11
ƘAZAMIN TABO
11
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir.
*karshen freepage*
Abba yana isa gidan Alh. Abba ya yi parking a tsakar gidan yana kokarin kirashinsa sai ga Alh. Abban ya fito saboda yaji karar shugowar motarsa, ya mika masa hannu suka gaisa, a yadda yaga Abba a ya yamutse yasan babu lafiya, sai ya jashi zuwa falonsa suka shiga suka zauna Alh. Abba yace.
Abokina yana ganka haka? Ince dai ko lafiya?
Alh. Abba komai ma ya faru, kafin na fada maka abinda ya faru, ina so ka fadamin ko maganin nan yana sanya mutum ya fita hayyacinsa?
Gaskiya baya haka sai dai in ka sha wani magani bayan shi wata kila su hadu su gusar maka da hankali, sannan tunda nake sha bai taba yimin haka ba, da fatan bai jefaka a matsala ba.
Hmmm a babbar matsala kuwa ya jefani, domin yasa na aikata abinda ya zamemin mummunar kazamin tabo wanda harna koma ga Allah ba zai gogu ba.
Meya faru ne haka Alh. Auwal?
Alh. Abba ya fada yana tashi zaune daga jinginar da yayi a kujera, idanun Abba suka yi ja kamar zai fasa kuka, sai ya danne zuciyarsa ya shiga ba shi labarin duk abinda ya faru. A tsananin zabura Alh. Abba ya mike tsaye yana rafka salati, ya daura da cewa cikin damuwa.
Wannan wace irin kaddara ce, wlh dana san wannan abin zai faru da tun farko ban baka ka sha ba, kaicona.
Aikin gama ya riga ya faru sai dai ban san ta ina zan fuskanci matsalar ba, khadija ta kwashe kayanta dana Amira tabar gidan da asubahi, tsorona karta fallasa wannan barnan da nayi, ban san da wani ido zan kalli iyayenmu ba da mutanen gari, ina cikin tashin hankali Alh. Abba, yanzu menene mafita?
Alh. Abba ya koma ya zauna cike da zurfafa tunaninsa sai da ya dauki minti biyar kafin ya sauke numfashi yace cikin damuwa.
Daga can gidansu an kiraka? Ko ka kira kaji ko taje can?
Babu wanda ya kirani kuma ban kira kowa ba.
To ina ganin inda taje gida ya isa zuwa yanzu wani daga mutanen gidan sun kira ka musamman in sun ganta da kaya niki niki. Yanzu ina so ka kira daya daga cikin yayyinta ka tambaya ko ta zo gida muji ta yadda zamu shawo kan matsalar.
Cikin rawar jiki Abba ya kira yaya Aminu yayi sa'a wayar tana hannunsa, kiran na shigowa ya dauka, suka gaisa kamar yadda suka saba kana Aminun yace.
Ina me taurin kai? ai jiya sai da ta sha duka, da fatan dai lamura sun fara dai daita.
Abba ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace cikin damuwa.
Ai yanzu ma kiran dana yi maka kenan akan naji kota zo gida, saboda tun asuba ta kwashe kayanta dana Amira ta bar gidan.
Amma khadija anyi mai taurin kai, kuma bata zo gida ba, dan yanzu nake baro sashin su Baba kuma ya ce dama zai kira ka akan ka kara hakuri da halinta, ina ga wani gun ta nufa bari yanzu naje na sanar dasu domin susan halin da ake ciki.
Abba yace masa to kafin ya kashe wayar, ya duba alh. Abba.
Kaga kuwa bata je gida ba, to ina ta nufa?
Nayi tunanin haka da wuya taje gida, saboda ma kota fadi abinda ya faru babu mai yarda da ita domin zasu yi tunanin bakin kishinta zai sa ta iya yi maka sharri, dan haka mafita shine kafin ta bata ka a gunsu gwara kai kayi hanzarin kare kanka ta hanyar nuna musu tsantsar damuwarka akan barinta gidanka, kuma ka tabbatar musu da jiya data dawo ko magana ba kuyi ba, kawai ka wayi gari ta kwashe kayanta ta bar gidan bayan ka tafi masallaci yin sallar asubahi. Daga nan kuma sai muje wajen malam Ilyasu yayi mana aiki akanta ta yadda zai rufe mata baki ta kasa fadawa kowa abinda ya faru, kaga munyi maganin matsalar. Amma shawara ce in tayi maka to in bata yi ba sai ka yi abinda zuciyarka ta yanke maka.
Haba alh. Abba ai nasan zan samu mafita shiyasa ma nazo wajenka, dan haka wannan shawaran naka tayi, domin zan iya aikata komai akan mutuncina kar ya zube a idon mutane, tun yanzu ma zan fara wanke kaina a gunsu baba, bari na kirashi.
Ya kare maganar yana laluban number baba, Alh. Abba yayi kasake yana sauraren me zai ce, yana kira baba ya dauka suka gaisa kafin yayi magana ma baba ya tari numfashinsa.
Ashe khadija ta yi gaban kanta ta tafi da Amira, yanzu Aminu ke fada min, kayi hakuri nasan matakin da zan dauka akanta kuma aurenka babu fashi sai dai bakin kishinta ya kasheta, nasa Aminu ya kira yayarka Amina akan koda taje zan wajenta ta koro ta, sannan mun kira maiduguri suma munce in taje wajensu karsu amsheta, sannan nace kar wanda ya kirata a waya balle tayi tunanin an damu da ita. Kayi hakiri kaji Auwalu Allah yayi maka albarka.
Amin baba nagode, ni dama wlh na bayar ko ta zo gida ne saboda tasha alwashin saita ruguzamin farin cikina, tace saita yimin sharrin da sai na gwammaci mutuwa da rayuwa, shiyasa hankalina ya tashi nace bari na fada maka tun kafin ta aiwatar da abinda ta shirya min, da harna fara tunanin fasa auren bilkisu na hakura kawai.
Ina bata isa ta hana auren nan ba, kuma duk sharrin da zata yi maka ba zai yi tasiri a kanmu ba, domin ai mun san bakin kishinta babu abinda ba zata iya yi ba, ka kwantar da hankalinka duniya ce ta isheta riga da wando kuma duk inda taje zata dawo ta sameni.
Abba ya sauke ajiyar zuciya ya yiwa baba godiya kafin suka yi sallama ya kashe wayar, alh. Abba ya jingina masa yana cewa.
Yanzu ne ka zama cikakken namiji Alaji, ta shi muje wajen malam insha Allah cikin kankanin lokaci matsalarka ta kau.
Abba ya mike cike da kwarin guiwa sai yanzu yake jin hankalinsa ya kwanta ganin yana niman kauda matsalarsa cikin kankanin lokaci, duk da yana kaunar khadija amma zai iya yin komai don kare martabansa, kuma in har yanada laifi itama tanada laifi, domin da bata nuna kazamin kishi akan aurensa ba da duk haka bata faru ba. Haka suka kama hanyar zuwa gidan malam ilyasu Alh. Abba yana kara masa karfin guiwa akan lamarin.
Bayan sun isa alh. Abba ya kira malam din a waya ya sanar dashi suna bakin gate, yace su shigo zuwa dakin da yake tarban bakinsa, suka shiga ciki har zuwa dakin tare dayin sallama, daga ciki malam ya amsa kana yace su shiga, bayan sun shiga suka zauna kan daddumar dake malale da dakin, ga malam din zaune akan nashi daddumar ga carbi me guda dubu a gabansa da wani kasa a cikin tire, suka gaisa kana alh. Abba ya koro masa bayanin matsalarsu, malam ya shiga buga wannan kasa yana zanata, bayan ya gama ya dago kai ya kalle su ya soma magana.
A yanzu haka matarka ta kama hanyar fita daga garin nan tayi nisa, ta tafi wani gari da nufin zuwa wani lokaci zata dawo. Yanzu me kake so ayi?
Malam ina so a rufe bakinta ko da ta dawo ba zata fadawa kowa ba abinda na aikata ba.
Malamin ya kara zana kasar kafin ya dauki tsarbin nan ya mikawa Abba akan ya zabi daya, ya zaba ya mika masa, malamin ya kama wanda ya zaba ya fara ja zuwa guda hamsin kafin ya tsaya ya kuma buga kasa yayi zane kafin ya ajiye tsarbin ya dago kai yana cewa.
Duk abinda za a yiwa matarka bakinta ba zai taba rufuwa ba sai dai a cikin abu biyu ayi daya.
Me kenan malam?
Abba yace cikin zakuwa, Malamin ya cigaba da cewa.
Ko ayi mata kurciya tayi nesa daku ba zata waiwayo gida ba wata kila kafin lokacin ta rasu ma, ko kuma a haukatata ta yadda tana dawowa kano zata fara hauka da nufin tsinuwar da mahaifinta da yayi mata ya tabbata akanta, to a gaskiya ba zata taba warkewa ba harta mutu tana fama da hauka.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
Abinda Abba ya fada kenan yana duban malam cike da tashin hankali.
****
Khadija tunda ta fara tafiya bata tsaya ba domin tana da mai sosai a motar, duk in Abba zai sauya mata sabon mota to yakan cika mata shi da mai tare da extra a galam, shiyasa ta zabi data dauki sabon motan domin ta san zaifi mata dadin tafiya me nisa, dama gashi bata bata tuka kanta wajen yin tafiya me nisa ba, sai dai a tukata sannan duk yawonta iyakarta cikin kano, haryar kaduna ta nufa wanda a lokacin harta wuce zaria kasantuwar safiya ce haryar babu cinkosan ababan hawa, bata samu wani matsala ba duk da zuwanta kaduna sau daya ne, amma da yake ta san in aka miko titi babu wani yanke har sai an shigo kaduna. Amira sai barci take tana sauke numfashi a hankali, mami tana tuki tana kallonta tare da jin tsantsar tausayinta yana ratsa dukkan jikinta, hawaye kebin kuncinta tana yi tana sharewa tare da tuki, sun kawo jaji lokacin ana bin one way saboda gyaran da ake yi a hanyar tafiya zuwa zaria, motocin sai suka rage gudu amma wasu sukanyi over taking domin suyi saurin wuce one way din, Amira ce ta farka mami ta kai hankalinta wajenta tana shafa fuskarsa, wani mota me zuwa zaria yayi over taking ga babbar mota danya wuce ta, ga mami kuma ta doso su hankalinta yana gun Amira, sai da suka zo gabda ita taji hon din babbar mota, sai ta yi saurin mai da hankalinta titi taga motar tayo kanta gadan gadan, da sauri ta kauce daga kan titi ta fada dajin dake ke gefensu, tana kokarin danna birki amma ina yaki controlling, salati kawai take zubawa tare da kuka me sauti, sai danna birki take tana murda kan motar amma ina lamarin yafi karfinta, ga wasu motoci sun biyota domin su kawo mata dauki, ganin ta kusa cimma wata katuwar bishiya tasa ta saki gigitaccen ihu wanda yasa Amira itama din yin ihu mai karfi.
_______
KADUNA
Anas tunda wannan kaddara ta auka masa sai Allah ya sanya masa tsananin hakuri da tawakkali, duk da da yana yaro amma lamarin bai dame shi sosai ba, musamman yadda yaga iyayensa suna bashi kulawa fiye da yadda suke masa a baya, wani lokacin har mamakin Abbansa yake bai taba tunanin yana da saukin kai haka ba, har gani yake kamar an sauya Abbansu ne an kawo musu wani, a hankali dan zaman da yayi a dakin Abba yaji kaunar mahaifinsa, sabanin da da yake jin haushinsa ko rabarsa baya so yayi, sannan wani irin mugun shakuwa ne ya wanzu a tsakaninsa, wanda Abba yake nuna tsantsar so da tausayinsa a bayyane gaban kowa, wani lokacin momy har korafi take akan ya rage nunawa Anas haka gudun kar sauran yan uwansa suga kamar yafi sonsa, Abban yakan ce mata.
Kema kin san Anas yana bukatar a nuna masa so na zahiri domin ya fahimci duk abinda na aikata masa banyi domin ban sonsa ba, kuma a wannan lokacin yana bukatar kulawa fiye da ko wani ɗa a gidan nan, in dai ba ke ce zaki raba min kan yayana ba bana tunanin abinda nakewa Anas zai kawo rabuwar kansu.
Momy dai bata gamsu da zancensa ba sai dai kawai tayi masa shuru domin batason suyita musun zancen.
Anas ya fara zana exam dinsa na waec Abba da kanshi yake kai shi makarantar ya kuma jira har sai ya gama zanawa ya dawo da shi gida, ya ajiye duk wani hidimominsa na kasuwa ya barshi a hannun babban yaronsa na kasuwar ya maida hankali sosai wajen jarabawan Anas, lamarin ba karamin bawa Momy mamaki yake ba, yadda lokaci guda Abba ya sauya halinsa sosai har take jin abin baya mata dadi, kar hakan yasa Anas ya samu gurbin da zai rika tsula tsiya a gidan, dan haka yasa ta samu kakus da batun, amma abin mamaki kakus ta gwaleta tare da sace mata guiwa, tace in Abba be yiwa Anas haka ba ya take so yayi? ai dole yanzu ya nuna masa yanada gata hakan shine zaisa Anas din ba zai damu da lalurar daya ke ciki ba, Momy dai da sanyin guiwa ta hakura ta zuba musu ido.
Bayan Anas ya kammala zana exam dinsa gaba daya, jamb da waec da neco sai Abba ya soma tafiya kasuwa da shi yana nuna masa harkan kasuwancinsa, saboda nan gaba shi zai sakarwa ragamar komai ya rike, Anas ya saki jiki sosai da Abbansa dan ba yi da wani aboki sosai wanda ya wuce shi.
***
Bayan wata uku.
Sakamakon jarawarsu ta fito wanda cikin ikon Allah wannan karan Anas ya samu gaba daya, iyayen sunyi murna sosai, a ranar da daddare Abba ya kira shi falonsa ga momy zaune yace ya fada masa inda yake so yayi jami'a, Anas ya yi magana cikin zancen bebe da kuma hannunsa.
Kasar turkiyya nake son naje, ina so nayi karatu a can, zan karanta harkan kasuwanci domin na zama kamar kai Abba .
Da kyau dan Abba insha Allah zan fara nima maka makaranta a can, in dai ina raye babu abinda ba zanyi maka ba.
Abba ya bashi amsa da magana tare da kwatanta masa da hannu yadda zai gane sosai, Anas yayi dariya har hakoransa suna bayyana, yayi masa godiya kafin ya mike yayi musu saida safe ya wuce dakinsa. Momy ta kalli Abba da mamaki.
Gaba daya Alhaji ka sauya akan yadda kake da, kaine fa da kanka kace babu wani ɗa da zai fita kasar waje yin karatu sai dai suyi a kasar nan, amma gashi ka yarda Anas zai yi karatu a turkiyya kuma kasan zaka kashe makudan kudi.
Eh, a yanzu Anas babu abinda ba zan yi masa ba muddun zai sashi farin ciki, kuma ki rubuta ki ajiye daga kansa babu ɗan da zai je waje karatu.
To wai meyasa kake nuna fifikonka akansa? gaskiya ina guje maka rabuwar kan 'ya'yanmu, ko da su Bushra basu je waje karatu ba ya kamata shima Nabeel ka bari yaje kasar waje karatu.
Kin san in har na yanke hulunci bana taba sauyawa, kuma shima Anas din dana yarda yayi karatun a waje kinsan dalilina ai.
Zata kuma yin magana wayarsa yayi kara ya duba yaga Brr. Ahmad, sai ya dauka dole yasa Momy yin shuru, bayan ya gama wayar yace da ita.
Brr. Ahmad ne, tashi mu je bangaren Hajiyata akwai maganar da nake son za muyu a can.
Ba musu ta mike suka jera tare har sashin kakus sai suka shiga ciki, sun samu brr. Ahmad suna gaisawa da Kakus, lauyansu ne da duk wani abu in ya ta so na dukiyarsu shike zame musu jagora, kuma dama kakus da Abba sun san da zuwansa, suka zauna sannan suka gaisa, bayan sun taba hira sai kakus tace.
Ni kam barci ya soma kamani ina so ayi maganar nan na samu na kwanta da wuri.
Abba ya ce to kafin ya soma magana.
Haj. Kausar ke ce baki san da maganar ba sai yanzu ne zan fada miki a takaice. Dama akan abinda ya samu Anas ne wanda nine na zama silar yi masa kazamin tabo, hakan yasa na tattauna da hajiyata akai kuma ta amince min sai na kira brr. Ahmad muka yi maganar, shiyasa yazo yau domin muyi maganar a rubuce a gabanki dan ki sani.
Ok wace magana ce kenan? kamin dalla dalla.
Cewar Momy tana muskutawa. Abba ya cigaba da cewa.
Kausar na raba dukiyata gida biyu na bawa Anas rabi halak malak, ko da bayan raina wannan maganar haka take, sannan za a raba gado kuma da shi a sauran abinda na mallaka.
A zabure momy ta mike tana dafe da kirjinta tare da cewa.
What???
karshen freepage