BAMBANCI AƘIDA

CHAPTER 2

by @queennasmerh08

🎐🎐BAMBANCIN AƘIDA 🎐🎐

( ƙaddarar Soyayya )


Based on true life story



Haƙin Mallaka

Queen Nasmerh

&

Nana M Sha'aban



*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*




_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._


*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*


WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.


*Wannan Littafin na kuɗi ne. Book one naira Ɗari ne kacal 100#.Domin biyan Wannan kuɗin, ka tura katin mtn na Ɗari zuwa ga wannan number*

*****

*Domin nuna shaidar turawa ka tuntuɓi akwatin sirrinmu na whatsapp ta wannan number, ****.

*Ko kuma wannan number*

*****, *ku faɗa biya domin free pages ba mai yawa za mu yi ba gsky, a fara payment.*


_*FREE PAGE*_

*_CHAPTER 02_*


Kasancewar yau ranar hutun ma'aikata ce (weekend) ya sa gidan cika fal. Saɓanin ranar aiki (weekdays) za ka tarar da su Lareesa kawai. “Abbu ka ganta ko? "Mehreen ta faɗa ta na yamutsa fuska, kallon Mehreen Abbu ya yi ya ce “Ƙyale ta ƴar Abbu", Lareesa ta ce “Adda Allah ki daina wannan abun, ke fa kin girme mu, ji su Lareefa da Laiha, fisabilillahi shi Shaheed ya ce me, ke kullum yarinya ki ke zama ", ba ta kalli kowa ba ta maida kanta kan cinyar Ummu, Ummu ta ce “ni ɗaga ni, ga Autana nan ban ɗaura a cinya ba sai ke", Abbu ya ce “Haba Jamila, du-du-du shekarar yarinyar nan nawa ", Yaya Mateen ya ce “Haba Abbu shekara 18 ba wasa ba ce, yanzu ku Larisa da ke da shekara 16 ai ba za a ma haka ba", Ummu ta ce “kana maganar Lareesa, ko Lareefa me 13 ai bazan bi ta kai ba, kai in kai maka ƙarshe ko Laiha me shekara 10 fa ", Lareesa ta ce “Ummu ai duk Abbu ne ya mana haka, ji Shaheed shekararshi takwas ba ya shagwaɓar da Yaya Mehreen ke yi". Ummu ta ce “ai duk Sulaiman ne ya sangantar da ita, Abbu kawai ƙarasawa ya yi".


“Assalamu Alaikum" su ka ji yo sallama, juyawa su ka yi a tare suna kallonshi da mamaki, “ɗan halak ka ƙi ambato " yaya Mateen ya faɗa ya na tashi domin taro shi , murmushi ya yi ya ce“Yayana ina wuni", hannun Mateen ya miƙa mishi, sannan ya ƙarasa gurin su Abbu. Durƙusawa ya yi kanshi har ƙasa ya ce “ina kwananku", “lafiya ƙalau Sulaiman ", da ɗaɗɗaya ya dinga gaisawa da mutanen parlorn, banda Mehreen da ta rufe ido ta gefen Ummu. Ummu ta ce “ke ban son shirme ba ki ga yayanki ba?", zumɓuro baki ta yi ta ce “Ummu! ", “eh Ummu ɗin, maza tashi ku gaisa". Tashi ta yi daga ginciren da ta ke, can ciki-ciki ta ce “ina wuni ", murmushi ya yi wanda ya bayyana kyanshi ya ce “lafiya lau ƙanwata", turo baki ta yi ta na danna waya. Murmushi ya sake yi kamar dai ɗazu. Nan su ka shiga firar duniya, wannan ya ɗauko labari wannan ya ɗauko, Sulaiman ya ɗan ƙanin Alhaji Jameel Auta ne wato Alhaji Abubakar Auta, kuma shi ne ɗa ɗaya tilo a gurinsu. Kansu ɗaya da Mateen shiyasa ba ya da gurin zuwa in dai Mateen na gari irin gidansu Alhaji Jameel Auta.



Sai dariya ake yi parlorn ya cika da nishaɗi, Mateen ya ce “oya oya, tsaya, yauwa ga Ramla na kirana video call bari mu kashe gaddamar ", ɗagawa ya yi, yayinda ya ɗaga wayar sama ta yadda za ta iya ganin duk mutanen da ke parlorn" nan ta ke duk yaran su ka tashi tsaye har rige-rigen yin magana su ke yi, “Aunty Ramlah mun yi kewarki matuƙa, su ka faɗa a tare, suna rige-rigen tura fuskarsu, ba su yi aune ba su ka ture Yaya Mateen, Tim! Ka ke ji ya faɗi ƙasa, duk su ka bishi ƙasa, Sulaiman da ke gefe sai dariya ya ke yi,



Da ƙyar ya samu ya taso, duk su Lareesa sai dariya su ke yi, Ummu ta ce “matsala ta da ku kenan, yanzu a yi magana ma kun ƙi bari ", Mateen da ke ɓata fuska ya ce “kun ma ja ma kanku ba zuwa outing gobe", Mehreen da ke zaune tun ɗazu ba ta ce komai ba ta ce “sun ja ma kansu dai, ni gobe sai ka je da ni outing ai ban maka komai ba ", wani mugun kallo ya watsa mata ya na ɗaga wayar ya ce “ai sai ki zo ki ja ƙafata mu fita", dariya Abbu ya yi ya ce “Mu dai yanzu ka yi magana da Ramla ɗin", dafe kai Mateen ya yi ya ce “ohh Allah Ramlah kin ga yaran nan ko ba sa jin magana ", dariya ta yi ta ce “ai zuwa yanzu ya ci ka san halinsu", “yauwa Ramla, ranar da mu ka kalli film ɗin zare da abawa, cikin Hashim da Muhammadu wa ya auri Aisha ", “Muhammadu mana ", “yauwa ba na faɗa mu ku ba, yanzu Abbu ka yarda na fi su Lareesa gaskiya ko ", Ramla ta ce “ni dai bani ƙannena mu gaisa na yi kewarsu", miƙawa Mehreen wayar ya yi, ya na faɗin “ki fara da uwar mita ", karɓa Mehreen ta yi, sannan ta yi ƙasa da muryarta su na fira, daga baya ta miƙawa Lareesa, kowa a, parlorn sai da su ka yi waya da shi, sannan su ka mata sallama, ta na jin kamar ta zama tsuntsuwa ta zo gida. In ji malam bahaushe ya ce kowa ya bar gida, gida ya bar shi.



Sun jima sosai a parlorn su na fira a parlorn har aka kira sallar isha'i sannan kowa ya watse, Abbu da su Sulaiman su ka wuce masallaci, Su Ummu kuma ya nufi Ɗakinshi yin sallah. Lareesa da Mehreen ɗakinsu ɗaya, Lareefa da Laiha ɗakinsu ɗaya. Da su ka yi sallah kawo ta nufi dinnig area su ka ci abinci sannan kawo ta koma ɗakinta. Bayan sun gama cin abinci Sulaiman ya masu sallama, sannan ya wuce.



---------------------

Ɓangaren Zainab kuwa tun da su ka dawo daga gidan Aunty Zaliha ta ka sa samu natsuwa a ranta, tun da ta ɗaura idonta a kan na Aimar ta ke ji bugun Zuciyarta na ƙaruwa, ta rasa dalili, haka ya sa ta rasa kuzarinta gaba ɗaya, komai su-ku-ku ta ke yi, har Inna ta lura da yanayinta “Oh ni Inna Larai ina ganin Ikon Allah, wai me ya sa ki ke abu kamar ba jini jikinki ne? ", firgigit ta farga daga tunanin da ta ke yi, ta ce “Innata babu komai kawai dai ba na jin daɗin jikina ne, amma Aunty Zaliha ta ba ni magani na sha" ta Ƙarashe maganar a ɗan daburce, “wayyo, ai da kin faɗa min Zainabu, to tashi ki je ki kwanta na hutar da ke, bari ne ƙarasa aikin", hannunta ta cire daga cikin ruwan wanke-wanken ta na yarfi da hannun, sannan ta nufi ɗakinta, ɗakinta matsaƙaici ne, dai-dai gwargwado, dan ba za ka kira su talakawa, ɗakinta gaba ɗaya hotuna ne na Sheik Zakzaky, ga littatafai da dama kan taburinta, sai katifarta matsaikaciya. Kwanciya ta yi kan katifar ta na juyi, yayinda ta sauke Idonta kan wani ƙaton hoto na Zakzaky, cikin sauri ta ɗaga hannayenta biyu ta haɗe tafin hannaye wuri ɗaya ta ce “ka min jagora ", sannan ta runtse ido, ta jima a haka kafin ta gyara kwanciyarta ta na nazari. “Albarkacin Nana Fatima Allah ka min mafita". Yadda ta ga dare haka ta ga safiya, dan zuwa yanzu ta gama yadda wutar son Aimar ta ruru matuƙa a zuciyarta. Wanda haka ne a ɓangaren Aimar be samu ya yi barci ba.


A ɓangaren Zeenat kuwa kwana su ka yi suna ba soyayyarsu ruwa, domin kuwa sai da su ka cika lungu da saƙo na zuciyarsu da Kalamai masu ratsa zuciyar me sauraro.


--------------------------

Raheema ba dan ta so ba haka ta haɗa kayanta, Abban Fareesa ya zo ya ɗauke ta su ka wuce, dan Abbansu ya tsaya kan maganarshi. Da kukanta ta tafi, Mamy sai mita ta ke yi, “Raheema tun ba yau ba kin san halin Abbanku miyasa ranki ya ke ɓaci har haka, ba ga Hazan can gidanta ba, kin ji ta na rigima zaman gida, ke da Allah ya rufa miki asiri ki ke zaunenki ƙarƙashin inuwar mijinki, shi ne ki ke ɗaga hankalinki, abunda kowace mace ke buri ke kin samu. Yaranki nawa, yaranki uku fa, Fareesa, Fatima ga Amina nan kina goyo, amma duk ki ka zo gidan nan sai an yi taƙaddama da ke ki ke komawa ", ta na jin Mamy sai faɗa ta ke mata su ka wuce, shi ma Abban Fareesa haƙuri kawai ya ke bata, akan wani wata zai kawo ta ta yi musu yini sai su koma.





Nan zamu dakata sai kuma mun haɗu a next chapter.


*Share and comments*


*NASMA & DIJARTY* ✍️

AMINAN JUNA💃