DEEN MARSHAL

2

by @mamuhgee

*_DEEN MARSHALL_*

_Mamuhgee_



2

Da wani irin kallo Hanifa kebin Naj dake tsaye bakin wardrobe daure da towel me kauri da girma brown color fuskarta fayau Kamar ko yaushe Babu wata damuwar abubuwan dake addabe da rayuwarta Kamar fitinar ummanta data su dattaji uwa uba ta Abaas datafi ta kowa zama abin baqin ciki da takaici.


Sake kallon fuskarta Hanifa tayi tana zaunawa kan gadon tareda ajiye wayarta gaban madubi tana cewa"


Nayi waya da Sarah dazu.


Batareda ta juyoba tana zare Yan kunnayenta tace"


Kada ki damu da abinda tafada Miki 

Idan Akan Abaas ne zuwa yanzu kema kinsaba da halinsa,

Abinsa ya daina damuna yanzu saidai kawai yanda Naga kamar abin nasa kullum rikidewa yake zuwa ga zargi

Zarginma me muni Wanda nake dannewa Ina sharewa sbd Umma dasu Dattijo...


Sai alokacin Hanifa ta katseta da cewa"


Meyesa Zaki daure sbd su umma bayan su dinma da zasu bude ido da kyau su duba dabi'u da wasu abubuwan tako Ina Abaas Bai cancanta ba bama Haka ba yaushe Kika fara damuwa da abinda ake fada na cewan kece Kika qi aure da har Kika zabi auren Abaas lamido Wanda Ni kwata kwata baima kwantaminba 

Gabaki daya Banga halayen maza masu hakuriba ko iya tattala mace atareda Abaas.


Ajiyar zuciya Naj din ta sauke Jin ran Hanifan yafara baci da zancen ta waiwayo ahankali ta kalleta tareda sakin wani irin lafiyyan murmushi Wanda kusan Arayuwarta tunda tazama budurwa cikakkiya kaf kannenta sukai aure aka sakota gaba tako Ina Hanifan ce kawai take iya ganin murmushinta me fidda asalin kyawunta Wanda yafito daga ainihin cikin zuciyarta sai kuwa Dr sa'id Wanda yake tamkar 'dan uwa Kuma aboki agareta shima idan tana tare dashi takanji nutsuwa da kwanciyar hankali sbd ya fahimceta tareda sanin halayyarta fiyeda 'yan uwanta na jini duk da kuwa Bata hada komai dashi ba face kasancewarsa likitan Hanifa tun suna yara har yanzu dasuka girma.


Zama tayi gefen Hanifan tana kallonta tace"


Ba abun damuwa bane basai kin saka damuwan Abaas ba aranki 

Mubar maganan ma sunan Harya fara sakamun ciwon Kai.


Hanifa Sam ko sunan Abaas din tafi kowa takaicin saurara sbd tun ranar farko da zancen Yana son Naj din ya sauka a kunnenta ta qarewa background dinsa da halayyarsa bincike bataga ta inda ya cancanta Naj ba kafin daga baya taji fara aikinsa da zuba hannun jarinsa a ALFA'S dinsu Wanda Sam bataso hakan ba Amma sbd zagayen da yayi akai Masa Hanya ya bullo ta gurin JALALUDDEEN qaninta Wanda dukiyarsa tafi ta kowa yawa acikin ALFA'S din hadda kuwa mahaifinsu da shine me asalin companies din na Nan portharcourt dama na wajenta.


Miqewa Naj din tayi tana cewa"


Bari nayi wanka nafito zamuyi mgna akan Isma'eel ya kirani dazu akan maganar zuwanki ganin likita A Jamaica.


Kallon kyakkyawar fuskarta Hanifa tayi tana murmushi tace"


Allah sarki Zawj.


Da yanayi na sanyi Naj ta kalleta zuciyarta na yin sanyi da dukkanin wata damuwar Hanifa ko ciwonta.


Toilet din dakin nata ta shige Dan dama wanka zatayi Hanifan ta shigo.

Bayan shigarta wanka miqewa Hanifan tayi ta sauko daga kan gadon ta zura flat slippers dinta na _Jimmy choo_ ta fita dakin ta nufi gurin umma dake zaune har lokacin tana aikin zuba wasu turaren wuta masu tsananin qamshi ta zauna gefen umman tun kafin ta qarasa zama umman tace"


Kun gamo shawaran yanda zaku fuskanci Dattijo da Dadah idan Maganar aurenta da Abbas ta fasu Dan nasan wannan doguwar fuskar da Kika shigo da ita bata lafiya bace Dole akwai abinda yake faruwa tsakaninta da Abbas.


Dan guntun murmushi Hanifa ta sauke tana Taya umman rufe kwalaben turarukan tace"


Umma meyesa kuka kasa gane irin taurin zuciya da qarfin imanin da Naj take dashi sbd ba kowane zai iya hadiyewa ba yakuma danne irin Gori da takura tareda cin fuskan da ake Mata akan rashin yin aure ba?


Umma kowa Yana yiwa Naj kallon taqi aure sbd zurfin ilimi da karatun bokon datayiba a cikin gidan Nan hakama Ana Mata kallon wadda ta Raina maza sbd ganin Kamar matsayinsu da nata daya ne Wanda umma keda Kika haifi Naj kinsan ba Haka takeba kawai dai ita Allah Haka yayita miskila me halin ko oho ga abinda ake fada akanta bayan Haka shi fa aure nufi ne na Allah Kuma ba lallai ne ita lokacin nata auren yayi ba idan lokacin yayi zatayi.


Hmmn Hanifa nagaji da bin bayan Najma akan maganar fasa aurarrakin Nan nata da akeyi kusan Kashi biyar tun Ina yadda da qaddarane a gaskia yanzu na yadda da hadda halinta na miskilanci Wanda kesa mazan ganin Kamar tafi karfinsu ne kokuma tana tuna tafi karfin nasu,

Kunfi kowa sanin yanda Dadah da Dattijo suka sakoni gaba a cikin gidan Nan akan Najma

Kullum fa qara shekaru akeyi ba ragewa ba yanzu ke da Allah yakawo rabo na haihuwa aurenki da yanzu ba kinada yara biyu ko ukuba koma hudu idan anyi haihuwar ritsa Amma Sam Naj ko 'yar damuwar Nan Bata nunawa kullum itace a nutse a kammale saikace wata lissafi ahaka takeson qarewane saidai aiki kawai..

To ku zauna ku dasa sabuwar shawara wannan karon wlh Dattijo rantsuwa ce a bakinsu shida Dadah matuqar aurenta da Abbas ya fasu to wlh bazata rufa sati ba agidan zasu aura Mata duk Wanda ya samu ciki kuwa hadda sojojin dake gadin gidanku yace zai kaiwa tayi idan hakan ta faru Ni kaina danake mahaifiyarta wlh zuciyata zata iya bugawa bare ita Dan Haka ki zaunar da ita kuyi shawara koma menene matsalar su zauna suyi sulhun abarsu itada Abbas din asamu ayi auren Nan ta tafiyarta ta huta Nima na huta da zancen kullum din.


Batasan wane bayani zata yiwa umman ta fahimta ba sbd matsuwar su dattijon tariga tasaka umman itama gajiya tana kasa fahimtar 'yar tata,

Tana tsananin qaunar Naj tamkar 'yar uwarta ta jini dasuka fito ciki daya Dan kuwa tsananin qaunar datake Mata har kasa tantance cikin su biyun tsakanin ita da marshal batasan waye tafiso ba duk da shi din jinintane dasuka fito ciki daya,

Bazata iya Bari Naj ta cutu takowane irin Hanya ba Dan Haka ita da kanta zata nema Ganin Abbas lamido suyi magana idan har yanason Naj da dukkanin zuciyarsa da gaskia to yakamata ya sauya su fuskanci rayuwar aure zasuyi su fahimci juna tun yanzu.

Idan har zai qaunaci Naj da gaskia zaifi Mata ace Dattijo yabada auren Naj wa duk Wanda yasamu.


Wanka ta fito taga Hanifan Bata dakin tasan tana gurin umma ko anty Amina Dan Haka Kai tsaye ta nufi gaban mirror ta zauna ta kalli fuskarta zuwa kirjinta da kafadunta dake bayyane suna wani qyallin haske da samun lafiyar fata ta maida kallonta kan fuskarta datafi komai kyau da daukan ido atare da ita ta lumshe fararen idanuwanta ahankali tareda sauke numfashi kadan kafin ta janyo lotion na jagggins tana shafawa kadan kadan Dan batason Mai da yawa Ta miqe bayan ta shafa turaren POSSES ajikinta tareda mist na Rednight ta zare band din kanta ta gyara daurin gashinta tayisa sako sako sbd Taji dadin kan nata ta nufi wardrobe ta Ciro doguwar riga Mara nauyi zata saka wayar Hanifa data bari kan mirror din nata takawo haske tana vibrating ahankali ba qara sbd Wanda Dabi'arsune rashin sakawa waya qarar ringing Dan kusan itace ta koyawa Hanifan hakan qarar waya na damunta shiyasa Sam wayarta Bata qara idan Ankira saidai vibrating shiyasa itama Hanifan ta koya sbd Naj din.


Ahankali ta waiwayo ta kalla wayar taga sunan dayake Kai _MARSHAL_

 dauke Kai tayi tana cigaba da saka kayanta Dan tunda takeda Hanifa Bata taba daga wayar 'dan uwanta ba idan yakira Wanda shi kadaine kawai Bata daukan wayarta idan shine yakira idan har Bata kusa tun kuwa tasowarsu suna qananu haryanxu.


Sanin baya Kira biyu 'daya yakeyi yasa ta sake waiwayo wayar tana kallon sunan destination dinda caller ID ta rubuto _HAWAII US STATE_ 

Hanifa Babu wani Abu a duniya dayafi Mata qanin nata Wanda su biyu kacal mahaifiyarsu ta Haifa ta bar duniya Wanda tazarar shekara uku ce a tsakaninsu yanayin aikinsa da girman matsayinsa yasa baya tareda ita wayama sai yasamu lokaci suke iya Yi Dan Haka Babu abinda Hanifan Bata Wasa dashi irin waya da marshal din Dan Haka bazata so ta rasa kiranba takai hannu a natse ta dauka tareda nufar kofa ta bude ta fito ta kalli zainab dake kusa tace"


Miqawa Hanifa wayarta Ana Kiranta.


Karba zainab tayi ta nufi Hanifan da sauri ta miqa Mata cikin sa'a kuwa har lokacin Kiran Bai katseba tana ganin me Kiran ta dauka tana Kiran sunansa cikin tsananin kaunarsa da kowa ya shaida kaunace me girman gaske a tsananinsu.

#MAMUH#





*_ZAFAFA BIYAR 2022๐Ÿ”ฅ_*


*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*

*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada'dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*

_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

Dโ€™aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


***


*Kokuma katin waya na MTN anan*๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


***