04
ƘAZAMIN TABO
04
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
Nabeel nan take tunani ya fado masa akan ya ajiye kudin adakin Anas ya san babu abinda zai faru, sai ya wuce dakin ya bude ya shiga, ya soma waigen in da zai boye, sai kawai ya yanke shawarar daga littafan Anas din dake bisa table din karatunsa ya sanya a kasansu ya mayar da littafan, sai ya sauke ajiyar zuciya ya koma falo ya kunna tv ya cigaba da kallo cike da Addu'ar Allah yasa ya fita da kudin lafiya ba tare da an gano komai ba.
Sai wajen karfe biyar da rabi Anas ya dawo ya dibi abinci yaci ya wuce dakonsa ya kwanta, lokacin da aka kira sallan magrib ya fito ya tasa keyar Nabeel suka wuce masallaci, a lokacin momy ke dawowa da sauri ta shiga kitchen ta daura sanwar abinci fried rice, ba ita ta fito ba sai da ta hada komai kafin ta zo tayi sallah, tana idarwa ta fito ta koma kitchen ta duba abincin kadan ya rage yayi sai ta fito da sauran pepper chicken dake fridge ta dumama ta zuba a mazubi, a lokacin abincin ya karasa ta sauke tare da zubawa a food wormer ta jera komai a dinning, lokaci ya kure Bata samu hada musu juice ba sai kawai ta bari suyi amfani da drinks duk da ta san yau sai ta sha mita a wajen Abba, saboda ba kasafai yake son Shan drinks ba sai dole yafi na'am da natural drink Wanda ta hada da kanta, cikin sauri ta koma daki ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da dauro alwala ta fito ta shirya, sannan ta gabatar da sallar Isha'i, lokacin duka yaran sun dawo gaba daya suna falo, ta fito ta samesu suka gaisheta kafin ta zauna tana cewa.
Leema ya dai na ganki wani iri ne.
Ba kin tafi kin barni ba duk ba dadi yau.
Ayya sorry my baby ba halin na tafi da ku saboda taron babu yara a ciki. Idan kuna jin yunwa ga abinci can kuje ku fara ci, in kuma zaku jira dawowar Abbanku to.
Babu wani jiransa da zanyi.
Cewar Anas ya mike tare da isa dinning din ya ja kujera ya zauna, ya zuba iya wanda zai iya ci ya kira Bushra data kawo masa ruwa ya soma ci, Leema ma zuwa ta yi ta zauna Bushra tana kawo masa ruwan yace ta zubawa Leema, ba musu ta sanya mata itama ta zuba nata ta zauna suka fara ci, Momy ta dubi Nabeel.
Kai ba zaka ci ba tunda sun kasa jiran Abbanku.
Ai su duk yan ruwan ciki ne Ni dai Zan jira ya shigo nasan ya kusa dawowa.
Ya fada yana murmushi, momy ta dauki wayarta ta soma kallon hotunan da suka yi yau, minti goma sai ga Abban ya shigo da sauri Nabeel ya isa gareshi ya amso jakar hannunsa yana yi masa sannu da zuwa, suka shigo ciki ya zauna sauran yaran Suma suka yi masa sannu kafin ya mike ya wuce dakinsa Momy ta bi bayansa, rage kaya yayi ya sanya jallabiya suka fito, dinning suka isa suka zauna, dai dai lokacin Anas ya mike da zummar ya koshi, harya juya zai wuce Abba ya dakatar da shi.
Kai Anas zancen exam dinka an sanar dani cewar an fara biya Insha Allah gobe ko jibi zanje nayi maka registration saika zauna cikin shiri, amma kaga daga wannan ba zan sake biya maka ba, in dai baka maida hankali ba kayi abin kirki dan bazan cigaba da asarar kudina ba, kaga sai ka koma zuwa kasuwa in kasan mahimmancin niman kudi sai ka biyawa kanka nan gaba.
Anas be ce komai ba ya juya ya soma tafiya, momy ta dakatar da shi cikin mita.
Ba zaka ce komai ba zaka wuce ko da hakuri ka ba shi ba, ka tabbatar masa da zaka yi abin kirki sai kawai kasa kai ta tafi.
Rabu da shi ai in beyi hakan ba bai cika sunansa ba, tashen balagar iskanci yake ji kuma ni da shi mu zuba mu gani dakikin banza kawai.
Cewar Abba cikin fada, Anas kuwa kala be ce ba ya wuce abinsa cike da jin haushin irin hantarar da Abba ke Masa, banda ya San shine ya haifeshi daya ce ko kila shi dan riko ne, ko kuwa dan yazo a dan fari shiyasa yake masa haka, amma da yawan iyaye suna matukar nunawa Dan fari so wanda har basa iya boyewa ga sauran yaransu, haka ya isa daki cike da damuwa, a yadda yake yanzu yana ganin yayi girman da ya wuce irin wannan abin, ace ko waya baida ita tsabar dokarsa, kuma wannan takuran ba shine zai sa ya zama mutumin kirki ba abinda Abba ya kasa fahimta kenan, haka ya zauna gefen gado yayi ta zancen zuci daga bisani ya nisa ya isa table din karatunsa ya soma duba littafinsa na chemistry wanda aka yi musu dazun.
*
Da safe.
Karfe bakwai su Nabeel sun gama Shirin zuwa boko, suka sauko wajen dinning suna karyawa amma Nabeel sai gaggawa yake duk ya kosa su tafi saboda ya tsira da kudin daya sata, haka ya azalzalawa su Leema akan su tafi Kar suyi latti basu gama karyawa ba suka tafi, momy tana masa sababi akan ya rabu dasu suci a hankali Amma Inna sai da ya jasu suka tafi kafin hankalinsa ya kwanta. Bayan sun tafi shima Anas ya sauko ya karya ya yiwa momy sallama tace ya tsaya su fita tare zata je banki in yaso ta sauke shi a hanya, ba musu ya tsaya jiranta, ta shiga dakinta da sauri ta dauki wannan kudin bata tsaya kirgawa ba saboda ta san dari ne tsif, ta dauki ATM dinta da key mota tare da waya ta fito suka wuce.
A kofar makarantar da yake lesson ta tsaya ya sauka ya shiga ciki ita kuma ta wuce bank, ta isa ta samu layi kadan sai da ta jira ya zo kanta kafin ta mika musu kudin tare da details na account din da za a sanya kudin a ciki, ma'aiciyar ta sanya kudin inda ake kirgawa, sai taga 90k sabanin 100k da sauri ta dago tana cewa.
Hajiya kudinnan basu cika ba 90k ne.
Kamar yaya fa? Ni gaskiya 100k ne domin jiyan nan na kirgasu na gani.
Da safen nan kin kara kirgawa kin gani?
A'a ban kirga ba saboda nasan 100k ne.
To gaskiya ki koma gida ki sake dubawa maybe kin bar sauran a inda kika ajiye.
Ma'aikaciyar ta mika mata kudin tare da komai, momy ta amsa jiki a sanyaye ta fito zuwa mota ta shiga ciki ta kunna ta juya zuwa gida, tana hanya Amma tunani ya cika mata Kai da mamakin bacewar sauran kudin, sai tambayar kanta take wa zai dauka kuwa? Amma ba amsa a haka ta isa gida ta yi parking ta fito, tana shiga falo ta wuce dakinta ta isa wajan drower din ta bude, taga wayam babu ko sisi a ciki ta zauna bakin gado tana fadin.
Kudin da suke a hade da robali taya zan bar saura a ciki, sai dai in hannu ya zara.
Tana fadin haka ta tuno da Anas cewar shi ne kadai yasan da ajiyar kudin, saboda a gabansa jiya ta adana su sannan ma ta tuna da irin jayayyar da suka yi akan kudin lesson da bata ba shi ba, nan take zarginta ya fada kansa duk da tana jin a zuciyarta da wuya ya daukar mata kudi, amma saboda ta cirewa kanta shakku sai kawai ta fito ta wuce dakinsa ta shiga, ta soma duba cikin kayansa da drowers din dakin, ta san in shi ya dauka ba zai kashe su duka ba dole zai bar saura tunda kudin lesson din 5k ne, haka ta dinga dubawa sai da ta bata lokaci sosai domin ta cirewa kanta shakku, tana cikin hakane garin ta matsar da kujerar da yake zama in zai yi karatu ta ture table din takardun da suke kai suka zubo kasa, sai ta risina tana dibansu tare da sababi akan duk wanda ya dauki kudin, ta dago kenan taga kudin akan table da sauri ta ajiye takardun a gefe ta dauki kudin hannunta yana rawa ta kirga, dubu biyar ras gasu Kuma Babu abinda ya banbantasu da wancen sauran kudin, da gudu ta fice a dakin ta isa dakinta ta hada kudin Dana hanunnta kalarsu Daya kuma kamshinsu daya, momy ta zauna jabar a gefen gado ta shiga tsananin mamaki da tashin hankali, kenan Anas ya fara satan kudi, koma shine yake dauke mata 'yan kudaden da take rasawa a dakin, nan take zuciyarta ta gasgata mata haka, sai kawai ta ajiye kudin a drower zuciyarta ta cika da tsananin bacin rai, ita kadai take kissima irin hukuncin da zata yi masa ko Kuma zata fadawa Abbansa yayi Masa ta yadda ko da zai ga kudin wani ya fadi koda tsintuwa ne ba zaiyi sha'awar dauka ba, nan take ta daga wayarta ta kira Abba ta shaida masa, hankalinsa in yayi dubu ya tashi.
_______
KANO.
Da safe, Mami ta shirya yaranta zuwa makarantar hadda, ta gama hada musu breakfast ita da Abbansu hade da kara dumama musu wannan farfaesun ta jera komai a dinning, me aikina tana zuwa ta Soma gyaran gidan ita Kuma ta wuce dakinta tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ready made, ta yi kwalliya kadan sai ta isa dakin Abba ta same shi zaune yana waya, daga ganinta yayi saurin katsewa yana washe baki, ita dai jikinta yabata wani abu yadda yana ganinta ya yi saurin katse kiran, yace cikin zolaya.
Da kyau matar Auwal wannan irin kyau haka, ai sai ki sani na shagala da kallon ki har na kasa fita kasuwa.
Uhum dawa kake waya? Naga kana ganina ka katse.
Wani customer ne ganin mun kare magana ne yasa na kashe.
Ya Bata amsa cikin dakiya da nuna Babu komai, ganin haka yasa ta gasgata shi kana ta sanar dashi abin kari yana dinning, ya mike tare da cewa suje su karya shima ya shirya, haka suka jero tare har dinning din suka shiga karyawa, sai kiransa ake tare da turo masa sako wanda yake da yakinin Bilkisu ce amma sai yayi biris da Kiran yama dauki wayar ya sanya ta a airplane mode, Khadija tana kallonsa bata ce uffan ba ita dai jikinta ya bata macece ke kiransa sai dai bata kawo zargin komai a ranta ba duba da ganin ta riga ta rufe kofar zuciyar Auwal Babu wata mace bayanta. Suna gamawa suka wuce dakinsa ta taya shi shiryawa ta rakoshi har mota kamar yadda suka a, ya wuce kasuwa ita kuma ta dawo daki danta huta kafin 12pm yayi ta daura abincin rana.
_
Bayan sallar la'asar su Baba suka je gidansu Bilkisu, anyi musu kyakkyawar tarba, ba bata lokaci suka zanta akan batun auren, waliyyan Bilkisu suka ce sun basu suka yanka musu sadaki dubu sittin sai sauran kudin da ake bayarwa wanda ya tashi a dubu dari da hamsin, nan take suka bayar da kudin suka tsaida ranar biki nan da wata guda me zuwa, haka suka rabu cikin farin ciki da mutuntawa. Baba suna dawowa gida ya kira Auwal akan ya zo, haka ya bar kasuwa ya je gidan, ya samu Baba a dakinsa suka tattauna akan maganar, ba karamin farin ciki Auwal ya yi ba, yayi godiya sosai kana ya daura da cewa.
Baba akwai abinda nake so ka bani shawara a kai.
Ina saurarenka Auwalu.
Dama batun Khadija ne, nace ko in bari sai abin ya zo na fada Mata.
A'a ka sanar da ita da wuri zaifi, a ganina akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninku zata fahimce ka.
Wlh Baba Khadija tana da zafin kishi ta wuce yadda kake zato, shiyasa nake tsoron fada mata.
Ashasha karka bani kunya Mana Auwalu, tun yanzu ya kamata a ce kazama jajirtacce a gidanka, karka sake ka nuna mata rauninka in ba haka ba da shi zata ci galaba akanka. Ka je kasanar da ita ka saurari duk borin da zata yi maka da kanta zata natsu, kuma in ta dawo nan babu me goyon bayanta.
Da wannan bayanin Auwal ya samu karfin guiwa ya yi godiya ga Baba kana ya fito waje ya hadu dasu Yaya Aminu suka shiga hira, sai bayan sallar Isha'i ya yi sallama dasu ya isa gida cike da fargaban abinda zai wakana tsakaninsa da Khadija.
Rahma ce