Page 5&6
by @babyluv
*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_
*RASHEEDAH SULAIMAN BABYLUV*
***
5️⃣&6️⃣
Motar farouk ta gani gaban hostel ɗinsu but Bata ganshi a tsaye ba ,kawai saita juya ta nufi hostel ɗinsu a nufinta ta ɗauko bag ɗinta sannan suyi sallama da Latipha ,
"You saw me, kuma zaki huce?" jin maganarsa yasa tayin saurin juyawa Dan duk tunanin ta baya kusa saboda ya taba zuwa picking ɗinta a school ,kafin tafito yatafi gun friend d'insa shiyasa yanzu ma tayi tunanin ko can ya tafi, murmushi ta ƙaƙaro Wanda ya tsaya iya gefen bakinta ,Ashe Yana cikin motarsa a zaune may be ya kira batai picking ba saboda phone ɗin ta Bata fita dashi ba, ahankali ta iso gunsa haɗe da faɗin " naduba ne ban ganka ba fa dama zanshiga na ɗauko bag ɗina ne saina fito but am sorry"
"Okay" was abinda yace haɗe da fitowa daga car ɗinsa,Yana sanye cikin wata blue din shadda me tsadar gaske, farouk baki ne ko kuma na iya cewa chocolate color dan babansa yayo kasancewar Wanda ƙanwar Granny ke aure ba fari ne kamarsu ba dan Sam beyo farin familyn su Sabrine ba
"Jeki ɗauko bag ɗin taki saimu tafi ,Kinga yanzu 11 "
Bata ce komi ba ta juya shikuma kawai ya bita da kallo,yanda SABRINE keyimasa halin ko inkula bega macen data isa tayi masa haka ya cigaba da sauraronta ba Yama rasa meyasa yake son SABRINE haka,komawa yayi cikin motar sa ya zauna waiting for her to come..
ADNAN nashiga office ɗin da saurin sa yazo kusa da Dad ɗinsa ya zauna gaba ɗaya yayi losing control ɗinsa akan yarinyar ,shida yayi Rayuwa da turawa ma Sam baya shiga sabgarsu inba wai harkar karatu ba da tazama Dole .
Kamar wani Yaya da ƙani ya zauna da zumunɗi ya fara faɗin "Dad! wannan yarinyar wace ,who is she please"
Yanda ya jefo masa question ɗin Sai da yasa ƙirjinsa bugawa da Ɗan ƙarfi but saiya daure with smile on his face yace "why are you asking"
Baya son babannasa yayi tunanin wani abu shiyasa ,ya maze cike da control ɗin kansa yace "Dad is nothing kawai dai Bata da kunya can you imagine yadda take harara ta tazo fita wata ƙarama da ita Amma hadda wani murguɗan baki" yakai ƙarshen maganar cike da hasashan yadda SABRINE ta murguɗa masa small mouth ɗinta,Amma saiya haɗe fuskarsa sosai like abun ya Bata masa Rai dinnan,
Sai sannan yaji Zuciyarsa tayi sanyi Dan duk tsoron sa da hasashensa Yana bashi kar dai ADNAN ko SABRINE tayi masa ne? thanks God is nothing between them was abinda yafada cikin zuciyar sa
Yadda yaga Dad ɗin nasa ya sauke ajjiyar zuciya like something is bothering him sai ya kalleshi with full respect yace "Dad are you alright?"
"Yes, why asking" yayi maganar had'e da Miƙewa daka Kan kujerar dake zaune sannan yayi Kan table ɗinsa ya ɗau laptop ɗinsa Yana niyar fita
"Dad this days you change alot please Dad what's up,? what
Happened? Did everything alright? Jiya mom take complain rashin dawowar ka gida da wuri and yadda kake ta tunani bawai ita kawai ba nikai na I notice that , please Dad, all this things isn't good for your health Dad" yadda ADNAN yayi maganar with so worried yasa shi yin murmushi ,sannan a hankali ya koma yayi dropping ɗin laptop ɗin ,sannan ya riƙo hannun ADNAN zuwa kan kujerar yazaunar dashi and then Shima yazauna still holding his hand cike da love between son and his Dad ,sannan a hankali ya fara magana "ADNAN is nothing, idan ma akwai ai shiyasa musulmi ko yaushe keyin addua saboda ya samu peace of mind right?" ɗaga masa Kai ADNAN yayi cike da gamsuwa da maganar sa,ganin hakan yasa ya cigaba da magana "yesterday night I explain to your mom nothing wrong with me but she didn't agreed duk tabi ta damu I even tell her na girma, enough da zanyi tunani akan well-being na yarana ,all abinda zatai mun shine addua,yess I agree akwai abinda ke damuna but isn't too much dazata damu please explain to your mother"
Sosai ADNAN yayarda da maganar babansa ,bece komi ba kawai yayi hugging Dad ɗin nasa with so much love yace "I love you dad" and I will explain to mom" wani soft murmushi ya sake ya ƙara rugume son ɗinsa sosai and he said "I'm having lecture now " yayi maganar Yana ɗago shi daga jikinsa
"Okay Dad zan huce hospital nima naga har 12 tayi am getting late let me have my way"
Gaba ɗayan su tare suka fito ,hannun sa nakan kafaɗar ADNAN suka fito gaba ɗayansu cike da murmushi Inka gansu zaka zacci wasu Good friends ne not son and Dad,saboda yadda sukai, messenger nagani sun fito yayi saurin tasowa daga inda yake zaune sannan yajaa office din yarufe like usual.
Gaba ɗaya Sabrine ta gaji dayin shiru ɗin nan tasan da salisu driver ne datuni yananan Yana Bata dariya Amma shiyayi mata shiru ,jefi jefi yakan yimata tambayoyi yawanci a harkar karatuntane tana kuma bashi amsa dai-dai da tambayoyin sa.
Ahaka har sukai shiga kaduna gaban wani tangamemen gida me kyan gaske ,tsayawa fadan kyansa Bata lokacine domin kana gani kasan bakananan mutane ke zaune agidan ba ,
Megadi na bude wa ,yadanna hancin motar babban parking space na gidan ,yanayin parking ,kafin yajuyo tuni SABRINE ta bude motar da kaguwa dason ganin Granny ,binta kawai farouk yayi da kallon kafin Shima yabude kofar ya rufa mata baya
Granny nazaune a daya daga cikin manya kujerun dake kawace a babban parlourn ,hannuta rike da carbi ta kashingida idanta lumshe Kamar wadda bacci ke Shirin dauka ,jin ihun SABRINE yasa saurin bude ido kafin tayi wani yunkuri sai jin SABRINE tayi ajikinta ta rukunkumeta sosai Kamar wadda zaa daukemata ita abin har kusan dariya yabawa Granny
Farouk ne shima yashigo hadi da sallama ganin yadda SABRINE tayiwa Granny yasashi fadin"Kinga temaka ki dagamin mother saboda ba takice ke daya ba ko" yayi maganar Yana sitting kujerar dake facing wacce suke zaune"
Granny ce tayi murmushi hade da kallon SABRINE tace" yauwa farouk fada mata ,kullum ita kenan tambayar lafiyar kafa funa Amma na fahimci itace keneman karasa minsu "jin abinda Granny tace yasa SABRINE yin murmushi ta Kara hugging Granny sosai and said"Granny I miss you alot " yadda take zata zakai irin tayi years dinnan without Granny din alhali duk weekend suna tare,baiya SABRINE itakanta Granny tasan she missed SABRINE alot jitake gidan Kamar ba kowa in tana school sai ta dawo takejin dadi, farouk kam kallon su kawai yake especially yadda yake kallon SABRINE duk sonda yake mata yafuskaci baya gabanta kwata kwata ,shiyasa yaso SABRINE ta dawo gidansu da zama atlist yasan suwa take tare dasu,koda yake Yana da tabbacin Bata sauraron kowa balle yace kodan shi take shareshi Yama rasa gane inda ta dosa
Granny ce ta katse masa tunaninsa da fadin"farouk sannu da hanya kaji yau kazama driver din SABRINE ko"Kamar ta Sosa masa inda ke masa kaikayi yayi saurin fadin"Granny not only today, as from today nizan dinga picking dinta from school"
SABRINE najin hakan kawai ta tashi azuciye tadau back dinta with phone dinta tayi upstairs da gudu -gudu
Har mayafinta abayan na sauka daka kanta lafiyayyen gashinta daya Sha parking ya bayyana , all abinda SABRINE tayi akan idon farouk yadda take gudu gudu abenan yasa hips dinta mugun motsawa beson lokacin dawani mugun feeling dinta with love yataso masa duka alokaci daya, idon Granny nakan farouk yadda yakafe jikarta ta da kallo , tasan farouk nason SABRINE and ita kanta tana so SABRINE ta soshi but she can't force her in Bata sonshi cos she love SABRINE alot Dan tunda mahaifiyyar ta , ta kwanta ta rasu mahaifin farouk yayi nacin SABRINE Takoma cikin su waleedah Amma Sam Granny taki Dan Sam bazata iya barinta yin nisa da ita ba, jitake Kamar Maryam take gani a idonta.
Saida SABRINE ta bace masa da gani sannan ahankali ya sauke ajiyar zuciyar Hadi da juyowa Dan shi yamanta Sam Granny nagun ,yadda yaga Granny na kallon sa yasashi jin kunya sosai yasunkuyar dakai najin kunya ,saurin mikewa yayi hade da fadin"Granny Bari naje gida" kafin ma tayi magana tuni yafice da sauri
Dariya kawai Granny tayi hade da fadin"inzaka cire kunya kacire kazo ayi magana garin kallon ruwa kwado Yama kafa yaro" yaji me Granny tace , sai maganar tafarayi masa yawo akwakwalwa karfa yazauna Wasa wani can yazo ya aure SABRINE, dawannan tunanin yashige motar sa yayi horn driver yabude masa get yafice zuciyar fal tunani akan maganar Granny
dakine me girman gaske with toilet , yayi kyau da tsari sosai ,kana ganin yanayin dakin zai tabbatarma da Wanda yake zaune cikin sa tabbas me tsaftar gaske ne Dan ko tsinke Babu a kasan teyles din dakin ,ganin yanayin dakin zai tabbatar maka da Wanda ke rayuwar cikinsa tabbas babban doctor ne
Jin yadda agogon dakin ya kad'a karfe shabiyu yasashi saurin kallon agogon ,mamaki sosai yakamashi ,shida karfe shadaya ma yakwanta bacci Amma shine har Sha biyu koma alamar baccin Babu,tunda yadawo daga office din Dad dinsa Babu abinda yake tunani sai abu daya koda da Wasa yarufe idonsa abu daya kawai yake gani harma baison abinda zaisa ya rufe idon sa "why" shine abinda ya furta afili hadi da mikewa zaune daka kwanciyar dayake Kan makeken bed dinsa hade da dafe all his hands afuskar ,all he want now is to look at her face again koyasami sauki,but how? Yatambayi kansa Dan gaba daya yaji kwakwalwarsa naneman zaucewa ,ganin bashida mafita at this hour yasashi zuro kafafunsa zuwa Kan bedroom slippers dinsa , ahankali ya zura kafarsa yasa sosai ,Sanya yake da wata white t-shirt dataiwa faffadan kirjin kyau , sai wani black 3guater din wando yayi kyau sosai so handsome , kofa yanufa yasa hannu yabude ahankali , parlour ne mekyau with black and red Royal masu kyau ga wata plasma babba with gotv
Zamewa yayi slowly yazauna Kan 4sitter din kujeran dake parlon , zama yayi sannan yacire shoes din dake kafarsa sannan ya kwanta hade da mikar da legs dinsa akan kujeran sosai , phone din dake hannun ahankali ya kalla hade da sa fingerprint dinsa , wayan ce ta bude direct data dinsa yayi switching on , kawai yashiga WhatsApp , all this abinda yakeyi soyake yahana kansa tunanin wannan small yarinyar mekyau Kamar na aljanu,Amma kamar karawa kansa ma tunanin yake Yama rasa mezaiyi , koma mene Dole saiyaje office din Dad tomorrow , what if Daddy yasan he is in love with this girl? No yafada ahankali , I can't let Daddy find out I'm in love zemin dariya ne, yadda yayi maganar afili kamar wani yaro karami yadda yayi maganar ahankali kuma saiya Kara furta "so what then in Dad yasani alist ai na'isa aure harma nayi yawa"
Dawannan tunanin bacci yayi gaba dashi with so much dreams about SABRINE especially her hips Dan koda yatashi da safe Saida yayi wanka biyu(hhh lol azababbe)
_comments and share_
*Forbidden love group*
***