BAMBANCI AƘIDA

CHAPTER 5

by @queennasmerh08

🎐🎐BAMBANCIN AƘIDA 🎐🎐

( ƙaddarar Soyayya )


Based on true life story



Haƙin Mallaka

Queen Nasmerh

&

Nana M Sha'aban



*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*




_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._


*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*


WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.


*Wannan Littafin na kuɗi ne. Book one naira Ɗari ne kacal 100#.Domin biyan Wannan kuɗin, ka tura katin mtn na Ɗari zuwa ga wannan number*

*****

*Domin nuna shaidar turawa ka tuntuɓi akwatin sirrinmu na whatsapp ta wannan number, ****.

*Ko kuma wannan number*

*****, *ku fara biya domin free pages ba mai yawa za mu yi ba gsky, a fara payment.*


_FREE PAGE_

*CHAPTER 05*


Irin yadda suke yi wa junansu kallon soyayya, abin zai yi matuƙar burgeka, Zeenart ce ta rufe fuskarta tana dariya ƙasa-ƙasa tace "dan Allah ka daina kallona haka ai sai ka saka na dinga jin kunyarka" Sani yace "Kinga dan Allah ki buɗe fuskarki, wa kika taɓa ganin yana jin kunyar mijinsa" Zeenart ta buɗe fuskarta tace "to na daina" tayi magana tana kallon zabgegen carbin hannunsa tace "Honey! wai wannan ƙaton carbin amman yafi guda dari biyar ko?" Dariya Sani yayi yace "guda dubu ne cif" Murmushi Zeenart tayi tace "gaskiya ne! to amman ka na yin kwana nawa kafin ka gama janshi","A yau ma zan gama janshi, saboda kin ga yau jumma'a zanje wajen zikiri bayan sallar magriba, to ina so na gama kafin na lokacin yayi" jinjina kai Zeenart tayi tace "Yayi kyau! Allah ya taimaka" Sani yace "Amin ya rabbi!" Zeenart tace "wallahi idan muna tare ba na son mu raba ko kaɗan, gashi ba kullum ka ke zuwa ba, kuma ni ina so ka dinga zuwa kullum gaskiya idan ba haka ba zanyi fushi" Sani yace "nima ba asan raina ba ne, kin san dai dalilin da yasa muke yin hakan, dole ne mu cigaba da ɓoye soyayyarmu har sai lokacin da Allah yasa tare da taimakon shehu muka samu mafita, kiyi haƙuri kinji uwar ƴaƴana, alfarmar Annabi Muhd komai zai zama tarihi" Zeenart ta turo baki tace "yanzu ka na nufi idan ka tafi ba zan ƙara ganinka ba sai nan da kwana uku sai dai mu dinga waya" Sani yace "kiyi haƙuri kin san dai akwai ƴan gulma, kuma nan kin ga hanyar wucewar mutane ce, duk da cewar dai ba lallai a gane su waye ba, tunda mun rufe fuskokinmu da facemask, amman karki manta rayuwar nan mutum ake kiwo da dabba ba, akwai waɗanda dole suna sane damu, za'a iya kai gulma gurin iyayenmu kin ga ai ba za ki so ace hakan ta faru ba, amman tunda ƙorafinki akan kwana ukun da nake yi ban zo ba, to gobe ki shirya zan zo, amman da daddare wajen ƙarfe takwas, amman a wajen shagon Dogo zamu haɗu, saboda yana da kyau mu dinga chanza wajen haɗuwa saboda tsaro" Dariya Zeenart tayi tace "yauwa ko kai fa! Allah ya kaimu goben" Sani ya amsa da "Ameen" daga haka suka cigaba da hirar soyayyarsu, Sani ya raka Zeenart ta wajen gidansu, ya tsaya daga nesa sosai da gidan, ita kuma ta ƙarasa gidan tana tafiya tana waiwayensa har sai da ta shiga gida, shima ya nufi gidansu.

________________

Angela ce zaune tana darzar kuka, iyayenta, yayanninta da ƙannanta sun sakata a gaba suna tayi mata faɗa, ɗagowa tayi ta kalli babban yayansu Samuel wanda ya kasance yana da sauƙin kai da fahimta sosai, kuma yana ƙaunarta fiye da tunanin mai karatu, miƙewa tayi ta kama hannayensa tana kuka tace "Am sure kai kaɗai zaka yarda dani kuma zaka fahimceni, ni ban yi haka dan na ɓata muku rai ba, kuma Abbakar ni na nuna masa ina son muyi aure, da farko ya ƙi amincewa, sai da ya ga na daina yi masa magana ko ya kirani ba na ɗauka, shiyasa ya amince, ban san hakan zai ɓata muku rai ba kuyi haƙuri, kuyi min duk hukuncin da ku ka ga dama, amman na rokeku karku saka Abbakar a ciki, ni na tilasta masa ya amince mukayi aure" Merry wacce ita ce take bin Samuel ta ware hannayenta ta ɗaga ta yarfawa Angela akan kunci, gigicewa tayi, saboda marin yayi matuƙar shigarta ta ƙanƙame Samuel tana cigaba da rera kuka tana kiran sunansa "ka taimaka min bro zasu kasheni" Momy tace "Ai baki ga komai ba, tunda har kika zaɓi ki auri wanchan musulmin ai gwanda mu kasheni mu huta da baƙin ciki da abin kunyar da kike son janyo mana" Momy tana rufe bakinta Merry ta ɗauka ta cigaba da cewa "Momy i swear to god, wannan yarinyar yau sai ta bar gidan nan, dan ba zan iya zama da ita ba" Samuel cikin kakkausar murya yace "Merry! ba inda zataje, kin ji na faɗa miki idan har kika saka Angela ta bar gidan nan to sai dai ku tafi tare dan kema ba za ki zauna a gidan ba" Papa ya dora hannu akai yana cewa "jesus me nake ji yana fitowa daga bakinka Samuel so kake ka bi bayanta" Samuel yace "baku fini jin baƙin cikin abinda Angela tayi ba, na fi ku shiga tashin hanjali da baƙin ciki, duk hukuncin da zakuyi mata ku yi mata, amman banda korarta domin kuma ba zan bari ta bar gidan nan ba" Yana gama faɗar haka ya ɗago Angela daga jikinshi cikin tsawa yace mata ta shiga ɗakinta, da gudu ta shige ɗakinta ta kulle kofar da key, shima ya haye sama ya shige ɗakinsa ransa duk a ɓace, iyayensa da su Merry suka bi bayanshi da kallo, Anna wacce take auta tace "Momy yanzu ba za'a raba auren ba kenan? shikenan sister Angela ta auri musulmi" Ester tace "kotu zamu kai su ai, dole a raba auren nan, dan kuwa ba za'a janyo mana abin kunya ba, Papa kuwa saboda baƙin ciki bai iya ce musu komai ba, ya shige ɗakinsu Momy ta bi bayansa, Merry ta kalli ƙannannata tace "Ku tafi ɗakinku" tayi maganar tare da samun guri ta zauna a tsakar gidan ta zabga tagumi, tana jin wani irin tuƙuƙi a cikin zuciyarta, Ester da Anna suka tafi ɗakinsu kamar yadda Merry ta basu umarni.


_______________

"Kaiii Abbakar ɗago ka kalli ni ka ba ni amsar tambayata, meye haɗinka da wannan bayahudiyar?" Abbakar wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa yana tsiyayar hawaye ya fara magana cikin rawar murya yace "Matata ce!" Ai bai ƙarasa rufe bakinsa ba ya ji saukar mari, ki kake tas! tas! tas!, hannu hagu da na dama, Abbakar ya durƙushe ƙasa daga zaunan da yake, tare da dafe kuncinsa yana jin wani zugin raɗaɗi, nan da nan kukan da yake yi, ya tsaya cak, tabbas sai yanzu ya san cewar kukan ma rahama ne, duk yadda yake son yayi kukan amman ya kasa, rufeshi da duka yayi, dakyar Mama ta samu ta kwaceshi, Abbakar ya samu ya ja jiki ya fita daga gidan, zuciyarshi cike da baƙin ciki, amman ko kaɗan bai yi danasanin auren Angela ma, gidan Abokinshi Mansur ya tafi da yake babu nisa sosai da gidansu.


****

Zainab tana zaune akan katifar ɗakinta tana kallon bango, tana sakin murmushi, irin yadda take kallon bango, zakayi tunanin bangon take kallo, amman kuma sam ba shi take kallo ba, kawai dai idanuwanta ne akan bangon, amman hankalinta da zuciyarta sun lula cikin duniyar tunani, wayarta ce ta shiga ruri, kallon screen ɗin wayar tayi, ganin sunan wanda take burin ya sake kiranta yasa ta lumshe ido, tana murmushi tace "My Aimar!" wayar ta ɗauka tare da ɗagawa ta kara a kunnanta ba tare da tace komai ba, "Assalamu alaikum" Yayi sallama cikin sanyin murya, Zainab cikin muryar raɗa ta amsa sallamar "wa'alaikassalam" Lumshe ido Aimar yayi yace "Yammatana wato har aji ake ja min ko?" Zainab ta zame ta kanta akan katifar tare da tura kanta a cikin pillow tana dariya, Aimar jin sautin dariyarta yasa shima ya shiga murmushi mai kunshe da zallar farin ciki, "meya sakaki dariya?" Aimar ya tambayeta "bakomai" ta bashi amsa a hankali, "ban yarda ba" Aimar ya faɗa yana murmushi, "da gaske nake bakomai" Aimar yace "kin san me?" Zainab tace "A'a","ina sonki" Zainab ta zaro ido tare da ƙara tura kanta cikin pillow ta kashe wayar tana dariyar farin ciki, juyowa tayi tana kallon hoton Zakzaky tace "Ina godiya, ka bani farin cikin da na daɗe ina burinsa, a yau na samu farin cikina Aimar" tayi maganar tare da haɗe hannu biyu alamun nuna godiya.


_________________

Raheema ce zaune tana ba wa Ameenarh abinci, Abban Fareesa yana kusa da ita, ya ƙura mata ido, ɗagowar da za ta yi idanuwansu suka gauraya da juna, murmushi sukayi gaba ɗaya tace "Abban Fareesa ya da kallo, ai sai ka sakani na fara ɗaga kai" Dariya yayi sosai yace "Ai kin chanchanci ki ɗaga kai, uwar gida kuma Amaryar Abban Fareesa, saboda duk lokacin da na kalleki, ina jin kamar babu wanda ya kai ni gata a duniya" Raheema tace "nima haka nake ji Abu Fareesa"


_Yanzu aka fara, ku dai ku yi hanzarin siyan wannan ƙayataccen littafin nan domin jin yadda zata kaya, book 1 is #100_


*#SHARE*


*NASMA & DIJARTY*

_(AMINAN JUNA💃🏼)_