Chapter 13
🎐🎐BAMBANCIN AƘIDA 🎐🎐
( ƙaddarar Soyayya )
Based on true life story
Haƙin Mallaka
Queen Nasmerh
&
Nana M Sha'aban
*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*
_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._
*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*
WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.
*CHAPTER 13*
"Zeenart kai na ya kunce, ba na cikin nutsuwar da zanyi kawo mafita, tunda na ji iyayenki sun ce ba za su ba ni aurenki ba, hankalina ya fita daga jikina, Zeenart iyayenmu suna neman ruguza alaƙarmu" Ya faɗa yana jin wani zafi a ranshi, hawaye ne yake bin kuncinta, cikin ƙarfin hali tace "Sani bazan bari BAMBANCIN AƘIDA ya zama silar ragujewar alaƙarmu ba, ni ba zan iya nesa da kai ba, mafita ɗaya ce kuma wannan mafitar shine mu gudu mu bar gari muje inda za'a ɗaura mana aure muyi zamanmu a chan" A take a gurin Sani ya amince da maganar Zeenart ko gida basu koma ba, suka kama hanya suka bar garin.
___________________
Aimar ne tsaye a gurin da suka saba haɗuwa da Zainab, kusan mintina biyar ya ɗauka a gurin sannan Zainab tazo, da sallama ɗauke a bikinta "Assalamu alaikum masoyi" Aimar ya amsa yana murmushi, zama tayi a gefenshi tana kallonsa "Zee ɗita ya gida?" Zainab tace "lafiya ƙalau alhamdulillah" Aimar yace "Ya mamana?","tana nan ƙalau" Aimar yace "amman kin san me?" Zainab ta girgiza kai alamar Aa, yace "Ya kamata Mama su san sirikinsu fa, dan mu daina wannan laɓe-laɓe" Nan da nan fuskar Zainab ya chanza, ta ɓata rai tare da cewa "Ba yanzu ba dai, sai nan gaba" Aimar yace "to meyasa?" Zainab tace "saboda akwai matsala" Aimar yace "kawai dai kice min bakya sona" Zainab tace "meyasa zaka ce haka? kawai danna faɗa maka gaskiya, duk irin yadda nake nuna maka soyayya zakace ba na sonka, idan har kace haka kuwa bakayi min adalci ba wallahi" Aimar yace "ai dole nace haka da kina sona ai zaki je gida ki faɗa cewar ni kike so, amman ke naga kin fi ganewa ace muna laɓe, saboda bakya ƙaunata, shiyasa bakya son kowa ya sanni" Zainab cike da baƙin ciki ta miƙe tare da cewa "tunda haka kace, to naji bana ƙaunarka, wai meyasa ka fiya son kanka ne?","kece kika fiya son kanki, bari in faɗa miki gaskiya idan har ba za ki faɗawa iyayenki game da soyayyarmu ba, to ba zan ƙara kula ki ba, meye amfanin baɗi ba rai, na daina wahalar da kaina wajen laɓe-laɓe" Zainab tace "yayi kyau, tunda haka ka zaɓi dan na rabu da kai, kana tunanin ba zan samu kamarka ba, ko kuma kana tunanin ba zan rayu ba, ba tare da kai ba, karka manta ba tare aka haifemu ba, cikin mahaifiyata ni kaɗai na rayu, kuma ko da ta haifeni ba tare da kowa nayi rayuwata ba, dan haka zan cigaba da rayuwata kamar da, dan mun rabu sai me" tayi maganar tare da yin gaba, Aimar ma tashi yayi ya hau mashin ya bar gurin, Zainab tana tafiya tana kuka, kwata-kwata bata so ta faɗawa Aimar maganganun nan ba, kawai dai tana gudu kar su rabu, dan idan ta faɗawa iyayenta ƙarshen rabuwarsu tazo, amman ta fuskanci Aimar idanuwansa sun rufe, a ɓangaren Aimar kuwa hankalinsa a tashe yake, shi yayi mata ne dan ta faɗawa iyayenta ayita ta ƙare, dan yasan duk daɗewa sai sun sani, shiyasa yake ganin gwanda ta faɗa musu ko zasu iya tausaya musu.
____________________
"Sweetheart yau kin burgeni fa sosai" Angela tayi murmushi tace "Da aka yi me fa?" Abbakar yace "wato so kike ki siyewa Baba zuciya ko? shine har yi masa zogale" Angela tace "Me nayi kuma dan nayi masa zogale, ai wannan ba siye zuciya ba ne, nayi ne dan Allah" Abbakar yace "To yayi zan ƙara miki wasu dabarun dan ki samu Baba ya fara sonki, dan idan ya nuna yana ƙaunarki to wallahi ƴan gidannan ba wanda ya isa ya nuna miki yatsa, har nima idan nayi miki lefi kika kai ƙarata to ranar sai dai ya gudu daga gidan" Angela cike da farin ciki tace "me zanyi masa ya ƙauna ce ni irin haka, ni ba na jin daɗi yadda suke nunawa ba sa sona, kuma ka faɗa min yadda zanyi Mama ita ma ta so ni, duk da naga ita bata sona sosai, dan ko ganina bata son yi" ta ƙarasa maganar cike da damuwa kunshe akan fuskarta, Abbakar ya rumgumeta yana cewa "Sweetheart itama zata ƙauna ce ki sosai wallahi karki damu kin ji, ki kwantar da hankalinki, kinga Baba yana son mutum mai ɗa'a da biyayya, kamar ni kin ga kullum da safe ina zuwa na gaishesa, kuma ina tafiyar masa da ruwan tea mai na'a na'a, dan yana so idan ya tashi ya fara shan tea, kuma kamar yadda kika yi zogale yana son zogale, ki bari zuwa anjima zan faɗa miki sauran abubuwan da yafi so kinji, amman ki fara riƙe wannan a kanki" Angela tace "thank you sweetheart" Abbakar yace "never mind sweetheart" Nan suka shiga hirarsu ta soyayya abin gwanin ban sha'awa, kiran sallar isha'i ne yasa Abbakar ya tashi ya nufi masallaci, Angela ta haye kan gado, tana waƙoƙinsu na church, Ana idarwa Abbakar ya dawo, suka kwanta zuciyoyinsu cike da farin ciki.
*WASHE GARI.*
Angela da wuri ta tashi, kallon inda Abbakar yake kwance tayi, murmushi mai ƙunshe da soyayya zalla ta sakar masa, sauka tayi daga kan gadon kunna risho ta dafa ruwan tea, da yake Abbakar ya nuna mata na'a na'a ta sakata har da citta da kanumfari ta haɗa, ta dafasu tare, ta zuba sigar sannan ta sauke ruwan tea ɗin da ta ga yayi, ta zuba musu nasu a flask ta zuba na Baba a wani ɗan madaidaicin kofi mai murfi, ta miƙe ta fita daga ɗaki, ɗakin Baba ta nufa tana zuwa ta shiga bubbugawa, ya ɗauki kusan mintina biyar kafin ya buɗe ƙofar, tsugunnawa tayi har ƙasa "ina kwana Baba" Baba ya amsa mata fuskarsa babu yawo babu fallasa "lafiya ƙalau" tashi tayi ta miƙe masa cup "Baba ga tea nan na kawo maka" Baba ya karɓi cup ɗin tare da cewa "nagode" juyawa tayi ta koma ɗaki, har lokacin Abbakar bacci yake, ƙarasawa tayi ta zauna kusa dashi tana wasa da hannunsa a hankali, idonsa ya buɗe yana murmushi "Good morning sweetheart" Angela ta faɗa tana murmushi "Morning how was your night?" Angela tace "fine ooo, and you" Abbakar yace "same to you" Angela tace "kasan me?" Abbakar ya girgiza kai yana duƙunƙunna, a cikin bargo, Angela tace "yanzu na kai wa Baba tea" ware ido Abbakar yayi yace "Are you serious? (da gaske kike?)" Angela tace "yeah baby am serious kuma ya karɓa har yace min ya gode" Abbakar yace "lallai baby da zafinki haka"
*Anan zamu dasa aya✍🏽*
*NASMARH & DIJARTY*
_[Aminan juna💃🏽]_