KAICO NAH

Page 33

by @sadisakhna

   🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

      

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

Gaskiya yan uwa duk yanda nakai da matse lokacina na gama littafinnan,indai comment dinku yana karanci to zai koma shafi dayansa,inyaso daga baya sai mu cigaba bayan sallah in allah ya kaimu.

Uhm uhm an dabo gidan inna team din inna a motsa💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

🏵🏵🏵

...33....

_________________________________

"Kai kai wallle wannan leshi da kyau yake,kuma shiya siyamiki da kansa shema'u,wannan ai har kina nema ki wuce tunanina ma a farin jininki,ashedai ban tsugunna na haifi mai kama da bakar karyah ba"

Kobare baki shema'u tayi kafin ta gyara daurin dankwalin sabuwar atampar dayake kanta,

"Haba inna hadda zagi kuma,ai na fadamiki kosha kuruminki,indai alhaji Sama'ila ne sai yamana yafi haka ma wlh"

"Ai ga shi kam ina gani,saidai kaman yamda na fadamiki ba daga nan take ba,tashi tsaye zamuyi a akansa kema ki aureshi kaman yanda mutari ya samu yah wanna hajiyar,ke kiga fah yanda idan ya tashi zuwa take bashi kayan alatu yana kawomana,naji ance ma ina wai honi man(honey moon) zasu je jibi koh"

"Kai inna duk da mun kile mun sanja amma kina nan da kyauyancinki,waye kuma yake cewa wani honi man honeymoon ake cewa fah,duk da daga jss 3 na tsaya hakan ma ba kullum nake ziwaba banaso naga kina disga mu wlh"

Shiru inna tayi shema'u tana sukureta akam abunda bai kai kara ya karya ba,wai kuma suna itace uwarta,duk wannan fada na inna yanzu babu shi,biyyaya takeyiwa shema'u sauda kafa saboda tsoron karta daina dan bata abu idan ta samo,dan yanzu babu abinda inna take na sana'a,wai itama ta mike kafah y'ay'a sunyi abin arziki.

Saurin tashi inna tayi ta sabi gyalenta tareda yafawa tana cewa,

"Kinga ta shi yanzu bata honi man ake ba,in ban iya fada bama ai ba dole bane,yanzudai muje ayi abun dolen shine mallakeshi ta yanda duk abinda mukace to babu maraba haka zayyi ko baya so,in kuwa ba hakaba mukayi wasa saidai muji anayi a wani wajen"

Tashi sukayi itama shema'u ta dauko gyalenta mai kyau sosai yayi matching da kayan jinkinta,takalmi ma dan dubu uku aka saka ana taunar cimgam,ita a dole ta yuwace ajin yaro saidai uban yaro.

Mai keke napep suka tara tareda yimasa kwantancen inda zai kaisu.

Wani wajene can wajen gari hakan ma sai an sauka a shiga a mashin,dan keke napep bazai iya shiga ba,surkuikiyace sosai da sosai.

Mashin su inna suka hau ana tafiya dasu kaman bazasu sake ganin wani bil'adama ba kuma saigasu a gaban wata bukka a saman wani dutsi,kallon wajen sukayi bayan sun sauka daga kan mashin din.

Mai mashindin tsuka yayi bayan sun bashi kudinsa yace,

"Allah ya shiryah,Allah ya isan maza,an zo za'a kashe wani a tsaye a maidashi matacce da rai,wlh da nasan nan zakuzo bazan kawo kuba,nayi zaton rugar ardo zaguje wlh,batattu kawai"

Haka yagama yimusu tatass suna tsaye suna jinsa sun kama baki,bayan ya tafine ma inna ta bishi da wani ashar har tana cire takalminta tana jifansa.

"Kaji lalataccen yaro,nayi uwarka a haife ka dunga zagina haka,saboda tsabar raini da iskanci,shege kayi iwarka"

"Kinga inna dan Allah kiyi shuru muje,ya tafi bajinki zayyi ba dai"

Kama hannunta shema'u tayi suka fara hawa tsaunin tana mita wai ota takalminta zai karye,

"Lallai ma ke ta takalmi kikeyi,kinsan da yanda akayi na samo Gidan nan kuwa,saida nasha wuyah,kuma kinsan duk bokan dayake zaune a jeji aikinsa yafi kyau bare irin........"

"Hehe hehe menene na wani yimata rarrashi,idan bata son aikimmu ta koma da baya,ba ma son munafurcin banza da wofi,har mun gano soyayyar dayake miki kuwa ta kusa zama labari,dan har yafara ganin wata yana sonta a kwana ukun da suka wuce"

Wani bakincikine da tururin kishi yakama Shema'u jin abinda bokan yafada,har batasan lokacin data kai karshen dutsinba ta tsaya a bakim bukkar tana haki.

Tana nan tsaye a bakin wajen har inna ma takariso kafin sukaji sautin dariyar bokan a bayansu,

"Wannan magana haka take,yana dafff da barinki ya samo wata wacce zuciyarsa ta karkata akanta,kuma dama bake kadai ya so ba a baya,yaso yam mata dayawa,saidai tun da yarabu da uwargidansa shekara bakwai da suka wuce har yanzi bayyi aure ba,idan kinaso akwai aikin dazamuyi ke kishiga gidan a matsayin amaryarsa"

Tuntuni shema'u ta nemi wata gajiya da haki ta rasa jin abinda boka yace zata samu duniya yanda take so.

"To boka yaza'ayi kenan,a fadi kowane aiki a shirye nake dana yishi matukar hankalin sa zai dawo kaina nayi nasarar aurensa na mallaki dukiyarsa"

"Karki damu ba aikine mai wuyaba,matukar kika bi umarnina to nan da wata daya ma kin zama amaryarsa kuma zai mallaka miki dukiya fiyeda yanda bakya zato"

Gyara zama su inna sukayi jin bayanin bokan,tareda buga hannu suna rangada shewa,

"Dama ai na fadamiki shema'u,dayanzu na biyeki bamuzo ba da bamuji abinda yake ransa ba kinga yanzu zamuyi maganin shege mu kamashi gam"

Dariya shema'u ta rangada baki har kunne kafin ta kara maida hankalin ta wajen bokan cikin mazari.

"Boka fada min sharadin ina jinka,kuma zan aiwatar komai wuyarsa indai zanyi nasara"

Mahaukaciyar dariyarsa yasake bugawa kafin ya daga hannunsa saiga wata kwalba da wani mai ya bayyana a ciki.

"Wannan shine mahadin aikinki,zaki sakashi a gabanki yayi kaman minti biyar kafin ya kusanceki,indai har hakan yafaru to sai yanda kika yi dashi,ana san aikin a cikin kwana uku daga yau ya tabbata,idan kuma ba haka ba aikin ya ruguje gabadaya"

Saurin kaiwa hannu shema'u tayi ta fizge maganin a hannunsa,itadai inna yanzu idone nata,tasan hakan bakomai bane tunda tanada masaniyar shema'u tana kwanciya da alhajin dama tun hadiwarsu,dan dai babu yanda zatayi ne kawai.

"Aiki zai kammala yamda ake so karka damu,yanzu nawane kudin aikinka toh"

"Hhahahaha kudin aiki kuma yanzi yarinyah,kedai kije ki jarraba magani,idan har yayi aiki saiki biyani kudin aikin"

"To shikenan zakuwa kajini idan aiki yayi"

Daga haka shema'u tatashi ita da inna suka kama hanyar sauka daga dutsen,yanzu kam babu korafin cewa ai wajen yayi mata tsayi,cikin mazari ta sauka ko jiran inna batayi ba,ita kuwa inna said binta take da kallo kaman ta samu tv.

Bayan sun saukane suna jiran abin hawa inna takalle ta tareda cewa,

"Ma'u naji yace saikin kwanta dashi kafin auren fah kafin maganin yaci"

"Eh to inna menene a ciki,ake na banza ma bare gana dalili,karki ma sawa kanki damuwa aikin nan sai yaci kaman yankan wuka,ni nasan yanda zanyi"

Sakin baki inna tayi tana kallon shema'u,lallai wannan shi ake cewa (taka shi yazo ya fika tsayi),ta haifi yar a cikinta amma tafita iyah shege yanzu.

Basu suka koma gida ba har wajen magriba tukunna suka isa.

Babu zancen sallha bare dora girki,dan sun cika cikinsu a waje,yarane mazan suna almajiranci,dije kuwa uwarta ta dauketa wai tana yi mata tallah itama.

Wanka shema'u ta shiga bandaki,an dade ana dille jiki kafin ta fito ta fara sheka kwalliya,inna ce ta kalleta tana tabe baki tace

"Yau zakiyi aiki da maganinne?"

"Ahah inna karki damu ba yau zanyi aiki daahi ba,aikinsa rana ta musamman za'a ware masa "

Tana fadar maganar tana kashewa kanta ido a madubi bayan ta gama daurin dankwali.

     _____________

"Haba hajiyata yanzu zamu tafi jine din amma kice baxan je na fadawa inna zamu tafi ba,karki manta fah yau kwanan mu uku da aure,kuma tunda mukayi aurennna banje ko ina ba ina gida ina hidimtawa bukatarki,saboda tsabar aikin danakeyi har kunkumina ciwo yake dukkuwa da maganin danake sha kafin na fara"

"Lallai ma honey to yimin gori ka kirani da hajirah,inba hakan ba menene aikinka,abinci kake nemowa kokuma aiki kakeyi ka tufatar da kanka da har zakayimin korafi"

Karyar dakai mutari yayi kaman zai kuka,duk yanda jikinsa ya yayi jawir saboda hutu da abinci mai kyau, amma daga idonsa zaka gano yanda stress ya taru a cikinsu.

Yunkurawa tayi ta tashi daga kwancen datake tareda kawar da plate din kayan marmarin dayake gabanta,gefen mutarin ta matso tana wani murmushi irin na yan duniya ishashshu,

"Haba mai lovly baby menene na bata ran,kasan yanda nake mahaukacin sonka banason wani abu ya tanaka,fadan dakaji nayi yanzu ma dan kace zaka barni ne,nikuma banajure rashinka ko kadan ka sani,indai har wajen inna ne ka shirya kaje gobe,ga can kaya a can wajen ma ka kai mata,kace ina gaisheta."

Duk da cewa mutari yaji dadin ganin kayan data nuna masa,amma har yanzu bai saki ransaba,dan duk jarabar sa dabin matansa yaga wacce ta ninkashi,lokaci daya ta maidashi kaman rubabbiyar kabewa dan sakewa,duk yayi laushi.

"Please my baby smile mama,kasanfah na fadamaka banason fushinka ko kadan,karka damu ka fadamim duk kasar dakake so can zamuje,kuma sai ka gaji kafin mudawo garinnan,so nake ka shakata kaji dadinka"

Ai dagajin haka mutari bai san lokacin daya warware ba yafara murmushi,shi yanzu wayonsa daya ma shine yanda zai samu ya kwashi dukuyar nan ya gudu.

Washagari da safe mutari yah tashi daga kan gadon yana hamma,jan kafarsa yafarayi amma yaji kaman an dora masa karfe,har zayyi ihun neman taimako sai kuma ya tuna da wacce yake aure.

Sauke ajiyar zuciyar takaici yay,danshi a rayuwar sama ya tsani mace lukuta,ace wai matarsace bare kuma katotuwa irin hajiya Murja.

Kare mata kallo yayi farace sol kam amma fah naman jikinta kaman an cucura mata su haka suke.

"Kalleta tana bacci shirim kaman bazata iyah komai ba,sai jaraba da ko tsohon maye bai isa gwada mata ba,hmmmm wai wannan abinne matata,ni sai yanzu ma nake nadamar abinda nayiwa sumayyah,mace mai kyau da aji ba irin wannan ba,ko tana ina oho yanzu,nasan bazata taba mantani ba da abinda nayi mata,ko iyayenta sun barta ta zauna a gidansu oho.

Wani juyi hajiya murja ta sake tareda murkushe kafar mutari,sanadiyyar fitowarsa kenan daga tunanin tsohuwar matarsa dayake yi ya dawo tuna zahiri dakuma Wacece a gabansa,wani ihu yayi niyyar sakawa jin kaman an saka kafarsa a cikin injin marlade,sai kuma yayi saurim toshe bakimsa,dan yanzu idan ta tashi ma aikin jiya za'akoma,wamda a yanda yake jinsa bazai iya komaiba.

Dabara yafari a hankali har yasamu ya dan fara tureta daga kan kafarsa,ajiyar zuciya yayi dayaga yayi free.

Kafin ta sauri yafada bandaki da miyyar wanka,dan ya tuna abinda tace masa na cewar zai iya ziwa gidannsu yau.

Bai dade a bandakin ba ya fito tareda bude wajen kayansa,a shake yake tabb da kaya kala kala sai wanda yake so zai saka.

Kananan kaya ya zaro masu tsada yasaka tareda gyara kai.

Makullin motar ta ya zara a jikin drawer yasaka aljihu,sandawa yayi a hankali yayi kafin yafita daga gidan.

Hhhhhhh to mutari fah an zama matar hajiya murja kuma mijin,hmmm kwadayi mabudin wahala,wanda bai ji bariba yaji hoho.





🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵