Page 27
by @sadisakhna
🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......
DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER
Wattpad:SAKHNA03
🏵🏵🏵
...27....
"Banji mai kikace ba sumayyah anya kuwa najiki dakyau?"
"Eh abbah hakane,yah Ahmad na fitar a matsayin miji"
"Miji Ahmad kike nufi Ahmad dai wanda na daurawa aure da maryam"
"Eh abbah shine,........shine na fitar a matsayin wanda zan aura"
"Kuma shidim ne ya fadamiki zai aureki?"
"ahah abba bai san zancen ba nice dai na fitar dashi"
"anya kuwa sumayyah baki samu tabin hankali ba kuwa,kimsam mai kike fada kuwa,Ahmad zaki aura? Lallai ki farka daga mafarkin dakikeyi,wato kinga Allah ya rufa masa asiri ya auri mace tagari wacce tasan darajar nagaba da ita mai tarbiyyya,shine bari ki shiga cikinsu ki tarwatsasu koh,to baki isa ba,Ahmad da kika sani a da babu shiyanzu,wannan Ahmad din yafi karfinki ya wuce sa'ank,kuma ban lamunta ki shiga cikin zuri'arsa ki dagula ta.
Idan dan kin rasa wanda zaki kawone yasa kika fadi haka to aikinki yayi kyau,na baki nan da sati biyu kiyi nazarin maganarki kuma ki fiddah wanda zaki aura,tashi ki bani waje anan"
Ta shi sumayyah tayi kafafunta suna karkarwa tafito daga dakin abban,a bakin bangon dakin ta wake ta jingina tareda da dafe kanta dayake barazanar fashewa.
Wannan masifah wace iri ce,a rayuwar nan da wanne zataji,wai uban daya haifeta ne yake kiranta da masifa mai tarwatsa zaman lafiya idan ta shiga wani waje.
Wane abuse ta aikata haka daya gagara daina bibuyarta,anya kuwa zata iya jurewa.
Tafi kusan minti biyar a wajen kafin ta samu ta isa dakinta.key ta sakawa dakin ta zube akan gado tana fashewa da kuka,dan abinda abban yafada mata sunyi mungun tsayawa a cikin zuciyarta.
Hajiyah mama tana zaune akan gado tana gyara kayan su farouq tasuka zo suka cire Muhibba ta wanke musu ta kawo mata.
Daga kai tayi taga abbah ya shigo dakinnata ba cikin yanayin nutsuwa ba,abinne yabata mamaki,dan sai lokaci ziwa lokaci abbah yake shigowa dakinnata,saida kwakkwaran dalili tukunna.
Zama yayi aka kujerar dake dakin kafim yace,
"Maman yara kinji kuwa abinda yarinyar nan ta fadamin yanzu dana tambayeta akan waye ta fitar a matsayin miji?"
"Mai tace maka?"
"Hmm Wai Ahmad ta fitar a matsayin mijifah,kijimin wata magana mai rikita tunani"
Razana hajiyah mama tayi saidai bakaman yanda abbah yayi ba dazun.
"Haka tace,gaskiya abin da daure kai,to kodai dan ka tambayeta a gaggawane shiyasa ta fadi hakan dan babu wanda zata ce,inaga ka jinkirta mata kadan tayi tunani"
"Nima hakan na fada,shiyasa na ce nabata nan da sati biyu,amma zancen Ahmad wannan babu shi Kwata kwata,inbaso take ta maidani mutumin banzaba "
Daga haka abbah suka cigaba da tattaunawa da hajjya mama akan al'amarin har zuwa wani lokaci.
Ita kuwa sumayyah a yanda ta takwanta tana kuka haka bacci ya dauketa.
Da safe bata tashi da wuri ba,gashi kuma ranar aiknta ce,amma shiru bata fito ba,ganin hakane yasa su ladidi yin komai da komai,dan sun sa akwai abinda yafaru,dan saida dalili yanzu sumayyah take zama a daki da safe.
A wajen cin abinci hajiya mama hajiya mama take fadawa Muhibba abinda sumayyah tace a wajen abban,lokacin da ta dameta akan mai yasamu sumayyan taki fitowa,itama mamakinne yakamata har tana rike baki,
"Tabb hajiyah mama wanna bakaramin al'amari bane,taya sumayyah zata iyah kishi da maryam a yanzu,rannan fah ina ganin yanda yah Ahmad ya yi kaman bai ganta ba lokacin daya zo."
"Hmm nima nasan abinnan babbane,saidai bansan menene dalilin sumayyah na ambaton sunan Ahmad din ba,duk da tafi kowa sanin ya yakeji akanta yanzu,mudai idone namu yanzu kawai,Allah ya takaita kawai"
Saida aka shiga kawana na uku amma sumayyah ta daina sakewa da kowa tun abinda ya faru,yanzu takoma tamkar lokacin data dawo gidan,tsohon tabon yadawo danye shakaff,sai ta shafe lokaci bata sakkoba,shima abinci take zuwa dauka,duk yanda Muhibba tayi da ita ta sake da ita abin ya faskara,kullum idanuwanta a kumbure alamar tayi kuka ta koshi.
Wasa wasa magana ta bazu na cewar sumayyah tace Ahmad zata aura,shikansa uban gayyar yaji labarin,ranar bakaramin bacin rai yajiba,har saida maryam ta tabbatar ransa ya baci,lallai ma ta raina masa hankali,mai ta daukeshi,abin wasan ta wanda ko kuma riga,wanda zata saka lokacin da take some ta cire lokacin da bataso.
Yah mu'azzam ma dayaji labarin har gida yazo yana ta fada,hajiyah mama tana zaune a kujera tana jinsa.
"Hajiyah mama kinji abinda yarinyar nan ta fada amma ba'a dau mataki ba,dan tsabar rainin hankali har tana da bakin kiran sunan Ahmad akan bakinta bare har tace shi zata aura,taje angama wajigata an maidata second handa shine za'akawo masa ya kwasa,to wlh bazai yiyuba,koni nan saina dau mataki akan hakan.
Saboda batasan halin daya shigaba lokacin data watsa masa kasa a ido koh,nine shaidar yanda yayi ta fama da soyayyar ta ransa kafin ya warke,shine zata kara lalubowa takarayimasa tabon dazai kasheshi,toh wlh ina ji ina gani bazan bari hakan ta faruba,wannan ai zalunci ne,wato bari ta wargaza musu gida idan ta shiga koh"
Duk maganar dayake yana daga murya cikin bacin rai hajiya mama tana jinsa,harda sumayyah wacce ta sakko ajiye kwanon abincinta.
Hawayene yake zuba a idonta kaman famfo jin furucin da dan uwanta yake akanta,kuma ma wani abin takaicin gaskiya yake fada,idan akwai third hand ma to itace,dan a ragwabe take taciki da ta wajen ta.
Idonsa ne yakai kanta inda take tsaye a hanyar sakkowa daga kan benin kaman wacce aka sassaka da itace,
Nunata yayi da hannu yana murzasu kafin yafara cews,
"Mai kike nufi da zaki auri Ahmad,wai so kike ki samu farinciki su ki tarwatsasu koh,to barkiji na fadamiki soyayyar dayake yi miki a bayane amma ba yanzu ba......."
"Nasani nafi kowa sanin baya bukatata kuma bazai taba ba,hasalima nasan idan aka bashi bindiga ya harbe wasu mutane nice ta farko,sannan ba farinciki zan samu a gidan Ahmad ba,bakinciki zan samu,kuma ba tarwatsasu zanyi ba,dan rayuwata nata shafi Ahmad bama bare maryam,zan tafi inda yadace na zauna ne kawai,saboda wata magana da aka fadamin akan abinda nayi,ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai faru da abokinka,zaka sameshi cikin koshin lafiya koda ina gidan,saboda zanyi kokarim zama invisible a gidan,dan haka abinda yake cikin rayuwata bai shafeka ba yah mu'azzam,kaji da taka rayuwar ma "
"Ke Ni........."
"Ya isa haka mu'azzam,tunda kaji mai tace sai hankalin ka ya kwanta,babu abinda zai samu abokinka,iyah ita abin zai shafa,sai kaje kayi baccin dadi a gidanka,inkuma so kake kasake cewa wani abu dayafi wannan to katsya na Shiga dakina sai ka cigaba da fada,danni kam na kai makurar abinda zan iya ji"
Tashi hajiya mama tayi tai hanyar dakinta,duk da tana kokarin boye abinda yake ranta amma sun riga sun rubutu akan fuskarta,na bacin ran abinda yah mu'azzam din ya fada.
Jikinsa ne yayi sanyi daya tuna koba komai Y'a yake aibatawa a gaban uwarta,duk da bashida da tukunna amma yasan abin ba sauki,tun kafin yasake cewa komai har hajiya mama tabar wajen.
Hannun sa ya buga a cikin dayan yana fuszar da iska,bacin ya kaishi ga kwafsawa,gashi har mahaifiyar sa ranta ya baci.
Itakuwa sumayyah ta dade dama da komawa dakinta.
Salma ce tazo gidan su sumayyan,tun a bakin kofah ta hadu da Muhibba zata tafi makaranta,
"Aunty salma kece a gidan"
"Nice wlh ya gida dasu hajiyah mama,lecture rana ne dake ne?
"Eh fah kuma zankai project ne nayi ma latti,hajiya lafiya kalau bata nan ma ta tafi gidan anty hajara ta haihu,sai gobe zata dawo,dayake ta dan samu matsalane"
"Ayyah to Allah ya sawwake,sumayyah tana ciki?ko tare suka tafi"
"Ahah Ita tana nan,dazu ma naga ta sakko tayi dauki abinci,ba tare suka tafi ba"
Daga haka Muhibba ta wuce makaranta ita kuma ta shige cikin gidan wajen sumayyan.
A bakin gado ta sameta a zaune tasaka abinci tana kallo,ita bata ciba ita bata ajiye ba kaman kuma mai tunanin wani abu,maganar da salma tayine yasata zabura,dan bataki shigowarta ba sai magamarta taji kawai.
Dariyah salma tasaka lokacin da taga dagaske sumayyah ta tsorata sosai,itama murmushi tafara yisai kuma ta dan bata rai ganin dariyar da salma take harda rike ciki.
"Allah salma ke munguwace menene na tsoratanin toh"
"Sorry naga kinyi shirune ko motsin kirki bakyayi,anyway yakk ya gida"
"Ba lafiya ba salma,zancen serious kenan,nasan kinji abinda yake faruwa koh,dan abin yabaza ko ina sosai"
"Wane abune yafaru,banji ba ,kinsan nace miki bana garin jiya ma dawo fah da daddare,mai yake faruwa"
"Hmm mm ai salma kedai bari kawai,lokacin dana kiraki dama so nake mu tattuna zancen dake,abbah ya kirani akan na fada masa wamda nafitar a matsayin miji"
"To ya akayi wa kika fitar,ko kin hadu da wanine kai,,
Ahah ban hadu da kowa ba,cewa nace masa Ahmad na fitar shi zan aura"
"What!!!! Do you know what you are saying sumayyah?"
"Yes am sure"
"Menene dalikinki na fitar da Ahmad sumayyah,koda baki da kowa dazaki fitar ai saiki fada masa,nasan koda zayyi fada amma zai karamiki lokaci"
"Yakamin lokaci salma,saidai karin lokacin na banzane,dan koda yasake tambayata nan da satin haka zan sake fada"
"To miyasa,kinsan fah yanzu baya sonki,nasan kinfi kowa sanin haka,sannan kawarki fah yake aure ,yamzu ita yake so ,kina ganin xaki iya zama a tsakaninsu kuwa sumayya?"
"Babu abinda ya dameni da soyayyar sa gareta,zancen gaskiya zan fadamiki salma duk da nasan ba lallai ki yarda ba amma har yanzu bana son Ahmad a zuciyata,har yanzu bansam so ba,mai dauke da kauna ba,so nasani mai dauke da soyayya wamda nayiwa mutari,amma shi Ahmad kiyyaya nayi masa wanda yanzu banason mutari sannna bana kin Ahmad,kauna kam har yanzu babu wanda nake yiwa"
"Wai abinnaki akwai daure kai sumayyah,to yanzu auren daxakiyi na menene to a yanzu,tinda kince ba sonsa kike ba?"
"Nagyara abinda nayine salma,koda wani yazo bazan iya aurensa,saboda bazai iya tayani gyara abinda nayi ba koda kuwa komai ya wuce,Ahmad kadai wanda zai iya tayani gyara abinda nayi a baya,shi din ma kuma har yanxu bansan shin zai tayani guaran ko akasin haka,abinda nasansi shine aurensa matakine nafara maida komai inda yake,kkda kuwa nasan hakan yanada matukar wuyah a gareni"
"Ni gaskiya ban yadda da wannan zamcennaki ba,taya zakice wani bazai iya tayaki gyara abinda kikayi ba sumayyah,ni ina ganin sai kinfi gyara komai idan wani kika aura akan auren Ahmad"
"Bazaki gane bane salma,amma "ta inda aka hau dole tanan ake sauka,koda mutum yabi wata hanyar dole zai dawo ta inda ya hau"
Ta inda nayi barnar salma ta nan zan iya gyarata,koda kuwa hakan zai min wuyah amma bazan gazaba saina cimma ga nasara,saidai idan bana numfashi"
............Toh fah su yasriba sun yunkuro............😀😀😀😀
🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵