Page 14
by @babyluv
*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_
*Inaso pls nasan wani abu yakamata kowa yayi comments , cikin Adnan da LEC A. M wakukeso ya kasance da Sabrine , Ina jiran raayinku kowa tarubuta cikin comments d'inta kunji bhabibties*🥰😍😍
1️⃣4️⃣
*Rasheedah SULAIMAN* _(babyluv)_
*Forbidden love group*
***
Koda Adnan ya dawo gida jiyayi shi Sam bazai iya jiran komi ba kawai zai fad'a wa daddy cewar yanason yarinyar Nan Dan yasan zaiyi munnna sosai aganin Adnan tunda dad d'in nasonta haka to tabbas zaiyi farin cikin had'a su tare
Dawannan tunanin Adnan yafito daga d'akisa direct part din mahaifinsa ya shiga , part dinnsa nada girma sosai , ahankali yayi nock Yana jiran abashi permit nashiga Dan haka tsarin gidannan yake indai zakaje part d'in dad d'in to Dole saikai nock anbaka izinin shiga haka hajiya saleemeh duka ta daura yarannata a wannan tsarin
LEC A. M na zaune a parlor d'insa Wanda yayi mugun tsaruwa ga kujerun royal masu balain kyau , Yana zaune da jallabiya ajikinsa akan d'aya daga cikin kujerun d'akin da tunani kala kala aransa Dan ayanzu zuciyar sa tagama yanke masa cewa koma mene Dole kawai yafito ya fallasawa Sabrine sirrin dake ransa koma me zai faru kawai ya faru, dawannan tunanin yaji anyi nock d'in kofa ahankali ya d'ago sannan yace come in
Da sallama Adnan ya shiga kansa a kasa kamar Wanda ya dau kayan wani , ganin Adnan ne yashigo yasashi sakin smile Yana fad'in ”adnan come in , zoka zauna Nan ”yayi masa nuni da kusa dashi Fruit da hajiya saleemeh ta yanka masa agabansa, ahankali Adnan ya karasa inda dad d'in nasa yayi masa showing kusa dashi ya zauna had'e da kallon flat d'in dake gaban LEC A. M Yace “dad can I have it”batare da ya kalleshi ba Dan waya yake dannawa yace “yeah sure”sannan ya d'ora da fad'in “adnan pls ga laptop d'ina can pls d'auko zan tura wani mail yanzu”
“okay dad ”ya furta had'e da ajiye apple d'in daya d'auka Yana niyyar Sha ajiyewa yayi sannan ya Mi'ke, yana d'auko masa yami ka masa had'e da fad'in “here you go Dad” thanks ya furta Yana karbar laptop d'in , sannan ya bud'e ahankali , kan screen d'in laptop d'in idon Adnan ya sauka akai , hoton Sabrine ne ya bayyana sosai tana sanye da kayan matriculation rana ta farko a school , gawannan murmushin nata dake killing d'insa , gaba d'aya saboda dariyar datake hakoran kamar an jere dimple dinta sun loba kana ganinta ahoton yanayinta zai tabbatar maka tana cikin farin ciki sosai
Da sauri Adnan yarike hannun Dad ganin zai gotar da hoton daka gun had'e da fad'in “yess Dad please don't Skip this picture I love it”
“you love it” LEC A. M ya furta had'e da wata faduwar gaba data ziyarci kirjinsa , Amma ahaka ya daure ya furta“ wane hoton kake magana ne Adnan”yayi maganar babu ko alamun Wasa ko fara'a atare dashi
Shikam Adnan with one heart yace “wannan yarinyar taka mana dad ”bekawo komi azuciyar sa ba Adnan yayi maganar dan shi yadda yake jin son Sabrine aransa jiyaye gaba d'aya kunyar dad d'inma ta gudu Dan gani yake baban nasa zaiyi matukar murna inyaji cewar Yana son Sabrine
Ajiye laptop d'in LEC A. M yayi sannan ya zare farin glass d'in dake fuskarsa Yana kallon Adnan yace“and what does that mean yimin bayani yadda zan fahimta me kake nufi adnan”
sunkuyar da kansa yayi and said“dad wannan…. yarinyar taka…nidai kawai ka bani ita Dan I love…?”
“dont even start Adnan , karka sake ka fara !! you mean San Sabrine kake for what reason ehe waye yasaka ehe Tell”all this maganan da LEC A. M yake cikin fad'a yake Dan gaba d'aya zuciyar sa bugawa take na 'bacin rai dakuma fargabar abinda zaije yazo
Shikam Adnan kallan Dad d'innansa kawai yake Dan abin ya mugun bashi mamaki meyasa Dad zaiyi fad'a akan yace yana sonta? meyasa ya Bata Rai haka? Ko tana da wani bakin hali ne haka
Cikin sanyin jiki Adnan yamiki Yana fad'in “relax dad please come down this isn't good for your health, kadena fad'a haka pls zauna”yayi maganar ya dafa kafad'ar daddyn da niyyar ya zaunar dashi, Amma LEC A.M ya ture hannun Adnan d'in Yana facing d'insa Yana fad'in “no Adnan bazan kwantar da hankali na ba untill You promise me bazaka 'Karamin zancen kanason Sabrine ba saika min alkawarin you stop loving her sannan hankali na zai kwanta pls promise me kaji”yayi maganar Yana mikawa Adnan hannu alamar yayi masa alkawari
Kallon dad d'in yayi cikin rashin fahimtar abinda dad d'in ke nufi , Taya ma zai masa alkawarin gyale Sabrine ?meye aibu Dan zuciyar sa taji tanasonta , girgida Kai Adnan yayi Yana matsawa baya kad'an had'e da fad'in “no Dad I love her, Ina sonta Taya zan Dena sonta meye aibu dannaso ta ? Shin tana da wata illa ne Dad please tell me so that I will understand your point , kana tacemin karna sota Amma baka fad'a min dalilin ba dad pls fad'a min aibun ta and I. Promise bazan ko kara maganar ta please”
Cikin kama hannun Dad d'in duka yayi maganar Yana rokansa akan yafad'a da masa meye aibun Sabrine har 'kasa ya durkusa Yana rokarsa,
Ahaka hajiya saleemeh ta bud'e kofa tashigo ta samesu Adnan ya durkusa ri'ke da hannanun LEC A. M Yana rokarsa, kusan tun maganar sa ta farko da LEC A. M yayi cikin d'aga murya tazo huce wa hakannan jikinta yabata something is wrong shiyasa kawai direct tayo flat din alhajin to See what's going on, gashi kuma ta tarar da Adnan ya durkusa Yana rokar alhaji akan abinda batasan meye ba
Cikin mamaki hajiya saleemeh ta tako cikin parlour d'in cikin tafiya irin tasu tamanyan Mata wad'anda jin dad'i ya zaunawa ta karaso had'e da dubansu su duka tana fad'in “what is happening here meyake faruwa ne baban yara, Adnan what's going on. Here”babu Wanda yayi magana daka Adnan har LEC A. M , ganin haka ta 'kara furta“can someone pls tell me meke faruwa haka , alhaji najika Kamar cikin bacin Rai , I hope ba Adnan bane ya Bata ma rai…….?
*Adinga share habibties🤗*