KAICO NAH

Page 25

by @sadisakhna



   🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵


       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......



DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER


Wattpad:SAKHNA03


🏵🏵🏵

...25....



 Shirye shiryen tafiya wajen arabian day akeyi,Muhibba sai kokarin saka kayan event din take amma sumayyah tana zaune ko alamar shiri batayi.

Muhibba ce ta juyo ta kalleta tareda cewa,

"Aunty sumayyah ya naga bakya shirin tafiya event din har yanzu,bayan kuma ga kayanki nan na ajiyemiki a gabanki"

"Eh nagansu kawai inaga bazanje bane Muhibba,dan bansan yanda zanyi a wajen ba,gashi dole zanga kwayena wanda maryam zata gayyata,beside ma banason haduwa da maryam,banshirya hakan ba yanzu Muhibba"

"Karki ce haka anty sumayya,bai kamata ki dunga avoiding din ta ba,tunda kinsan komin daren dadewa dole zaku hadu da ita,so ni inaga kawai ki fuskanceta kawai"

"Hmm abinne har yanzu yake tsaye a raina shiyasa,okay shikenan bari na tashi na shirya,amma kawai ki tafi abinki ina nan zuwa idan na shirya,karna bata miki lokaci dayawa"

"Okay barina nayi gaba zamu tafi da kawayena "

Daga haka Muhibba ta fita tana baza uban kamshi ansha sabin kaya.


Bayan tafita sumayyah juyawa tayi ta kalli kayan dayake gefenta,

"Hmm Ni Kayan ma zasu yimin dadai ne,wannan uban ramata haka,baridai na saka naje,kona dan rage kadaici"

Daga haka sumayyah ta dauki kayan tasaka,dan dama ta yi wanka tun dazu,kwalliyah tayi sama sama,ta saka mayafi fari akan purple din yadin,kayan sun amshi jikinta kam ba laifi,saidai har yanzu wannan ba sumayyan da bace,duk da yanzu kokari take ta kawar da waccan sumayyan a ranta.

Sakkowa tayi daga dakinnata zuwa harabar gidan,dukka motocin yawanci sun tafi,sai wata homa kadai wacce zata debi wasu mutanen.

Babu wani bata lokaci na neman mota mai aji sumayyah tashiga ciki aka tafi da ita.

Wajen babu wani nisa daga gida,shiyasa basu wani dadeba suka isa.

Bayan sun isa ne sumayyah ta sauka ta gyagygyara rigar ta data dan fara squizing saboda zaman motar.

Hanyar hall din ta nufah zuciyarta tana bugawa,amma takawar da hakan a zuciyarta tashiga,dan idan bata saba da irin wannan abubuwan ba a sabuwar rayuwarta sai yaushe zata saba.

Sanda ta isa amarya da angon basu shigoba,sai mutane kawai dasuke ta kai kawo kowa ya sha kayan larabawa ,abaya ta mata dakuma jallabiya ta maza.

Saidai wasu kaman sumayyah doguwar riga suka sa sai gyalen da aka masa rolling.

Hanyar da taga Muhibba tana zaune tabi domin zuwa inda take.

Wasu matane taji suna magana a baynta lokacin data wulgasu,kuma da alama maganarta sukeyi.

"Eh fah ai sha'anin duniya saidai a barshi,kigafah golden girl ce wacce ko malamai shakkarta suke amma kalleta yanzu kaman mujiya a cikin tsuntsaye,Allah sarki Ahmad ana gobe daurin aure amma taki aurensa,gashinan ya auri kawarta suna zuba sosayyar su,naji ance har guduwa tayi daga gida akan bazata aureshiba"

"Guduwa kuma,akace aure tayi ina koh,wani dan mai kudi,ya kulleta a gidan baci basha zayyi tsafi da ita dakyar ta samu ta fito"

"Lah hhhh kawata kice Allah tsafi kuma"

"Kwarai kuwa,kuma in fadamiki daga majiya mai karfi naji wannan zancen,hmmm ai kedai bari,inaga har yanzu ma batta da lafiya fah"

Sumayyah kasa jure maganganunnasu tayi,wanda hakan yasa ta koma da baya zuwa inda suke tsaye,dan dama rashin hakuri a jininta yake,saidai ace halinta na tsiya wannan kuwa daban.

Shuru sukayi suna inda inda ganin yanda sumayyah ta tsaya akansu tana kallon idanuwan kowacce a cikinsu.

"Ahh sumayyah dama kece,bamu ganki ba ai yagida dakuma abinda yafaru"

"Tambaya kike nafada miki gaskiyar abinda ya faru bayan karyar dakika shuka musu?"

"Ahah golden girl bahaka bane kawai......."

"Karki sake kirana da golden,kalar fata tace ba irin takowa ba komai,kuma so nake ki fadamin waye ya fadamiki cewar tsafi ake dani,ki fadamin a inda kikaji maganar nan yanzu,ko kuma maganar takai inda bakya zato bakya tsammani"

Jikinta ne yafara rawa tana karkarwa kaman mazari,idan ita kanta shaidace ta halin sumayyah lokacin suna makaranta.

"Fauziyya jiranki nake ki fadamin a ina Kika ji wannan maganar ?"

Suna cikin hakanne Muhibba tazo wajen dan ganin abinda yake faruwa,zuwa sannan har hankalin mutane yafara kaiwa kan abinda yake faruwa.

Saurin matsowa Muhibba tayi tareda jan sumayyah wacce take fincike hannunta a na Muhibba n.

"Muhibba kyaleni ,saita fadamin inda taji,ba ita munafurcine aikinta ba,mutane bazasu yi harkar gabansu ba saita gaban wani,ki banni da ita "

"Please aunty sumayyah kidaina mana kiyi hakuri,bakya ganin yanda mutane suke kallonku,dan Allah ki kyaleta ba danniba"

Shuru sumayyah tayi tareda bin bayan Muhibba n,har suka wice kuwa tana harar fauxiyan kaman idonta zai fado.

Wani table suka samu suka zauna ita da muhibban,wacce ta juba mata ruwan sanyi tana mikamata,karba tayi tareda shan kadan kafin ta ajiye.

Har ta bude baki zatayi magana sai kuma suka jiyo sautin shigowar ango da amaryarsa,kawayen amaryane wasu a gabansu wasu a baynsu sunsha kaya iri daya,tabbas kam zancen da yah Mu'azzam yayi nacewar kyakykyawa ce hakane,dan ba laifi sai mashaallah.

Jallabiya ce a jikinsa baka anyi mata adon golden,yayinda amaryar kuma take sanye da wata doguwar riga baka anyi mata rolling golden.

Rigar har kasa ta zuba tana jan kasa,inda kawayenta na baya kuma suke rike da rigar ta baya.

(Balaifi sunyi kyau kam,saidai a ce roga taje har kasa tana sharar kasa babu kyau,sannan pre wedding da kuma event da mata da maza yanzu sukeyi kafin aure shima ba wasu bakyau,saidai muce Allah yasa a gyara,dan ba al'adarmu bace mu hausawa)

Bayan sun wucene an gama hayaniyar zuwan amaryah kuma saiga wasu couple din ma sun bayyano,wani ihunne yah kara tashi ganin matching couple din da suka shigo,hankalin su sumayyah ne itada Muhibba ya koma kansu,banu karya kam sunyi kyau sosai,kowa ya gansu sai yaji sun bashi sha'awa.

Ahmad ne yasha jallabiya baka mai adon blue,yayinda ita kuma maryam ta saka itama doguwar riga baka ta yafa mayafi blue,hannunsa yana sakale da nata kaman wani zai fixgeta a cikin taron.

Fuskarsu dauke da murmushi sunayiwa kowa barka,bayan amarya da ango to hankalin kkwa yana kansu.

Tunda suke shigo duk inda suka gifta idon sumayyah yana kansu,murmushi tayi tareda cewa mashaallah,har cikin ranta take nadamar abinda tayiwa wannan bayin allahn a rayuwarta,sune wanda suka nuna mata so tsakani da Allah bayan yan uwanta,amma haka ta watsa musu kasa a ido ta nuna musu si bakowa bane a wajenta.

Hawayene ya zubo acikin idonta wanda tayi saurin daukeshi kafin kowa ya gani.

Kowa hidimar gabansa ya cigaba dayi,musaman ma maryam,wacce dama ita ce tayi kwangilar hada wajen,sai zagayawa take tana dubawa,shikuma Ahmad ya hau sama wajen kujerar babban abokim ango.

Wata wakar larabawa aka saka lokacin da kowa ya tashi zayyyi serving kansa na abincin dayake wajen,dayake abune da aka yishi da tsari kowa a hankali yake yin komai.

Tunda sumayyah tayi fada da fauziyya dasu Muhibba take wajenta a zaune,dan a ganinta sumayyah tunda ba wanda take kulawa a wajen zata iya shiga cikin kadaici,wannam ne dalilin daya saka ta zauna duk da tanason zuwa wajen nata abokan.

Lura da hakan da sumayyah tayine yasa tace mata.

"Muhibba yanaga kina zaune kina leke leke ne,idan wani kike nema kije mana "

"Ahh aunty sumayyah karna barki a wajen ke kadaine babu kowa shiyasa"

"Jim in yarinya yaushe na zama babysitter a wajenki,lallai kawainana nenki yayi yawa Muhibba,tashi kije idan wajen wasu zakije bazanso ki bata shagalinki da farin cikinki a dalilina ba,karki damu yanzi zanje wajen can na karbo snack ma"

Tana gama fadan hakan Muhibba ta tashi ta tayi wani wajen,murmushi tayi kafin itama tanufi wajen da abincin yake.

Tana cikin deba ne ta kai spoon taji wani spoon din wani ya saka akan nata cikin rashin sani,dagowa tayi dan ganin wanene,mamaki tayi ganin sun hada ido da maryam,itama mamakin tayi tareda saurin sakin murmushi.

"Lahh Sumy Ashe kece,Allah yayi zami hadu ne ,ya gida dasu hajiyah mama?"

Mamakin fara'ar da maryam take mata tayi,amma ta basar tace,

"Lafiya kalau ,maryam kwana biyu ya ykk yah gidanki"

"Gida alhamdulillah,tunda mun hadu kuma kin gama diban muje table mu tattauna koh"

Har sumayyah zata zame ta tafi sai kuma taga rashin dacewar hakan,babu dadi kayiwa mutum abu kuma yanuna maka ya wuce kaikuma ka ja baya dashi.

Hakanne yasa sumayyah bin bayan maryam din suka samu wani table bakowa suka zauna.

Bayan sun zauna kowa rike yakeda cokali amma yakasa kaiwa abincim dake gabansa cikin bakinsa,saboda kowanne a cikinsa yana dauke da maganganun dayake son tattaunawa da dayan.

Maryam ce tayi saurin fara magana cikin yanayin rashin jin dadi.

"Sumy sai kuma naji abinda ya fari,hakika banji dadi ba kuma naji haushin yazeed sosai,atleast kodan zaban sa dakikayi kika nuna masa so bai kamata yayi miki hakaba"

"karkiji haushinsa maryam,wacce take gabanki zaki ji haushi ba wanda bai cancanta kiji haushinsa ba,banyi mamakin halin ki ba maryam dakika kulani,saboda nasan haka kike da manta abinda aka miki,amma da watace bazata ko kalli inuwata bama"

Hannun sumayyan maryam ta riko cikin yanayi na kulawa tareda cewa,

"Idan har tsawon lokaci kina tunanin inajin haushinki to kinyi kuskure sumayyah,kuma baki gama sanin halin kawartaki ba,nasan ba haka kawai kikayi ba,makauniyar soyayya ce ta debeki,wadda kamata yayi a fahimceki kuma a tausaya miki,sumayyah ni nasani ba'a tursasa mutum yayi so sannan bayin kansa bane ya nuna kiyayya ga wani,jin hakan yake a ransa dam babu yanda zayyi,ni banga lafinki ba tunda ba kisa kikayi ba,kawai kinki wanda bakyaso ne kawai"

Saurin buga table din sumayyah tayi hawaye yana bin kumatunta,takasa yin magana hakan yasa dole ta buga table din saboda Maryam takula da sabon da take fada ta daina.

Bayan tayi shiru ne sumayyah tafara magana cikin kasa kasan murya,

"Ya isa haka ya isheki maryam wannan sabon dakikeyi,wanda gani nake kaman zunubi kike kwasawa kanki,wane irin haline dake,wanda ba iya rashin jin haushina kike ba hadda ganin banda laifi? Wannan kuskurene wanda ya harmata a gareni na cigaba da jinsa maryam.

Nayi niyyar neman yafiyarki a bisa kuskuren danayi miki,saidai hakan na kula bazayyi tasiri a wajen ki ba,tsawon lokaci na sakaki auren wanda baya cikin agendarki,dam ma hakan baya damuna sosai tunda nasan Yana kukada ke sosai,da abin sai yayi min yawa.

Amma ke cewa kike banda laifi?,zan tafi maryam bazan iya cigana dajin abinda kike cewa ba,idan har kin gane na cuceki toh saina baki hakuri dakuma neman yafiyarki,amma yanzu kam hakan bazai yi tasiri ba"

 Daga haka sumayyah tashare hawayen fuskarta tareda kokarim hadiye abinda yake cikin ranta tabar maryam a zaune itama cikinnata jimamin.



🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵