FreeArewaPen original
KAZAMIN TABO
- 1views
- 28chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciyar littafin hausa
Sample · 01
ƘAZAMIN TABO01Rahma kabir Mrs MG.***@rahmakabir*LUBABATU COMPLETE DOCUMENT*Ga masu jira a kammala littafin to an gama zaku iya samunsa a kan N300 kacal👌🏽Pay N300 to 0106956864, Ramatu Muhammad Kabir, Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card ***, a tura shaidar biya ta number ***. Dan Allah banda vtu.MARUBUCIYAR:-Rayuwar SuhailatD'an AmanaKad'aiciSo ne Sanadi'Yar ShugabaMai HakuriKarshen MakirciSo SartseDa iyayenaKaddararren Al'amariAkan IdonaHantsiLubabatu.*SADAUKARWA ga Haj. Aisha Bashir Danguguwa uwata tagari, Allah ya ja kwananki yasa ki gama da duniya lafiya ya yiwa zuri'a albarka, ya bude miki taskokin alkhairi ya bunkasa business dinki da yalwa yasa kifi haka*_Ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani irin fuska, dan haka a kiyaye_Kagaggen labari ne in yayi iri daya da rayuwar wani to arashi ne.BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.KANOSharadaDa gudun gaske Amira ta shigo cikin gidan zuwa falo suna tseren shigowa ita da Nura, ganin ta riga shi ta saki ihu cike da murna, Nura ya turo baki cikin jin haushin haka, Maminsu ce ta fito daga kitchen tana cewa.Ihun me kike yi ne haka Amira? Wai ke har yau baki san kin girma ba ne? Shekarunki Sha hudu fa kike wannan wautar ki shigo gida babu sallama sai ihu kamar sakarya.Mami wai dan ta rigani shigowa falo take wannan ihun dan naji haushi.Nura ya katse Mami yana kumbure kumbure.To Allah ya kyauta, Ni dai ba tarbiyyar dana baki kenan ba, sannan duk irin shirman da kike yi kamar kina koyar da kaninki ne.Mamina kiyi hakuri ba zan sake ba kin ji.Amira ta fada tana kama kunnuwanta duka biyu tare da langabe kai cikin shagwaba, Mami tayi murmushi tana fadin.Dole kam nayi hakuri irin wannan yaudara da kika zomin da shi, sai kuyi maza kuje ku cire kaya kuyi wanka tare da kwalliyar juma'a, dan kunsan yau zamu je gidansu Baffa mu yini sai dare Abbanku ya dawo damu.Da gudu suka wuce cike da tsantsar murna saboda a rayuwarsu suna kaunar zuwa gidan kakanninsu, sallamar da Ma'u kawar Mami tayi ya katseta komawa kitchen, sai ta juyo da sauri tana amsawa fuska cike da farin cikin ganinta. Marhabun da kawar alkhairi, da zun nake zancenki a raina nace wannan baiwar Allah ta kasa cika alkawarin zuwa.Bari kawai Haj. Khadija wlh abubuwa ne sai Allhamdulillahi, kema kinsan yadda lamura suke hade mana yan kasuwar online.Na shaida haka domin Nima kullun fama nake da customers, Allah dai ya kara rufa mana asiri.Haj. Ma'u ta amsa da Amin tare da zama a daya daga Cushing din falon, Mami ta karasowa ta zauna a kusa da ita ta mika mata hannu suka yi musabaha tare da gaisawa da tambayar iyali, daga bisani suka shiga hirar business dinsu da suke yi, da yake manyan mata ne suna wandaka da kudi Masha Allah, ko wacce tanada babban shagonta, Mami nata na kayan sawa ne irinsu leshina atamfa da sauran kayan mata harda...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.