MARAICHI

Page_2

by @nanatoou

____MARAICHI

BY_NANATOOU

WATTPAD_ @Nanatoou


Na kuma rungume shi ina sakin murmushi, ina matuqar qaunar daddy. sai kuma na dago na dubesa ina fadin, "Daddy ina gift dina".


"surprise ne, karki damu zan baki".


Murmushi nai na kiqe tsaye,ina hamma nace, "feeling sleepy daddy.., pls daddy get ready for the party".


"karki damu princess din daddy".


"to bara naje wajan mummy" na karasa maganar ina nufar kofar fita. Yayin da daddy ya bini da kallo harna fice, cike da so da kauna. Na samu mummy sunata hira a dakin mu, na haye cinyarta, su sanah su na ta yi min dariyar wai har yau ni baby ce. Nikam kota kan su ban bi ba, dan nasan, they're jealous ne kawai, amman inba hakaba ina ruwansu dani, ai, I'm the last born, sai yacca naga dama zanyi. 


Na dubi aunty bilkisu tare da fadin, "nifa har yunzu baby ce..., I'm just twelve (12).." 


"Kin manta ma, zato ce ke"sanah ta fadi tana dalla min harara. 


Mummy kam cemin tayi na rabu dasu ,ni ce dai babyn ta. Nai ta jin dadi kuwa, dan su bilkisu inda sabo sun saba da halina. Ana haka mummy take gayamin ai aunty fa'iza autarsu daddy ta karaso jiya da daddare. Murna na hauyi dan ina matuqar kaunar ta, she's among my favs, dan tana matuqar riritani sosai. Mummy taci gaba da fada min ai yan agadez ma, a Abuja suka kwana, zuwa karfe takwas zasu hau flight zuwa kano.wata sabuwar annushuwa nakeji, saini yar'gata kowa ji yake yi dani, duk saboda ni akazo. Inata murna dan ina matuqar san dangin mummy, dan kauna kam, 100% suke nuna mana ita. 


Ana cikin hira bacci yai awon gaba dani, daman ni da asuba kullum saina koma bacci, yunzu delay din rashin komawa ta ma, dan dokin da nakeyi na birthday dina ne. Mummy ta kwantar dani kan gadona,hijab din dake jikina ta ciremin, ta shafa kaina tare ta lullubeni. Nan ta tisa su Sanah a gaba, suka fice a dakin. Lokacin kam shida harda kusan mintina talatin.


Kitchen suka nufa, sukaje suka fara aikin hada breakfast, yayin da talatu daya daga cikin house help dinmu take tayasu da wasu abubuwan.


Mummy macace da bata yadda da girkin yan'aiki ba, indai lokacin shiga kitchen yayi, zata saka yanmatan ta a gaba su shiga, tun tasowata mu hakan take yi.


Ni kuwa ko da na bisu kitchen din, ba abinda nake tsinanawa,inbanda uban surutu dazan ishe su dashi. Shi yasa wani lokacin in na bawa Sanah haushi take kirana parrot.


Bayan mummy sun gama hada breakfast din su, mai rai da lafiya, suka jeresa dinning din part din daddy. Already daman house helps sun yi daily duty dinsu, na gyaran gida. 


Su sanah suka koma daki, in da ni kam, har lokacin baccina naketa sha. sanah ta dubeni ta dubi agogo,takwas harta wuce,,ta girgiza kanta tana fadin, "wallahi mummy sun gama shakwaba yarinyar nan". 


Bilkisu tai murmushi, "sai kace ke ba kiyi na ki lalacin ba...".


Sanah bata kulata ba, taci gaba da gyaran gadonta da takeyi. 


Dakin mu babbane, wanda yake dauke da gadaje guda uku. Gadajen matsakaita ne girman su basu karasa family bed ba, kowa da nasa gadon Wanda a gefena sa Yana dauke da side bed drawers dinsa, dauke da lamp din ka akai. A dakin akwai wardrobe katuwa guda daya wacca kowa yake saka kayansa a ciki, sai dress mirror din mu wanda yake cike da kayan kwalliya kala--kala wanda akasarin su, suke kusan mallakin sanah ne, dan itace maiyar painting din fuska. Sai perfumes kalakala designers masu kanshin gaske.


Ba wani tarkace ne acikin dakin mu ba amma an kawata mana shi daidai misali, yacca take daukan hankali.


Kan gadona kuwa harda teddies, an kawata min gadona da su, abokanai na kamar yacca nake Kiran su.


Dankin mu ko da yaushe cikin tashi kamshi yake, ga gyara ko Ina tas tas, babu datti ko kadan, dan Sanah da Bilkisu kam suna bauta masa daidai gwargwado, dan Allah ya hore musu tsafta. Yayin da ni kuwa, ina daga gefe, ana gyara ina yacca raina yaso, kuma ba yacca suka iya yi dani. Kullum mummy cikin tausars u takeyi akaina, cewar zan dena, wata ran da kai na ma zan gyara dakin ba tare da an saka ni ba. Ko da yake ma wata rana in na cika mata ciki, ita kan ta mummy makeni takeyi, sai daddy yayi aikin lallashi, shiyasa nake cewa ni daddy's girl ce.


Ina matuqar kaunar mahaifin namu ko dan yacca yake tattalamu, ni daman i'm everyone's favourite, Kowa ji yake yi dani, uwa tsokar nama daya a miya. Yawanci tsokana ta ce ma ke hada ni da su sanah.


Kan sanah ta gama gyaran dakin, aunty bilkisu tayo wankanta, tana fitowa sanah ta shiga. Itama bayan tafito suka tasheni daga baccin, ba yacca na iya haka na mike naje nayo wanka. Ina fitowa kuwa already sanah ta daukomin wata sabuwar gown da mummy ta siyo min ita, colour din baby pink. Na daga rigar na duba ta inata murna, yayin da sanah ta zaunar dani akan stool din dress mirror, Aunty Bilkisu ta dauko straightener ta fara gyaramin kaina yayin da sanah ta shafa min body lotion din da muke sawa.


Bayan aunty bilkisu ta gama gyara min kai na, sanah ta danyimin light makeup. Ai kuwa ta na fara yi min, na nutsu waje daya dan ina san a gan ni na yi extraordinary beauty.


Banyan ta gama min tace ai nahin makeup din sai anjima zata yi min.


Sai murmushi kuwa nakeyi inajin wani dadi. Na mike da sauri na dauki kaya na na soma sakawa, bayan na shirya muka nufi bangaran daddy dan muyi breakfast.


Akan dinning din, muka tarar dasu mummy har da Aunty fa'iza, su na ta hirar su.


Muka karasa mu ka gaishe su, sannan muka zauna, mu ka kuma yiwa aunty fa'iza ya gajjiyar hanya.


Ai kuwa sai tsoka na ta take yi, anatayin dariya.


Sanah ta tambayi abokin ta wato dan gidan aunty fa'iza, me sunan daddy. Age mate din sanah ne, tare sukayi yarintarsu akwai shakuwa atsakanin su sosai.


Aunty fai'za tace, "ai makaranta ce ta hana sa zuwa amma yaso yazo" 


Aunty fa'iza ta dubeni cikin sigar tambaya da tsokana tace "a'ahh kun ga yammatan daddy, yar gaban goshi, aunty kausar din mu an girma, yunzu shekarar ki nawa ne?" 


With full excitement nace "twelve". Ai kuwa suka sa ka dariya yacca sukaga nayi.


Cikin tsokana kuwa aunty fa'iza tace "kice yarinyata ta isa aure". 


Jin haka ma zumburo da baki, a raina Ina fadin Auren lfy. Suka kuma sa dariya kuwa.


Bayan kammaluwar breakfast din, muka koma cikin parlour din daddy aka zauna anan. munata hira cike daso da kauna as one family.

Anan maama(aunty fa'iza) take tambayar sanah batun karatunta, tare da cewa, "dear what are your plans, nan gaba for the future, ko kuma dai har yunzu kina nan yacca na sanki..."


Murmushi sanah tayi, "maah, ina nan dai akansa, nidai bana san in canja, next year by now, insha allah munyi candy, so...I'm planning na nema a B.u.k..."


"Naji dadi kam daughter, ai course ne mai kyau, Allah sa mi ki Albarka". Maamah ta fada tana karfafa mata gwiwa.


"Hmmm...., Wlh duk abinda yarannan sukeyi, to da sa hannun ku aciki, amma a ce yarinya ta dage sai tayi wani fashion design, duk courses din duniyar Nan, maimakon ku kwabeta, se wani cewa yayi yayi kukeyi" Mummy ta karasa maganarta tana hararar sanah.


Nikam dariya nayi, ban ga komai a abun da sanah din ta ke so ba, amma mummy kullum bataso, in ta Bata Rai da Sanah to akan maganar karatu me, sai tace ai akwai course bola adadin da suka fishi. Daddy kam yace bazai matsa mata ba, tayi wanda ta san tana so.


Gyaran murya daddy yai tare da fadin "Fa'iza ai akwai wata makaranta da nake planning din in kaita insha allah".


"wacce kenan yaya" Maama ta tambaya tana bawa daddy duka attention dinta Wanda mu ma mun mayar da hankalin mu kan sa.


"FASHION SCHOOL OF LUXURY AND DESIGN ce, na PARISIAN ROOTS INTERNATIONAL VISION ". 


Ai tunkan daddy ya idda maganarsa, Sanah ta wani rukunkume aunty faiza,cikin tsantsar farin ciki da nuna murnar ta.


Ba ita daya ba ko ni nasan makarantar, nasan cewa makarantar itace best fashion school in the world. Dukan mu, muma farin ciki muke yi sosai.


Mummy da ta ga yacca mukeyi, sai tai murmushi kawai. Macace ita me san ta ga ahalin ta cikin farin ciki, shiyasa ko da yaushe take ma Allah godiya daya ba ta daddy amatsayin miji. Duk yacca Daddy zaiyi ya kyautatawa iyalansa ya sani.


Daddy ne yai gyaran murya, tare da soma fadin, "to school din tana da three campus, akwai a paris_france kenan, sai shanghai_china kenan, saikuma istanbul_Turkey...," Ya Dan dakata, kafin daga bisani ya cigaba da fadin, "to har yunzu banyi deciding wacce zata je ba, a good friend of mine, yana zama da iyalansa acan paris din, kuma gidanshi is very close to the school..., secondly sai ta turkey din, kinga akwai gidan ki" ya karashe maganar yana nufi da aunty fa'iza yake yinta.


"Aikam dai yaya, abar maganar wani aboki, tazo istanbul din kawai muyi zaman mu, sai tafi jin ma, more comfort acan tunda ga dan uwanta ma, she'll feel more home a gurina, ko sanah?" Aunty fa'iza ta karashe maganar ta da tambayi sanah.


Sanah ta gyada mata kai,tana murmushi, na dubeta, kaidaka ganta kasan she's over joyous, ta ma rasa inda zata saka kan ta dan farinciki. Daddy ne yace, " to hakan ma yafi"


"kun yanke shawara ni ba ku nemi jin ta bakina ba, haka akeyi" mummy ta fada fuskar ta dauke da murmushi..


"to ai na naga, bakya goya mata bayane, so..., nikam kinsan, indai abu ba haram ta shi akayi a addinance ba, zanyi wa ya'yana, to wai ma bayan mu wa suke dashi...?" daddy ya karashe maganar sa ta sigar tambayar mummy.


"babu". Mummy ta fada a takaice, sannan ta dora da fadin, "nifa ba cewa nai kar kayi musu abin da suke so ba, kawai dai ina tinasar da kai ne akwai mutuwa me marabawa, wata ran in mune tare dasu watarana ba mu ba ne, shiyasa nake san su san ba komai da ka ke so ka ke samu ba, yunzu dan Allah jibi Alhaji bashir waye zai bashi mutuwa, duk da dai bata da kama, amman yau gashi kwanan sa hudu a kasa, Allah ya jikan rai" Mummy ta karasa maganar cike da alhini tare da jimamin mutuwar abokin Daddy.


Jikinmu duk yai sanyi dan mun tuna da mutuwar gaba dayan mu. 


Alhaji bashir business partner din daddy ne, and a good friend of his, zazzabi yayi na sati daya, rai yayi halinsa. Babban mutum ne, kuma ya manyanta bashi da karamin yaro ko daya, asali ma, autansa ma ya kare karatunsa this year. 


Tunowa da nayi mutuwa me yankan kaunace a ko da yaushe, sai idanuwana sukayi narai narai dasu suna shirin zubda hawaye, murya ta na karkarwa nace, "amman daddy kai ba yunzu zaka mutu ba ko?" Na karashe maganar cikin sigar tambaya da yarinta.


Shafa kaina yayi cikin sigar lallashi tare da kwantar min da hankali yace "haba princess di ta, itafa mutuwa da ki ke ganin ta, ta wajabta akan kowa, in lokaci yayi, dolan mu ne mu amsa kiran mahaliccin mu, ko muna so ko ba ma so, kuma ita hutuce a gurin mumini" 


saiya tsagaita da maganar tasa, cikin sigar tsokana kuma yace, "uhm, ashe dai princess na sona da gaske, ba ta san ta rasa daddyn ta".


Dariya ta cubcemin, hakan yabawa hawayena damar gangarowa fuskata, daddy yana murmushi ya gogemun su, Amman duk jikinmu sai yayi sanyi...sai kawai na rungume daddy tare da fadin "i love you daddy". Murmushi yai tare da cigaba da shafamin kai na. Na daga Kai na dube sa tare da fadin, "Ni dai Kam mutuwa ba zata dauke min daddy na yunzu ba".


Suka danyi dariyar yacca nayi maganar, Maamah sai yace, "Yaya karko zai yi irin na Dabino".


"Insha Allah...". Muka fada a tare. Daddy yai murmushi kawai. Sai kowa Kuma yayi shuru batare da an kuma fadin wani abun ba.


Ringing din wayar daddy, yai breaking silence din, ya dauka tare da karawa a kunnan sa. Kusan maganar mintina biyar, sannan sukai sallama.


Ni dana riga nayi bacci a jikinsa, ya fara kwantar dani, akan kujerar, Ya dubi su mummy tare da cewa, "to ni zan fita, akwai wasu kaya da sukazo".


"Kaya Kuma, ba akwai wanda zasu tsaya ba". Mummy ta fada.


"Akan wayan nan wanda mukayi maganar da dake, to dole sai naje na tsaya akan su, amman bazan dade ba zan dawo" 


"Ashe kam in kausar ta tashi za'a sha rigima, bayan yau tace ba inda zakaje, throughout kuna tare" mummy ta fada idanun ta akaina, tana kallan yacca nake bacci na cikin kwanciyar hankali.


Daddy yai murmushi, "karki damu i won't stay long...kuma it's urgent shiyasa zanje, Kuma kin sani, Insha allah zan dawo da wuri"


"Allah ya yarda" cewar mummy.


Cikin sigar wasan wa da kanwarsa aunty fa'iza tace, "tunda yunzu twelve o'clock minti shabiyar muka baka...."  


"Insha allah bazan wuce azahar ba zan dawo,dan ko rigimar princess" daddy ya karashe maganar yana nufin hanyar fita yayin da duk suka mike, suka rufa masa baya.


A compound kuwa, bayan driver ya dauko mota, Daddy ya kuma duban su gabaki daya, tare da cewa "And, pls... kar kubar princess tayi kuka, make her comfortable har na dawo, kunsan ban san tana dunga yin rigima" ya tsagaita tare da mai da dubansa kan mummy, "ga amanar ya'yana nan dai, na bar miki, kar a takuramin yarana, let them feel my presence ko da yaushe pls..." Daddy ya karashe zancan cikin yanayin neman alfarma.


Dariya mummy tayi tana fadin "insha allah" Daddy ya dubi su bilkisu da sanah yace "to...daughters, I'm going, pls take care of yourselves, ga kanwar ku can ku kular min da ita, kunsan dai dai kunsan akasin hakan, so, pls take care"

"to daddy" suka amsa suna murmushi.


Ya shiga motar sai kuma ya leko ta window, fuskar sa dauke da madaukacin murmushi tare da fadin..., "I love u all..pls take care" su ma murmushin suka mayar masa har mummy tana fadin, "daddy kodai za ka dawo ka zauna a fasa fitarnan ne, kafi kula da mu baki daya". ta karashe maganar cike da tsokana. 


kai kawai ya girgiza sannan yace"i wish...i can do so...." yana gama fada yai ma driver alamun su tafi. Su kam su Mummy tsayawa su ka yi suna masa waving din a dawo lfy. Sai da aka aka mai da gate aka rufe, sannan suka juya dan komawa. Horn sukaji anyi, hakan ya saka su dan dakatawa, motoci guda biyu ne, suka yo cikin gidan bayan bude gate din da aka Kuma yi.


Motocin ba suyi parking lot ba, suka yo inda su mummy suke, sukai parking a gaban su. 


Yan uwan mummy me, Yan agadez suka fito daga motocin, su su takwas, Aunty sadiya, aunty suwaiba, aunty ramlat da aunty yahanasu sai yaransu uku Ahmad, yusuf da mufeeda.


Cikin tsantsan farin cikin ganin juna suka rugume juna, suka hau murna gaba dayan su Dan ganin juna.


A haka ana masu maraba da zuwa, sukayi cikin gida gaba daya. Sai nan nan mummy da aunty fa'iza sukeyi dasu, nan suke gaya musu ma ai tun nine (9) ma suna kano. Sun biya gidan kawar aunty suwaiba data haihilu sun mata barka, to acan suka shantake sai yunzu suka karaso..


Hayaniyarsu ce ta tashe ni daga bacci, ai kuwa naita murnar ganinsu. Musamman da naga harda yarinyar aunty Ramlat, mufeeda, wacca daman age mate ditace. 


Sai na ware, koda nasan daddy bayanan ban wani damuba, nashiga harkar gabana. Amman jikina yayi weak Kuma banji dadin fitan daddy ba, Dan alkawarin me tsakanina dashi akan ranar yau tawace ni daya.


Mummy babban sitting room din gidan suka nufa, a cewarsu, zasuyi decorating din wajan tun yunzu, yacca za'ayi komai akan lokaci, tunda birthday partyn zaiyi taking place by four zuwa ko five.

Ana haka snacks din da akayi order akayi delivery din sa. 


Ni kam, jan hannun mufeeda nayi, muka tafi garden, naji farin ciki mara misaltuwa.


Karfe daya bayan an kira mu, munyi sallah.muna idar da sallar, na dauki wayar mummy na kira daddy, Dan hankalina Yana kan sa. Ganin har lokacin Bai dawo ba, Kuma mummy ce min su kai yace bazai dadeba, he should be home by now. bayan ya dauki kiran ya hau lallabani tare da rarrashina, yace min wani abu ne ya tsaida shi amman gashi nan tawowa. Yana ta lallashina waikar nayi kuka dan yasan tabarata.


Bayan ya tabbatar ya lallashe ni Kuma ya hau yi min nasiha, sannan yace nayi keeping kaina busy har ya dawo, amman banda yi wa su sanah rashin kunya gaba suke dani, nidai to kawai nake cewa, sannan mu kai sallama.


Mun ci gaba da wasan mu da mufeeda, sai naji bazan iyaba gabaki daya, jikina yai wani weak, uwa an zare min lakata. Sai kawai na koma parlour din mummy na kwanta. Bana jin dadin jikina ko kadan. Mufeeda sai tambayar abunda ke damuna takeyi, ni kuwa cewa nayi, ba komai, bacci kawai zanyi kan daddy ya dawo.


Mummy ma, anata bangaran, yin abu kawai takeyi ba'a dadin rai ba, har suka gama abinda zasuyi, suka dawo side dinta. Nan ta shige dakin ta, tace zata huta. To haka dai aka koma gidan duk bamajin dadi. Su aunty suwaiba ma sama sama suka dunga yin hirar.


Har zuwa 2:30pm, ina jiran daddy babu shi ba alamun sa, gashi na kusan awa daya ina ta trying number dinsa...da farko tana ringing amman daga baya sai naji switch off. Duk nabi na damu,zuciyata Bata min Dadi ko kadan idona ya ciki uwa zanyi kuka bakina kuwa uwa me, na bi nayi pouting na Bata fuska Wai ni a lallai ba hakan mukayi da daddy ba.


Ina wannan yanayin ne, kira ya shigo wayar ta hau ringing, na duba da sauri azatona daddyne amman sai naga akasin hakan, Matar Baffa ishaq ce ke kira aunty hajara. Uwa zan daga kiran saina fasa kawai.


Na mike daga kan sofar da nake akwance, na nufi bedroom din mummy nakai Mata wayar ma Kiran ya katse. Zan shiga bedroom din mummy, Aunty suwaiba fito, sai ta dakatar dani, tace mummy ta kwanta kanta na ciwo. Zanyi magana wani Kiran ya Kuma shigowa wayar, sai ta amshi wayar tare da daga kiran. Ni kuwa na tsaya ta gama kiran, ta Kara wayar a kunnan ta tare da sallama. Daga haka shuru ne ya biyo baya, tana sauraran dayan bangaren, sai na ga gaba daya ta rude tana ta ambatar inna lillahi wa inna ilaihi raji'un..... Fada take yi tana Kuma ambata babu kakkautawa.


Hankalina ya tashi, sai kawai na fashe da kuka. Su aunty sadiya suka fito daga dakin suna tambayata menene, sai suka mayar da tambayar kan Aunty Suwaiba. 


Sai da ta fan saisaita kanta sannan ta ce wai daddy ne yai accident a hanyarsa ta dawowa, amma Kar mu daga hankalin mu minor accident ne gasu nan ma dawowa gida.


Kafin ta Gama bayanin ta ma, gabaki daya ni da su sanah kuka mukeyi, hakan yasa mummy ta fito a birkice, naje na rungumeta ina kuka.


Ita ta ma rasa me zata tambaya ganin yacca ta daburce tana kokarin lallashina da jin meke faruwa, sai mufeeda ta gaya mata abin daya faru.


mummy sai ta zama mutun mutumi a wajan, bakin ta ya bushe, tama rasa Mai zata fada.


Haka muka zauna a parlourn kowa dauke da damuwa, Sanah nata faman Kiran wayar daddy baya shiga. Jikin kowa ya mutu a parlour din.

Aunty suwai ba ta shiga daki sai ta Kira aunty Ramla, sai ga aunty Ramla ta fito halittun fuskarta ya canza kuwa tayi kuka, Amman ban bi takan hakan ba.


Yacca nake a jikin maamah a kwace tana ta lallashi na.


Bayan wasu mintina, aunty Hajara suka iso tare da tawagarta. Zuwan su ne ya kuma cakuda komai, Basu zo mana da Alkhairi ba, zuwan su ya kusan haifar mana da rasa rayukan mu.


Suna shigowa parlourn suka kalle mu yacca muke azaunen kowa yayi shiru. Na daga ido Ina kallan su, Wanda kusan dukan mu kallan na su muke, amman sai naga ba daddy, kafin nace wani abu, Maamah ta rigani Yi musu magana tana tambayar Ina daddy din.


Aunty Hajara ba tare da wani boye boye ba, ta kalle mu, straight forward tace mana daddy ya rasu.


Ai kam ta ga karamin hauka a gurinmu, Sanah ihu nima ihu... cewa wallahi ba dai daddyn mu ba. Aunty fa'iza kam da tazamo karamar mai tabin hankali, shaketa tayi, bayan zagin da take aika mata da shi.


Dakyar aka samu aka bambare ta daga hannun aunty fa'iza, sai kuma aunty fa'iza ta zube a wajan tana kuka uwa ranta zai fita. Nikam birgima nakeyi a parlourn, tare da ihun Kiran Daddy. Sanah kuka da ihu da iyakar karfinta yayin da itama bilkisu kukan takeyi uwa ranta zai fita.


Tashin hankali wanda ba'a saka maka rana kenan, domin kuwa ashe somin tabi muka fara.


Isowar baffa ishaq da gawar ya dakatar da komai, sai dif kakeji a palourn, mun zama mutun mutumi, kafin mu farga mummy da tun dazu take a tsaye kamar an dasata, ta yanke jiki ta fadi.


mukai kan ta mu na sakin sabon kuka, mun shiga wani yanayi mai wuyar fassara, wani Hali da bamu taba tsintar kan mu a ciki ba.zan so ace na tashi daga wannan mummunan mafarkin da ban taba yin sa ba, Amman hakan sai ya gagara, Wai babu daddy, Yama za'ayi hakan ya zama gaskiya, sai dai a mafarkin.


Maimakon hakan ya tabbata karya na tashi daga baccin Nan, Sai Mutanen da suka fara zuwa ne, suka kara cakuda komai.


Gaisuwa Wai daddy ya mutu, wai kuma za'ayi jana'izar daddy bayan sallar la'asar.


"INNALILLAHI WA'INNA'ILAIHI RAJI'UN....DADDY IS NO MORE"..........


#COMMENT

#VOTE

#FOLLOW

#Share fisabilillah





ASTAGFURILLAH WA'ATUBI'ILAIK