AUREN KADDARA KO BIYAYYA?

17

by @bilynabdul

ganin yanda yake magana cikin jin haushi tasan gatse yay mata, dan haka tace to bari nagyara,ta fara kakka b'e gadon, dady dake kan kujerar madubi zaune, yace ai wannan zanin gadon saidai ki cire shi, dan bazan iya barci akansaba,sai jikina yazo yana kaikayi,

Azuciyarta tace magulmaci ai k'ilama nan gaba uwarkama saikace mata k'azama, dole ta canja zanin gadon suka kwanta,shikam harga ALLAH ya gaji barci yakeji, amma yasan fitinar husna,jiyyayi ana shafashi doleya daure yabata hakkinta sannan sukayi barci.


Da safe bayan sunyi sallah suka koma barci , cikin barci sukaji ana buga k'ofa kamar zata cire, dady ya daure ya tashi husna ma ta mik'e, sanda suka fito ikileema ma ta fito har tana k'ok'arin bud'e k'ofar, 

Jabir ne da umma kakarsu da alama ma jabir abuge yake, ikileema tad'anja baya danganin jabir yana k'ok'arin fad'owa kanta.

Cikin muryar maye yace ina Abdul'aziz d'in dan uwarsa bilkisu, yau saika gaya mana ubanda ya d'aura maka aure batare da saninmuba,

Dady yana tsaye jingine da bango hannuwan sa hard'e ak'irjinsa, yace jabir ganinan ince ko kazo ka dake nine??

Umma tace to mara kunya koka manta jabiru yayankane, dady yace ban mantaba umma, amma kinaji ya kira sunan mom d'ina yazaga,saboda tarbiyya tamasa k'aranci, dady ya nuna jabir kasn ALLAH ka k'ara zagin iyayena saina yimaka rashin mutunci.


Umma tace kai Abdul'aziz rashin mutincinka har yakai haka, tsaki dady yaja yay shigewarsa d'aki harda saka key.

Ikileema da husna sunyi mutuwar tsaye danjin furicin yayansu jabir, cikin k'arfin hali ikileema tace umma bafa mugane abinda kuke nufiba, waye yayi aure??

 Jabir yay taga taga zai fad'i ALLAH yabashi sa'a yadafe kujera, yace wannan d'an iskan mijin naku mana, shine yaje yole shida wad'ancan muna fikan iyayen nasa suka d'aura masa aure, yanzu haka amaryar tana gidansu,

  K'ara suka kwallah atare suna fad'in dady ka cucemu, ikileema tanufi kofarsa tana bugawa da k'arfi tana masifa.


Shikam yana jinsu yay musu banza k'arshe ma dayaji sun damesa da hayaniya sai ya kunna karatu awaya yasaka iya fis ya k'ure k'arar


Bayan kamar minti talatin yaji gidan shiru saiya cire ya kashe yay murmushi sannan ya mik'e ya bud'e kofarsa ya lek'a falon, dariya yayi mai sauti yara darobon tafiyarku ta kasance kun tafi kenan, dan dama hanyar rabuwa daku nake nema wallahi, ya koma cikin d'akinsa yana k'yalk'yala uwar dariya, kamar wanda akaima bishara da gidan aljannah....


 dady ya shirya ya nufi gidansu dan yau za'a kawo amarya, bayan ya gaida mutane ya haye saman dad mom ma tana can, ya dur kusa ya gaishesu, cikin fara'a suka amsa, cikin dariya dad yace zonan babana, dady yaje kusa dashi ya zauna, dad yashafa kansa babana kana fushi damu ko ??

  "Dady yad'ago cikin murmushi yana kallon dad, ya girgiza kai dad danmi zanyi fushi daku mikuka yimini, ya cigaba wallahi dad bana fushi daku,ko kad'an kawai na d'auka wannan yana cikin K'ADDARA ta ne, dan haka dan ALLAH ku daina damun kanku, ni yanzuma nazone akan maganar inda za'akai Munneerah ne??

  " dad yay dariya to shikenan babana ALLAH yayi maka albarka ya baka 'ya'yan daxasu yimaka BIYAYYA kamar yanda kayi mana""

  "Amin mom ta amsa"

Dad ya d'akko mukullaye da yawa ya mik'awa dady, cikin rashin fahimta dady yake kallon dad, dad yace karb'a babana wannan makullayen gidankane, dake HOTORO, a SAKKOTO ROUND,

angama zuba ko mai sai kaje kasanar da matanka su shirya yau sukoma, zuwa anjima kuma akawo maka sabuwar amarya.


Dady ya mik'e ya rungume dad yana godiya, ya koma ya rungume mom itama su duka dariya sukeyi dan yau sunga farin cikin d'ansu tilo namiji dasuka dad'e basu ganiba.


Dad yace kar kadamu babana zan iya yimaka komai arayuwa matsawar inda shi dan nima kan mini BIYAYYA, dady yace to dad saidai fa su ikileema basanan, d'azu umma tazo itada jabir sun tafi dasu kuma wallahi dad bazanje nadawo dakowaba tunda bani nace su tafiba


Mom da dad suka dubi juna har suna had'a baki wajan fad'in umma kuma??

"Dady yace eh"

Dad yace karka damu anjima zanje gidan umman da kaina, yanzu kaje kagano tsarin gidan idan yayi maka.

 "Dady ya mik'e yana godiya yatafi.

 Dad yace kinga abinda nake gaya miki ko bilkisu nasan akwai wani kulli azuciyar su yaya amma anjima zanje gidan, mom batace komai ba sai ALLAH ya kyauta kawai ta mike ta fito..


 daga nan gidan dady sabon gidan da dad yabashi ya nufa, lallai gidan ya had'u🏘, idan natsaya baku labarin gidan sai mu b'ata lokaci, amma gidan b'angare hud'une kowa danasa baruwan wata da wata, yagama zagaye gidan ya koma gida.


Gado ya haye yay barcinsa tunda yau babu karnika agidan.


Su ikileema kuwa suna zuwa kowa gidansu ta wuce, suka zayyane ma iyayensu abinda ya faru k'arya da gaskiya, suka d'aure musu gindi wai su zauna har sai dady yazo.


Da daddare dad ya shirya ya nufi gidan umma, acan yasamu yayyenasa, abban ikileema da abban husna, ya gaishesu kowa ya amsa fuska acinkushe, baibi takansuba yafara basu hak'uri akan yaran da abinda ya faru, yace kuma suyi hakuri abashi yaran ya maidasu yanzu.


Umma ta watsa masa harara to ubanmu Mansur ba dole abaka yara katafi dasuba tunda yaran wasane su, agabana yaron yaci mutincinsu ya had'a dani sannan kawai dan karainamu, kai mai d'a da kud'i kazo kace abaka yaran ka maida masa, in kaga sun koma sai yazo dakansa gidannan ya basu hakuri, yakuma saki wacan farar koman dannasan farintane yake d'ibarsa ba wata tsiyaba.


Dad yace umma kiyi hakuri saboda yarannan duk d'ayane awajanmu bashi da damar sakin wata yabar wata, dan hakan zai iya b'ata mana zuminci gabad'aya, dan haka kuyi hak'uri kawai sukoma.


Abban husna yace kai Mansur kaje kawai inhar kun yarda da sharad'in umma to yasaki wadda kuka auro masa agobe adawo masa da 'yan uwansa d'akinsu.


Dad ya mike.yana fad'in kudaiyi tunanin mai yuwu wa, duk shawarar dakuka yanke muna jira ya fice abinsa batare dayabi takan kiran da abban ikileema yake masaba........✍️