JUYIN KADDARA
by @fanan
Page 1️⃣
"tafiya muke nida yan uwana dalibai munzo yawan Bude ido"
"nifa dajin Nan ya matukar burgeni saboda akwai abubuwan danake so sosai a wajen" ummi ta fada. "kallo na na maida kanta nayi murmushi Wanda ya Kara fito da dimful Dina nace nima gsky wajen Nan ya Burge ni sosai , ina MA a ce za'a Kara mana ko kwana biyu ne"
Dariya ramkat ta fashe da ita tare da cewa "haba ashna yaufa kwanan mu biyar a wajen Nan ya kamata ace Nan da kwana biyu mun tafi Sai dai idan zamu barki anan,
Kallo na mayar Kan Latifah ita kuma naji abinda zatace tare da cewa" ke kuma Latifah me Zaki ce?
Kwafa tayi tare da cewa "hmm ni kinsan me yafi Bata mani rai a wannan camping din yadda Malan Umar ya mayar da hankalin shi Kan wannan mayar malama munubiyar, Sai wani rawar Kai yake akanta ni nama rasa menene yake burgeshi a jikin ta, tare da maida kallon ta Kan ummi ta cigaba da cewa, jiya da dare Bayan kunyi bacci ina kallon ta ta fita ta tafi wajen shi Sai wani turu kirji take kamar wata agwagwa. Takai karshen maganar tare da rungume hannuwan ta a kirji.
Murmushi ramlat tayi tare da mayar da kallon ta kan Latifah "haba Latifah nidai a ganina ba wani sonta yake ba kawai dai itace take shishshige masa, kuma Kinga ranar da zamu tahu ta wani saka wata uwar bra Mai cuku Sai wani gantsaro kirji take taje zata shiga gaban Motar shi ya koro ta yace ta shiga female school bus haka ta turu uban baki ta shigo bus din kafin muzo camp din Nan tayi tsaki yakai dari biyar.
Dariya Mai dauke da farin ciki Latifah ta sake saboda taji an kushe wacca take Nema ta shige ma masoyin ta tare da cewa yanzu mutanena tayaya zanyi na "Raba Malan Umar da munubiya saboda Bana so tana shiga sabgar shi?.
Kallo na na mayar kanta nace" "haba Latifah kedai kawai kice kina kishi da ita neh saboda ba kya so ayi maki kwacen Maso......... Ummi ce ta katse mani hanzari tare da cewa" Kai kufa kalli agogo ku gani lokaci tafiya yake yanzu fa wajen shida da minti ashirin ya kamata mu kuma. Tana Kai karshen zancen muka bayana a gaban wani katon dotse Mai fitar da ruwa(wajen yayi kyau sosai gashi ya kawato da fure yellow da green da fari ga bakan gizo ya bayana a wajen ni ban masan yadda Zan musulta maku wajen wajen kawai Sai Wanda ya gani)
Latifah ce ta kamu hannu ta Jani wajen tare da cewa sauran "Dan Allah ku tahu muje wajen Nan ko hoto uku ne muyi" muna isa wajen
Nida Latifah da lamrat muka jeru a wajen ummi ce take yi mana hoto "wow ladies kunga yadda kuka yi kyau a wannan hoton Amma fa Latifah da Ashna suka cinye hoton Mika Mata hannu nayi tare da Amsar wayar ashe tare muka Mika hannun tare da Latifah hannun mu suka sauka Akan wayar aiko Nan muka fara kiciniyar kuwa ya amshe I wayar a hannun da uwan shi
Zan wayar Latifah tayi tare da turani baya saboda tafi karfi na cikin rashin sa'a sulbin laka ya kwasheni nayi baya Tim Karan fada wata ruwan kawai suka nayi nayi Naga na kubuta Amma ina na makara domin Har nayi kasan ruwan wani katon dotse naje na buga da karfe...........