KAICO NAH

Page 10

by @sadisakhna



   🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵


       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......



🏵🏵🏵

...10....



Da safe da tashi gyara gidan tayi tsaf,ta hada musu break fast kafin ta shiga wanka.

Fitowa yazeed yayi daga dakinsa yana hamma,daga gani tashinsa kenan daga bacci,shanshana iska yake kaman anyiwa mage dangwalen nama jin kanshin abinci a gidan.

Share tanta ma yayi tareda nufar kitchen din don ya tabbatar da kansa,hakane kuwa dan idonsa tozali yayi da abincin.

Dakin sumayyah ya dawo ya nufah,wanda shigarsa dadai fitowar ta daga vandaki daure da towel a kugunta.

Kallo daya tayi masa kafin ta dauke kanta tayi gaban madubi.

Binta yayi can din cikin sanyin jiki cike da shakku.

Har tagama shafa manta da kuma duk abinda zatayi a gaban madubin,yazeed bai ce komaiba,duk da kuwa bai matsaba yana inda yake a tsaye,duk zuba mata idon da yayi tana kallonsa,ita mabatace komai ba har ta tashi ta nufi wardrobe wajen Kayan ta.

Doguwar riga ta dauko marar nauyi ta saka,kafin ta feshe jikinta da turare,hanyar waje ta nufah domin yin break fast.

Shima binta ya sakeyi a baya kaman jela har kitchen din.

Duk da cewa abincin ba iya cikinta tayi ba harda shi,amma da ta tashi diban abincin nata kawai ta saka ta dawo falo ta zauna.

Nasa abincin shima ya saka tareda zama a gefenta,kallo ma ta kunna ta bawa banza a jiyar sa,kaman dama ba'a halicceshi a wajenba.

Abinne yafara damunshi wanda hakan yasaka shi ya ture duk wani abu a zuciyarsa tareda cewa,

"Sumayyah maganar gaskiya badan bana sonki ba na zubar da cikin jikinki,kawai dan naga yanda kika fara wahala ne tun ba'aje ko ina ba,tsorona kar na rasaki shiyasa na yanke hukunci batareda saninki ba"

Ajiye cokalin hannunta tayi ta zuba masa ido har yagama fadin abinda yake zuciyarsa,

"Oh saboda ina wahala shiyasa ka zubarmin da ciki ba tare da saninaba,rai fah ka kashe amms kana zancen wai kar na wahala,wai ma so kake na yarda da abinda ka fada yazeed?"

"Nidai na fadamiki dalilina,sannan kiyi hakuri zance ya wuce"

Hmm dama da ka fadamin gaskiya kawai,cewa zaka ce banason haihuwa shiyasa na zubar,abinda zai sameki kuma ke kika sani".

Karar buga kofar da ake ne yasashi fasa bata amsa yayi hanyar kofar dan ganin waye,zaro ido yayi yana karewa wacce yagani kallo.

A hankali cikin karamar murya yace,

"Zully mai ya kawoki gidannan kuma?"

Jin ana magana kus kus yasa sumayyah daga murya daga dinnig tace,

"Waye ya zone naji shiru?"

Bangaje yazeed zully tayi tareda nufar cikin falon jin muryar sumayyah.

Akan kujera ta zauna tana tauna chewing gum kass kass,dora kafarta tayi daya kan daya da takalmanta masu matukar tsini.

Kallon kallo suke ita da sumayyah kowa na na tunanin abinda yake ranta,zully ce tayi saurin yin magana duk kuwa da yanda yazeed yake kifta mata ido akan tayi shiru da bakinta,wani kallon kayi kadan tayi masa tareda zan iska ta fara magana.

"Oh sorry golden girl Ni nasanki kece baki sanni ba,nayi mamaki da aka cemin wai wannan mutumin kika aura,nasan baki sanni ba tunda ban taba zuwa gidanba,sunana Zully.

Nazo karbar kudina ne a wajen mijinki,dan sarai yasan duk kawana daya dani dubu hamsin ne amma haka yayi,dan haka kudina nazo karba tun kafin naji a salansa.

Dama daga uban Abdurrahim yake samun kudi to shima kuma ya mutu jiya da daddare,dayake ba gadonsa ne dashi ba to a ban kudina zuwamin da daddare ya kare kuma sai a nemi wani sarkin"

Wani zaro ido sumayyah tayi,sai a yamzu abubuwa suke zuwa mata a daidai,wato zaman daren dayake a wajen wannan bushashshiyar yake kenan?

Masifar korar kunya yazeed ya fara yana inda inda,

"Ke zully banason walakanci,ya zakizo har cikin gidana ki cimin mutunci"

"Oh dama kanada mutuncin ne da za'a ci,ai wallahi wacce ta zauna dakai tayi asara,kuma kudina dole ka bani dan baka debi romon banza ba,lokacin dakake yimin ihu da daddare naga har wannan gidam hayar ma kabani shi,ko taya zaka bani gidan wani ban saniba "

Shiru yazeed yayi ya kyale zully ganin tana ta kara tona masa asirin dayake tunanin ya binne.

Ita kuwa sumayyah kasa cigaba tayi da sauraren maganganun nasu dasuke tamkar dafi a cikin zuciyarta,dakin ta ta shige ta rufo kofar gifff.

Sun dad'e suna magana,tana jinsu har kuma daga baya taji babu motsin komai,abubuwan da suke fadane ya dawo mata cikin ranta.

Yanzu mai ta ragi yazeed har da zai tsallaketa ya tafi wajen wata Yana biyanta dubu hamsin dan ya kwanta da ita,abinda yafi girgizata ma shine,kenan Alhj Sulaiman ba shine mahaifinsa ba,to su waye iyayensa?.

Zumbur ta tashi ta mike ta fito daga dakin zuwa falo,saidai wayam daga wajen babu kowa,hakan bai mata ba ta koma ta dakko mayafinta tareda tarar mai napep ya kaita gidan Alhaji Sulaiman din.

Tun daga bakin kofar gidan taga mutane sun cika fal,maganar mutuwar alhj Sulaiman da zully ta fadane ya dawo mata cikin kai.

Gyara mayafin tayi ta sanda zuwa cikin gidan kaman wata munafuka,wuce mutane tayi tayi har ta isa sashen hajiya Saratu.

A dakin ta tasameta ita da yan uwanta suna zaune susha hijabi da carbi kaman malmai.

Tsugunnawa tayi a gefe ta gama gaishesu,hajiya saratu kam da kyar ta amsa sai hararar sumayyah takeyi,magana tayi bayan ta amsa gaisuwar wanda iya sumayyah ce taji abinda ta fada,

"Tare kuka zo da yazeed ne?"

"Ahah"

Shine amsar da sumayyah ta bawa hajiya saratu cikin gaskiyar ta,dan itama zuwa lokacin haushinsa takeji kaman ta kasheshi.

Ta dan dade a zaune kafin ta tashi xata tafi,.

Hajiyah saratu ce tasake kallonta tace,

"Hmmmm duk abinda mutum yake dole Allah zai kawo iyakarsa,kicewa mijinki munga sakayyar dayayiwa alhaji,kuma baici bulus ba dole tunda yaci muzuru said yayi aman gashinsa"

Tana gama fadar hakan tacigaba da jan carbinta kaman ba ita ba.ita kuwa sumayya da aka fadawa hakan juyawa tayi fita daga dakin.

Komawa gidannata tayi,zuwa yanzu abubuwan da suka faru a yaudin sun kullemata kai dayawa.

Kan kujera ta fada ta kwanta bacci ya dauke ta .

Ji tayi ana bubbuga pillown kujerar da take kwance,wanda hakan yasaka ta tashi a firgice tana kallon yazeed dayake tsaye a kanta.

"Kee ki tashi,har wani bacci ma kika samu yi a wannan halin da muke ciki,kishiga ciki ki tattaro kayanki kaff,dan magriba tanayi zamu bar anguwar nan musan inda dare yayi mana"

"Wane irin mubar anguwa ina zamu to?,wai tukunna ma mai ya farune,kaje wajen gaisuwar kuwa"

"Wane gidan gaisuwa ana yi miki zancen neman mafita,to kinji nace ki tashi mutafi koh,idan kika ki wlh tafiya zanyi na barki,gobe idan mai gidan yazo korarki sai kisan yanda zakiyi toh"

"Mai kake nufi dama ba gidanka bane nan din?,yazeed anya kuwa kai mutumne ma,a iya safiyar nan naji abubuwa dayawa da suka wuce tunanina akanka"

"Hmm bakiji komai ba ma,ke bariki ji inyi miki mai kankat,daga nan gidan mu zan wuce dayake can farkon gari,idan kinga zaki bini kizo mutafi a can zakiji komai,idan kuma gidan iyayenki zaki tafi to,wanda nasan baki isa yin hakan ba,dan inada labarin duk abinda ya faru.

Kije ki hada kayanki na sawa,dan shine kadai mallakinki a cikin gidannan,sauran shirgin nayiwa mai gidan kudinsu ya biyani na karbi kudina,dan haka ki shirya motar katako ta abokin babana tana zuwa wucewa zamu hau muyi gida"

Daga haka ya wuce dakinsa yasake barta a duhun daya saba barinta akan sanin lamarin mai yake faruwa.

Itama ganin da gaske yakene yasata zuwa dakinnta ta hada dukkanin kayanta da ta san natane a akwatinta tsaf.

Idonta tabb da hawaye take ganin dakinnta lokacin da yazeed yace ta fito su tafi,yanzu kuma ina zata cigaba da rayuwa bata saniba,idan yankata zayyi ma dole ta bishi tunda bata da inda zataje,gashi wani abun takaicin ma babu dama ta fadawa wani dan uwanta inda zataje,saboda tasan babu wanda zai saurareta.

Jawo akwatin tayi cikin sanyin jiki tabi Bayan yazeed wanda dama ya dade da fita daga cikin gidan,ita yake jira ta fito ya rufewa mai gidan abinsa yakara gaba.

Ta gama fitowa kuwa ya garkama masa kwado tareda jan akwatinsa zuwa bakin titi,dama sunyi magana da abokin babannasa inda zai samesu.

Zare ido sumayyah tayi tana kallom motar da zasu shiga din,babbar motace mai irin ta diban kayannan duk da rakwarkwace.

Yazeed yana kallon yanayinta amma ya shareta,saima zefa akwatinsa da yayi ciki tareda shima fadawa bodin motar,hannu ya miko mata ta bashi akwatim ta kafin itama ta miko hannunta ya zawota cikin motar.

Bayan an fara tafiyane sumayyah ta kalli yazeed tareda cewa,

Yanzu saboda Allah akan ka biya mana kudin mota shine ka hawo damu nan?"

"Banni da kudin mota,in inada shi ma bana hawa mota bane"

Jin irin amsar daya bata itama said tayi shiru bata sake cewa komai ba daga haka.

Ana kiran isha suka isa inda yazeed ya kira da sunan gidannasu.

Wata anguwa ce mai matukar matsi da kwata,ga tako ina kashin dabbobine akan hanya,bakin hanya aka saukesu saboda motar bazata shigo ba,haka suka dora akwatina akai suka kutso har zuwa gidan su yazeed din.

Inda daga yazeed din ya shiga ne abin yabata tsoro bama mamaki ba,dan wani gidane da baifi gida uku yafi a anguwar kyau ba,ko kofa babu a kofar gidan sai wani buhu da aka daura.

Tsakar gidan duk kwata dasu agwagi da awaki harda kare.

Takawar farko daga shiga gidan sumayyah tajita a cikin wani ruwa,yazeed ta kallah tareda cewa,

"Yazeed inaga ruwane a tsakar gidan gashi na saka kafata a ciki"

"Ba ruwa bane kwata ce kika saka kafarki a ciki da bandaki,dan ta wajen take wucewa zuwa waje"

Wani ihu sumayyah tasaka jin maganar da yazeed din yayi,dan anguwar dilim take babu alamar hasken wutar nepa.

Mutanen gidanne suka fara fitowa dan ganin wanene a gidan.

Yaran gidan ne suka fara ihu suna cewa,

"Mutari! Mutari!! Mutari!!! Lah inna mutari ne yadawo wlh,harda wata mata ya dawo ma"

Wacce aka kira da inna ce ta fito daga wani daki mai kama da dakin mahaukaciya,gashi ginin ya rube kaman zai zube.

"Lah ahee kuwa mutari ne,saukar yauhe haka,hee yau kaga damar zuwa inda muke,wai ana gari daya dan muna can gefe saidai muji labarim mai yake faruwa,toh yanzu daka zo da daddare fadamun mai ya faru,dan nasan ba lafiya ce tasa muka ganka,to bari kaji na fada maka indai wai zuwa kayi da matar dakace ka aura ku zauna mana to ka sanja shawara,dan y'ay'an ka ma daka tafi ka barmin sun iheni basai ka kawomim wasu ba.

Saida nace karka saki matarka ka saketa wai kai ka tafi neman kudi,hinee yanzu zaka sake dawomin da wata matar na rike maka,to ko ubanka ma Audu bai isa ba bare kai eheee"

........Toh fah ya kukaji😀😀😀😀




🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵