KAZAMIN TABO

06

by @rahmakabir13

ƘAZAMIN TABO


06


Rahma kabir Mrs MG.

Wattpad@rahmakabir.


_Masoya ina godiya da addu'arku gareni Allah ya kara zumunci ya saka da alkhairi_



Momy ta shiga jijjgashi amma ina Babu numfashi, a gigice Abba ya karaso wajen ya sunkuce shi a kafada Yana cewa Momy ta dauko masa key motarsa a daki, sai ya fice da shi a guje, da sauri momy ta dauko key din tabi bayansa ya bude ya kwantar da shi a back seat ya zauna mazaunin driver Momy ta bude gefensa ta zauna ko gyale babu a jikinsa ta manta saboda rudewa, me gadi ya bude musu gate ganin yadda suke a rikice ya san ba lafiya, Abba ya ja motar da matsiyacin gudu suka wuce. Nabeel da su Bushra kuka kawai suke yi sunyi cirko cirko a tsakar gidan, Leema ce ta ruga sashin kakus ta sanar da ita cewar Anas ya mutu su Abba sun tafi da shi asibiti, a gigice ta fito tana rafka salati nan suka iske su Nabeel ta shiga tambayarsu abinda ya faru dan bata gane bayanin Leema ba, Nabeel ya bata labarin abinda ya faru a takaice, sai dai ya sanar da ita bai san musabbabin dukan da Abba yayi masa ba, salati kawai take jerowa hankalinta a tashe, haka ta tasa karyarsu zuwa cikin falo suka shiga suka zauna jugum ko wanne da abinda ya dameshi, duk yunwar da suke ji ya gushe sai tsananin tashin hankali.


Su Abba wani asibitin private suka nufa da shi dake kusa dasu, suna shiga yayi parking ya dauki Anas suka shiga ciki, da sauri nurses suka tarbesu tare da yi musu jagora zuwa wani daki, suna shiga ya kwantar da shi saman gado, sai ga likita ya shigo da sauri saboda ya samu sakon zuwansu, yace su Abba su bashi guri, ya shiga duba shi, sun dauki minti sha biyar kafin likitan ya fito yana goge gumi, Abba ya tare shi da cewa.


Likita ya mutu ko?


Bugun zuciyarsa yana harbawa yana bukatar taimakon gaggawa, dan haka gaskiya sai dai ku kai shi babban asibiti, Zan baku referral letter zuwa asibitin 44 akwai wani abokina Likita ne a wajen zai taimaka muku.


Yana gama fadar haka ya wuce office dinsa ya rubuta musu transfer, Abba kuwa dafe kansa yayi jikin bango duk yadda ya yi ya daure ya kasa Sai da kwalla ta zubo masa a kunci, da sauri ya share su saboda Kar ya kara tada hankalin Momy, ita kuwa tsugunawa tayi cike da tashin hankali tana zuba kuka mara sauti, dana sani ne ya cika musu zuciya cike da alhini, likita ya fito da sauri ya mikawa Abba takardar yana cewa.


Na kira shi yanzu, yace da kunje ku tambayi Dr. Abdul Kankia za a sadaku da shi.


Da rawar jiki Abba ya amsa yana yi masa godiya, ba bata lokaci aka fito musu da shi har mota suka sashi a back seat suka wuce asibitin 44.


Da isarsu suka tambayi Dr. Abdul nan take wani soja ya kaisu har inda yake, har ya riga ya shiryawa tarbansu su kawai suke jira, yasa ma'aikatansu suka shiga da Anas wani daki su Abba suka tsaya a kofar suna jiran tsammani, likitoci biyu ne akansa sai nurses hudu masu taya su aiki, sun kwashi kimanin awa guda suna duba shi daga, bisani suka kammala aikinsu tare da sanya masa oxygen wanda zai taimaka masa wajen numfashi, ga drip makale a hannunsa, nurses suka gyara shi duk suka goge jinin jikinsa sai suka fito, Dr. Abdul yacewa su Abba suje office dinsa, haka suka bishi a baya har ciki suka zauna, Dr. Abdul ya gama rubuce rubuce kana ya dago yana dubansu da cewa.


Da mota ya yi accident ko mashin?


Abba da Momy suka kalli juna kana Abba ya ce a takaice.


Fadowa ya yi daga matakalar bene.


Lallai yayi mummunar faduwa, sai dai alamu sun nuna akwai sashin bulala da yawa a jikinsa wanda hakan ya sanya min zargin dukansa aka yi.


Eh laifi yayi na bige shi.


Shine ka turo shi ya fado dan ka kashe shi.


A'a likita, ta ya zan nima kashe d'ana? kawai wannan fadowar nasa tsautsayi ne.


Allah ya kyauta. Gaskiya yanzu ba zan iya fayyace muku abinda ya same shi ba har sai ya farka munga yanayinsa, domin yayi mummunar buguwa a kai Wanda ya haifar masa da samun internal injury, shiyasa ma ya fitar da jini ta hanci ta baki.


Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun. Likita ka taimaka mana ya tashi cikin koshin lafiya.


Wannan sai abinda hali ya yi, mun sanya masa oxygen Insha Allah nan da Safiya kila ya dawo hayyacinsa. Zaku iya tafiya kuma dan Allah banda hayaniya.


Abba ya mike jiki a sanyaye, Momy itama mikewa ta yi tana zubda kwalla, sai take ganin duk itace ta janyo matsalar da tayi hakuri da duk haka bata faru ba, Karin damuwarta ita ce ta kara ingiza Abba akan ya hukuntashi, da ta san wannan bakin hukuncin zai masa da ta yi hakuri ta bar maganar a zuciyarta. Haka suka shiga dakin, ganinsa da oxygen ba karamin Kara tayar musu da hankali yayi ba, haka suka zauna jugum jugum ko wanne cikin tashin hankali, duk Babu wanda ya dauko waya balle su sanar da kakus halin da suke ciki.


Kukus kuwa tana zaune a falon har kusan d'aya na dare ta kasa runtsawa, su Nabeel kuwa tuni suka yi barcin damuwa a kan carpet din falon, Kakus ganin zaman ya isheta sai kawai ta mike ta shiga bayin dake falon ta dauro alwala ta zo ta tayar da sallan nafila, sai da ta jero raka'a shida kafin ta zauna ta shiga jero addu'a, sai da ta dauki kusan awa biyu a zaune a haka barci ya dauketa zaune a dadduma tayi filo da gefen kujera. Kiran sallar asubahi ya tashe ta, ta mike taje ta kara dauro alwala ta gabatar da sallah, bayan ta idar ta tashi su Nabeel suka je suka yi alwala suka zo suka yi sallah. A 3seater ta kwanta ba bata lokaci barci ya kara daukarta suma barcin suka yi a nan inda suka idar da sallan.


Su Abba kuwa sunyi kwanan damuwa domin kuwa babu wanda ya runtsa, da aka kira sallar asubahi Abba yaje ya yi a masallacin asibitin, ita kuwa Momy babu mayafi balle tace zata yi, koda Abba ya dawo yace mata ga key motarsa taje gida ta kintsa in yaso sai driver ya dauko kakus tazo ta zauna da Anas, daganan driver ya dauko shi ya samu yayi wanka in sun huta sai su dawo tare, ba musu ta amsa key din ta fito zuwa wajen motarsu ta shiga ta nufi gida, Abba kuma ya cigaba da kula da Anas din.


________


KANO


Mami tana isa gidansu sai ta wuce sashin Yaya Aminu ta samu baya nan yana bangaren su Baba, sai matarsa ce ta tare ta da tambayar lafiya ta zo cikin dare? Ba amsa sai ta saki kuka me cin rai ta zauna dirshen a tiles din dakin, Matar Yaya Aminu ta zauna a kujera cike da damuwa ko bata fada mata matsalarta ba ta san baya wuce zancen auren Auwalu da zai kara, tace cikin rarrashi.


Khadija hakuri za kiyi komai ya samu bawa ya dauke shi a matsayin kaddara, auren da zai kara ba yana nufin ya wulakanta ki bane, mijinki Yana sonki kuma babu irin gatan da baya baki, ki danne zuciyarki ki barwa Allah komai.


Wlh ba zan iya hakuri ba, Yaya Auwal ya cuceni, dana zauna da kishiya gwara ya sakeni, wannan ba kaddara bace da gangan yayi, domin ya gama cin moriyar gangan zai yada korenta.


Ashsha ki daina fadar haka, Karki manta Auwalu dan uwanki ne ba zai taba yin abinda zai cutar dake ba, domin kuwa in ya yi haka bai yi halacci ba, ki yi kokarin danne zuciyarki kiyi yaki da shaidan Kar ya samu galaba a kanki.


Aiko ya gama cutar dani tunda ya karya alkawarin dake tsakaninmu ya hadani da kishiya.


Ganin ba saurarenta zata yi ba yasa ta mike ta shiga kitchen ta dibo Mata ruwan sanyi a kofi ta kawo Mata, ba musu ta amsa ta sha ruwan Wanda ya jika makoshinta daya bushe dan bacin rai, maganar Yaya Aminu ne suka ki yana kokarin shigowa gidan, Khadija ta mike da sauri ta shiga dakin yaransu, Matar yayan ta rufa Mata baya tana cewa.


Da kin tsaya ya ganki wata kila Zaki fi jin maganarsa.


A'a anty Karki bari yasan na zo gidan har sai zuwa gobe in Allah ya kaimu, in ba haka ba wlh Baba cikin Daren Nan zai korani gida.


Ashe kema kin san baki kyauta ba.


Antyn tace tana wucewa falo lokacin Yaya Aminu ya shigo, ta tarbeshi kamar yadda ta saba ta gabatar masa da abinci sai da ya kammala ci suka wuce dakin barcinsu, suka yi shirin kwanciya lokacin wajen goma da rabi, sai a lokacin matarsa ke fada masa zuwan Khadija da yadda suka yi, cikin fushi ya mike zai fita, ta tare shi da cewa.


Dan Allah kayi hakuri ka barta ta kwana a nan saboda kaga dare yayi, kuma zaka tashi hankalinsu Baba ne in ka sanar dasu yanzu. Ka bari da safe sai ka tasa keyarta ku je cikin babban gida sai ayi wacce za ayi.


Dawowa yayi ya zauna a gefen gado cike da bacin rai, dole ya danne zuciyarsa ya hakura zuwa wayewar gari.


***


Da safe 


Amira ta fito falo ta samu Babu kowa ta shiga kitchen babu alamar an daura wani abinci, sai kawai ta fito taje dakin Mami ta samu bata ciki, sai ta isa dakin Abbansu ta shiga bugawa, cikin barci ya farka ya sauko ya bude yana ganin Amira ce ya saki fuska.


Amiran Abba har kin tashi?


Eh ina kwana Abba.


Lafiya lau, Ina Nura.


Yana dakinsa yana dhirin hadda. Dama na duba ba a dafa komai ba shine nazo na duba Mami.


Ayya Maminku ta fita zuwa dauko kayan oder, kiran gaggawa aka yi Mata shiyasa ta tafi. Yanzu kije ki hada muku tea kusha da cincin kinji.


Da to ta amsa masa ta wuce shima ya koma daki ya kwanta, yau Sunday baya fita kasuwa. Amira ta hada musu tea Nura ya fito suka karya, bayansa sun gama suka je dakin Abban ya basu dubu daya akan su ci abinci a makaranta saboda yau ba a yi musu abincin lunchbox ba, suka amsa suka wuce cike da damuwar rashin ganin Maminsu saboda ba haka ta sabar musu ba, duk inda zataje dole saita kammala musu duk abinda zasu bukata kafin ta tafi. Abba daya koma daki wanka yayi ya sauya kaya ya fito, duk da yau ranar hutunsa ne a gida sam baya Jin dadin zaman gidan sai kawai ya fice a motarsa, ya wuce wani restaurant ya yi breakfast a wajen kana ya kira Alh. Abba ya tambaye shi inda zasu hadu, ya sanar dashi wani wajen hutawa da su hadu a can, yana gama waya da shi sai ya kira Yaya Aminu suka gaisa kana ya tambayeshi ko Khadija ta zo nan, ya tabbatar masa da a gidansa ta kwana kuma ya kwantar da hankalinsa anjima nan zata dawo ya kara ba shi hakuri, Abba ya nuna ba damuwa tare da godiya sai suka yi sallama.


Yaya Aminu yana sauke kiran yana duban su Baba da suke zaune a falonsu,, ga Khadija a gefe tana ta sharban kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa, ya ce.


Auwalu ne ya kirani ya tambayi khadija.


Baba ya ce cikin fada.


Ai ka yi sakarci, da tun jiya ka zo ka sanar damu da zuwanta, da ba zata kwana ba zata koma gidanta.


Ayi hakuri Baba wlh bana son na tashi hankulanku ne shiyasa.


Babu wani hankalinmu da zaka tasa, domin iskanci kawai ya sata ta dawo gidan.


Cewar Innansu a fusace. Baba ya daura da cewa.


Khadija maganar da zan miki na karshe shi ne, ki yi hakuri ki zauna a dakinki, in ba haka ba jayayya kike da Allah domin shi ne yace a kara aure, Kuma Auwalu yana da duk sharuudden kara aure, in wani ne ma da tuntuni ya kara, dan haka ki koma dakinki babu inda yafi miki can, in kuma kinki ji kika ka so aurenki, wlh ba gidana ba Kuma sai dai ki sauya wasu iyayen, sannan wlh saina tsine miki albarka.


A gigice Khadija ta dago Kai tana kallon baba, ya cigaba da cewa.


Kwarai abinda na fada babu sauyi a ciki, kin san in har na fadi magana bana taba sauyata, in kin ki jin maganata to gaki ga duniya ya isheki riga da wando, yau koda Alwalu yana yankan namanki ne bance ki dawo min gida ba domin ibada kike yi, kuma duk wanda ya cuci wani a tsakaninku Allah zai saka masa, na kara jan kunnenki ki zauna a dakinki kiyi wa mijinki biyayya, in Kuma kin ki ji babu ni babu ke kuma tsinuwata sai ya tabbata akanki.


Khadija ta rushe da kuka me tsanani, gaba daya Babu wanda ya goyi bayanta, baba na gama nashi Inna ta daura da nata duk zancen nasu kusan iri guda ne, Yaya Aminu yayi mata tas kamar zai ari baki ya tsine mata, ji tayi duk ta tsani kanta meyasa ma ta zo gida? Gashi babu abin da ya haifar Mata sai karuwarbbakin ciki da damuwa, haka ta mike tana jan kafa tabar falon, suka bita da kallo cike da tausayi babu wanda ya dakatar da ita, sun san tana cikin damuwa Wanda Suma sun danne nasu ne suka yi mata haka domin ta zauna dakinta cikin rufin asirin Allah, ba dan basa sonta ba ko basu damu da halin da take ciki ba. Sashin yaya Jabiru ta nufa tana shiga ta samu matarsa a tsakar gida, Isa gareta ta yi tana kuka, Matar yaya Jabiru ta rungume ta jata zuwa dakinta da yake yayan nata ya fita, suka zauna bakin gado Matar yaya Jabiru ta shiga bata hakuri da kyar ta shawo kanta ta daina kuka, Matar yayan taje ta hado mata tea me zafi ta amsa ta rika sha kamar magani harta shanye, gumi ya sauko mata sai ta cire gyalen kanta ta kwanta a gadon, ba jimawa barcin wahala yayi gaba da ita, Matar yaya Jabiru ta fito ta rufe mata kofa ta koma tsakar gida ta cigaba da aikinta cike da tausayin khadijan, dukansu suna jin damuwa alan halin da take ciki saboda sun san irin shakuwa da son dake tsakaninta da Auwal.


Rahma ce.