Page 15
by @babyluv
*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_
*Naji dad'in comments d'inku sosai habibties my group members Ina sonku sosai Dan haka wannan page d'in nakune kuyi yadda kukeso dashi I love you all ,😍🥰💃🏻*
*BABYLUV*✍🏻
*****
1️⃣5️⃣
LEC A. M bece komi ba cikin Bacin Rai kawai yajuya yashige cikin bedroom d'in sa , Shima cikin sanyin jiki Adnan yamike yabar parlor d'in yazama saura hajiya saleemeh kadai da duka tazubawa sarautar Allah ido ganin yadda kowa beyi magana ba yabarta agun , harta nufi bedroom d'in daddyn Amma saita tuna Yana cikin fushi ita kam a 'ka'idarta Bata yimasa magana cikin wannan yanayin, kawai saita juya ta fita daga section d'in alhajin zuwa nata section damamakin abinda yakawo haka tsakanin alhaji da Adnan what could that be?
Karfe Tara daidai na dare kenan a kaduna , farouk ke gaban mahaifinsa zaune ya sunkui da kansa kasa da alama magana Mai muhimmanci suke Dan Shima alhaji Adamu kana kallonsa zakasan maganar bata Wasa suke ba ,iya yanayin alhajin zai tabbatar ma da hakan , gyara zama yayi sosai Yana kallon farouk sannan yace“banason magana ta Wasa farouk ka tabbatar da abinda kake fad'an I mean ka tabbatar kanason Sabrine banaso nashiga maganar kazo kanamin Wasa ka tabbatar” 'kara sunkuyar da kansa 'kasa yayi sannan cikin ladafi yafara magaba“daddy ba Wasa amaganar Nan abinda yasa nayima magana yanzuma shine duba da tana shekarar karshe a makaranta"
girgid'a Kai alhaji Adamu yayi cike da gamsuwar abinda farouk ke fad'a masa Dan ya gamsu sannan kuma har zuciyar sa yaji dadi saboda Yana d'aya daga cikin abinda da yasa ya takura Sabrine ta dawo gidan sa Dan soyake ya had'a auransu da farouk saboda ya tabbatar da nutsuwar Sabrine da hankalinta ta Amma hajiya tahana shi Amma bega lefinta ba kasancewar yadda ta rasa mahaifiyar Sabrine , ayanzu zata kalli Sabrine ne da gurbin mahaifiyar ta
Komawa yayi ya jingina da kujera dayake zaune sannan ya Dora kafa d'aya kan d'aya had'e da fad'in “tashi kaje sannan katuromin mahaifiyar ka ”cike da ladabi ya Mi'ke Yana fad'in “to daddy thank you”sannan ya fice har lokacin kansa na kasa
Yana niyyar barin parlor saiga hajiya dije wadda ta kasance mahaifiya wurin farouk , tana ganinshi tayi murmushi tare da fad'in “nikam wannan fara'a haka me aka tattauna ne dakai da mahaifinnaka Naga kana ta sakin murmushi ” shafa Kai kawai farouk yayi yace“mama dama alhaji nakiranki dama nizan huce company ne aimana addua”
"To farouk saika dawo Allah ya kiyaye hanya Allah ya tsare”amsawa yayi Yana fita itakuma ta karasa shigowa parlon tana zama kusa da alhaji adamu kasan cewar kujerar 3ster ce ta zauna had'e da fad'in
“alhaji Ashe ka shigo ai ban Shina ba natsaya Kitchen sannu da wowa”amsawa yayi cike da fara'a sosai da harsaida hajiya dije tace“alhaji wannan farin ciki haka wai nikam me kuka tattauna kaida farouk ne Kai farin ciki Shima hakan Haba nima a sanmin mana ”tayi magana cike da zolaya, sosai farin cikin sa ya karu yadubi matarsa sannan yace“aa danki ne yazomin da wata magana data sani farin ciki sosai hajiya”rike ha'ba hajiya dije tayi tace“tooo farouk d'in to sanar Dani nima na tayaka farin cikin ai”gyara zama alhaji yayi had'e da fad'in “yanzu kuwa, farouk ne daga shigowata yasa mene akan maganar yanaso nayiwa , hajiya magana akan yanason Sabrine kuma yanaso as Soon as Sabrine ta gama makaranta ayi auran”
Murmushin hajiya dije tayi ta dubi alhajin sannan tace“lallai abin farin ciki ne kam sosai , Amma alhaji bawai muyi farin ciki ba shi farouk d'in ya tuntubi Sabrine da zancen I mean ita Sabrine d'in ta amince da zancen kasan fa yarannan namu ka haifesune Amma baka haifi halinsu ba ko, ashawarance abinda zaiyiwu alhaji kabari shi farouk d'in yasami Sabrine d'in su daidaita kansu sannan saimu shiga cikin maganar nidai aganina”
Cike da gamsuwa da abinda hajiya dije tace alhaji adamu ya girgid'a Kai sannan yace“maganarki haka take to Amma ke kina ganin Sabrine zata'ki 'Dan uwanta na jini ne kenan"
Girgida danyatsa hajiya dije tayi had'e da fad'in “bance zata 'kishi bane Amma kasan dai halin yaran zamaninnan sai suce basusan auran zumunci shiyasa kawai Naga ya dace shi farouk d'in ya fara tuntu'barta ”
“zancen banza kenan ”alhaji adamu ya katseta sannan yace“zancen banza zancen hofi kamarya basusan auran zumunci to yanzu ko had'a su mukai sai suyi musu , ai wannan maganar banza ce dacewar basusan auran zumunci”
“kaga alhaji shawarar dai Dana fad'a itace mafita nasan halin yaya indai Sabrine tace batason abu to saita goya Mata baya kasan da hakan”
“Shikenam saikiyi wa farouk d'in maganar”yafad'a Yana cire babbar rigar hajiya dije ta kar'ba sannan yace“ Ina yaran suke naji gidan shiru ”
“suna sama suna karatu ,nakawoma furar nasan for now tayi sanyi ”
“eh ”
Mi'ke wa tayi cikin girmama ta tatafi d'auko masa
**** ****
Saida hajiya saleemeh tashirya sosai cikin kayan bacci doguwar riga irin Mara nauyinnan sannan ta fesa turare mekamshi , dakinsu deeja ta fara shiga kasan cewar Afiya tayi candy yanzu tagama boarding school shekaranta Sha takwas yanzu kasancewar tana da 'Dan girman jiki saika zacci tayi shekara ishirin
Deeja ce tayi bacci Afiya ce da system agabanta tana kwance tana kallo
Saida ta tabbatar duka sun kwanta sannan ta rufo musu d'akin tayi section d'in LEC A. M
Baya parlour d'insa Kamar yadda ya Saba zama adaidai wannan lokacin ta danyi mamaki , haka ta nufi bedroom d'insa ta tura 'kofar had'e da sallama , Yana gefen bed d'insa ya sakko da 'kafarsa 'kasa da laptop ahannunsa Amma gaba d'aya hankalinsa baya kan laptop d'in duk yashiga cikin tunani sosai Amma inbaka lura ba zakace hankalinsa nakan laptop d'in
Har kusa dashi taje ta zauna sannan hankalinsa ya dawo jikinsa yabasar Dan beson tasan tunani yake kawai yacigaba da Danna laptop d'in batare da yasanma inda yake dannawa ba
Cikin magana me cike da lallashi hajiya tace“baban Yara Dan Allah nace muyi magana mana”batare da ya bar Danna laptop d'in ba yace “ehen inaji” sotake yabata full attention d'insa Amma taga haka bazai samu ba sai kawai ta fara magana da fad'in “nikam babansu what's happening between you and Adnan Naga Kamar d'azu Yabatama Rai Dan Allah ka fad'a min nasan dai Adnan me ladabi ne ga duk abinda ka fad'a Amma this time around Naga Kamar tasauya zani Amma ka fad'a min”
Dafe kansa yayi da hannu biyu Dan wallahi Sam besan abinda zai fad'a mata ba gaba d'aya yama rasa mezai ce Mata , ahankali yazame hannunsa daka kansa had'e da juyowa ya dubeta sannan ya sauke wata ajiyar zuwa yace“look saleemeh Adnan bemin lefin komi ba Amma I will assure you abinda yake shirin yi ayanzu to tabbas zamu samu matsala me karfi so please go and talk to him yafahimta ya goge abinda yake niyyar aikatawa wannan shine kawai”yana kaiwa Nan kawai yami'ke yad'au wani towel dake rataye Ya nufi toilet, binshi kawai hajiya saleemeh tayi da kallo azuciyarta tana fad'in “nashiga uku meke Shirin faruwa ne ,? What's going on between alhaji and Adnan, jitai kawai bazata iya hakurin jiran gari ya waye ba , kawai ta d'au hijab d'inta dake d'akin alhaji kawai ta bud'e kofa tanufi section d'in Adnan Dan koyayi bacci saita tasheshi yasanar da ita meyayiwa alhaji ,
Tana shiga taga babu haske a parlon Amma , tagano hasken fitilar bacci a bedroom d'insa hakan yasa kawai direct ta nufi d'akin, tana shiga ta kalli bed , amamakinta saitaga taga Adnan azaune yahada Kai da guiwa , abinda bata taba gani yayi ba aduk tsawon rayuwar sa, dasauri ta karasa gefen gadon tana zama kusa dashi had'e da d'ago da kansa tana fad'in“adnan what's happening why are you like this meyasa bakai bacci ba”gaba d'aya rasa me zaice Mata yayi Dan Zuciyarsa zafi take sosai da bazai iya magana ba kawai ya zame ya kwanta acinyar hajiya saleemeh ahankali yafara fad'in “mommy I love her, wallahi inasanta in my holl life babu wata yarinya da zuciyata taji tanaso sai ita pls mom”yakarasa maganar Yana d'ago da kansa daga kwanciyar da yayi Yana ri'ke Mata hannun, fuskarsa hajiya saleemeh ta shafa tana fad'in “yimin bayani meke faruwa wacece ita yimin bayani yadda zan fahimta”
“mommy Sabrine I love her nayi tunanin Inna fad'awa daddy zaiyi farin ciki kasancewar she's one of his students and suna da good relationship between Dad ,he even told me iyayan yarinyar suka bashi amanarta and now Mom nace inason ta but can you imagine abinda dad yace”
Girgida Kai hajiya saleemeh tayi tace“mene shi baban naka yace”dasaurin Adnan ya marairaice Kamar zai kuka yace“mommy yace ban Isa na aureta ba yace karma na fara tunanin aurenta mommy nikuma I love her sosai mom please”
Cike da mamaki sosai tace“shi alhajinne yace bazaka sota ba to akan me ka tabbatar kuma yarinyar mutuniyar kirkice,Taya alhaji zaice haka shida kullum yake fad'a akan ka'ki fito da Mata yanzu kuma yace haka , definitely there's something fishy tabbas akwai wani abu ”tayi maganar had'e da jinjina kai
“mommy wallahi I'm very sure yarinyar kirki ce and inma bahaka ba dad yayi bincike ya tabbatar indai har ansameta da hali Mara kyau to ni nayarda zan hakura dan ita for sure”
Cike da lallashi tace “kaga is okay now I will talk to him kaji inaga kunsami misunderstanding ne Amma yanzu promise me zaka kwanta nikuma zanyi wa alhaji magana and insha Allah nasan zai amince and now sleep kaji”tayi ganar tana tashi tsaye tana masa nuni da ya kwanta ,sai asannan Zuciyarsa tayi sanyi Babu musu ya kwanta ita kuma taja masa blanket ta lullube shi sosai sannan ta kashe masa wutar gaba d'aya ta jawo masa d'akin zuciyar ta fal tunanin wace yarinyace haka har Adnan ya makance a soyayyar ta ,da wannan tunanin har ta Kai section d'in alhaji ta tarar har ya kwanta ,batako saurareshi ba ta kwanta kwai da tunani kala kala aranta ciki harda abunda suka faru wasu shekaru dasuka gabata
Shikuwa Adnan jiyayi bazai iya jiran komi ba yasa hajiya saleemeh nafita kawai ya jawo wayarsa yashiga bangaren Kira yayi dialing number d'in Sabrine aikuwa babu dad'ewa tafara ringing Amma cullertone ne ajiki instead of normal ringing , wata romantic song ne ajiki ta jonnydrill 'kara lumshe ido yayi Yana Kara Danna wayar kunnansa burinsa kwai tai picking call d'in
Sabrine jitai gaba d'aya bacci ya kauracewar idanunta tarasa meyake damunta gashi kusan karfe shabiyu na dare Amma ko alamar bacci babu a idonta , da tayi tunanin ko rashin Granny ne hakan yasa ta kirata tun d'azu sukai waya sosai Amma gashi still kuma Babu abinda ya canja gaba d'aya abinda Latipha ta fad'a Mata bayin dawowar akan Adnan da LEC A. M kemata yawo azuciya duk da tasan cewar LEC A. M ba wani sonta yake ba Amma batasan meyasa abinda Latipha ta fad'a Mata kemata yawo azuciya ba
Da wannan tunanin taji wayarta na rigging , da Bata ko kalli wayar ba Amma saitai tunanin who will call her awannan Daren , sai kawai ta zaro wayar ta ta, ganin ansa Adnan hakan yasa ta d'an bud'e ido alamar mamaki badai wannan likitan bane Yama akai number d'insa tashiga wayarta harda rubuta Adnan,har wayarta tsinke tana kallon sunan ,ahaka wani Kiran yasake shigowa ,kawai saita d'aga ta kara wayar akunne Batare da tayi magana ba kawai tai shiru
Jin ta d'aga wayar batace komai ba har minti d'aya yacika Batare da tayi magana ba sannan kuma Bata yanke wayar ba yasa kawai yayi murmushi sannan ahankali yafurta“sabrine meyasa kike da sonkanki ne dayawa muryar dazaki danyi magana naji dadi shine kikemin bakin cikin hakan ,why Sabrine why please,kinganni fa ko baccin na kasa I'm here only thinking about you ko rufe ido nayi only your face please Sabrine say something to this soul that love you alot pls”yakai karshan maganar dawata shegiyar murya dasaida Sabrine taji wani yarrrrrr ajikinta
Bata ko motsa ba balle tayi tunanin yimasa magana , Dan shiru tayi Bata cemasa komi ba Dan this is the first dawani d'a namiji yayi mata da wannan romantic voice d'in shiyasa kawai taji Tama rasa mezatace masa, ganin Bata da niyar ko yin magana yasa Adnan cikin slow voice irin na Wanda yagama zurmawa a soyayya yace“okay bazaki magana ba kenan ko Sabrine is okay Amma ki shirya ganina gobe Dan dole wallahi saina ganki ni dazaki yadda ma wallahi I will come see right now kinji pls”dasauri Sabine ta kashe wayar tayi wani mugun cusa kanta a pillow Dan wannan mutumin nema yake ya shallakewa tunaninta
Shikam Adnan jin wayar ta yanke yasa kawai yayi murmushi sannan yace “bakyagane wannan yaren Amma kishiryawa yaren dazan fara koyamiki silly girl”yakai karshan maganar had'e da ajiye wayar sannan yayi adduar bacci had'e da lumshe ido , shikanshi besan lokacin da bacci yayi awan gaba dashi ba cike da mafarkin burin rayuwar sa……
*Share and share again habibties😍*