08
ƘAZAMIN TABO
08
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir.
_Masoya da fatan za kuyi min afuwa na rashin samun update, hakan ya faru ne bisa babban dalili, nagode da kulawarku jazakallah khair_
Cikin jan kafa Khadija ta shiga falon har tsakiya, ta samu babu kowa sai key din motar Auwal da wayarsa sai ta dankara musu harara sai kace shi ta gani, taja tsaki kafin ta isa dakin Amira taga bata ciki, sai ta shiga kiran sunanta ko tana bayi nan ma taji shuru sai ta fito ta wuce dakin Nura a tunaninta suna tare, tana shiga ciki ta ganshi yana barci bisa gadonsa sai ta isa gareshi ta shafa kansa cike da kewarsa, ta tofa masa addu'ar barci duk da tana zaton kila yayi domin ta koyar dasu haka, ta gyara masa kwanciya sai ta fito tana tunanin Amira tana dakinta, saboda ita tafi Nura kulaficin uwa shiyasa ta fi makale mata sosai, sannan lokuta da yawa in ta tafi anguwa in ta dawo tana samun Amira ce a dakinta tana kallo ko ta yi barci, hakan yasa bata rufe kofarta in zata fita take barinsa a bude, saboda ko da Amira sun dawo daga makaranta a nan zata yada zango. Ta wuce dakinta da tunanin yaranta, sai hakan ya sanya mata wani natsuwa a cikin ranta, har take jin zata iya sadaukar da farin cikinta a kansu ta yi hakuri ta cigaba da zama da Abbansu domin ta kula dasu sosai su samu ingantaccen tarbiyya. Haka ta isa dakinta ta tura sai ta ga hudu ba haske, sai ta shiga ta soma daluben inda makunnin hasken dakin yake daga gefen, har ta lalubo sai ta kuna haske ya gauraye dakin ta tura kofar ta rufe sai ta jiyo idonta ya sauka akan gadonta, wani irin mummunar faduwa gabanta yayi tare da jin bugun zuciyarta ya harba da tsananin karfi wanda yasa ta kasa tsayuwa da kafarta sai da ta dafe bango kafin ta da dafa gefen zuciyarta, ta furta Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun da karfin gaske, sai ta su lale a kasa tana jin wani irin daci a makoshinta wanda yake tun daga kirjinta har wuyanta, a zabure Abba ya farka sai ya kai kallonsa in da yaji salati, yaga Khadija ce kwance a kasa tana salati ga jini yana fita ta bakinta, a matukar gigice ya dawo da kallonsa kan gadon, ganin Amira ce kwance cikin jini wannan ya tabbatar masa da ya yiwa yar cikinsa fyade, hannu ya daura duka biyun a kansa yana fadin.
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, na shiga uku na lalace.
Ya mike cikin tashin hankali ya zo wajen Khadija, sai ta shiga korarsa da hannu duk da tana kakarin amai, tace cikin murya kasa kasa.
Zaka kasheni da sauran raina ka fita bana son ganinka.
Cikin matsanancin tashin hankali Abba ya fice daga dakin zuwa dakinsa ya rufe kofar da key, domin gani yake Khadija zata biyoshi da wuka ta kashe shi sablda yayi Mata laifin daya cancanci haka, ya zauna dirshen a jikin kofa ya sanya fuskarsa a tsakanin guiwarsa ya shiga rusa kuka kamar wani karamin yaro, wannan bai isheshi ba ya dago ya shiga Marin kansa kamar zautacce, a takaice dai Abba ya yi haukar wucin gadi.
_____
KADUNA
Momy tana isa gida ta samu duk suna falo cikin dakiya take cewa su Nabeel.
Ku kuma meyasa ba kuyi shirin zuwa makaranta ba? Maza kuje ku shirya.
Taya zasu samu karfin guiwan shirin zuwa makaranta? Bayan basu san halin da dan uwansu ke ciki ba. Kun barmu a duhu cikin damuwa, jiya barci barawo ne ya sace ni, na kwana cikin zullumi Kausar, da fatan Anas yana raye?
Cewar Kakus da ta fito daga kitchen dinsu tana taya yar aikinsu hada breakfast, Momy ta zauna a Cushing cike da gajiya tace cikin damuwa.
Hajiya jikin Anas sai dai muce da saukin hausawa amma har yanzu be farfado ba, yanzu ma na dawo ne na runtsa saboda jiya sam bamu samu barci ba, Abbansu yace in kin kimtsa sai driver ya kaiki ki zauna da shi kafin anjima na zo na amsheki.
Ya salam, Allah ya bashi lafiya yasa kaffarace. Amma ni naji wani zance ne a wajen su Nabeel, wai Habeebu dukansa yayi harya fado daga matakala, meya yi ne haka harya cancanci irin wannan hukuncin?
Kakus ta fada tare da zama a Cushing tana kallon Momy cike da damuwa, Momy ta runtse Ido ta bude gaba daya sai taji babu dadi domin itace tayi silar komai, tace cikin matsanancin damuwa.
Hajiya kudi ya daukarmin ban sani ba shine na fadawa Abbansu ya hukuntashi ta yadda ba zai sake ganin wani kudi ya dauka ba, shine tsautsayi ya afka masa garin dukansa ya fadi sai ya tuntsiro daga matakala, amma Abbansu baiyi Masa duka da nufin ya kassara shi ba.
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, zan iya rantsuwa cewar Anas bazai taba ganin kudi ya dauka ba da sunan sata, wannan wace irin masifa ce, ke baki yi bincike ba kisa ubansa yayi masa irin wannan lahanin, to wai har nawa ya daukar miki?
Dubu goma ce ya dauka a cikin dubu dari na kungiyarmu, kuma abinda yasa nace shine a gabansa na ajiye kudin shekaran jiya, sannan jiya da safe naga dubu biyar ya boye a karkashin littafansa kuma Babu abinda ya banbantasu da kudin dana ajiye, shiyasa na tabbatar da shine ya dauka.
Kakus ta jinjina lamarin amma har zuciyarta ta kasa amincewa da Anas shi ne ya dauka, Nabeel kuwa daya ji kanun zancen sai duk hankalinsa ya tashi ya tabbatar da anyiwa Anas hukunci ne akan kudin da shine ya sata, sai ya mike kamar wanda kwai ya fashe masa a ciki ya wuce dakinsa sadaf sadaf, Babu wanda ya kula da shi har ya hau sama ya shiga daki ya kwanta a gado tare da sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya, dana sani ya gama cika masa rai yana tsoron ranar da gaskiya zata bayyana a gane shine ya dauki kudin, ya tabbatar sai anyi masa hukunci fiye da wanda aka yiwa Anas, sai ya kara rudewa cikinsa ya murda sai ya mike a guje ya shiga bayi domin zawo ne yaji ya kama shi saura kiris ya saki a wando.
Kakus dai ta yi ta yin fada akan bai da ce a rika yin hukunci ba tare da kwakkwaran shaida ba sannan ma hukuncin yayi tsauri da yawa, haka ta mike ta wuce dakinta ta yi wanka da sauri ta shirya ta fito, a lokacin me aikin ta gama breakfast, Momy ta zuba na asibiti koda Anas ya farka wata kila ya bukaci cin wani abu saboda jiya bai samu yaci abincin dare ba, bayan ta sanya komai a basket ta sanya me aikin ta kai mota, Kakus ta shiga kujerar baya driver ya jata suka wuce asibiti. Momy kuwa lallaba su Bushra ta yi suka karya kafin ta wuce dakinta ta yi wanka tabi lafiyar gado danta huta, bata san halin da Nabeel ke ciki ba a zatonta barci yake yi, shiko da ya fito daga bayi kwanciya yayi ya cigaba da karanta wasikar jaki har barci me nauyi ya dauke shi, a ranar dai ba suje makaranta ba.
Suna zuwa asibitin basu sha wuya ba wajen gano dakin, Kakus hankalinta ya yi matukar tashi saboda ganin Anas a kwance rai kwakwai mutu kwakwai, har kwalla sai data fitar ta zauna kusa da gadon tanata karanto masa addu'a tana tofawa, banda gaisuwa babu abinda ya shiga tsakaninta da Abba, ganin fuskarsa babu annuri yasa shi shan jinin jikinsa ya tabbatar da ta samu labarin duk abinda ya faru a bakin Momy, sai kawai ya mike jikinsa a sanyaye ya ce mata ya tafi gida, Kai kawai ta gyada masa ya wuce jiki ba kwari, ita kuma ta cigaba da tofawa Anas addu'a.
Abba koda suka isa gida, wanka ya fara yi kafin yabi lafiyar gado ya kira babban yaronsa na kasuwa ya shaida masa ba zai samu damar zuwa ba ya kula da komai, kansa ke sara masa saboda rashin barci da kuma fargaban da suke ciki, ga yunwa dake damunsa kuma baya sha'awar cin komai, haka barci ya dauke shi mai nauyi.
2:00pm
Suka koma asibiti, sun tadda Hajja mama da uncle Kamal a can Momy ce ta kirasu take sanar dasu, suka gaisa tare da kara jajantawa juna akan jikin Anas, haka suka cigaba da zama suna jiran farkawansa tare da yin hira kadan kadan gudun kar suyi da karfi ya tashe shi, su Nabeel kuwa suna gida tare da me aikinsu tana kula da su tare da yin girkin gidan.
Bayan sallar magrib.
Likita ya shigo ya duba Anas ya cire masa oxygen din domin numfashinsa ya dawo dai dai, bayan ya gaba duba shi yace zai iya farkawa a kowani lokaci dan haka da zarar ya farka su sanar da shi sai ya wuce. Ana kiran sallar Isha'i su Abba suka tafi masallaci suka bar su Momy a dakin, Hajja mama ce ta tashi ta fara gabatar da sallah su Momy suna jira ta idar suma suyi da ya ke dadduma guda daya ne, Kakus tana kusa da gadon Anas tana jan carbi Momy kuma tana danne danne a waya da alama chart take yi a group din kungiyarsu ta sanar dasu halin da Anas ke ciki sai jero masa addu'a suke da fatan samun lafiya. Anas ya yi wani irin mika wanda yasa duk suka maido da hankalinsu akansa ya fara bude Idonsa a hankali har ya bude duka ya zaro su waje kamar zasu fado kasa, ya yi wani irin tashi da iya karfinsa ya fincike allurar drip din dake jikinsa, ya soma fisge fisge tare da gurnani yana kokarin saukowa daga gadon, Kakus ta mike da sauri ta danne shi iya karfinta, Momy ma ta danne masa kafa, Hajja mama cikin tashin hankali ta idar da sallah ta fita da gudu ta Kira doctor, minti daya sai gasu tare sun shigo da sauri, ya danna wani abu na Kiran nurses sai gasu sun shigo su uku, cikin sauri ya fasa wata allura ya zo yayi masa a duwawu, cikin kankanin lokaci jikinsa ya saki a hankali idanunsa suka rufe ya soma barci, likita ya ce su Kakus su basu waje haka suka fito suka tsaya a kofar dakin jugum jugum cike da damuwa. Su Abba suka dawo suka same su a wannan yanayin, suka tambaya ko lafiya? Hajja mama ce ta iya warware musu komai domin Momy banda kuka Babu abinda take yi, ita kuwa Kakus ta kasa cewa komai sai lazumi take, likita ya gama duba shi suka fito dashi zuwa wani daki, Koda suka fito su Abba suka tare su da tambayar matsalar dake damunsa, hannu ya daga musu yace su jira tukuna sai suka wuce, Abba da Kamal suka rufa musu baya, ana shiga dashi dakin gwaji suka rufe kofar su Abba suka tsaya jiran tsammani, Dr Abdul ya kira likitoci guda biyu wanda suke da sani sosai akan abinda ya shafi kwakwalwa, basu bata lokaci ba suka iso da yake gidajensu yana cikin asibitin, suka shiga duba Anas domin su gano matsalar dake damunsa.
Sai wajen karfe goma suka fito daga dakin suka maidashi ainahin dakin da yake, suka daurashi akan wasu magunguna kafin suka bar bayani a wajen Dr. Abdul Wanda zai masu Abba kafin suka wuce. Dr. Abdul yace su Abba su same shi a office dinsa yace su Hajja zasu iya shiga dakin su zauna amma a kula banda hayaniya, ai gaba daya suka nufi dakin likita domin jin abinda ya samu Anas, Hajja mama da Kakus sune suka zauna su Abba kuwa suka tsaya da yake kujeru biyu ne, Dr. Abdul ya zauna ya goge fuskarsa da hankacif ya maida tabaronsa ya soma bayani kamar haka.
A gaskiya Anas yayi mummunar rauni akansa wanda buguwan da yayi ya samu internal injury jini ya Soma taba kwakwalwarsa wanda shine ya haifar masa da farkawa a firgice, yanzu dai mun daura shi akan magani da yuwuwar mu shawo kan matsalar, in kuma lamarin ya faskara zamu turaku asibitin psychiatry domin ya samu kyakkyawar kulawa akan matsalar tabin hankali. Addu'a yake bukata sai ku cigaba da yi masa domin shi ne kadai g
atan da zai samu a wajenku.
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun dukansu suka furta ko wanne kaga fuskarsa zaka tabbatar da cewar suna cikin matsanancin tashin hankali, Abba kuwa jiri ne yaji yana dibansa da sauri ya dafa Kamal yana runtse idonsa, saboda wani irin ciwon kai da yaji lokaci guda, kafin yayi yunkurin dai daita kansa lamarin ya yafi karfinsa, haka ya yanke jiki zai fadi Kamal ya yi saurin tare shi, amma duk da haka sai da ya kai kasa a hannun Kamal din, nan take ya suma.