HARAMTACCIYAR SOYAYYA

Page 20

by @babyluv

*💫FORBIDDEN LOVE💫*

 _Haramtacciyar soyayya_



         2️⃣0️⃣


 *Yanzu fa aka fara fans agyara zama a kakka'be zani*




      *BABYLUV*

        *****





Hakika adaren yau Adnan ya tabbatarwa da kansa Sabrine Shima kamar yadda daddy ya fad'a rayuwarsa sace , tabbas amai makon soyyar Sabrine tayi kasa Amma Kara zafi take masa , kirjinsa har wani d'aukan zafi yake , gashi adaren yayiwa Sabrine Kira yafi a irga Amma taki picking call din abin duka yayi masa zafi , shiyasa ya yanke hukuncin Kara komawa gurin Sabrine washe gari Dan tabbas akwai abinda yakeso yaji daga bakinta, dawannan tunanin yasamu bacci ya d'auke shi , abangaren hajiya saleemeh da LEC A. M kuwa yadda sukaga Rana haka suka ga dare ganin damuwa na neman yima hajiya saleemeh yawa yasa ta d'auro alwala ta fara gabatar da sallah da rokon Allah ya kawo Mata mafita a rayuwar mijinta da yaranta Adnan sannan kuma Allah ya yafe Mata zunubanta *KOWADANNE ZUNUBI NE*?



 Washe gari da safe Adnan yaji shi yadan Sami 'kwari

  Dan shi likita ne yasan yawan damuwa meyake jawo wa Dan haka yake tilastawa kansa gujewa damuwa, sosai ya shirya cikin wani yadi kufta mekyau da tsaruwar d'inki hakannan ya tsinci kansa da matso kyansa duk da dama shi kyakkyawan 

 Koda yafito ri'ke da makullin mota ahanunsa da yayi Kamar zai huce basai yashiga part d'in mommy ba Amma sai yaji ya kasa Dan Yana masifar San mahaifiyar sa hakan yasa ya juya Yana nufar part din mommyn

  Afiya da deeja kawai ya gani kan dinning sa'banin yadda ake had'uwa duka, jin ransa yayi babu dadi gaba d'aya, karasawa yayi gun dinning d'in Yana fad'in sarkin surutu cakwaikwaiwa tawa me aka samu ne, Dan turo baki deeja tayi Dan tasan da ita yake sannan tace“kai yayanmu nice cakwaikwar Allah kuwan saina fadawa daddy ”jinta ambaci daddy yaji gaba daya yanayinsa naso ya sauya hakan yasa ya basar da maganar da fad'in “Afiya Yana ganku ku kad'ai Ina mommy fa”cikin sanyin jiki tace“ brother bansan meke faruwa but tun jiya mommy Bata cikin mood yanzuma Dana aika deeja nagama break tace wai muyi mukad'ai and daddy ma bai fito ba kaga brother deeja takasa ma cin abincin kasan halin ta”k

 Kallon deeja yayi sannan ya kalli Afiya had'e da murmushi yace“kunsan dama arayuwa bakoyaushe mutum ke cikin jin dadi ba maybe ko bata feeling well ne Amma Bari naje Naga kuyi break d'in”yana fad'in haka ya nufi part d'in mommyn , tana zaune ta had'a Kai da guiwar gaba daya ta shiga cikin tunani , samin guri yayi ya zauna sannan yariki hannun hajiya saleemeh yace“mommy Dan Allah kiyi hakuri ki yafemin lefin danai Miki akan Sabrine wallahi mommy kema sheda ce ni bame kula Yan Mata bane bare nace zan Samo wata na aura ba Sabrine ba and tunda daddy yace na fita harkar ta mommy wallahi kullum zuciyata Kara samun kusanci take da Sabrine mommy meya kamata nayi ”yakai karshan maganar Yana share kwalla hakika Adnan mutum ne me juriya tunda har hajiya saleemeh taga Yana kwalla akan yarinyar Nan to lallai ba abune karami ba ya rabu da Sabrine, dafa kafardar da tayi tana fad'in “take heart Adnan Allah Yana sane da komi nayi Imani zai kawo wata mafita a almarinnan kaidai abinda nakeso dakai kada kayi fushi da mahaifinka saboda hannunka baya taba rubewa ka Yar kaji kaci gaba da addua”bece komi ba sai d'aga Mata Kai dayayi , murmushin jin dad'i tayi sannan ta ce“yanzu kuma sai ina”samun kansa yayi da boye Mata inda zashi kawai yace zai leke asibitine 'Dan kwana uku kenan beje ba , aikuwa taji dad'i tayi masa adduo'i kamar yadda ta Saba sannan yayi Mata sallama ya fita



Direct school d'in su Sabrine ya nufa da zumud'in San ya ganta Dan seriously dayasan cewar abinda zai faru jiya dayakai Sabrine ke Nan toda tabbas ba'abinda zaisa ya kaita shiyasa yanzu yakeso ya Bata hakuri dakuma San yaga fuskarta Dan ya tabbatar sunsata a damuwa


 Har hostel d'insu yakai Dan yasan asabar ce babu class shiyasa kawai ya huce Nan direct

 Parking yayi sannan ya bud'e motar Amma Sam be fito ba Dan yasan indai ya Kira sabrii tabbas bazata fito ba , shiyasa ya zauna Yana ta jira yaga meya kamata yayi

 Yana tunanin mezai yi d'innan yaga wata ta nufo hanyar hostel d'in and yana da tabbacin ciki zata shiga , tun kafinta karaso yafito ya rufe motar ya tsaya ajikin motar , duk macen da taga Adnan to tabbas sai ta Kara kallonsa,

 Tazo zata gifta ne kamar bazai magana ba saikuma cikin wata shakakkiyar murya kamar Wanda aka tilasta wa yin magana yace“ excuse me pls “ dama sai wani karairaya take da fatan Allah yasa guy d'innan yayi Mata magana, aikuwa cikin washe baki ta juye ta tsaya tace“yess how may I help you”jiyayi gaba d'aya ta bashi haushi Mace ko class babu jibi yadda take wani washe Mai baki, danne abunda yaji na haushi yayi sannan yace“ please Latipha fa”



Yatsina hanci tayi jin ba abinda take tunani taji ba tace“tana ciki ” 


“owk please tell her tana da

Ba'ko please”kamar bazatace komi ba ta juya had'e da fad'in okay 

Wani kallon ta kaici yabita dashi Dan ya tsani mace ballagaza Mara kamun kai , yananan tsaye Latipha ta fito tana Dan dube dube tanaso wake kiranta gaskiya Bata Bari kowa yazo gunta a school , ganin Adnan a tsaye tayi mamaki sosai ta karasa gurinsa da murmushi tana fad'in “a'a Dr badai kai ka aiko kirana ba” ganinta da shiga ta kamala yasa yaji har Zuciyarsa har kallinsa ya kwanta taraiyarta da Sabrine , gyara tsaiwarsa yayi had'e da fad'in “wallahi kam nine Latipha , kinganni da safe”

Murmushi tayi tace“wallahi kam Allah yasa lafiya ”d'an Jim yayi sannan yace“lafiya qalau Latipha kawai dai 'kawar kice ta sani a kwana Allah yasa dai tananan”

Da mamaki a fuskarta tace“to ai Sabrine tun jiya ta tafi gida ”


“ta tafi kuma”


“eh ta tafi Bata fad'a ma bane Aida ka kirata awaya”wata ajiyar zuciya Adnan ya sauke kafin ya dubi Latipha da fad'in “shikenam abinda zai faru Latipha ko zaki temakamin da address d'in gidan su”murmushi saoai Latipha ta karayi da har cikin zuciyarta tanason Adnan da Sabrine kuma ta tabbatar ita kanta Sabrine ta fara son Adnan kawai dai yarinta ta hanata gano hakan“eh meze Hana ”bud'e motarsa yayi ya d'auko wani memo da pen sannan ya rufe motar Yami 'kawa Latipha , karba tayi tarubuta masa address d'in dalla, dalla yadda zai gane Dan zataji dadi in har Adnan yaje har gida yasamu Sabrine at least Granny zata San da zaman Adnan, godiya sosai Adnan yayi Mata sannan ya bud'e motar raper d'in dari biyar ya bawa Latipha Amma Sam Taki karba Saida yasha fama da ita sannan ta karba tai masa godiya da adduar Allah ya bashi Sabrine aikuwa Latipha taga fara'ar da Bata ta'ba gani ba a fuskar Adnan ahaka yashiga motar ya bar school d'in , itama Latipha da farin ciki ta juya ta bar gurin


Jiyayi bama zai iya Bari sai gobe ba hakan yasa kawai ya koma gida ya karayin wanka , ya d'auko wata shegiyar shadda maroon Banda kyalli babu abinda take ya d'auko huka kalar aikin shaddar yasaka with black takalmi , inkaga Adnan yadda yayi kyau rantsewa zakai wani balarabenne ba d'an kasar Nan ba yasa manyan Kaya, turare Babu kalar Wanda be fesa ba , sannan ya d'auko key din wata sabuwar motarsa da befiya hawa ba sai lokaci zuwa lokaci, sannan ya fito hakannan yakejin Zuciyarsa cikin farin ciki kodan zaiga Sabrine ne oho


 Ta saman bene LEC A. M dake zaune Yana duba wata news paper ya hango Adnan zai shiga motar yadda yaga Adnan ya dau wanka yayi kyau Saida yaji kirjinsa ya buga a Zuciyar sa yace“ Allah yasa ba gun Sabrine zai je ba”akan idonsa driver ya bud'ewa Adnan gate ya fice , jiyayi gaba d'aya Yama kasa duba news paper d'in hakan yasa kawai ya tashi yabar gurin………


*Share and comments habibties*