BAMBANCI AƘIDA

Chapter 14

by @queennasmerh08

🎐🎐BAMBANCIN AƘIDA 🎐🎐

( ƙaddarar Soyayya )


Based on true life story



Haƙin Mallaka

Queen Nasmerh

&

Nana M Sha'aban



*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*




_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._


*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*


WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.



BAMBANCIN AƘIDA IS NOW FREE SABODA SOYAYYAR DA KU KE MA LITTAFIN KUN CI KYAUTAR BAMBANCIN AƘIDA.


Mu Haɗu a littafanmu - *SILAR YAUDARA NA HAƊU DA ALJANA* , da kuma *NAWA ƁANGAREN* nan ba da jimawa ba.



*CHAPTER 14*


Tun daga wannan ranar da Angela ta samu sauƙi a gidan dan yanzu idan Baba na gida ta na ɗan samu hutu. Amma duk in da aka ce Baba ba ya nan to ita kam ta san watan shan wahalarta ya kama.


Abu ne me wahala gurin masoya biyu su jure junansu, haka ne a ɓangaren Aimar domin kuwa sosai ya shiga tashin Hankalin rashin Zainab amma ya ƙudurta a ranshi ba zai taɓa kula ta ba in dai har ba za ta iya tunkarar iyayenta da maganar ba, wanda haka ya yi matuƙar tunzura Zainab ta ɗau alƙwarin ba za ta kula Aimar ba ko me zai faru idan dai ba zai yarda da uzurinta ba.


---------------------------

“Ni dai idan ba ki yi sauri ba wallahi tafiya zan yi " Mateen ya faɗa daga bakin ƙofar ɗakin Mehreen, “wayyo Allah ɗan uwa gani nan zuwa fa" ta ƙarashe maganar ta na ɗaukar Jakarta, ta fito su ka wuce. Ummu na zaune su ka iso parlorn “mun wuce "su ka faɗa a tare, Ummu ta ce “yauwa ƴaƴana ku gaida min Sulaiman da jiki", “insha Allah "Mateen ya faɗa, Mehreen kuma da to ta amsa, Ummu ta ce “Mateen kar ka manta ka baro Mehreen can, idan su Laiha suka dawo daga makaranta za su zo, in ya so zuwa anjima da marece sai ka dawo da su in ka dawo daga aiki", “ashe yau sai na kai motata an wanke min ita "ya faɗa yana rufe hancinshi cikin sigar zolaya, Mehreen ta ce “me ka ke nufi", Ummu ta ce “ƙyale shi ni dai kar ku tsira min rigima, ke da shi kullum cikin faɗa kamar ka ji ", dariya Mateen ya Ƙyalƙyale da ita har da riƙe ciki ya ce “wayyo Allah cikina, kuma wallahi Ummu kin canka dai-dai yarinyar nan kamar kaza", Ummu da ta kasa Riƙe dariyarta ta ce “ku dai ku ka sani ". Har su ka fita waje Mehreen na mita wai ya ce mata ƙazama dole sai ya wanke motarshi, kuma ya ce mata kaza, shi kuma ban da dariya babu abunda ya ke yi.



Kai tsaye rijiar lemu su ka nufa, dan anan unguwar Sulaiman ya ke, wani katafaren gida ne na ji na gani su ka tsaya gaban gate ɗin, su ka shiga yin horn, me gadin gidan Malam ya buɗe musu gate ɗin su ka shiga ciki. Gidan ya haɗu matuƙa, cikin parlorn gidanma abun kallo ne, wata mata ce zaune da alama ita ce mahaifiyar Sulaiman, za ta yi tsara da Ummu dan ta ɗan manyanta, Mateen ya zauna ya ce “ina wuni Ummin Sulaiman " haka kowa ke kiranta, matar da ya kira da Ummien Sulaiman cikin far'arta ta amsa da lafiya ƙalau, Mehreen ma ta ce “ina Wuni" cikin jin kunya, Mateen ya ƙyalƙyale dariya ya ce “wai waya kwaɗo sai wani noƙe kai ki ke yi ", Ummien Sulaiman ta ƙara faɗaɗa murmushinta ta ce “lafiya ƙalau ƴata zo nan" hannun Mehreen ta ja ta rugume ta tsam jikinta, sannan ta ce “Mateen ka fita idona fa, ka fiya tsokanar surukata", “Ummien Sulaiman kina cikin suruka, ina me jiki "ya canza topic ɗin maganar nan take, “ya shiga wanka, amma na san ya gama yanzu zai fito abincinshi na jiran shi",fira su ka dinga yi, banda Mehreen da ta yi luf a jikin Ummien Sulaiman, duk a takure ta ke jin kanta. Ba a yi minti biyar ba sai ga shi ya fito, murmushi ya saki, sannan ya zo ya zauna yana cije leɓensa da alama ya na jin jiki, Mateen ya ce “Sannu da jiki ", “yauwa sannu ɗan uwa, yaushe ku ka zo" ya tambaya, Mateen ya ce “ba mu daɗe da zuwa ba gaskiya ", “haba ai da kun kira ni" ya faɗa, Ummien Sulaiman ta ce “ni na ce musu kana wanka ", gaɗa kai ya yi, sannan ya kalli Mehreen, dai-dai nan ta ɗago su ka haɗa ido, da sauri ta kawar da fuskarta ta ce “Yaya ya jiki", murmushi ya yi ya ce “na warke garas tunda ga ki na gani ", gefen gyalenta ta sa ta rufe fuskarta irin ta ji kunya, aiko me Mateen zai yi in banda dariya, har da riƙe ciki, Suleman ya ce “kai ka fita idona fa", Ummien Sulaiman ta ce “wallahi ko na ga ya raina min inlaw ", “haka ya ke mata wallahi sai na saɓa maka" Sulaiman ya faɗa, Mateen ya ce “ko kunya ba ka ji ba wai ka ji sauƙi tunda ka ganta, wannan matsitsiyar yarinyar ". Haka Mateen ya dinga tsokanar Mehreen a ɗakin, su Ummie tun su na Riƙe dariya har su ka fara yi, Mehreen ko ta kai ƙul dan har ta fara kuka, da Mateen ya fahimci ya yi latti gurin aiki ya tashi ya musu sallama sannan ya tafi.




---------------------

Sani kuwa daga Kano ba su tsaya ko ina ba sai haɗeja dan shi ne gari mafi kusa da su, wani abokinshi ya kira Musa ya zo ya ɗauke su a tashar mota su ka wuce. Kafin su iso Sani ya riga ya mishi bayanin abunda ke faruwa, shi ne kawai amintaccen Sani saboda haka Sani be yi shawara biyu ba wajen kiranshi.



Gidanshi ya wuce da su, ya ma matarshi bayani a taƙaice musu fatan alkhairi, sannan ta nuna ma Zeenatu wani ɗaki ta ce nan zata zauna har komai ya dai-daita, Sani kuma ya ce ba matsala zai zauna wajen gidan, tunda gidan baya da ɗakuna wadattu, ko ɗakin da aka kai Zeenatu ɗakin tarkacen kaya ne, saboda haka za a gyara mata shi, dan Musa ba wani hali gare shi ba, rufin asirin Allah ne kawai, dan wani lokacin ma sai a nemi abinci a rasa a gidan, yaran su biyu Aliyu da Azeema, Azeema ta ke goyo dan bata wani jima da haihuwarta ba.




Anan zamu daka ta sai gobe in Allah ya kai mana rai.







_✍🏽Dan Allah kuyi share zuwa grp 10 da ku ke dashi🤌🏽_


*#comments*

*#share*


*NASMA & DIJARTY*

(Aminan juna💃🏽).