KAICO NAH

Page 29

by @sadisakhna



   🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵


       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......



DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER


Wattpad:SAKHNA03


🏵🏵🏵

...29....





Tafiya suke zuwa wajen da yayi parking din motarsa,ita dai binsa take batareda tace komai ba bare kumashi.

Motar ya Shiga ya bawa wuta tukunna kafin ya tsaya yayi shiru,shi bai tafi ba shi bai cewa sumayyah ta shigo ba .

Ganin hakanne yasata kama murfin motar a hankali ta bude ta shiga.

Tafiya suka farayi akan hanya zuwa gidan su sumayyan,ko kallon inda take bayyi ba har suka dan bawa asibitin tazara kadan,har suna shirin kawai unguwar su sumayyan.

Kallon window take yi tunda aka fara tafiyar bata kalleshi,dan ita kanta a takure take da zaman motar tasa,jin datayi motar tatsaya ne yasata juyawa ta kalleshi,har sannan kan hanya yake kallo amma kuma fuskarsa a daure kaman bakin hadari a tsakiyar damina,kumatun sa har rawa yake kaman an taba kububuwa a cakin raminta.

Duk da hakan yabata tsoro amma bata ce komai ba sannan bata dauke idonta daga kallonsa ba,juyiwa yayi yana kallon cikin idonta dana sa idin wanda sukayi jawur kaman gauta.

"Mekika daukeni sumayyah,kin maidani abin wasan ki daxaki bawa wahala sanda kike so,menene dalilinki na son aurena,wane irin mungun nufi kika boye a zuciyarki kike son ki cutar damu ta hanyar shiga cikin rayuwarmu nida matata.

Cutar da kika mana a baya bai ishaeki ba saikin sake yimana wata cutar,yanzu kuma so kike ki kashemu koh,dan in ba kashemu zakiyiba me kuma yarage a duniyar nan bakiyimin ba na hukuncin ki sumayyah.

Idan kina tunanin wai har yanzu ina sonki zan zauna dake cikin so kaman da to ki sanja tuanin tun wuri,dan ina baki sani ba to ki sani yanzu,zaman cikin gidana dakike kokarin yi a yanxu tamkar kin yanki ticket din ukubarki ne na wahala a cikin gidana,ina gargadinki ne da karki kwafasa kizo kiyi danasani,amma idan kinga zaki iyah fine Allah yabaki sa'a.

In kunne yaji jiki ya tsira"

Duk maganar dayake idon sumayyah ya gagara barin kan fuskar Ahmad,duk wani yanayi da yake kan fuskarsa tarewa yake a cikin kanta,sannan kuma duk wani sauti da amon muryarsa yake fitarwa,buga wani abu yake tamkar ganga a cikin dodon kunnenta.

Wani irin bugawa zuciyarta takeyi kaman zata fito daga kirjinta,ikon allah ne kawai ya dakatar da ita daga fitowa.

Kawar da duk abinda yafada take kokarin yi a cikin zuciyar ta tareda bude baki zatayi masa dalilin aurensa,

"Yah Ahmad bad an.........."

"Yi shuru karkicemin komai,na manta ban fada mikiba,acikin abinda banaso kuma na tsana harda muryarki,dan tun ranar data gasa min maganganun da suka zamemin tamkar tabo a kirjina na tsani jin muryarki koda a mafarki ne bare na jita a kunnena a zahiri,na tsani komai naki sumayyah.

Ki fita min a motata yanzunnan,bazan iya cigaba da tuki kina gefena ba,dan ji nake kamar ina tafiya a tsakanin dutsen wuta,sannna ba sanyi nake ji ba saima tururun dayake kara hauhawa,dan haka fitamin a motata.

Motar dakika raina kike ga kin fi karfinta ma bansan mai yasa kika shigeta ba yanzu,dan haka fitamin a motata tunda badake muka siya ba,kuma ba bazawarinki ne yasiyamin ba ko kuma wannan kazamin tsohon mijinnaki"

Ganin Ahmad magana yake ta yaba mata babu tsayawa yasa ta saurin bude motar ta fita da sauri,dan takai makurar inda bazata iya jureba sam.

Tana fita daga motar tasa ta dafe dukkan kunnuwanta da hannayenta,babu abinda takeji sai bugun zuciyarta a cikin dodon kunnenta,ko karar jan motarsa yabar wajen ma batasani ba.

Tafiya take tana rike da kunnuwanta wanda takejin kaman ana kara a ciki,ga idanunta wanda suke zubar da hawaye batareda yardarta ba,kai tsaye kukan da takeyi daga zuciyarta yake fitowa zuwa cikin idanuwanta,wanda suke ta zubar hawaye batareda yardar ta ba.

Ba ita takai gida ba sai bayan isha likis,dan har dare yafara, kasancewar da kyar kafafuwanta suka temaka mata suna mika ta gaba a duk lokacin da ta taka su.

Hanyar dakinsu ta wuce kai tsaye,ko gaisuwar baba mai gadin ma bata amsaba kaman yanda takeyi a kullum yanzu,sa'arta daya kuwa babu kowa a falon har Allah yabata sa'ar shigewa dakinnasu.


Kusan kwana sumayyah tayi tana nazarin abinda Ahmad yafada mata,amma ko kadan ta kasa ganin dalilin dazai sa ta sanja ra'ayinta,saima kara karfafawa kanta gwiwa datakeyi,dolene ta zauna a tareda su,tahaka ne kawai zata iyah saka su fahimci ita wacece yanzu,idan ma ta kyaleshi kaman yanda ya fada zata cuci rayuwarta ne har ma da tasa,saboda duk wanda ta aura komin abinda zai mata bazata iya mantawa dasuba da kuma abinda tayi musu,musamman idan ta tuna kiyayyarta tana cikn zuciyarsu musamman ma Ahmad,sannan shima zai rayune kullum da tunanin cutarwar da tayi masa,idan har ba jure wahalar dayake fada zata shiga tayi ba,bazata iyah tsamoshi daga kiyayyar dayke cikiba,zai cigaba da rayuwa yana jin haushinta.

Dan haka kashedin dayayi mata tamkar bakin mai ya zubawa wutar muradin aurensa a zuciyarta,kuma ba gudu babu ja da baya sai taga abinda ya turewa buzu nadi,dolene tun daga yanzu tafara shanye duk wani abu dazata ji kokuma da tagani daga gareshi idan har tana son cimma burinta.

Sati biyun da abbah yabawa sumayyah lokaci guda duka zo kaman ma ba'a ambacesu ba,fargabar da takeyi a lokacin baya bai kai na yanzu ba da tasan tasakawa ranta wani buri da take some cimmawa.

Wannan kiran a gaban su yah naseer da yah mu'azzam abbah ya kirata dan suji mai ta kudurta a ranta,duk wannan karon addu'ar abbah shine ta zani wani ba Ahmad ba.

Lokacin data shigo falon bayan ishane shima lokacin da hijabin ma a jikinta bata cire ba,kanta a sunkuye ta tsugunna a gaban abban tareda gasheshi,wannan karan ya amsa ba kaman na wancan ba.

"Kinsan Akan me na sake kiranki koh?*'

"Eh Nasani abbah"

"To mashaallah tunda kin sani ina jiran amsarki wacce kika yanke,sannan wannan karon banason shirme,dan bazan sake karamiki lokaci ba,dan haka ki fadamin abinda Kika yanke.

"Abbah kaman yanda na fada a baya yanzuma hakane,ban sanja ra'ayi ba,Ahmad na fitar a wanda zan aura,abbah kayi hakuri da hukuncina amma kaman yanda ka fada nayi abinda ya dace wannan ne ya dace dani "

Jan numfashi abbah yayi yana kallon su yah naseer,musamman ma yah mu'azzam wanda ya hade girar sama da ta kasa kaman ya shaketa yake ji a ransa.

"Tun kince haka munji to,zamuyi shawara sannan mu tuntubi lamarim,idan yace bai aminceba ki sani bazan masa dole dake ba,saidai na auramiki wanda na ga dama,tashi ki bani waje"

Haka cikin sanyin jiki sumayyah ta tashi ta bar cikin dakin.

Duk yanda kirjinta yake bugawa amma kuma batajin zata janye kudurinta a kan auren,tausayin maryam ne ya darsu a zuciyarta ganin zata sake takurawa rayuwarta a karo na biyu,tabbas bata kyuta mata ba saidai babu yanda zatayi da lamarin,abin ya shafesu dukka su ukun

Sannan bata fatan ta shiga rayuwarsu yamda zata cutarsu,iyah iyawarta zatayi ganin bata takuramusu ba,wannan alkawari tayiwa kanta.

Bayan fitarta daga dakin abban,kallon su yah naseer yayi kafin yace,

"Kunga abinda ya faru koh,bansan menene a ranta ba data kudurta auren bawan Allah nan,gashi ni bana da wani dazan bata a yanzu haka,Allah dai yasa babu wani sharrin dazai biyo baya.yanzu abinyi dole nakira Ahmad naji daga bakimsa,idan da yardarsa to babu yanda zanyi,amma idan har banu yardarsa to dole saidai ta hakura"

"Ai abbah babu wani yardarsa,kawai ita take abinda dan ta cuceshi,taya zai yarda da ita bayan abinda tayimasa"

Shine abinda ya mu'azzam yafada cikin fushi da kufula

"Karka ce haka mu'azzam,baridai nayi magana dashi gobe,koma menene zanji daga bakinsa ai"

"Shikenan Allah ya kaimu"

Daga haka dukkan su kowa ya fito yakama hanyar gidansa da tunanin abin a ransa,basuyi tsammanin sumayyah zata kara kiran sunan Ahmad a matsayin mijinta na biyu ba,sai gashi ta basu mamaki.


Washagari kaman yanda abbah yafada kuwa hakane,dan aikawa yayi akan yana neman Ahmad diin

Baiyi kasa a gwiwa ba kuwa ya amsa kiran abban wajen yamma dan magirba takusa lokacin daya zo.

Dakin hajiya mama yaje akan zasu gaisa,dan da ladidi suka hadu ya tambayeta hajiya maman,tana Shiga ta fito tace masa ya Shiga tana ciki.

Suna ciki suna gaisawa ladidi tazo ta samu sumayya a kitchen tana abincin dare,

"Anty sumayyah bari na debi ruwa za'a kaiwa Ahmad"

"Ahmad kuma yaushe yazo meyasa"

Yar dariya ladidi tayi kafin tace,

"Duk wannan tambayar da razanar taya zan sani anty sumayyah,kawai nima ganinsa nayi ya shigo,yana dakin hajiya mama suna gaisawa"

"Okay shikenan"

Duk da haka dai hankalin ta bai kwanta ba,tambayarta daya mai yazoyi gidan a wannan lokacin,dan batada masaniyar kiran da abbah yayi masa sam.

Harta hada ruwan zata kai masa said kuma ta tuna bazai shaba idan ita takai,hakanne yasa ta bawa ladidi akan ta kaimasa ita kuma ta cigaba da aikinta.

KO badan hakan bama bata bukatar ganinsa a yanzu,dan abinda ya faru a tsakanin su rannan a motarsa har yanzu bai bar cikin kanta ba.

Lokacin da ladidi ta kai ruwan ma har yabar dakin ya nufi wajen abbah inda yake kiransa,dan yaso zuwa tunda safe aiki ya rikeshi.

Sallama yayi cikin nutsuwa yashiga wajen abban.

Gaisawa sukayi cikin mutunci da mitunta juna,dan tun Ahmad yana yaro dama jinin ya jitu da abban,kaman dansa haka yake jinsa a ransa.

"Ahmad gameda abinda yake faruwa na mijinda sumayyah zata aura,akwai wani abune a tsakaninku?.

Saboda nakirata har sau biyu akan ta fadamin wata fitar a matsayim mijin da zata aura tana cemin kai ta fitar,da farko na dauki abin a matsayin wauta,har na koreta na kara mata sati biyu.

Jiyane sati biyu ya cika nasake kiranta na tambayeta,abinda ta fadamin rannan shi tasake fadamin ha ilau.

To kasan aure ba'ayinsa saida bangare biyu wato miji da mata,ita naji ta bakinta,kuma bai dace na dauki abin a matsayin babba ba sainaji daga bakinka,tunda kaine jigo.

Sannan kasan abinda ya faru.a baya,yanda ta watsamin kasa a ido kaikuma ta nuna maka iyakarka,kai ba bako bane akan hakan,koda kai ne kasa da ita a wajen bangaren aure bazan taba yimaka dole akan sumayyah ba,dan haka ka kwantar da hankalin ka ka fadamin ra'yinka.

Mai kace a gameda maganar data yimin,shin dama kasanda maganar ko kuwa a'a.

Shiru a Ahmad yayi Yana sauraren maganganun abban sumayyah,wani gumine yake zirarowa a cikin jikimsa zuwa kam fatarsa duk kuwa da yamda sanyin ac yake iya kokarinsa a cikin dakin.

Kara sunkuyar da kansa yasake yi saboda kar su hada ido da abban,wanda ya tsira masa ido yana jiran yaji mai zai ce



 *sadi-sakhna ceh* 🏵