BAMBANCI AƘIDA

CHAPTER 7

by @queennasmerh08

🎐🎐BAMBANCIN AƘIDA 🎐🎐

( ƙaddarar Soyayya )


Based on true life story



Haƙin Mallaka

Queen Nasmerh

&

Nana M Sha'aban



*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*




_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._


*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*


WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.


Sha zaman ki *FA'IZARMU*, muna godiya sosai ubangiji ya biya ki.



*CHAPTER 07*


Samuel ya karɓi takardar yana juyawa, zuciyarshi cike da takaici, miƙewa yayi ya nufi ɗakin Angela, bubbuga ƙofar ɗakin ya soma yi yana kiran sunanta, Angela jin Samuel ne yasa ta buɗe ƙofar, har lokacin kuka take kamar zata shiɗe, idanuwanta sun kumbura, dakyar take iya buɗesu, dan sun ƙanƙance, fuskarta kuwa tayi jajawur abin ka da farar fata, muryarta ta dashe ta yadda idan tayi magana ba, ba za ka ji me tace ba, sai ka saurara sosai sannan zaka iya tsintar wasu abun, hannunta Sameul ya kama suka je wajensu Papa ya zaunar da ita, tare da miƙa mata takardar bayan ya zauna shima yace "kin ga abin da mahaukacin musulmin nan yayi! to wallahi tunda shi ya fara mu zuba mu dashi, zai ga yadda ake tijara kuma aurene dole a rabashi" Kuka Angela ta fashe dashi ba tare da ta iya buɗe takardar ta karanta ba, ko kaɗan bataji haushin Abbakar ba, dan kuwa ta san ya yi hakane dan kar a rabasu, ɗagowa tayi tana kallon Samuel tace "Ina jinka a cikin raina, saboda kai ne ɗan uwana wanda na fi ƙaunarsa, a duk lokacin da na shiga cikin wani mawiyacin hali, kai ne ka ke fitar dani, meyasa ba za ka taimaka mana a wannan karon ba brother? aure kawai mukayi ba wani abun mukayi me muni ba, meyasa ka ke jin haushin Abbakar, a tunanina ko da kowa zai juya min baya kai ba za ka juya min ba, za ka tsaya ka fahimceni sosai, a kullum maganarka shine ka na son na auri wanda zan ji daɗi kuma wanda ba zai taɓa wulaƙantani ba, na cika maka burinka ta hanyar auren Abbakar domin kuwa ina da tabbacin ba zai taɓa wulaƙantani ba, ni ina tunanin za ka yi murna, amman kuwa sai ka ke nuna min cewar baka farin ciki har ka na yi min faɗa" ta ƙarashe maganar tana ci gaba da kuka, jikin Samuel yayi sanyi sosai, janyota yayi ya rumgumeta yana bubbuga bayanta, Merry tace "au wato brother har kalamanta sun yi tasiri a zuciyarka, karka manta a kaf danginmu babu wanda ya taɓa auren arniya, dan haka dole a raba auren nan" Samuel yace "keee! Merry ki shiga hankalinki karna ƙara jin kin ce komai anan" cikin tsawa yayi maganar, Momy ta saki baki tare da cewa "Samuel me zan gani haka? ka na nufin daɗin bakin da wannan shashashar yarinyar tayi maka ya shiga zuciyarka, to wallahi ba ku isa, ba ku isa ba nace" Tayi maganar tare da zarar mayafinta ta fita waje, Samuel ya kama hannun Angela suka hau saman bene inda ɗakinsa yake, Papa ya bi bayansu da kallo tare da jan tsaki ranshi duk a ɓace, Merry kuwa zama tayi tai ta zuga Papa ya cika yayi fal, Ester da Anna suka tayata, sai da suka tabbatar Papa ya fusata sannan suka barshi, Papa mutum ne me haƙuri sosai, da wuya ka ga ranshi ya ɓaci, amman kuma idan ranshi ya ɓaci yana iya aikata komai.


________________

Soyayyar Sani da Zeenart kullum ƙara cigaba take, sun yi shaƙuwar da kowannansu yana ji a zuciyarsa idan har babu ɗaya ba zai iya rayuwa ba, suna matuƙar ƙaunar junansu fiye da tunaninku, kamar dai kullum waya ce a maƙale a kunnan Zeenart suna waya da Sani, Umma ce ta shigo ɗakin da sauri Zeenart ta sauke wayar daga kunnanta ta katse kiran ta shiga murmushin yaƙe tana cewa "Umma kece?" Umma ta ƙura mata ido tace "meye na ga kina ganina duk kin wani birkice ko baki da gaskiya ne" Zeenart tace "Aa wallahi ina da gaskiya Ummata, kawai dai na ga ɗazu na shiga ɗakinki kina bacci shiyasa, nayi mamaki dan naga idan kin kwanta kina daɗewa baki tashi ba" Umma tace "eh wallahi Abbanki ne ya tasheni wai tuwo miyar kuka yake so nayi masa kafin ya dawo" Zeenart tayi murmushi tace "Abbana ai yana son tuwo sosai" Umma tace "shiyasa na zo dan bamu da kuka, ga naira sittin ɗin nan ki siyo kuka a gidan Lantana mai kayan miya, dan har na ɗora tukunyar miya a ɗayan murhun kiyi sauri ki kawo min kafin ruwan ya tafasa" Zeenart ta karɓi kuɗi ta saka hijabinta ta fita dan siyo kuka, a hanya ne ta yi wa Sani text kamar haka *Habibi! karka ji na kashe wayar Umma ce ta shigo ɗakin, kayi haƙuri anjima zamuyi waya* tana gama rubutawa ta tura masa, ko minti ɗaya batayi da tura sakon ba, Sani ya maido mata da amsa *to ba damuwa uwar ƴaƴana, Allah ya kaimu anjiman* Zeenart tana shiga gidan Lantana ta ga saƙon Sani, bata bashi amsa ba har sai da ta siyo kuka ta tsaya a zauren gidan ta tura masa da saƙo *Amin Habibi ka kula* ko da Sani ya ga saƙonta murmushi kawai yayi tare da bin rubutun da kallo, yana jin soyayyar Zeenart tana ƙara shiga zuciyarsa.


•••••••••••••••••••••••

"Yaya Mateen! dan Allah na kawo wankina ka yi min kala biyu ne bashi da yawa" Kallonta ya shiga yi galala, ya tsame hannunsa daga cikin ruwan wanki ya miƙe yana kallonta ido cikin ido, "Lallai Mehreen ban taɓa tunanin baki da kunya ba sai yau, ni zaki cewa ki kawo wankinki nayi miki" Yayi maganar cikin ɓacin rai, turo baki tayi tace "Ai na ga wanki ba shi da yawa shiyasa nace maka haka, kuma na ga ai wankin ka ke yi yanzu" Mateen ya saka hannunsa a bakinsa yana kallon Mehreen, "Keee! Mehreen kalleni dakyau, wallahi ina faɗa miki ki fita daga idona na rufe, wallahi kafin ranki yayi mummunan ɓaci" Zumɓuro masa baki tayi tace "to menene dan nace na kawo wankina, idan ba ka wanke min ba ai me wankinmu zai zo na bashi ya wanke min" Mateen yace "ƴar wahala! zaki ɓace min da gani ko sai na fasa miki kai" Kuka Mehreen tasa tana cewa "wallahi sai na faɗawa Ummu ni ba ƴar wahala bace" Dariya Mateen yayi yace "ai kuwa idan kin ji ana cewa babbar ƴar wahala to kece, wawiya kawai" Duk cikin dariyar yake magana dan kuwa yasan Mehreen ta tsani ace mata ƴar wahala ko wawiya ko wani abu da ya danganci haka, kukanta ya tsananta ta shiga gida da gudu, a falo ta tarar da Ummu da Suleiman suna hira, miƙewa suka yi dukkansu suna tambayarta meyafaru, amman ta kasa faɗa saboda kukan da yake cin ranta, Suleiman ya matsa kusa da ita yana tambayarta "Me aka yi miki, ki faɗa min dan Allah" Mehreen tace "Yaya Mateen ne yace min ƴar wahala kuma yace min wawiya" Suleiman ya dafe goshinsa tare da cewa "ki shigo dan Allah, ki daina kukan nan ya isa haka, yanzu zanje nayi masa magana" Ummu tace "ai kamata yayi ka tambayesa me tayi masa, dan kuwa idan ɓera da sata to daddawa ma da wari" Suleiman yace "Ummu amman ko me tayi masa bai kamata yace mata ƴar wahala ko wawiya ba" Ummu tace "kawai dai kace kareta za ka yi" Ana haka sai ga Mateen ya shigo falon fuskarsa a ɗaure, Ummu tace "zo nan Mateen me Mehreen tayi maka da za ka ce mata ƴar wahala" Mateen yace "Ummu ina wanke vest ɗina kawai, wannan yarinyar ta zo tana ce min wai ta kawo min kayanta na wanke, ni ɗan aiki ne aka gaya mata" Ummu tace "to Suleiman ka ji dai, abinda tayi, dan haka ai dole yace mata ƴar wahala, saboda rashin kunya tace masa ta kawo kaya ya wanke" Mehreen ta tsananta kukanta jin abinda Ummu tace, Suleiman hankalinsa ya tashi zaunar da ita yayi ya shiga rarrashinta, Mateen ya kallesa tare da dariya yace "lallai kam! aiki ya sameka" Yayi magana tare da shigewa ɗakinsa, Ummu ma ɗakinta ta shige dan kuwa idan ta biyewa Mehreen ba za ta taɓa hutawa ba, Suleiman hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ga Mehreen ta daina kuka, anan ya shiga janta da hira, Mehreen tace "ka faɗawa Yaya kar ya ƙara ce min ƴar wahala ka ji Yaya Suleiman!" Mehreen tace "to angama gimbiyar mata! ai idan ya sake sai mun yi zanga-zanga a gidan nan" dariya tayi sosai, tare da cewa "yauwa Yayana"


__________________

Aimar da Zainab kuwa shafin soyayya suka buɗe, kullum cikin waya suke a rana sai ya kirata kusan sau goma, ga text message kullum da safe dashi zata fara cin karo, Zainab tana tsananin jin daɗin yadda Aimar yake nuna mata soyayya hakan yasa take gani kamar tafi kowace ƴa mace gata a duniyar nan.



A ZAHIRIN GASKIYA BAZA MU ƁOYE MU KU BA MUNA MATUƘAR FARINCIKI DA SOYAYYAR DA KU KE MA LITTAFIN NAN. COMMENTS ƊINKU SUN MATUƘAR YIN TASIRI A ZUCIYOYINMU.


*#SHARE*


*NASMA & DIJARTY*

_(AMINAN JUNA💃🏼💃)_