AUREN KADDARA KO BIYAYYA?

16

by @bilynabdul

Dady yana isowa gidansa yanufa kai tsaye, sai dai yana farga bar abinda zai tarar duk da ba son matan nasa yake yiba, amma yasan ba abinda mata suka tsana irin kishiya,tunda gasunan su biyu ma ya aka k'akare bare an k'aro ta uku,


Haka dai ya sauka daga motar da ya d'akko haya daga air port, yabiya kud'in sannan yanufi gidan, sun gaisa da mai gadi, sannan ya wuce cikin gida.


Cikin sanyin jiki ya tura kofar palon ya shiga da sallama, ikileema ce kad'ai apalon take karatun littafi,amamakin sa sai yaga tazo ta tarbe shi, harda dariya tana masa sannu dazuwa ya amsa fuskarsa ba yabo ba fallasa, yasan dai labarin auren sa yazo musu, ya kalli palon kaca kaca, da alama tunda yabar garin ba agyara palon ba.


Ya d'akko key ya bud'e d'akinsa, suka shiga, kamar daga sama husna tafad'o ko sallama babu, ta fisge jakkarsa dake hannun ikileema, malama ince dai yau kinsan nice dashi, amma dan tsabar muna finci kikaje kika tarosa.

Ikileema tace waike husna wacce irin dabbace ne, aiba gado d'aya kika gammuba, bare kice anacin amanar ki,

Husna ta harzik'o kin san ALLAH kika k'ara cemini dabba sai naci uwarki anan gidan banza jaka.


Dady ya daka musu tsawa kun ga, dan ALLAH ku barni nahuta daga fa anguwa nake amma ba wadda tabani ruwa bare abinci, amma kun tarbeni da masifarku dakuka iya, kwana biyunnan dabana gidannan har na fara k'iba, amma daga dawowa ta nafara karo da jarabar ku,

 Husna tai fari da idanu kayi hakuri honey ai gara nako yama wannan shegiyar hankali.


Ikileema tayi dariya yo husna ko uwarki ta isa ta koya mini hankali bare ke,

Dady yace ALLAH in baku yimini shiruba zan b'ata muku rai, ya shige bayi abinsa, ikileema kuma tafice tabar husna.


 ikileema har ta fita tadawo ta zauna,

Dady ya fito wanka ya kalli matan nasa dasuke ta harare harare,

Shikam wataran dariya suke bashi, tamkar ba 'yan uwaba,kuma k'awaye masu matuk'ar so da k'aunar junansu, yay murmushi, sannan ya fara shafa mai, ya gara sumarsa, jalla biya yasaka yace musu zaije masallaci, yafice abinsa batare daya jira amsarsu ba.

Yana fita suka hau danbe kamar dama jira sukeyi ya fita.


Daga masallaci gidan su ya wuce, gidan cike yake da dangi anata hidima, ya shiga sunata gai suwa da mutane, kai tsaye d'akin mom ya nufa dan bai ganta apalon ba,ba kowa ad'akin sai Munneerah dake bakin gado zaune,daga ita sai zani d'aurin k'irji, da alama wanka tafito, tana k'ok'arin bud'e akwati dan canja kaya amma sai fama take da key d'in yak'i ya bud'e,

Shikam ya tsaya yana kallonta, jitai ajikinta ana kallon ta, dan haka ta d'ago da sauri, ta kalli inda take zaton mai kallonta yake, da sauri ta rarimo gyale ta lullub'a dashi dan ganin dady yana mata kallon kurillah.


Baice komai ba itama ta maida kanta taci gaba da k'ok'arin bud'e akwatinta, a han kalli ya k'arasa wajanta, ya d'ora hannunsa akan nata batare da yayi maganaba, yazare key d'in daga hannunta ya dur kusa gaban akwatin yana bud'ewa, tad'an saci kallonsa kad'an ta kauda kai, mutum kullum fuska ad'aure kamar wani soja.


Mom ta shigo d'akin tana fad'in a'a babana kaine?

" yajuyo da sauri yana kallonta ya d'an sosa kai nine mom"

"Ina kika shigane"

 "Tace ina kichin ana k'ok'arin had'ama bak'i abinci"

 Ya mik'e daga gaban akwatin daya gama bud'ewa yana fad'in to sannunku da k'ok'ari.

"Mom ta zauna tana fad'in yawwa babana.

Shima ya zauna kusada Munneerah abakin gado,

   "Mom ta kalli Munneerah, Munneerah har kinyi wankan??

"Tace eh mom nayi"

    "Yawwa kinga yanzun zakiji k'arfin jikinki"

Mom.tace ai garama dakazo dama bata da lafiya kaga saika dubata, ya d'an kalli Munneerah miya ke damun ta?

 "mom tace zazzab'ine''

 "Tasamu paracetamol tasha, kawai zai sauka gajiyar tafiyace,

To shike nan bari taci abinci.


Babana karfe nawa kabaro yola?

Wlh mom sai k'arfe biyar nataho ina zuwa nasamu jirgi✈, gashi harna je gida nayi wanka,


Ya kalli Munneerah dake sallah to mom yanzu yaza ayi??

Itama mom ta kalleta to sai dai mujira muji abinda dad d'inku zaice ko,,

To shikenan zuwa gobe zan samu dad muyi magana dan nasan yau yagaji danni ko ganinama bazaiyiba, nima d'in zuwa zanyi na kwanta duk nagaji, yinwace ma ta kawoni gidan,

Mom tace to bari na kawoma abincin.

Bayan fitar mom dady ya kalli Munneerah data idar da sallah tun d'azu, amma takasa tashi,

Waike bazaki cire wannan hijja binba, ko zafi bakyaji, tace ai bangamaba, ya tab'e baki, mom tace ya akayine, yace mom naga tun d'azu ta idar da sallane, amma tak'i tashi ta cire hijjab d'in,

Mom tai dariya to ai kasan Munneerah da kunya.

Yace to mom kunyar wa zataji anan ai mu ba bak'inta bane, ya d'auki abincinsa ya hau ci.


 wai ina su kairat ?

Mom tace suna d'akinsu tare da k'awayen amarya, 

  "Yace okey"

Kad'an yaci abinci ya ajiye,

   "Mom ta kallesa ba dai ka k'oshiba babana??

  "Na k'oshi mom yafad'a yana mik'ewa, bari naje nayi sallar isha'i, nawuce gida barci nakeji,

   "Mom tace to saida safe"

"Itama Munneerah tace saida safe yaya, ya juyo ya kalleta batare daya amsaba ya fice,

Yay wa bak'in dake falo saida safe ya tafi.


Saida yay sallah sannan ya nufi gida, husnace kawai afalon yasan jiransa takeyi, azuciyarsa yace yarinya duk jarabar ki kya barni, dan yanda na gajinnan ba abinda zan iya tsinana miki.


Amma afili saiya ce lafiya kika zauna ke kad'ai afalo??

 "Tace k'alau kai nake jira"

"Yace to muje, d'akinsa suka shiga, ya kalli d'akin sannan ya kalleta, wai yanzu haka kika bar d'akin nan baki gyara ba??

 Tace to ai naga baiyi dattiba.


Ya kalleta cikin haushi akwana biyu ba a kwana ad'akinba, sannan kice babu datti, kinga ki gyara kokuma ki tafi d'akinki ki kwanta nina gyara nan.......✍