Twist of fate

Page 25 & 26

by @realeshaa

TWIST OF FATE

 (Karkatarwan Ƙaddara)






 By

 REAL ESHAA





 Free Page 25&26


_______________________________Azabure Ainah ta fincike hannunta daga riƙon daya mata cikin tsananin tashin hankali da ruɗun kalamansa tace"Me kake nufi Abdulll?,shin wace Ainah kakeso??Kai tashiga juyawa suwwan Muryansa na sake yawo acikin dodon kunnenta ta kasa gaskata abinda kunnuwan ta suka jiye mata.Dariya ta fashe dashi tace"You are so funny please stop jorking me I don't want this king of jok abeg",Ido RK ya ƙura Mata ganin yanda fararen haƙoronta ke sheƙi,Lumshe Idanunsa yayi tare da sakin murmushi cikin wata narkakkiyar murya yace"Ainatyyyyyy",Cak ta haɗiye dariyan da take tare da zuba masa manyan Idanunta,Hannu yasa ya matso da fuskarta daf nasa har suna shaƙan numfashi juna,Babu alamar wasa atare dashi yace"I love you Ainah Ina matuƙar ƙaunar ki Ina burin kasancewa dake amatsayin matar Aurena kuma uwar 'ya'yana kece zaɓin zuciyata ina Miki sahihiyar ƙauna Wanda bansan adadinsa ba.Cikin tsoro da al'ajabin abinda yake faɗa ta tsirawa ƙwayar Idanunsa kallo wanda take iya hango tsantsar gaskiyar kalamansa.Manyan Idanunta ta lumshe tare da janye hannunta daga cikin nasa tana kiran sun Allah aranta cikin son ɓagarar da maganar tace"Lalle ana cewa wasan ƙanin miji, Wannan Kuma wasan mijin Yaya ko?ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe motar da faɗin"Let me go kasan ba lafiya bace dani ina buƙatar hutu.Hannu yasa ya fisgota jikinsa tare da rufe ƙofar cikin tsareta da Ido yace"Waya faɗa Miki son da nake Miki da wasa nake"??,Wani irin kallo ta watsa masa babu alamar wasa atare da ita tace"Idan ba afilin wasa kake son in tanadarwa kalamanka ma sauƙi ba a filin mahaukata kakeson in tanadar musu?."A raunane yace"a irin wannan matsayin kibawa maganata muhalli??.Cike da tsiwa da takaicinsa tace"Irin muhallin daya dace dashi kenan domin babu wani mutum me cikekken hankali da nutsuwa da zeji kalamanka ya kuma bashi muhalli sama da wannan"!,Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana jin wani iri azuciyarsa Idanunsa akanta yace"Tabbas duk wanda zesa kalamaina a irin wannan muhallin haƙiƙa besan menene zafin so ba hasalima besan menene kalmar so ba!!.Cikin tsananin fushi tace"Allah yatsinewa wa So!,inde Irin wannan shine so!,Me za'ayi da soyayyar da zata ruguza zuciyar wanda ya aminta da Kai yakuma ɗauki duk kanan yadda da amana ya danƙa maka?,Shin kasan adadin ɗumbin so da ƙaunar da sister Sajnah ke nuna maka??tana matuƙar ƙaunar ka fiye da kanta, Sister Sajnah Bata da wani madubi acikin Rayuwarta wanda ke haska mata fuska da zuciya face kallon fuskarka,Sister Sajnah ta ɗauke ka amatsayin bango majin ginar ta wanda ko wani bugun numfashinta da soyayyarka take bugawa, Amma shine sakayyar da zaka Mata nacewa kana son ƙasa!???. Murmushin takaici yayi da faɗin"Ainah shi so ba ruwansa da wannan jawabin naki shi so makahone baya ganin gabansa bare kuma bayansa shi so mayunwacin zaki ne da bashi da buri idan yana Jin yunwa face yasamu abin farautar daya ke hari shi so tsuntsune da kan iya tashi daga inda yake zuwa wani wajen,Ya numfasa tare da ɗago fuskarta dake ƙasa yace" Dan Sajnah tana ƙaunata wannan ba abu ne me muhimmanci,ace Ina ƙaunar Sajnah tana ƙaunata shine me muhimmanci,Anma kisani zuciyar Abdulrahman Kabeer Shareef mallakin Aina'u Muhammad ne.Manyan Idanunta dake cike da ruwan hawaye ta zuba masa Araunane tace"Abdul kabani mamaki sam ban taɓa zaton zakayiwa Sister Sajnah butulciba sede inaso ka kwana da sanin cewa bana sonka ni Aintah ba zan taɓa son...Be bari ta ƙarasaba ya fisgota jikinsa tare da ɗaura laɓɓansa akan pinch lip's ɗinta kana ya tallafo kanta yashiga kissing ɗinta cike da shauƙi,Ya ɗauki minti ɗaya yana kissing ɗinta Kafin ya janye bakinsa daga nata ya jingina bayansa da jikin kujera yana sakin ajiyar zuciya kallonta yayi da faɗin"ki sani Ainah kunnuwana bazasu taɓa juran kalmar ƙi daga bakinki ba aduk lokacin da bakin ki yayi yunƙurin furta kalmar ƙi agareni irin hakanne ze cigaba da kasancewa.Tamkar wacce aka zarewa laka haka jikinta ya saki ta kasa furta komai Tun sanda taji sauƙan lips ɗinsa akan nata hawayen baƙin ciki da takaici suka shiga zuba daga Idanunta babu abinda ke tashi banda sheshsheƙan Kukan ta,Lumsassun Idanunsa ya lumshe da faɗin"Please stop crying Ainatyyyyyy My love.Da wani irin sauri ta buɗe motar ta fice da gudu tashiga gida batare da tayi sallama ba ta wuce Ummu da Abbey dake hira a falo,Da kallo Abbey ya bita cike da kulawa yace"meke damunta ko har yanzu jikin ne?,Taɓe baki Ummu tayi da faɗin"I don't may be daga sashen Mama take ko lefi tayi mata kasan Ainah da Mama ta ƙarashe tana murmushi.Martanin Murmushin ya mayar da faɗin"Ainah rigima!.Tana shiga ɗaki ta faɗa kan gado tare da fashewa da wani irin kuka me gunji cikin muryan kuka tace"Why Abdulllll?, Meyesa zaka min haka kiss dana tana darwa mijina shine ya karɓesa acikin sauƙi haka ta hanyar da be daceba shin wani irin kallo Sajnah zata min idan tasan abinda yafaru!...Ta daɗe tana kuka Kafin ta miƙe toilet tashiga ruwan sanyi ta sakarwa kanta kana ta sake shirya jikinta cikin kayan bacci mara nauyi ta kwanta lamooo,kwanciyarta babu daɗewa wayarta ta hau ruri Ahankali ta janyo wayar ganin number dake yawo a screen ɗin yasata Jan dogon tsaki tare da kife wayar tana sauƙe Ajiyar zuciya akai².Kiran ne yasake shigowa akaro na barkatai miƙewa tayi tare da picking call cike da tsiwa da jin haushinsa tace"Kiran Mekake min adaren nan??", Lumsassun Idanunsa ya lumshe tare da sauƙe zazzafan ajiyar zuciya,Yace"please am so sorry about what happen,banyi niyyan kissing ɗinki ba anma Kika janyo hakan kunnuwana baza su iya juran kalmar ƙi daga garekiba,"Afusace tace"Kaga Abdul ba abinda nakeson ji daga gareka ba wallahi bana sonka bana ƙaunarka, kasani bazan taɓa shamaƙi da duk wani abu da zekawo wa Sister Sajnah farin ciki acikin rayuwarta ba,Koda ace ni kafara cewa kanaso daga baya sister Sajnah ta nuna tana ƙaunarka zan iya sadaukar mata da soyayyar ka bare kuma ace itake mutuwar sonka anma saboda san kai inshiga tsakaninku, Abdul Ina me haɗa ka da girman Allah kafita acikin rayuwata dan bana ƙaunar abinda ze kawo matsala acikin rayuwata dana 'yar uwata".Iska me zafi ya zurfar yana jin wani irin zafi azuciyarsa kaman shi da 'yan mata ke tururuwan sonsa wata ke furta kalmar ƙi agaresa,tabbas so masiface kansa ya dafe da faɗin"Shin koda Sajnah ta amince da auren mu ba zaki yadda ba!??.A tsiwace tace"Eh dan haka kafita acikin rayuwata kuma kissing ɗina da kayi ban yafeba".Murmushine ya kufce masa jin yanda ta ƙarashe maganan kamar za tayi Kuka atunanin sa koda raping ɗinta yayi ba zata riƙa maimaita bata yafeba bare Kuma kissing."Ok in har kina so injanye maganan gobe ki sameni a office ɗina Misalin ƙarfe goma be jira Jin abinda za tace ba ya katse Kiran...Da kallo tabi wayar tana sauƙe ajiyar zuciya tabbas za tabi ko wacce hanya gudun kar Sajnah taji koda alabarine baza taso wani daga waje yajiba bare kuma Ace Sajnah...

Hannu Daddy ya sanya tare da janye tagumin da Ummi tayi cike da kulawa yace"Haba Fatima lafiya zaki tashi cikin dare kiyi tagumi bayan kinsan hakan ba kyau?,Araunane tace"Daddy ya zanyi 'ya'ya biyu Allah ya mallaka min yau tsawon shekara huɗu da auren Abdallah anma ko ɓatan wata matarsa bata taɓa yiba duk wani asibiti ko gurin magani daya kamata aje anje anma sunce lafiyarsu kalau Hanan taƙi Aure tace seta kammala karatu,Abdul dana ke saran Auren shi aƙaramin lokaci shima nema yake ya bijire Sajnah yarinyar kirkice nasan zeyi alfari da Aurenta.Hannu Daddy yasa yashiga share hawayen dake gangarowa daga Idanunta Anutse yace"ki kwantar da hankalinki Insha Allah burinki ze cika ki cigaba da yiwa Abdul addu'a Allah ya zaɓa masa mace ta gari.Kai ta gyaɗa tare da riƙe hannunsa acikin nata tace"Akullum addu'a ta baki ɗaya akansu nake,Murmushi yayi tare da shafa kanta yace"ki cigaba da yimusu addu'a Kuma insha Allah gobe za'a nemawa Abdul auren Sajnah kodan farin cikinki.Cike da farin ciki ta Rungumesa tace"Allah yabar min Kai","Ameen ya amsa yana Murmushi tare da rungumeta suka kwanta...

Anutse ya fito daga bedroom ɗin sa yana taka matakalan benin cike da jarumataka hannunsa ɗayaata sanye a aljihu ya yinda 'ɗaya hannun ke riƙe da waya sanyayyar ƙamshin tularensa ya mamaye falon tun Kafin isarsa,Kai tsaye dinning ya nufa inda iyayensa ke zaune cike da girmamawa yace"Good morning Daddy"Morning Daddy ya amsa Kallonsa ya mayar kan Mom,da Uncle Jabeer ya gasishesu atare suka amsa, Miƙewa yayi tare da bawa Faruk hannu sukayi shaking kana ya sumbacesa akuncinsa,Kallonsa Faruk yayi da faɗin"Oooo take me to My friend I want see her.Lumsassun Idanunsa RK ya zuba masa yana Jiyayi kamar ya kwaɗa masa mari,"Oooo talk to me Faruk ya faɗa kamar zeyi Kuka.Taɓe baki RK yayi yace"Aiki zan tafi bani da time.Kuka Faruk ya fashe dashi tare da miƙewa hannun Ummi ya riƙe da faɗin"Please Ummi talk to him I want to see My Friend.Hawaye Ummi ta share masa da faɗin"Don't worry Son ze Kai ka".Murmushi Faruk yayi tare d miƙewa ya koma wajen zamansa.Ahankali RK ya Miƙe tare da durƙusawa agaban Ummi cikin rawan murya yace"please Ummina ki dena fushi dani bazan iya juran fushinki atare dani ba tunda nazo nan ko kallon inda nake bakyason yi".Hannunta ta janye daga nasa still fuskarta na kan dining tace"Me kakeso nace"maka Abdulrahman?Bayan kana son nunawa duniya cewa ban isa da kaiba!,Da sauri ya toshe Mata Baki kamar zeyi Kuka yace"Dan Allah Kar kice haka Ummina duk duniya banida kamarki". Ajiyar zuciya ta sauƙe ko Kaɗan bataso suna samun matsala agaban Kowa bayaga hakama bataso kowa yasan Maganan hakan yasa tace"Idan ka dawo daga aiki kasameni kai ya gyaɗa sannan yamiƙe yanufi hanyar fita duk cikinsu babu wanda yayi yunƙurin tsayar dashi,Kuka Faruk ya fashe dashi da faɗin"Oooo I want follow him."Tsawa Ummi ta bugawa RK da faɗin"kazo ka kaisa wajen Sajnah.Kai RK ya dafe cike da takaici kana ya dawo yariƙe hannunsa suka fita.Choculate dake gaban motar Faruk ya dauka da faɗin"Oooo I want this.Afusace RK ya daki stairing motar cikin kakkausan kurya yace"Leave me alone for God sake Meyesa kakeson takurawa rayuwata ne??".Rufe fuska Faruk yayi ya fashe da kuka hannun yasa ya hargitsa tulin sumar kansa da yasha gyara yake ƙyalli manyan Idanunsa suka kaɗa sukayi jawur dasu yashiga taune gefen bakinsa.Tsaki RK ya cigaba dayi batare daya tanka saba,har suka isa babu wanda ya sake magana, RK nagama parking ya ciro wayarsa yayi dearling number Sajnah ringing biyu ta ɗauka tare da sallama cikin sanyayyar muryanta.Kafin RK yayi magana Faruk ya wufce wayar da faɗin"Oooo Came out friend", Murmushi Sajnah tayi tace"Really??, Kai ya gyada kamar tana gabansa,"Am coming ta fada tare da katse Kiran.Cike da farin ciki ta buɗe gate ɗin ta fito,Da gudu Faruk ya buɗe gaban motar tare da rungumeta,saura Kaɗan su zube aƙasa ya tallafo ta jikinsa yana dariya,Harara ta galla masa da faɗin"Dubi yanda kake son jefar dani,kunnensa ya riƙe tda faɗin"Oooo am Sorry,yayi maganan tare dasa hannu ya saƙalo wuyarta.Tsaki RK yaja tare da fitowa daga motar ya jingina ajiki kana ya zuba musu Lumsassun Idanunsa,Anutse Sajnah ta ɗago Kai tare da ƙura masa Idanu sosai yamata kyau sanye yake cikin white t-shirt da black jeans kansa sanye da F-cap baƙi Idanunsa sanye da farin glass daya haska fuskarsa, Hannunta da Faruk yaja ya dawo da ita daga duniyar kallonsa data tafi,Ƙasa da kai tayi cike da kunya tace"Good morning Yaya RK,Sajen fuskarsa ya shafa da faɗin"Kingama kallonawa??, Murmushi tayi tare da rufe fuskarta tace"Kushigo mana,"Ya mutsa fuska yayi da fadin"Nop wajen aiki zani Faruk ya matsa sena kawosa,Marerece fuska tayi tace"Plsssss tare da riƙe bakin hijab dake jikinta tashiga wasa dashi,Matsawo daf da ita yayi tare da sanya hannu ya ɗago fuskarta lumsassun Idanunsa ya zuba acikin nata dake ƙyallin hawaye,Cikin zazzaƙan muryansa yace"What do you want??Hawayen da take ƙoƙarin mayarwa sukayi nasaran zubowa Ahankali ta fashe mai da kuka,Kai ya dafe da fa'ɗn"Please Sajnatyyyyyy nifa ba kuka nace kiyi ba Just tell me me kike buɓata!, Fuskarta da hawaye ya ɓata ta ɗago tare da nunasa,Kansa ya nuna da faɗin"Ni kike buƙata"??,Kai ta gyaɗa batare da tace"komai ba,Anutse ya juya ganin babu hayaniyar mutane yasa ya janyota jikinsa tare da haɗata da faffaɗan ƙirjinsa cikin kunnemta ya raɗa mata Just Pray Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alkhairi.Kai ta gyaɗa tana shaƙar daddaɗan ƙamshin tularensa seda yaji ta dena sheshsheƙan Kukan Kafin ya janyeta daga jikinsa Kallonsa ya mayar kan Faruk daya kafesu da Ido yana murmushi.Harara ya zabga masa,Dariya Faruk ya sheƙe dashi da faɗin"Oooo Ni banga komai ba.Batare da RK yace"komai ba ya juya yashiga mota tare da barin wajen Kai tsaye hospital ya nufa yana tunanin mafita...Bakin su ɗauke da sallama suka shiga falon Ummu hannunsu sarƙafe,Ummu dake moofing ta juya furkarta ɗauke da murmushi tace"Wanake gani kamar Faruk??,"Oooo nine Ummu ya faɗa tare da zama kusa da ita,Yace" Good morning"Morning Faruk ya Hajara da Fatima??,"Oooo Suna lafiya."Good morning Ummu cewar Sajnah", Murmushi Ummu tayi tace"ya jiki Sajnah?Kanta aƙasa tace"da sauƙi miƙewa tayi tace"Ya jikin sister Ainah,"Da sauƙi Ummu tace"Da sauri Faruk ya Miƙe yabi bayanta,Juyawa tayi tace"ka jirani yanzu zan fito",Kafaɗa ya maƙale yana tale baki zeyi kuka.Da sauri tace"Don't Cry zo muje.Ƙofar Bedroom ɗin Sajnah ta buɗe hannunta riƙe dana Faruk,Da sauri ta saki hannun Faruk tare da ƙarasawa bakin gadon ta janye hannun Ainah data zuba tagumi tare da tsirawa waje ɗaya ido.Cike da damuwa tace"Meke damunki sister Ainah??,Ajiyar zuciya Ainah ta sauƙe tare da ƙaƙalo Murmushi tace"Nothing,Ɓata fuska Sajnah tayi tace"Ban yadda ba dole akwai abinda ke damunki.Miƙewa Ainah tayi tana gyara ɗaurin towel dake ƙirjinta tace"Kinsan tun jiya cikina ke ciwo shiyasa Kika ganni cikin damuwa,Cike da kulawa Sajnah tace"Sannu Allah yabaki lafiya"ameen ta amsa tare da Zama agaban dressing mirror,Ta fara shafa lotion ajikinta tana gamawa ta miƙe,Ƙafanta ne ya harɗe tayi baya luuuuu zata faɗi,da wani irin gudu Faruk dake bakin ƙofa ya ƙarasa ya tallafota jikinsa tare da rungumeta,Ajiyar zuciya dukansu ukun suka sauƙe,Hannu Faruk yasa ya ,damƙi ƙugunta da faɗin"Woow Friend dubi Aunty Ainah nada big bom-bom I like it".Afusace Ainah ta turesa daga jikinta cikin fusata tace"Banason iskanci da rashin kunya how dare you touch me?,ta faɗa tana tsaresa da manyan Idanunta."Rau rau yayi da Idanunsa yana kallon Sajnah yace"Oooo Let's go she shout at me.Zungure masa Kai Ainah tayi tace"Oooo ƙaniya seka dinga abu kamar wani sabon kamu Wallahi idan ka sake yimin irin haka sena maka dukan tsiya".Kuka ya fashe dashi tare da ɓuya abayan Sajnah,Dariya ce ta kufcewa Sajnah jin Wai zata yiwa Faruk duka,Harara Ainah ta galla Mata tare da faɗin"aidama duk ke kike ɓatasa yasa yake wani abin.Itade Sajnah Batace komai ba se Dariya take, Afusace Ainah ta ɗauko pillow tare da biyosu hannun Faruk Sajnah ta riƙe suka fice da gudu suna ƙyalmyala dariya.Ƙwafa Ainah tayi tare da buɗe siff Black trouser pencil ta ɗauka da top white me dogon hannun,se veil ta Sanya sosai kayan suka Mata kyau tare da fitar da shafe ɗin ta.Turarukanta masu daɗin ƙamshi ta feshe ilahirin jikinta dashi Jakarta dake rataye black ta ɗauka ta rataya kallon agogo tayi taga goma saura minti ashirin Ajiyar zuciya ta sauƙe ta fita.Afalon ta samesu har Granny se hira suke Suna ƙyalƙyala Dariya, Taɓe baki tayi tare da gallawa Faruk harara daga tsareta da ido,Tura baki yayi tare da lumshe idanu.Kallonsu tayi da faɗin"Ummu na tafi,"Adawo lafiya Ummu tace"tana maida hankalinta kan Faruk dake basu labari.

Seda ta fita bakin juntion Kafin ta samu Napep ta ɗauki Drop har asibitin ya kaita, Ahankali ta fita tare da sallamarsa tamkar kazar da ƙwai ya fashewa aciki haka take tafiya har ta isa haraban asibitin Kai tsaye office ɗin dake mallakinsa ta nufa.Hannu ta Sanya tayi Knowking,Daga ciki akace come in.Handle ɗin ƙofar ta murɗa tare da shiga duk da cewa safiya ce anma cikin office ɗin duhu kasancewar akwai hadari sannan winduna arufe,Wani irin laushi tajeji dake ratsa ƙafafunta kasancewar takalminta plat ne,Haske ne ya gauraye wajen,atake launin wutar blue ya bayyana Wanda be fiye haske ba.Babban hotonta guda ɗayan da wani irin wuta me Haske da ƙyalƙyali suka kewate,Ƙasan wajen wasu ja da fararen flowes ne masu kyan gaske cool music din _(I love you,I love I feel you,I feel ,I miss you,I miss you,satrey mujhabati.)_ ke tashi ga wani sanyayyan ƙamshi dana Ac daya haɗu.Wani irin lumshe manyan Idanunta tayi tare da ƙanƙame jikinta waje ɗaya,Cikin takun jarumataka ya ƙaraso daf da ita da sauri taja baya yasake matsowa baya ta Kuma ja Idanunta aƙasa Jin ta mannu da bango yasa tayi saurin ɗago kanta,Daf da ita ya ƙaraso tare dasa hannu ya dafa bangon ya zamana ya mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa,kawar da kanta gefe tayi Jin yanda numfashinsu ya gauraye waje ɗaya,hannu yasa ya ɗago fuskarta,Tare da tsura mata lumsassun Idanunsa,Runtse Manyan Idanunta tayi akasalance tace"Dan Allah Abdul kafita m arayuwata ka rungumi ƙaddara Sister Sajnah itace zaɓin mahaifanka itama Kaine zaɓinta wani irin ƙuna da baƙin ciki kake tunanin zataji azuciyarta alokacin da akace babu Kai acikin Rayuwarta??"...Shitttt ya faɗa yana ɗaura yatsansa akan warm lips ɗin da yasha golf yace"kamar yanda kike wannan tunanin haka nima nake yiwa kaina shin bakya tunanin wani irin halin zan kasance Alokacin da babu keba? hannunta ya ɗago ya ɗaura asetin ƙirjinsa yace"kiji yanda zuciyata ke bugawa ko wani sekon da soyayyar ki take bugawa,Idanunsa da suka tara ƙwalla yace"Dan Allah ki tausayawa rayuwata ki amshi soyayyata.Lumshe Ido tayi wani irin karyewa zuciyarta tayi tabbas gaskiya yake faɗa duba da yanda zuciyarsa ke bugawa,cikin rawan murya tace"am so sorry Abdul but bazan iya soyayya da mutumin da Yayata ke tsananin ƙaunarsa ba.Dur ƙasawa yayi Akan gwiwoyinsa ya rungume ƙugunta da faɗin"please help me Ainatyyyyyy My Life is Nothing without you I really love",Tsugunnawa Ainah tayi tare da ɗago kansa ido cikin Ido tace"Abdullllll ta wani irin jaa sunan kamar ranta ze fita.lumsassun Idanunsa da suka rine da tsantsar damuwa da tashin hankali ya zuba Mata.Kawar da kanta gefe tayi tace"kayi haƙuri kafita arayuwata domin bazan taɓa sonka ba tana gama faɗin"haka ta turesa daga jikinta ta miƙe,Wani irin miƙewa yayi da sauri ya fisgota jikinsa tare da haɗe bakinsu waje ɗaya yashiga kissing ɗinta, Afusace ta ingijesa daga jikinta tare da ɗaga hannu ta hanyarfa masa mari hagu da dama cikin gunjin kuma tace"Allah ya isa mugu!,macuci,"Hannu yasa ya dafa wajen da faɗin"Ko me Zaki min bazan fasa ƙaunarki ba I love you Ainatyyyyyy dede Lokacin da aka buɗe ƙofar, Alokaci daya suka juya,Wani irin zare ido Ainah tayi gani wacce ke tsaye aƙofar....






 AYI SHEARING SABODA ALLAH





 Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah ka Kai haske kabarinsa ya Allah kaji'kan duk kan musulman da suka rigamu gidan Gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani....







                ESHAA CE🤙