Chapter 16
🎐🎐BAMBANCIN AƘIDA 🎐🎐
( ƙaddarar Soyayya )
Based on true life story
Haƙin Mallaka
Queen Nasmerh
&
Nana M Sha'aban
*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*
_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._
*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*
WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.
BAMBANCIN AƘIDA IS NOW FREE SABODA SOYAYYAR DA KU KE MA LITTAFIN KUN CI KYAUTAR BAMBANCIN AƘIDA.
Mu Haɗu a littafanmu - *SILAR YAUDARA NA HAƊU DA ALJANA* , da kuma *NAWA ƁANGAREN* nan ba da jimawa ba.
*CHAPTER 16*
"Brother ni ba zan iya zuwa gurinsu Mummy ba, saboda sun ƙullaceni sun tsaneni matuƙa" ta ƙarasa maganar tare da ƙanƙame wayarta da take maƙale a kunnanta, tana zubar da hawaye, Samuel ya ce "waya ce miki tsanarki sukayi? sam ba haka kawai dai suna fushi da ke ne, amman babu wanda ya tsaneki, hasalima yanzu Mummy kullum cikin maganarki take ba dare ba rana, ki ɗaure ki zo" Angela ta share hawayen fuskarta tace "to zanzo anjima yanzu Yaya baya nan da yanzun nan zanzo dan ina son ganinku" Samuel yace "to yayi kar fa ki ƙi zuwa ki zo yau ɗinnan" Angela tace "zanzo ko da zasu tsireni" Samuel yace "good! take care, by the grace of god everthing will be fine, please stop crying sis" Angela tace "ok bro! i love you more" Samuel yace "love you too" daga haka kowannansu ya kashe wayarsa, Angela ta kwanta akan gadon ɗakin tare da lumshe ido tana tunanin cewar ko mahaifiyarta zata sauko ta yafe mata ita da daddynta.
-------------°°°-------------
"Assalamu alaikum" wata kyakkyawar matashi tayi sallama ta shigo falo, Mamy wacce fitowarta kenan daga ɗakinta tayi turus tana murmushi "lale marhaban da zuwanki yarinyata, meyasa zaki zo amman baki faɗa min ba, nayi miki girki" Hazan tace "Mamy ai ba na so ki wahalar da kanki, kuma kafin na taho sai da na ci abinci" Mamy tace "ai kina buƙatar ki ci wani tunda dai ace mutum ya taho tun daga Abuja ace kuma ba za'ayi masa wani ɗan girki ba, gashi da alama kin sha gajiya" Hazan ta nemi guri ta zauna akan kujera tana cewa "da gajiya sosai kan Mamy, amman ba na jin yunwa gaskiya" Mamy tace "to Masha Allah ya hanya?","Alhamdulillah Mamy" Zama Mamy tayi tana cewa "ya me gidannaki?" Hazan tace "yana nan ƙalau, Mamy ya su Raheemarh?" Mamy tayi murmushi tace "Raheemarh sarki fushi jiya ta tafi daga gidannan, ko sallama batayi min ba, saboda fushin da takeyi, fisabilillahi ace kullum ta zo sai nayi da gaske kafin ta tafi" Hazan tace "wayyoo Allah ƴar uwata bari na kirata na nemi sulhu, ba na son ganin fushinta sam" wayarta ta ɗauko ta shiga kiran layin Raheema, ringing ɗaya biyu bata ɗaga ba ana ukun ne ta ɗaga da yake wayar a handsfree Hazan ta sakata tace "Assalamu alaikum rabin rai" Raheemarh tace "wa'alaikissalam ƴar uwa ya kike? ya gidan" Hazan tace "lafiya ƙalau ya yarana?" Raheemart tace "suna nan lafiya alhamdulillah sun tafi makaranta ma" Hazan tace "Ayyah! ki gaisar min dasu dukkansu ki shafa min kansu kafin na zo" Raheema tace "insha Allah" Hazan tace "yanzu na shigo gida Mamy take ce min jiya kika tafi kina ta fushi" Raheemarh tace "dan Allah Hazan ni ba na son wannan maganar ba dai akan gida suke yi min haka ba, to wallahi ba zan"......"ya isa! ya isa nace Raheema" Hazan ta katse Raheema cikin sauri dan tasan idan har tayi rantsuwa akan ba za ta ƙara zuwa gidan ba, to ta zauna domin Raheema tana da zuciya sosai ga ta kuma da kafiya, Hazan ta cigaba da cewa "yanzu saboda Mamy tayi miki magana shine kikayi zuciya har kina ƙoƙarin yin mugun furuci, ban ji daɗi ba wallahi sam" jikin Raheemah yayi sanyi tace "yanzu abinda ake min a gidannan ya dace" tayi magana tana kuka, "yi shuru daina kuka yanzu komai ya huce, ita ma Mamy zanyi mata magana" Raheema tace "yayi to" Hazan tace "yanzu to yaushe za ki zo gida ki ganni kin san na daɗe ban ganki ba!" Raheema tace "sai dai ki zo gidana gaskiya" Hazan tace "wato hakan yana nuna min cewar baki haƙura ba kenan","na haƙura mana, kawai ke ki zo" Hazan tace "tunda ni na matsu zanzo ai" Daga haka Hazan ta kashe wayar, Mamy dariya ta shiga yi "Raheema sarkin rigima" Hazan tayi murmushi "Mamy ai kuwa dai Raheema taji haushin abinda kika yi mata" Mamy tace "naga alama ai ta ɗau zafi da yawa" Hirarsu suka cigaba da yi duk rabinta akan Raheema ne da yadda take da tsananin fushi.
___________________
Bayan sunyi sati guda a gidansu Abokin Sani, Sani ya ɗauku Zeenat suka tafi wani ɗan ƙaramin masallaci domin a ɗaura musu aure, suna shiga suka tarar da wani dattijon malami yana jan carbi, dukkansu suka tsugunna har ƙasa suka gaisheshi, ya amsa cikin sakin fuska, Sani yayi masa bayanin dukkanin abinda ya faru dasu har gudowarsu daga gida, da kuma buƙatar da suke tafe da ita na ɗaurin aurensu, Malamin yace "Allah sarki, babu komai ai addini bai haramta maka aurenta ba, saboda ita musulma ce kawai banbancin aƙida ku ke dashi" Sani yace "hakane Malam Yahya" Malam Yahya ya tambayesu sunayensu Sani ya faɗa masa, ya tambayi Sani "shin ka na da sadakinka a jikinka yanzu haka" Sani yace "eh Malam akwai dubu ashirin" Malam Yahya yace "Masha Allah" miƙewa yayi ya kira wasu dattijai guda biyar dan su zama shaidu, suka dawo suka zauna, aka ɗaura auren Sani da Zeenart akan sadaki dubu ashirin, Sani yayi wa Malam Yahya godiya suka tashi suka koma gida, zuciyarsu cike da farin ciki.
___________________
"Mage!" Mateen ya faɗa yana kallon Mehreen wacce take kusa da Sulaiman suna hira sama-sama, ɗagowa Mehreen tayi tana kallon Mateen ta kwaɓe fuska cikin shagwaɓa ta kalli Sulaiman tana cewa "Yaya Sulaiman ka ji wai ni ce Mage" Sulaiman yace "meyasa kike damun kanki haka, ba gashi nan na baki sunan da zaki dinga faɗa masa ba, duk sunan da ya faɗa miki ke kuma ki ce masa Mujiya" Dariya Mateen yayi yace "ai kasani dai kwarai wallahi idan tace min Mujiya ita ce zata kwana a ciki, dan zan faɗa mata sunan da zai mata ciwo a rai" Sulaiman yace "Mateen wallahi zan maka elbo a wuya" dariya Mateen ya shiga yi har da riƙe ciki, "La! la! la! la! la!, ɗa! ɗa! ɗan! ɗan! ɗa! ɗan! ɗan!" Mehreen ta shiga faɗa tana kallon Mateen, "zakiyi waƙa dakyau, Sulaiman ka ga alama ko, wannan yarinyar da Dila take kama!" Mehreen ta harareshi tace "kanka ake ji wai mahaukaci ya faɗa rigiya, kuma Yaya yace duk me yawan dariya to mahaukaci ne tabbas, kuma na yarda, Yaya ka haukace, Yaya Sulaiman a kai shi asibiti kar ya fara kai duka kuma" Sulaiman yace "gaskiya kam, princess kin faɗi abinda yake raina" Mateen yace "dan Allah idan kun kai ni asibitin ku kai ni ɗakin ƙarshe munji" Mehreen yace "ai ko ba ka faɗa ba, chan zamu ce a saka ka, saboda abinnaka yayi tsamari da yawa. haka dai Mehreen da Sulaiman sukai ta tsokanar Mateen, da yake mai baki ne, duk abinda suka faɗa masa sai ya mai dar musu da martani.
____________________
Juyi kawai yake yi akan madaidaiciyar katifarsa, kansa yake ji yana sara mai kamar zai rabe daga kansa "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un yake ta maimaitawa" Zuciyarsa ce ta raya masa akan ya kira Ruƙayya ƙawar Zainab dan ta taimaka masa ta haɗasa da Zainab suyi magana, anan take ya lalubo wayarsa ya shiga duba number Ruƙayya, yana gani ya shiga kiranta sai da ya kira yafi sau uku sannan a na biyar ɗin da ya kira ta ɗauka tare da bashi haƙuri na rashin ɗaukar kiransa, ta bashi uzurin tana toilet ne, yace babu damuwa, "Ruƙayya daman ina so ki je gidansu Zainab ne, ki haɗani da ita muyi magana" Ruƙayya da yake Mukhtar yayi mata bayanin abinda yake faruwa tsakanin Aimar da Zainab ɗin tace "to ba damuwa insha Allah zanje zuwa anjima yanzu ina aiki ne" Aimar yace "badamuwa" yayi magana tare da kashe kiran, ta dora wayar akan cikinsa yana cije bakinsa.
___________________
Angela kuwa Abbakar yana dawowa ta tambayeshi akan tana so taje gidansu, bai hanata ba ya barta da yake tayi shirinta daman shi take jira shiyasa bata tafi ba, ta saka kai ta fita, tana tafiya tana tunanin me zata ce idan ta shiga gidan, Samuel ta kira ta faɗa masa ta taho, ta kusan ƙarasowa ma, yace mata yana gida sai ta ƙaraso ɗin, jin Samuel yana gida yasa ta ji wani ƙarfi yazo mata dan tasan ba zai taɓa bari ayi mata wulaƙanci a gabanshi ba.
*Share, like and comments*
*NASMARH & DIJARTY*
_(Aminan juna)_