Page 18
by @babyluv
*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_
1️⃣8️⃣
*BABYLUV✍🏻*
*****
Hajiya saleemeh da alhaji na babban parlor Azaune, Afiya and deeja sunje gidan kanwar hajiya saleemeh , ita kanta hajiya saleemeh niyar fita take saboda yanzu akai Mata wayar kayan ta sunsu kasancewar yadda take business sosai
Duban LEC A. M tayi kafin tace“nikam alhaji Adnan fa be kwana a gida ba and I called him baayi answering wayar ba and nasan Adnan indai bazai kwana a gida ba saiya Min waya koda patience ne suka masa yawa a hospital Dole saiya kirani but look now nikam tsoro nake ji I hope he's fine”
Tana rufe baki baki Adnan yashigo parlor d'in hannunsa ri'ke Dana Sabrine Wanda ta rufe idonta da gyale da alama kuka take , ganin Adnan da yarinyar ri'ke da hannunta yasa daga hajiya saleemeh har LEC A. M saurin Mi'ke wa , har tsakiyar parlon Adnan yashigo da Sabrine duk da yadda take cijewa Amma hakan besa ya sake fa , tunda yashigo idonsa a mahaifin nasa , yadda idon Adnan yayi jajawur zai tabbatar ma da he's not in good condition
Har gabansa hajiya saleemeh taje tare da karbe hannun Sabrine daka hannun Adnan tana fad'in “adnan from where, who is this girl yimin bayani ”tayi maganar tana zame hannun Sabrine daka fuskarta ta ganin yadda take hawaye yasa hajiya saleemeh cikin fushi take sake fad'an “banason iskanci Adnan kamin bayani wace wannan d'in”
Cikin wata murya wadda ko fita batayi sosai ya furta“she is my world , mommy this girl here itace rayuwata and itace farin cikin yaronki mommy the choice is yours kince nafito da Mata mommy here you go” yakama hannun hajiya saleemeh ya had'a Dana Sabrine, murmushi hajiya saleemeh tayi kafin tace “to meye abin tashin hankali aciki , meye na Bata ran Adnan abinda muke jira kenan dukkanmu daga ni har alhaji abinda muke jira kenan kuma duka zamui farin ciki da hakan sosai right alhaji? ”ta kalli LEC A. M da tun shigowar su idonsa ke kan Sabrine dajin haushin abinda Adnan yayi, kallon hajiya saleemeh LEC A. M sannan ya juya ya kalli Adnan da Shima kallonsa yake sannan cikin bacin rai yafurta“never this will not happen, Don't even think of doing it, I repeat don't even start”yakai karshan maganar Yana nuna Adnan da yatsa”
Cikin wani kallo na abin tausayi Adnan yake duban babansa jikinsa du yayi weak gaba d'aya wani jiri, jiri ya kalli Sabrine da harta durkushe kasa , kukanta har cikin ransa yake ji yarinya karamar wadda Bata San tension ba Amma shida maifinsa sunsata cikin matsala , rintse idonsa yayi sannan ya furta“but daddy why”
Cikin d'aga murya LEC A. M ya furta because I love her, I love her so much”
Da sauri hajiya saleemeh ta dubi LEC A. M dawani shock dayashiga jikinta cikin rashin gamsuwa da abinda ya furta bakinta na rawa tana nuna alhajin ta furta“you…love …her”
Cike da gwarin guiwar yace”yess I love Sabrine and I will not let your son marry her no matter what”
“innalillahi wa innailairrajuun”ta furta tana dafe kirjinta tana kallon Sabrine yadda ko Afiya zata iya girmarta tace“alhaji wai kasan abinda kake fad'a kuwa kasan me kakeyi kuwa wannan ai zubar da mutuncine da kima Taya zakaso sa'ar yaranka alhalin kasan Adnan na sanka ko kasha wani abunne”
Nunata LEC A. M yayi da yatsa kafin yafara fad'in “and Bari kiji akan Sabrine kokece kika bani matsala to tabbas zamu samu matsala dake bama d'anki ba”sannan ya juya ya kalli Adnan had'e da nunashi da yatsaya yace“kai kuma stay away from her I repeat it stay away from her kaji ko”
cikin magana me had'e da kuka hajiya saleemeh tace“if not fa? eye idan ya 'kifa nace?, Alhaji kadawi hankalin ka abinda kake Shirin aikatawa wallahi ba daraja a idon yaranka ba har a idon jamaa sai darajar ka ta zube”juyawa kawai yayi bece komi ba yayi section d'insa
Ita kin Sabrine jin bazata iya jure abin da ke faruwa ba yasa da gudu ta tashi ta fice daga parlon ko takalminta ahannu ta diba tana kuka, Adnan ne yabi bayanta Yana Kiran sunanta amma Ina ko tsayawa batai ba , tana zuwa get man ya bud'e Mata kofa ta fice , fitar ta ke dawiya kuwa tasamu wani me napep ya kawo wasu cikin area din aikam da sauri ta tsada shi tashiga tana masa nuni da yayi sauri yabar gurin, kafin Adnan yazo tuni tayi nisa cikin 'bacin Ran abinda ya faru Adnan ya buga hannunsa ha gate d'in gidan har Saida me gadi ya tsorata Yana gudun yayi masa magana Dan yaga baya cikin tunanin da sosai yasa Dole me gadin yayi shiru Yana jimanta abinda ya faru
Adnan be Kara shiga parlon ba kawai bangaren sa Shima ya huci Zuciyarsa nayi masa
Hajiya saleemeh ma kam kusan mutuwar tsaye tayi da ko zama kasayi tayi gashi tanada problem na ciwan kafa abin du ya hadu yayi Mata yawa ,sai kawai ta sulale a carpet d'in parlon ta zauna bakinta Banda Karan innalillahi babu abinda yake
Tunda LEC A.M yashiga parlon sa Banda Kai kawo babu abinda yake gaba d'aya yarasa nutsuwarsa kasancewar yadda yaga soyayyarsa da Sabrine zata hadda sa masa mummunan tashin hankali a gidan sa ,hakika shikanshi yasan abinda yake shirin aikatawa bame kar'buwa bane a society Amma to ya ya'iya tabbas shijin Sabrine ya a Zuciyarsa sosai meye mafita yanzu…
Tun da ta hau batacewa me napep d'in ga inda zata ba Shima d'in kuma be tambayeta inda zata ba ganin halin da take ciki ,Saida ta fara samin nutsuwa sannan ta fad'a masa ya kaita makaranta ,gudun sa'ido na Yan makaranta yasata goge hawayenta sosai sannan tasa ta kalminta
Har kusan kofar hostel d'in su me napep d'in ya kaita,tunkafin ta karaso ta hango mota Kamar ta Yaya farouk a gaban hostel d'insu,jitayi a Zuciyarta dama ace Yaya farouk da tabbas saita bishi Dan jitai bazata iya Kara ko kwana daya ba batare da taga Granny ba
Sauka tayi sannan ta sallami me napep d'in ya juya ya tafi,tsayawa tayi kafin ahankali ta fara nufar hostel d'insu duk da yadda ta goge hawayen fuskarta Amma hakan bazai sa ka kasa gane kukan da tai ba ,gakuma hawaye daya taru a idon ta Yana Shirin zubowa,
“Sabrine”
Ta tsinkayi muryar farouk a bayanta ,da sauri ta juya,shid'in ne kam Yana sanye da wani yadin kufta a jikin sa mekyau
Jitai wani dad'i ya lullubeta ganin farouk ,. 'karasa takowa yayi har zuwa inda take tsaye ganin yadda idonta yayi kalar na masu kuka had'e da damuwa ,da sauri yace“sabrine meke faruwa ?why are you crying ? Are you sick or what yimin bayani”…
*Aimin share pls free book ne share kawai nake bukata👏🏻*