salamatu ta ce, "Za mu koma gida, tunda mijinki ya dawo".
Sanah ta ce, "Haba dai, wallahi da kun yi zamanku, shi da yana xakinsa?"
Salamatu ta ce, "A'a, gwanda dai mu tafi, anjima na sake shigowa".
Ta ce, "Shi ke nan, na gode".
ta xauki takarda ta rubuta wa Sa'uma.
'Ina godiya da ziyararki, sai mun zo shan biki'.
Ita ma Sa'umar ta rubuta mata.
'Ni ma na gode, sai na zo shan kunun jego, Ina son 'yarku sosai kamar ku bar min ita'.
Sanah ta yi murmushi, ta raaka su har bakin qofa suka tafi. Sam ba ta faxa wa El-Moonsir aman da ta yi ba, don ta san idan ya san ciki ne da ita farin ciki da kulawar da zai ba ta sai sun lunk n yanzu, ita kam Allah ya sani yanzu tausayi ya ke baa ta, tattalin da ya ke yi mata har ya so ya yi yawa.
Bayan sati biyu, El-Moonsir ya sanar da ita ta shirya ranar juma'a za su je Katsina, hankalinta ya tashi, saboda yadda ya yi mata maganar cikin rashin walwala, ga shi ta kwana biyu ba ta yi waya da mutanen Katsinan ba, sai ta yi tunanin ko mahaifiyarta ce Allah ya yi wa rasuwa? Ganin yadda ta tayar da hankalinta da kuma tsare shi da tambayoyi ta yi, sai ya kira mata lambar mahaifin nata suka gaisa, ta kuma tabbatar mata da kowa lafiya, sannan hankalinta ya kwanta.
Ranar alhamis misalin qarfe biyar na yammaci Salamatu ta dawo da Little Sanah wadda ta yini a gurinta, suna zaune suna tava hira, Salamatu ta ce, "Kin san mu ma fa gobe za mu je Katsina".
Sanah ta ce, "Don Allah?"
Salamatu ta ce, "Wallahi kuwa, kin san muna da 'yan uwa a can, to a na wani biki, za mu je tare da Sa'uma".
Sanah ta ce, "To ko na yi wa Daddyn Little magana sai mu wuce da ku?"
Salamatu ta ce, "Lah! Wallahi ba komai, ai da ya ke ma wanda zai auri Sa'uman ne zai kai mu".
Sanah ta ce, "Wace unguwa za ku je?"
Salamatu ta ce, "Masanawa".
Sanah ta ce, "Kin ga kuwa ba mu da nisa, ni a Farin Yaro za mu je, insha Allah zan zo muku gidan bikin".
*** *** ***
Kasancewar akwai tazara sosai tsakanin Zuru da Katsina, shi y sa su El-Moonsir ba su samu isowa birnin na Katsina ba sai misalin qarfe goma na dare, don haka a gajiye suke liqis, a gaggauce suka yi wanka da sallah, a ka gaisa tare da cin abinci, sannan suka kwanta a masaukin da Alhaji Adam ya ba su duk da El-Moonsir ya so ya zame wa kwana a gidan surukan nasa, amma Alhaji Adam ya nuna sam bai aminta ba, ga guri yaushe zai tafi ya kwana a hotel?
Da safe misalin qarfe goma na safe suna zazzaune a falo ana karin kumallo, Mandiyya xaya daga cikin masu kula da Rahinat ta shigo falon a matuqar rikice, ko sallama ba ta yi ba, ta ce, "Alhaji ka zo, hajiya jikin ya matsa".
Su duka suka nufi vangaren da Rahinat ta ke, sun tarar da ita tana ta zabura. Alhaji Adam ya umarci su Sanah su fito da ita a kai ta asibiti. Daidai lokacin da a ke fitowa da Rahinat wata baqar mota ta shigo harabar gidan bayan maigadi ya buxe get don fita da su Alhajin za su yi. Motar na tsayawa, su Salamatu suka fito, mamaki ya kama Sanah, ya a ka yi suka san gidan? Mamakin bai qara lulluve ta ba sai da ta ga Sa'uma ta nufo gurin Rahinat da gudunta tana yaye niqabin da ke fuskarta tana faxin, "Ki yafe min Umma, kada ki mutu da haqqinki a kaina! Don Allah ki ce kin yafe min Umma!"
Su duka mutuwar tsaye suka yi a gurin sakamakon ganin fuskar SANAH A da suka yi, musamman Sanah B da ta santa a matsayin kurma mai amsa sunan Sa'uma.
Duk qoqarin da Rahinat ta yi don ta yi magana hakan ya faskara, sai mimi da baki ta ke tana lumshe idanu, kasancewar hankali ba a kwance ya ke ba, ba su tsaya yin magana ba a ka saka Rahinat a mota, Alhaji Adam ya shiga mazaunin direba, Sanah B da Inna Unaiza suka shiga a gidan baya, El-Moonsir ya shiga gefen Alhajin, su Sanah A suka koma cikin motar da suka zo, nan da nan suka fice daga gidan zuwa asibiti.
Zambarwa Rahinat ta ke yi tana zabga ihu a cikin motar, kafin daga bisani dukka gavvanta su daina motsi, Cikin rikicewa Inna Unaiza ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Alhaji ina jin fa Allah ya yi mata cikawa".
Gabaxayansu suka xauki salati, Alhaji Adam ya xora da faxin, "Bari dai mu qarasa asibitin, wataqila suma ta yi".
Suna isa asibitin, binciken farko da likita ya yi ya tabbatar da Allah ya yi wa Rahinat rasuwa. Sanah A da B suka suka fashe da shi, suka rungume gawarta suna faxin, "Umma, ki tashi don Allah. Ki tashi mu samu albarkarki!"
Da qyar a ka rarrashe su a ka koma gida da gawar Rahinat.
Cikin lokaci qanqani mutane suka samu labarin rasuwar, sai dai duk wanda zai buxi baki ya yi magana babu alkhairin Rahinat xaya da ya ke ambata, da ma haka rayuwa ta ke, abin da ka shuka shi za ka girba. Da su Ummi suka zo Katsinan sun yi mamakin ganin '\yanbiyu, sai dai hankali ba a kwance ba ballantana a zanta wasu maganganun.
A ranar sadakar uku su Alhaji Ja'afar suka zo daga Kaduna a ka yi sadakar tare da su.
Washegarin sadakar ne suna zaune a falon gidan, Alhaji Adam ya dubi Sanah A ya ce, "Hassanah, a baya an ba ni labarin kin rasu a sanadiyyar haxarin mota, yanzu kuma sai ga ki kin bayyana, ya ya abin ya ke?"
Sanah A ta yi shiru, labarinta ba zai badu ga iyayenta ba, saboda ba ta son tuna rayuwar bariki da ta yi. Ganin ta yi shiru sai Mubasshir ya gabatar da kansa, sannan ya nuna dattijon da suke tare ya ce, "Wannan mahaifina ne, sunansa Malam Basiru, a zahirin gaskiya Hassanah ba rasuwa ta yi ba kamar yadda na kira Hussaina na shaida mata. Mun shirya hakan ne a dalilin ita Hassanar ta faxa min tana so Hussaina ta dawo gare ku saboda ba ta so ita ma rayuwarta ta gurvace. Bayan mun gama wayar na kai Hassanah ga mahaifana a matsayin matar da zan aura. Da ya ke da ma tun kafin na kai ta gare su na yi musu bayaninta, sun san irin jumurxar da na sha da ita kafin na kai ta a kan tsanar aure da ta yi. Mahaifina malami ne na zaure mai almajirai, shi ya ba da tabbacin akwai aikin sihiri a tare da ita. A ranar da muka cika kwanaki talatin muna ta fama da ita a kan maganar ta daina bariki na aure ta tana tuvurewa, a lokacin Malam ya samu makarin sihirin da ke jikinta, wanda ya ce sai an je can qasar Maraxi inda a ka yi asirin an tone abubuwan da a ka binne. Tare da haka na tafi Maraxi ranar da aka cika kwanaki arba'in cif na samu nasarar tone layun da gurayen da a ka binne, kuma Malam ya qarasa aikin karyawa a ranar".
Yana zuwa daidai nan Alhaji Adam ya tafi duniyar nazari, a ranar ne ya wayi gari da ciwon kai, a ranar ne ya ji nadamar abubuwan da ya aikata wa 'yan biyunsa ta shige shi. Ita ma Sanah B ta tafi duniyar nazarin, a ranar da a ka yi kwana arba'in xin ne ta ji ta wani iri, har ta soma kafa tubalin roqon El-Moonsir a fasa aurensu saboda tana ganinsa a matsayin haramtaccen aure, ke nan a ranar ne a ka karya asirin da Rahinat suka yi?
Mubasshir ya ci gaba da cewa, "Ina dawowa Zuru na tarar da abin mamaki, Hassanah ta karvi tuba, don haka tun a lokacin ta soma istibira'i. A yanzu haka ta kammala, shi ya sa muka dawo da ita gare ku, ta roqe ku afuwar abin da ya faru".
Alhaji Adam ya jinjina kai, ya ce, "Ikon Allah, wallahi a ranar da a ka karya asirin na ji a jikina, domin a lokacin na yi nadamar duk abin da na yi musu. Daga baya mahaifiyarsu ta dawo".
Ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da su.
An jimantawa juna, Sanah A ta roqi mahaifinta gafarar kura-kuran da ta aikata masa. Ya yafe mata, sannan Malam Basiru Zuru ya gabatar da kansu a matsayin waxanda suke nema wa Mubasshir auren Sanah. Alhaji Adam bai amsa musu ba sai da ya tambaye ta, kuma ta ce ta amince.
Sanah B ba ta gamsu da duk maganganun da a ka tattauna ba, tana buqatar a warware mata dukkan labari. Sun jima suna tattaunawa, ba su dai tashi a gurin ba sai da a ka tsayar da maganar auren Sanah da Mubasshir wata huxu masu zuwa, al'amarin da bai yi wa Sanah B daxi ba ke nan.
Da yammacin ranar ta kira El-Moonsir, Mubasshir da ita kanta Sanah A xin suka koma can qarshen gidan inda babu wanda zai ji abin da za su tattauna. Shiru ya gilma tsakaninsu, kafin daga bisani El-Moonsir ya ce, "Sanah, kin kira mu amma kin bar mu shiru".
Ta gyara zamanta a kan farar kujerar robar da ta ke zaune, ta ce, "Ban gamsu ba ne da labarin da Mubasshir ya bayar, don haka ina son a warware min zare da abawa, kai ma na san kana buqatar sanin yadda a ka mutu a ragaya".
El-Moonsir ya yi dariya ya ce, "Ke kuma da qawar zuci ki ke, abin da ya wuce ba shi ke nan ba, mene ne na bin qwaqqwafi?"
Ta ce, "A'a, in kai ba ka son sani, ni ina so. Har fa zuwar min ta yi a matsayin kurma ta shayar da ni mamaki sannan a ce ba ni buqatar qarin bayani?"
Sanah A ta yi murmushi, ta ce, "Qyale ta El-Moonsir, bari na warware mata komai... Mun haxu da Mubasshir a nan Kano, mun shaqu da shi saboda yana burge ni. Ban tava xaukarsa a matsayin wanda ke son aurena ba sai abokin rayuwar bariki. Kamar yadda ki ka sani koyaushe ba ni da burin da ya wuce na ga kin dawo gurin su Abba, haka Mubasshir ya san wannan lamari. Shi ya kawo min shawarar na qirqiri tafiya, inyaso sai a ce miki na rasu, na san dole za ki koma Katsina tunda da ma saboda ni ki ke zaune a Kanon, don haka na ce miki na tafi Abuja, duk tsayin kwanakin nan muna ta shirya yadda za mu villo miki da labarin rasuwata har ki yarda da zancen. Kwatsam sai muka samu labarin haxarin da ya faru a hanyar Abuja, sai muka yi amfani da wannan damar bayan mun bi diddigin su waye haxarin ya faru a kansu..."
Mubasshir ya katse ta da faxin, "To bari na ba su nawa labarin".
Ta yi dariya, ta ce, "A'a, ka barshi kawai".
El-Moonsir ya ce, "Ba mu yarda ba, ki bari ya ba mu".
Mubasshir ya ce, "Tun lokacin da na fara ganin Sanah Allah ya jarabce ni da qaunarta, na bi duk hanyoyin da ya dace na bi don na shawo kanta ta daina rayuwar bariki amma abin ya faskara, lokacin da ta kawo min zancen tana son ki dawo Katsina sai na ga wannan ce damar da ya kamata na yi amfani da ita don na kaita ga mahaifina, domin na daxe da fuskantar asiri ne ya qeqasar mata da zuciya. Saboda haka na ba ta wannan shawarar, na kuma samu nasarar tafiya da ita Zuru".
Sanah A ta xaga masa hannu, ta ce, "To ka qarashe naka, tunda ka bada labarin gwagwarmayar da ka yi ka karya asirin xazun, bari na qarasa mata nawa... Bayan komai ya lafa ne watarana na zo gidan su Salamatu, wadda da mahaifinta da mahaifin Mubasshir uwa xaya uba xaya, tun farkon dawowata Zuru mun shaqu da Salamatu, don haka ta kan zo gidansu, kuma ta san labarina.
Kwatsam ranar da na zo, sai na tarar da Little Sanah, ina ganinta na ruxe, ita ma yarinyar ta xafe min saboda kamanninmu tana zaton ke ce. Ganin ruxewar da na yi ya sa Salamatu ta tambaye ni. Ban voye mata komai ba na faxa mata 'yata ce Little Sanah, ta ce min da ma tun da ta fara ganinki ta shaida ki, mahaifiyarta ce ta tsawatar mata kada ta nuna miki ta san ni gudun abin da ka je ka dawo. Tun a lokacin Salamatu ta so mu shiga gidan, na ce a'a sai na zo miki zuwan basaja don na ga wa ki ka aura, kuma ya zamanku ya ke? Kwana biyu tsakani muka zo miki ina sanye da niqabi, na kuma zo miki a matsayin kurma mai suna Sa'uma. Sai dai na lura lokacin da ki ka ga rubutuna kin so ramfo ni. El-Moonsir na dawowa ba qaramin daxi na ji ba da na ga ya kasance mijinki, saboda a zahiri na san El-Moonsir yana miki so na haqiqa sai dai fuskata da ya ke gani ta katange masa bayyana miki soyayya. Ina da yaqinin zai riqe ki amana shi ya sa a tanar na kwana cikin farin ciki, duk da ina son El-Moonsir saboda jajircewarsa ga rayuwarmu, amma a wannan dare na sadaukar da gabaxaya son da na ke yi masa gare ki. Na yi ta jera nafilfili ina roqon Allah ya zaunar da ku lafiya.
Salamatu ita ta sanar da ni za ku zo Katsina, don haka mu ma muka shirya zuwa a ranar. To kin ji labarina, mene ne ba a fayyace miki ba?"
Sanah B ta ce, "Abubuwa da yawa".
Su duka suka zuba mata idanu, ta ci gaba da cewa, "Ba ki fayyace min matsayin Little Sanah ba!"
Dariya ta yi, ta ce, "Matsayinta zai sauya ne daga 'yarki halak malak? Kin manta bisa jajircewarku ke da El-Moonsir ta zo duniya? Wallahi har duniya ta naxe tana nan a matsayin 'yarki, domin ke ki ka raini cikinta, ki ka haife ta, sannan ki ka ci gaba da rainonta har kawo wa yanzu".
Sanah B ta ce, "Bayan haka ina roqonku alfarma a maida aurena da El-Moonsir AUREN RIQON QWARYA! Tunda kin dawo ya sauwaqe min ki aure shi".
El-Moonsir ya zare idanu cikin kaxuwa, yayin da Sanah A da Mubasshir suka yi dariya, Mubasshir ya ce, "Haba Sanah, ina ganinki mai hankali da ilimi amma za ki vata rawarki da tsalle? Ina ki ka tava ganin an yi haka? Je ki ma hakan za ta faru, ni ba ki tausaya min xawainiyar son 'yar uwarki da na yi?"
El-Moonsir ya langwave kai, ya ce, "Ban san me na yi wa Sana ba ta tsane ni".
Cikin raunanniyar murya ta ce, "Wallahi ban tsane ka ba, hasalima qaunar da na ke yi maka ba ta misaltuwa, kawai na yi SHAHADAR QUDA ne saboda na sadaukar da farin cikina a kan 'yar uwata".
Sanah A ta mirgina kai, ta ce, "Ai ba sai kin yi haka ba zan san kin sadaukar da farin cikinki gare ni ba, duk abin da ya faru a baya bai isa bayyanawa duniya SADAUKARWArki gare ni ba? Haba Sanah RASHIN JINI fa ba a tsaga ba, kada ki yanke wa kanki BAHAGON HUKUNCI ki dawo kina kallon kanki a matsayin KAZA DA HATSI. Ki riqi mijinki mai so da qaunarki, ni wallahi yanzu Mubasshir ya fiye min kowane namiji a duniya, domin ya yi min dukkan alkhairi, ya taimaki rayuwata ya rabo ni daga SANIYAR WARE ya dawo da ni cikin sahihiyar rayuwa, saboda Allah INA HUJJAR TA KE da ganin El-Moonsir zai sa na butulce wa adalin mutum irin Mubasshir? Gaskiya ban ji daxi ba, wannan ba HALAYYArki ba ce, don haka ki yi sauri ki ba wa mijinki haqurin shirmen da ki ka yi tun kafin mala'iku su yi miki tofin Allah tsine".
Tsam Sanah B ta taso daga mazauninta ta durqusa a gaban El-Moonsir, ta ce, "Ka yafe min mijina, na karvi kuskure na".
Cikin shariya ya ce, "Ba zan yafe miki ba".
Hawaye suka yo ambaliya a kumatunta, ta raunanar da murya ta ce, "Don girman Ubangiji ka yafe min".
Ya ce, "Daina kukan, na yafe miki duniya da lahira, ina roqon Allah ya qara kimsa miki sona da tausayina a zuciyarki".
Su duka suka amsa da amin.
Sanah A ta dubi El-Moonsir ta ce, "Ya maganar iyayen Abdulhalim?"
Ya dube ta cikin rashin fahinta, ya ce, "Ban gane ba?"
Ta ce, "Ina so ne lallai iyayensa su san da zaman Little Sanah".
El-Moonsir ya ce, "Wannan ba damuwa ba ce, zan binciko su can wajen aikinsa sai mu je musu da zancen".
Ta ce, “Haka ne, akwai ma nan makarantar da ya tava koyarwa za a iya samun cikakken adireshinsu”.
El-Moonsir ya ce, “Duk wannan ba abin damuwa ba ne, insha Allah zan yi qoqari don ganin an inganta rayuwar Little Sanah, idan ma iyayensa ba su musulunta ba, zan ci gaba da riqonta a matsayin ‘yata, don ba zai yiwu ba su karvi musulunci ba mu xauki ‘ya mu ba su ba. Ni xin nan cikakken uba ne ga Little Sanah!”
Ta ce, "Ina godiya El-Moonsir"
Ya ce, "Ni ma ina godiya Sanah!"
ALHAMDU LILLAHI
Abin da na yi kuskure Allah ya gyara mana, wanda na yi daidai Allah ya haxa mu a ladar.
Sai mun haxu a sabon littafina mai zuwa NA YI MUSU ZARRA!
Mai qaunarku yau da kullum.
Naja’atu Haruna Sale
Mummyn Faanah.
XANXANO
NA YI MUSU ZARRA!
H
awaye suka kwaranyo daga idanun Little Sanah, muryarta na wani irin rawa, ta ce, “Na rantse da girman Ubangiji Daddy, babu hannun Anwar a cikin laifin nan, tsana ce kawai da mahaifiyarsa ta yi masa, don Allah ku taimake ni a sako min mijina”.
Alhaji Abdulhalim ya mirgina kai, ya ce, “To na ji, daina kukan. Ciki da gaskiya ai wuqa ba ta huda shi… Amma ina mamakin wannan al’amari, a ce uwa mahaifiya ta kai xanta qara wai ya shigo mata gida ya yi mata fashi da makami? Kai qarshen duniya!”
Hajiya Sanah ta gyara madubin idonta, ta xan goge hawayen da ita ma ke kwaranya a idonta, ta ce, “Ni fa na gaji, kawai a raba auren nan kowa ya huta. Haba abu sai ka ce cin qwan makauniya, tun ranar da a ka kai Little Sanah gidan yaron nan masifar yau daban ta gobe daban, shin kan uwarsa farau auren mai kuxi? Ko mu ba mu da kuxin ne da za ta xauki karan tsana ta xora wa ‘yarmu? To wallahi na gaji! Ko dai ka xauki matakin da za su gyara a sakar wa ‘yata mara ta zauna da mijinta lafiya, ko kuma a neme ta a rasa, don wallahi ba zan ci gaba da zuba ido ana wulaqanta min ‘ya ba!”
Dr. El-Moonsir ya ce, “Ke kuma matsalarki ke nan Sanah, ba ki da haquri a kan lamarin Little, ke ko ‘yar alkunyar nan ba za ki yi ba?”
Ta ce, “Ku bar ni kawai! Allah ina nadamar aura wa Little Sanah Anwar, duk da shi yana da halin qwarai”.
Alhaji Abdulhalim ya ce, “To da ki ke cewa a raba auren, shin idan mun raba mun yi wa yaransu biyu adalci, ko shi Anwar xin mun yi masa adalci?”
*** ***
NA YI MUSU ZARRA! Labari ne mai matuqar ban tausayi da al’ajabi. Labari ne a kan wata uwa da ta tsani xanta na cikinta ta dinga ja masa jafa’i kala-kala don cikar wani voyayyen sirrinta mai tafiya da rayuka biyu zuwa uku, kamar yadda allon rayuwarta ya zana mata dakushe duk wani yunqurin samar da tsatson da za a kalla a ce jinin Anwar ne ko da kuwa ta bauxaxxiyar hanya ce!
Kada ku damu ga shi nan zuwa kurkusa.
Naja’atu Haruna Sale
Mummyn Faanah