HARAMTACCIYAR SOYAYYA

Page 8

by @babyluv

*💫FORBIDDEN LOVE💫*

 _Haramtacciyar soyayya_




8️⃣



*Yan Nijar mutanena kunsan me?💃🏻naji korafinku na yawan sa yaran bature da nakeyi a littafina wato turanci inshallah zan Dena sawa koban Dena duka ba tabbas zan yi yadda zaku fahimci sakona nagode sosai Ina yinku🥰🥰❤️ masu yimin korafin nafara sawa a whattpad kuma insha Allah nan ba da dadewa ba zakuji ni Ina godiya*


*RASHEEDAH SULAIMAN babyluv*

***



Duka hanyar da Adnan zai bi Dan ya sake ganin yarinyar Nan Amma abu yaci tura , haka zai d'auko mota yazo office d'in dad d'insa ko Allah zaisa wani abun yakawo ta Amma shiru haka zaizo ya gama hira da waige waigensa bazai ganta ba haka zai koma hospital , yanda yake yawan zuwa gun LEC. A. M sai yake doubt akan yawan zuwan nasa but sai yace masa akwai wani friend d'insa ne a school gunsa yake zuwa shine yake biyowa gunsa , bawani yadda yayi ba yadai kyaleshi ne Adnan d'inne yake da wani friend shida friends dinnasa ma suke complain Kan baya sabga dasu tabbas akwai abin da yake kawo shi to Amma mene?


Kusan two weeks kenan da dawowar Sabrine Dan Bata koma gida ba saboda yadda suke test Dan ta fadawa ma Granny , yadda LEC A.M ke kula da da ita da nuna kulawarsa ba karamin dadi take ji ba Dan har sawa yake aimasa kiranta yayi mata tambayoyi yawanci akan karatunta ne, Babu wani abu na soyayyar Sabrine daya ragu cikin zuciyar sa saima karuwa da yayi wani lokacin ma Zuciyarsa ma cewa take kawai yafada mata Amma Ina Sam baze iya ba yarinyar da take ganinsa kamar mahaifi Taya zaiyi hakan? Yananan Yana jira Allah yabashi wata dama koda karama ce Dan ya sanar da Sabrine sirrin dake zuciyar sa, tsoron sa guda d'aya ne kada yafada mata , ya zamo ganinta dayake samu yakeyi yaji dad'i ya zamto ta Gina wata katanga atsakaninsu a dalilin hakan ,to kodai yasa ayo masa binkicen iyayenta kawai ya biyota ta kansu ne?.



Kasan cewar satin Sabrine uku kenan Bata koma gida ba saboda yadda karayi yayi tsanani,

Tun safiyar yau asabar Sabrine ta tashi da wani ciwan Mara dako mikewa Bata iyayi ga zazzabi sosai daya rufeta duk dauriyar datake Amma Sam takasa jurar ciwan Dan da agidane Allah ne yasan mezatai ,sanin yau zata fara period yasa ahankali ta lallaba ta dau pad Dan taji ciwan gaba yake mata kada taje takasa tashi tasa ,ahaka ta lallaba ta je toilet tasa ,tana rike da mararta tafito ,jindatai mararta tawani irin murdawa daidai lokacin tafito kofar toilet d'in gaba d'aya taji duhu ya ziyarci idanunta laluben abinda zata dafa tai Amma Ina cikin rashin saa Bata samu ba agurin ta sulale sumammiya

  Muryar latipha taji sama sama tana fad'in"Sabrine meya faru ,meya sameki ko suma kikai wayyo Sabrine…" daga haka Bata sake jin komi ba d'uf ta Dena ji ,ganin ko motsi batai yasa latipha sakin Kara arazane ta fice daga hostel din nasu




Babban asibiti ne private mekyau da tsaruwa inbawai ka karanta daga babban gate din dake hospital din ba bama zakai tunanin asibiti ne ba  .

 Yana zaune cikin wani babban office Wanda akaf cikin asibitin Babu me girman sa Dan hadda bedroom mekyau with toilet but bama zakai tunanin akwai su ba Dan tacikin office din akwai kofa Wadda zata sada ka da dakin d'in

  Da alama niyar fita yake Dan gaba daya jiyayi baya da mood din zama all this days Yama rasa what to do and what to leave yama rasa wane tunani zaiyi ,ta Ina zai fara nemarwa kansa farin ciki , farar riga ce me dogon hannu na lins sai wani blue din wando dake jikin sa yayi stucking hannun sa yakai Kan blue din rigar dake rataye kusa dashi Yana niyar dauka yaji anyi nocking Kamar bazai magana ba saikuma yace"yes come in"

Ahankali aka turo kofar wata nurse ce tashigo cikin fararan kaya na nurse , kallo d'aya yayi mata ya dauke Kai yace"what ? Meya kawoki?"

Cike da girmamawa tace"doctor muna da Mara lafiya da aka kawo yanzu and naduba Dr imam baya section d'in kuma duty dinsa ne"

Kallonta yayi sannan yace" and what if Dr imam isn't Ina sauran suke ? "


" Doctor asiya taje duba wani patient Wanda akaiwa surgery jiya and you know is evening now shauran kananun sunje bada magani"kamar bazai Kara cewa komi ba sannan yace"ok ku kula da ita kubata first aid " okey was abinda nurse din tace ta juya ahankali tafita


Cikin shigarsa ta cikkakken likita me ji da kansa, Adnan yamike ahankali yanufi kofa 

   Yanda ake girmamashi da yanda kowa ke rusunar dakai  inya ganshi zai tabbatarma cewa bawai karamin likita bane zaikuma Kara tabbatar ma shine mamallakin asibitin


"Doctor, doctor please Kaine doctor Adnan din please doctor nanne room din please help her Bata da kowa anan garin doctor please help"


Yanda yaga latipha na kuka tana rokon sa, sai yaji abin yataba shi " Dan daga mata hannu yayi alamar ta Dena kukam kafin ahankali yace"Kinga please Dena roko na haka , aiki nane yin hakan so I will help " Yana fadar hakan yajuya d'akin dayaga tana masa nuni

  Yana shiga duka nurse din dake kanta suka bashi guri hade da fad'in "welcome doctor" be amsa ba yanufi gadon dayaga yarinyar kwance Yana zuwa yamika hannu yad'au file d'in nata yafara dubawa ,dasauri ya d'ago Kai yadubi gadon datake kwance, saidai baya ganin fuskarta  Dan reborm d'in kanta yakwance so duka gashinta ya lullube mata fuska kasancewar gashin nata is so long yasa ba'a ganin fuskarta  ,sai drip dake hannunta


"Period pain" yafada afili



“Yes doctor and akwai zazzabi with ciwan kai Wanda yasa ta suma but thanks God sun kawota akan lokaci , mun samu zazzabin ya sauka yanzu "


jijjiga Kai yayi kafin ahankali yakai hannunsa wuyanta Dan tabbatar da abinda suke fad'a , daidai lokacin tasaukee wata sassanyar ajiyar zuwa dayasashi saurin kallon face dinta , baya ganin fuskar saidai kawai lips dinta dayayi pink sosai , tsintar kansa yayi da karewa bakinta kallo hakannan Zuciyarsa ke Raya masa son ganin duka fuskarta d Amma Babu hali

  Hannunsa yandauke daka wuyanta kafin yayi rubuce rubuce akan file d'in nata sannan , yasamu wata karamar takarda yayi rubutu sannan yami'kawa nurse din hade da fadin"anemo wad'annan maganin da allurar  sai ayi mata yanzu tana da bu'katar su , allurar d'in zata sata bacci sosai shine abinda muke bukata so because of that zata kwana anan sai zuwa gobe innaga jikin nata yayi kyau sai mi in charge dinta"

cike da biyya nurse din ta kar'ba shikuma yafice Dan yunwa yakeji and bayacin abinci awaje Dole saiya koma gida   

  Saida ya koma office ya d'au rigar suit dinsa dake rataye yasa yad'au phone dinsa with keys sannan yafito cikin tafiyarsa ta cikkakken matashin doctor yafito daga office d'in tafiya kad'an yayi yakaishi parking space d'in dake hospital d'in, yana zuwa yabude yashiga cikin kwarewa ya Danna hancin motarsa zuwa gate me gadi cike da girmama wa yabud'e masa gate yafice Yana d'aga masa hannu Yana fadin"adawo lafiya likita bokan ture me alheri irin mahaifinsa Allah Kara lfy" daga masa hannu kawai doctor Adnan yayi saboda baya son wad'annan kirarin da ake


Wurin magrib Sabrine tafarka dawani ciwan kai cikin dafe Kai ta daure ta tashi zaune , ita gaba daya tunanin ta a makaranta take tayi bacci ta tashi all she know tasan Bata da lafiya and she even take pad taje toilet tasa but Taya har tazo takwanta, ahankali ta bude idonta dasuka Kara fitowa sosai ganin wani zanin gado da tasan Sam babu a hostel dinsu yasata saurin d'ago Kai ta Kara kallonsa ahankali kuma tafara bin gadon da kallo sam ba bed d'inta bane kenan a hospital take?

Tsaf tagama karewa dakin datake kallo tabbas asibiti ne , ahankali ta Kara dafe kanta da yayi mata wani mugun sarawa Dan ciwo yake mata sosai

  Turo kofar dakin akai ahankali Latipha ta gani hannunta rike da ledan restaurant an rubuta las Vegas ajiiki , ganin ta azaune yasa Latipha karasa shigowa da sauri , ajiye ledojin hannunta tayi , sannan ta dafa Sabrine fuskar ta cike da damuwa tace“sannu SABRINE  kina da headache ne ? Kona Kira Miki likita?”

Duka cikin damuwa tayi maganan Dan seriously jin Sabrine take tamkar wata yar uwarta ta jini


Ganin Latipha na niyyar tashi Kiran doctor yasa ta saurin riko mata hannu had'e da fad'in “a'a Latipha am fine now alhamdullahi kawai fa ciwon Kaine kad'an and Shima zai tafi ne”


"Dagaske" was abinda Latipha tace ta dawo tana zama, ahankali SABRINE ta daga mata Kai alamar yes, ledan datashigo dashi ta dauko tana fito da take away d'in ciki tana fadin “kina jin yunwa sosai Sabrine yaka mata kici abinci Kinga nima fa haryanzu banci komi ba my best friend ta d'agamin hankali". Kallon ta kawai Sabrine tai da murmushi afuskar ta kafin ahankali tace"kekam wai Taya kika kawoni nan , keda ko kwarin arziki babu”hararanta Latipha tai tace “ okay wato instead kimin godiya na ceci rayuwar ki shine kikemin tsiya ko , yarinya bakisan damuwar dana shiga ba bansan lokacin Dana fita hayyacina kawai nafita nakira motar school kinsan mota na baya nan , nace bakida lafiya and you know what wai zasukaiki wannan asibitin na makaranta  nikam naga ko hayyacinki bakyanan shiyasa nace ni kwai su kawoki Nan dakyar suka kawoki and naji dad'i asibitin nan suna da kirki sun karbeki da wuri fa saidai daka gani likitannan 'Dan girman Kai ne kinsan yadad'e beje dubaki ba sannan daya fito Yana wani Shan kanshi Dan yaganshi so kyakyyawa Saida yaga fa Ina kuka hmm" dukkan magannan ta Latipha keyi Sabrine kawai kallonta take tana ta murmushi Dan hirar Latipha sai ita irin mutannane masu surutu, and Latipha yadda take gudanar da rayuwanta bazaka taba cewa ita yarinyar masu kudi bace yadda zakaga suna daga Kai ita Sam Bata da wannan she is a nice person kirki gareta sosai…


_Comments and share_


*Forbidden love group*

***