Chapter 12
🎐🎐BAMBANCIN AƘIDA 🎐🎐
( ƙaddarar Soyayya )
Based on true life story
Haƙin Mallaka
Queen Nasmerh
&
Nana M Sha'aban
*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*
_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._
*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*
WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.
BAMBANCIN AƘIDA IS NOW FREE SABODA SOYAYYAR DA KU KE MA LITTAFIN KUN CI KYAUTAR BAMBANCIN AƘIDA.
Mu Haɗu a littafanmu - *SILAR YAUDARA NA HAƊU DA ALJANA* , da kuma *NAWA ƁANGAREN* nan ba da jimawa ba.
*CHAPTER 12*
Raheema tana kwance akan kujera wani irin bacci ta ke ji, idanuwanta sun yi mata nauyi har ta ya fara kwashe ta, Mamy ta shigo falon, ta daɗe tana ƙurawa Raheema ido, kafin ta ƙarasa kusa da ita, tashinta ta shiga yi "Raheema tashi ki zauna" Dakyar ta iya buɗe ido cikin muryar barci ta ce "Mamy barci na ke ji, dan Allah ki bar ni nayi" Mamy ta ce "karki manta yau kin cika sati guda a gidan nan, ya kamata ki tashi ki kama hanya ki tafi gidanki, kin dai ji me Abbanku yace miki ranar da kika zo, idan ba so ki ke ku saka ƙafar wando ɗaya da shi ba" Tashi Raheema ta yi zaune tana cewa "haba Mama meyasa bakwaso na zo gidan nan, kullum idan nazo ku dinga korata kenan, bayan ba haka ku ke yi wa Hazan ba, ni sam bakwa so na zo ma, ko zuwan da nayi last time haka ku ka min" Mamy tace "Ke kam rigimarki ta fi ƙarfinki, kuma ita Hazan da ki ke cewa ba haka mu ke yi mata ba, idan ta zo kin taɓa ganin tana ƙin tafiya ai kina ganin yadda take yi tana zuwa, muna gaisawa ta yini ta ke tafiya, amman ke sai anyi yaƙi ki ke tafiya har da kuka kamar wata ƙaramar yarinya''
Raheema tace "ita ai bata son gidan ne shiyasa" tayi magana tana turo baki, Mamy tace "Laaa yau na ga babbar tijara, Hazan ɗin ce bata son gidan?" Raheema ta gyaɗa kai alamar eh, Mama ta ce "yayi miki kyau, tashi ki bar min gidana to" Raheema ta ce "gidanmu dai" Mamy tace "Raheema ungo" tayi maganar tana saka hannunta a kan fuskarta, dariya Raheema ta yi tace "Abban Fareesa sai jibi zai dawo dan haka ina nan ba inda zan tafi, Abeey ma na faɗa masa ai ɗazun nan" Mama ta ce "bai faɗa min ba, dan haka ban yarda da ke ba!","ki tsaya idan ya dawo ki tambaye sa za ki ji abinda zai ce" Mama ta nufi ɗakinta tana cewa "bari ya dawo idan ma ƙarya ki ke , ai kin san abinda zai biyo baya" Raheema ba ta ce komai ba, ta zame ta kwanta bacci mai nauyi ya kwashe ta.
___°___°___°____°____
"Ado ina butocin gidan nan na ga kai ka kwashe su ɗazu?" Baba ya tambayi Ado ɗan ƙaninsa,"Eh Baba a wanchan ɗakin Mama tace na saka su" Baba yace "maza je ka ɗauko min ɗaya, na yi sauri na yi alwala dan na samu jam'i" Ado ya amsa da to, sannan ya miƙe zai tafi ɗakin, Angela ta nufo gurin da suke hannunta riƙe da buta ta cikota da ruwa, dan ta ji duk abinda Baban ya ke cewa, kuma ta ga yana son yin alwalar da wuri, shiyasa ta ɗauki butar Abbakar ta zuba ruwa ta kawo masa, "Daddy ga shi na kawo maka ruwan" Baba ya bi ta da kallo, ya kawar da kansa gefe, kamar ba zai karɓa ba, sai kuma ya karɓa tare da tsugunnawa ya fara alwala, Angela ba ta tafi ba, har sai da Baba ya gama alwalar ya bata buta tace "A dawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya" Juyowa yayi ya kalleta fuskarsa ba murmushi yace "nagode" yana gama faɗar haka yasa kai ya fita daga gidan, Angela ta koma ɗaki zuciyarta cike da farin ciki, saboda tana ganin tunda yanzu Baba yana karɓar abin hannunta zata samu hanyar siye zuciyarsa, saboda ta fuskanci Mama tana zafin rai, amman kuma tana jin maganar Baba, daga haka idan ta dace ta samu ƴancin kanta a gidan a dena bata aikin wahala.
Zaunawa ta yi a kan gadon ɗakin, anan take maganar Abbakar ta dawo mata kai lokacin da ta ganshi da kwaɗon zogale yake ce mata Baba zai kai saboda yana son kwaɗon zogale, miƙewa tayi zumbur kamar wacce aka tsikara ta shiga duba zogalen da Abbakar ya kawo mata jiya suka yi kwaɗo, kwano ta ɗauko tayi masa kwaɗo ya ji magi sosai, kasancewar Abbakar ya taɓa faɗa masa Baba baya son gishiri da kuma yaji, dan haka ta saka yajin ɗan kaɗan, ta rufe bayan ta gama haɗa kwaɗo ta samu guri tana jiran a idar da sallah, ana idar da sallah ta leƙa ta window Abbakar da Baba ta gani sun nufi babban falo sai da ta tabbatar sun shiga, ta ɗauki kwanon da tayi kwaɗon zogale ta nufi babban falo, zuciyar tana buga mata da sauri dan bata sani ba ko haƙarta zata cimma ruwa, ƙirjinta ya tsananta bugu lokacin da ta ƙarasa gaba ƙofar babban falo, dakewa tayi ta shiga buga ƙofar a hankali, Ado ne ya buɗe ƙofar yana kallon Angela ya ce "Laaa Aunty Angela ce" Ya yi maganar tare da komawa ɗakin Angela kuwa da sallama ta shiga falon babu wanda ya amsa, Abbakar ya miƙe tare da cewa "Angela me kike yi nan" kallonsa kawai tayi bata ce masa komai ba, Mama ta miƙe a fusace tace "ke tsohuwar bayahudiya, uban wa ya baki izinin shigo min falo?" Angela ta Kalle ta bata ce mata komai ba, ta ƙarasa inda Baba yake zauna ta tsugunna tare da ajiye masa kwano tace "Daddy ga kwaɗo zogale" tana gama faɗar haka ta tashi ta fita daga falon ta koma ɗakinta, Baba kuwa tunda ta ce kwaɗon zogale, ya ɗauki kwanon ya buɗe, wani kamshi ne ya daki hancinsa, ya saka hannu ya ɗibi zogalen ya kai bakinsa, idonsa ya lumshe tare da cewa "Uhmm ya yi daɗi sosai" Abbakar bai san lokacin da yayi murmushin jin daɗi ba, saboda ba ƙaramin daɗi ya ji ba, da ya ga Baba ya ci abincin da Angela tayi, Mama kuwa faɗa haɗe da masifa ta shiga yi ''Haba Baban Abbakar ka na da hankali kuwa, za ka ci abinda waccen kafirar ta yi, ka sani ma ko wani barbaɗen tayi maka a abinci ta kawo" Baba yace "Yanxu dai zaki bar ni na ci zogalena ko kuma faɗan zaki ci gaba da yi, jiya da na kawo miki zogalen na ce kiyi min kwaɗo kin yi? ai cewa ki ka yi sai dai ki siyo min na A'i me abinci, to yanxu yarinyar nan tayi min ta kawo shi ne kuma ki ke ta wani hayagaga" Mama tayi shiru, takaici da baƙin ciki ya turnuƙeta, fuuuuu ta fita daga babban falon ta huce ɗakinta, Baba kuwa ya ci-gaba da cin zogalensa, Abbakar da farin ciki yake neman ya shiɗar dashi a tsaye yayi wa Baba sallama ya fita daga falon.
___________________
Kukan da take yayi matuƙar ɗaga masa hankali, rarrashinta ya shiga yi, cikin kalamai masu daɗi da kwantar da hankali, Zeenart tace "Sani wallahi ba zan taɓa iya rayuwa ba tare da kai ba, dole ne mu samarwa kanmu mafita, domin ni kai kaɗai na ke da burin aura" Sani ya ce "duk na san da haka Zeenart amman koke-koken nan ba zai tsinana mana komai ba, ya kamata ki kwantar da hankalinki ki daina kukan nan domin kukanki yana ɗaga min hankali" Zeenart ta ce "Yanzu menene mafita, dan in har ban ji mafita ba, to hankalina ba zai taɓa kwanciya ba" Sani yayi jum yana tunani, maganar Zeenart ce ta katse masa tunaninta ya ɗago yana kallonta cike da mamaki.
_Anan zamu dasa aya✍🏽dan Allah kuyi share zuwa grp 10 da ku ke dashi🤌🏽_
*#comments*
*#share*
*NASMA & DIJARTY*
(Aminan juna💃🏽).