33&34
by @realeshaa
*TWIST OF FATE*
_(Karkatarwan Ƙaddara)_
_By_
_REAL ESHAA_
*Littafina na kuɗine gamai buƙatar karantawa #300 Via 6030406548 Abdullahi Aishatu keystone Bank ko kuma katin MTN ta wannan number *** sannan atura shedar biya ta hanyar screen short masu ɓuƙatar atura musu PC zasu tura#500...*
*Free page 33&34*
Kallonta Dada tayi da faɗin"wannan ba abinda zaki ɓoyewa bane Ainah You support to tell us.Cikin matsanancin kuka tace"Nayi zaton zan iyai dedeta matsalar da kaina,nayi zaton zan iya ɓoye maganar batare da kowa yajiba har na samu solution amma hakan ya gagara but am loosing,lumshe Ido Abbey yayi cikin yanayin tausayinta yasan Ainah baza ta aika son Kai irin hakaba,Hannun Ummu data ƙi kallon inda take ta riƙe tace"Ummu ako da yaushe ina sauraron Shareef ne saboda Sister Sajnah ban taɓa zaton cewa wani abu makamancin haka ze kasance atsakanin mu ba",Asanyaye Dada tace"Hafsat Kinfi kowa sanin halayyar Ainah baza ta taɓa abu makamancin haka dan ta cutar da kowa ba bare kuma ace 'yar uwarta,Still ƙin cewa komai Ummu tayi,cikin gunjin kuka sosai tace"Ummuna naje wajen ne adomin na fahimtar da Abdul irin soyayyar da Sajnah ke masa amma badan komai ba, Ummuna sister Sajnah baza ta taɓa rayuwar farin ciki da mutum irin Abdul ba, Akullum Abbey beda burin daya wuce yaga mun samu masoyan gaskiya amma ba haka Abdul yake ba shi mutum ne me son Kai dan Allah Ummuna ki yafe min idan na ɓata Miki",Ahankali Ummu ta juyo tare da shafa kanta tace"nasan bakida lefi Ainah,cikin kuka sosai tace"toh amma Meyesa kike ganin kamar nayi lefi har kike fushi dani!?...Ƙin cewa komai Ummu tayi takuma ƙi kallonta,sake hannun Ummu tayi ta toshe bakinta,Araunane tace"Um-Ummu, Ni-ni kasa ƙarasawa tayi sakamakon kuka da yaci ƙarfinta,Ahankali Abbey ya ƙaraso kusa da ita, hannu yasa ya dafa kafaɗarta Ahankali ta juya tare da ɗaga manyan Idanunta da sukayi ja tace"Abeey I didn't,I didn't do anything wrong to my sister.Rungumeta Abeey yayi da faɗin"I should have trusted my daughter,I should have realised,that you could never wrong your sister I'm so sorry".Ajiyar zuciya ta saki tana sake rungumesa, Ɗagato daga jikinsa yayi ya mayar da kallonsa kan Ummu yace"Hafsat ki yafemin zarginki da nayi I'm sorry."Batare data kallesaba tace"ba buƙatar hakan kawai ka manta da abinda yafaru abu ɗaya yakamata mudamu dashi ayanzu shine lafiyar Sajnah".Cike da damuwa Dada tace"Moh'd ya jikin Sajnah,kai ya girgiza yace"Har yanzu Dr bece komai ba",Insha Allah Sajnah zata ji sauƙi cewar Ummu.Kallon Dada Abeey yayi yace"Mama ya kamata ki koma gida dan kema ba cikakkiyar lafiya bace dake.Kai Dada ta girgiza tace"babu inda zanje nabar Sajnah acikin wannan halin.Kallon Ummu Abbey yayi da faɗin"Hafsat kiyi magana da Mama ta koma gida Insha Allah Sajnah zataji sauƙi",Kai Ummu tagyaɗa tace"Hakane mama ki koma kawai,kai Dada ta gyaɗa tare da tafiya bayan ta sake duba jikin Sajnah tare da yimata addu'ar samun sauƙi.Kallonsu Dr yayi yace"jikin Sajnah yayi tsanani idan har ba'a samu jini ba za kuyi rasata!,Hannu Abbey ya ɗaga da damuwa afuskarsa yace"yanzu meye abinyi Dr",Kai tsaye De yace sede muje agwada jininku wanda nasa yayi dede asa mata, kai suka gyaɗa tare da bin bayansa....
Wani irin dafe kai RK yayi suwwan Muryan Abeey na sake karaɗe ilahirin dodon kunnensa,jin motar ya tsaya yasa ya kalli inda suke wajene me dan girma Sede be fiye hayaniyar mutane ba ko wanne da abinda yake fita sukayi amotar suka shiga wajen,Mutumin da babu riga ajikinsa yana zane kansa da wata murtiƙeƙiyar doruna RK ya nufa,da wani irin sauri Dr Lucky ya riƙesa yace"baka da hankali ne kasan masu irin wannan abin wani irin lefi suka aikata har sukeyi?ko Kallonsa RK beyi ba ya nufi mutumin cikin Yaren Ikware yace"kaban kallonsa mutumin yayi batare daya basa,Duk yanda RK yaso mutumin ya basa ƙi yayi ganin shi baɗan ƙabilarsu bace ba,Ganin mutumin nason ɓata masa lokaci yasa ya ciri kuɗi masu yawa ya danƙa masa,Ganin yawan kuɗin yasa mutumin amsa tare da basa murtiƙeƙiyar dorinar.Da sauri Ummi ta buɗe ƙofar ward ɗin tashiga,Wajen Granyy da dake zaune ta nufa tare da sallama,batare da Granny ta amsa sallamarba tace"Meya kawo ki kitafi bama buƙatar ki!,cikin sanyi murya Ummi tace"Nasan bayan abinda Abdulrahman yayi wa Sajnah baza kuso sake ganin wani nasa ya raɓaku ba amma ina me baku haƙuri da ku yafe masa.kafin suce wani abu wato Norse ta fito tare da miƙawa Abbey da zuwan su kenan paper tace"yasayo magani, karɓa Abbey yayi tare da juyawa yabar wajen, Ahankali Ummu tayi ƙasa da kanta batare da tace da Ummi komai ba ganin mugun kallon da Granny ke jifanta dashi...
Da sauri Dr Lucky ya riƙe hannun RK yace"Dr RK nifa ban kawo ka nan dan kayi irin wannan abin ba wannan hukuncin da kake gani se wanda suka aikata mummunan aiki kamar wanda sukayi rapping Yara ko kuma tsafi da iyayensu amma kai meka aikata me muni har haka?,ɗauke kai RK yayi ya karɓi shirgegiyar dorinar da takai Hannunsa kauri,Da ƙarfin gaske ya ɗaga ya zuba adokin wuyansa Atake wajen ya tashi yayi wani irin ja rigar ta yage,rintse idanunsa yayi jin wani irin azaban raɗaɗi daya ratsa tun daga tafin ƙafansa zuwa ƙwaƙwalwar kansa da wani irin zuciya yake zubawa dukkan gaɓɓan jikinsa duk da yanajin azaban zafi na ratsasa anma zafin da zuciyarsa keyi yafi na dorinar,wani irin lumshewa idanunsa keyi yayin da jikinsa ke fitar da zufa tamkar wanda aka sanya shi a gidan biredi,mutane kuwa taruwa sukayi musamman 'yan ƙabilar da suka san irin wannan hukuncin na hawa kan babban me laifine,wani irin jiri ne ke ɗibarsa yanke jiki yayi ya faɗi,Da sauri Dr Lucky ya ƙaraso kansa yace"Please Enough Dr RK kada ka cutar da kanka,lumshe Ido RK yayi kalaman Ainah nayi masa suwwa acikin dodon kunnensa Natsaneka Abdul kai mayaudarine bakasan komai ba face son Kai!,miƙewa yayi tare da Ingije Dr Lucky akusa dashi ya cigaba da zubawa kansa dorinar fatar wajen na kwailewa...
Fitowa Dr yayi da sauri Abbey yataresa da faɗin"Ansamu jinin daya dace da ita?",Kai Dr ya gyaɗa tare da nuna Ummu yace"Madam muje aɗibi naki,kai Ummu ta gyaɗa,Wani irin kallo Granny ta musu tace"Dr ba za'a iya samun jini a lab ba?,"Da mamakin tambayarta yace"Za'a iya amma ze Kai Nanda minti talatin,Taɓe baki Granny tayi tace"zamu jira to",wani irin kallon mamaki da al'ajabi suke binta dashi musamman Ummu da Abbey.Ka faɗa Dr ya ɗage da faɗin"wannan matsalarku ce ta cikin gida amma ita majinyaciya bazata iya jiran wannan lokacin ba,"mDa sauri Ummu tace"Dr muje ka ɗibi nawa baza mu iya jira ba kana ta mayar da kallonta kan Granny tace"Dan Allah Mama kibari inbata jinina tamkar uwa nake ga Sajnah idan ma kinaso kiyimin hukuncine abisa wani lefi da namiki to kibari inbada jinin ta faɗa tare da juyawa tabar wajen,Wani irin kallon tsana Granny tabi ta dashi ...
Ahankali Ainah ta fita gaban asibitin ta tsaya wayarta dake cikin aljihu ta ciro,da mamaki take kallon sunan Dr Lucky dake yawo a screen kuma video call kasancewar datar ta abuɗe yake,kamar ba zata yi Picking ba se kuma tayi,Cikin yanayin tashin hankali Dr Lucky yace"Please Ainah I need your help,be jira jin abinda zatace ba ya cigaba da faɗin"Dr RK yana azabtar da kansa saboda ke dubi halin da yake ciki ya faɗa yana nuna RK dake dukan kansa cikin tsananin galabaita, Please Ainah kitemaka kizo kiceci rayywarsa,manyan Idanunta ta wara tare da toshe bakinta jin kuka na neman kufce mata Kai ta girgiza cikin Muryan daya dashe da kuka tace"a'a bazan zoba 'yar uwata na cikin mawuyacin hali adominsa dan haka yaje yayi duk abinda yaga dama ta faɗa tare da ajiye wayar kuka ta fashe dashi tana jin zuciyarta tamkar ya fashe.
Ahankali Abbey ya riƙo kafaɗar Ummu suka fito bayan an ɗebi jinin har zuwa lokacin Ummi na tsaye, kallon Abbey Ummu tayi tace"ina Mama?,Kallon wajen yayi da faɗin"tana tare da Sajnah kai Ummu ta gyaɗa.Cikin yanayin tashin hankali Granny ke Jijjiga Sajnah dake kwance da ƙarin jini, Asanyaye tace"Sajnah Akullum kina saurarana bakya min musu yauma kada kiyimin musu ki tashi Please!,wake up!,wake up Sajnah.Shigowa Dr yayi Ummu,Abbey, Ainah na biye dashi,hannunta Dr ya ɗaga tare da buɗe idonta yace"Agaskiya se ansata acikin crome idan ana so ta farfaɗo,cikin kuka sosai Granny tace"Kar kace haka Dr dan Allah katemaka mana...
Ahankali Driver Daddy yayi parking motarsa Anutse Daddy yafito tare da fitowa da wayarsa dake cikin aljihu yayi dearling wata Number ba daɗewa mutumin daya kira yazo,wanda zasu tattauna harƙan kasuwanci,kallon Massinger sa Daddy yayi yace"meke faruwa haka naga cincirindon mutane?.Da damuwa Massinger yace"wani saurayine yake dukan kansa saboda wani lefi da yayiwa Ubangiji,Da mamaki Daddy yace"Idan mutum yayi lefi kamata yayi ya nemi yafiyar Ubangiji,Da jimami mutumin yace"Wannan al'adar ƙabilar Ikware ne,Kai Daddy ya Jinjina da faɗin"Allah ya kyauta yana ɗan leƙawa sede be iya kallon fuskar matashin saboda mutane se bayansa daya fashe rigan jikinsa ya fatattake,juyawa Daddy yayi ze wuce,Dede lokacin da Cikin Ihu Dr Lucky yace"Please Enough Dr RK,Cak Daddy ya tsaya tare da juyawa ya nufi inda mutanen ke tsaye dan ganin wani Dr RK ne?w
Wani irin zare ido Daddy yayi ganin RK jini ya ɓata rigar dake jikinsa...
Cikin matsananci kuka Granny tace"Sajnah ki tashi kada kibarni,tale baki Ainah tayi tare da ture Dr ta ta zauna gefen gadon ta riƙe hannun Sajnah tace"Dan Allah ki tashi sister Sajnah babu abinda ze sameki",Wani irin kallo Granny ta mata da faɗin" Stay away from my granddaughter,"Kai wannan mata tafiye jaraba da faɗa cewar Dr aƙasan ransa amma a fili se yace"Mama kibarta kalamanta zasu iya tasiri ga ƙwaƙwalwar Sajnah har ya temaketa.Banzan kallo ta watsa masa ta lura dashi zeyi kinibibi,(Granny duniya🤣🤣🤣🤣).Cikin wata raunan'niyar murya Ainah tace"nasan kina fushi dani sistrr amma kisani rayuwata baze taɓa cika ba idan babu ke acikinta dan Allah ki buɗe idanki nasan kina jina kada kice zakiyi fushi dani na tuba",wani irin kallon tsana Granny ke jifan Ainah dashi...Wani irin kallon mamaki da al'ajabi Daddy kebin RK dashi ya gaza ƙarasawa wajen,zuciyarsa tashiga saƙa masa wannan ba ɗan sa bane shin me zekawo ɗansa wannan wajen,Ɗago kai RK da zeyi Idanunsa suka sauƙa akan Daddy dake tsaye, yanke jiki RK yayi ya faɗi,akuma dede Lokacin Sajnah ta buɗe Idanunta da taji sunyi mata mugun nauyi...
Da wani irin farin ciki Ainah tace"D..Doctor Sajnah D...Doctor Sajnah ta buɗe Idanunta, Ahankali Sajnah ta sauƙe Idanunta akan Granny dake kuka yayin da hawaye suka shiga bin kuncinta, Ahankali ta buɗe bakinta da maganan be fita tace"Ummu,wani shegen kallo Granny ta watsawa Ummu tare da miƙewa daga wajen,da sauri Ummu ta zauna inda Granny ta tashi tare da riƙe hannunta tace"Sajnah munji tsoron wani abu ya faru dake, Murmushi Sajnah tayi hawaye na zuba daga Idanunta.Murmushi Dr yayi yace"Alhamdulillah jikinta yayi sauƙi da alama da akwai wanda ya dage da addu'a, Lumshe idanu Ainah tayi tare da tuno video RK da Dr Lucky yayi, Ahankali Sajnah ta juyar da Idanunta gefe akan Ainah dake riƙe da hannunta ta sauƙe Idanunta, Ahankali kalaman Granny suka shiga dawo mata cewa Sajnah Abdul baya sonki Ainah yakeso wacce kika ɗauka amatsayin 'yar uwa taci amanarki,rintse idanunta tayi tare da janye hannunta dake cikin na Ainah batare data sake kallon furkartaba,wasu hawaye Masu zafin gaske ne suka zubowa Ainah hannun tasa tashare Miƙewa tayi da faɗin"zan tafi,cikin dabara Ummu ta maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata tare da sakarwa da Sajnah Murmushi.Abakin ƙofa Ainah taga Ummi tsaye,kawar da kai tayi gefe tace"Sajnah ta masu sauƙi zaki iya shiga",Alhamdulillah Ummi ta faɗa cikin sanyin murya tace"bari na tafi kada na dameku,Shiru Ainah tayi tanajin tausayin matar,har ta fara tafiya Ainah tace"Ummi,Cak Ummi ta tsaya tare da juyawa, batare da Ainah ta kalleta ba tace"Abdul yana cikin yanayin temako ta faɗa tare da barin wajen...Da wani irin gudu Daddy ya nufi kan RK tare da ɗagosa ya rungume.Jirgin ta kadda Faruk ya naɗa tare da kallon hoton Ummi, RK da Daddy,yana nuna kan RK Abdallah dake gefensa ya miƙa masa ayaba daya ɓare,kafin Faruk ya karɓar wayarsa ya hau ruri cirowa yayi tare da Picking Arazane ya miƙe yace"Ummi kina ina yanzu,Ok ganinan zuwa ya faɗa tare da katse kiran.Cikin ƙasa da murya Faruk yace"bayan Accident ɗin Sajnah da alama Akwai wani sabon labari daze riskeni", Ahankali Mom tace"Nima ban saniba Sede mutsaya mu gani, Abdallah na fita yaci karo da Daddy dake shigowa da RK cikin tashin hankali ya tallafesa suka shigo dashi,Arazane Mom ke kallonsa ganin yanda ya jiwa kansa ciwo,miƙewa tayi tare da faɗin"meyasa meshi,ba Wanda yace"da ita komai suka kwantar dashi Abdallah yaciro waya tare da kiran Dr,Cikin ɗaga murya Daddy ke Kiran Fatima, Fatima,ƙasa da kai Mom tayi tace"ta fita,Afusace yace"ɗan ta ba lafiya shine za tasa ƙafa ta fita?.Cikin tashin hankali Ruƙayya tace"Daddy Meyesa mesa?,"kuskuren daya aikata ne yaje adomin ya gyara cewar Ummi data shigo cikin matsananci kuka,da kallon suka bita yayin da Faruk ya taɓe baki ƙasan ransa fari,kusa da RK Ummi ta ƙarasa tare da dafa kafaɗarsa, kwallonta ta mayar kan Abdallah tace"ka kira Dr?",kai ya gyaɗa,tare da ciro wayarsa wanda yayi dede da shigowan Dr,"Ummi gashi nan ma da sauri Dr ya ƙaraso yace"Excuse me cikin gaggawa ya ɓalle botiran rigan tare da sassaka masa bandeji ya gyara duk inda yaji ciwon.miƙewa Dr yayi yace"Kubiyoni kai Abdallah ya gyaɗa yace"muje sannan suka fice,Wata mahaukaciyar Dariya Faruk yasheƙe dashi tare da wurgawa RK da babu alamar numfashi ajikinsa jirgin takaddan yace"Oooo kai mugune kaga saka makonka ko?ka cutar da rayuwata kaima ga naka ahaka!",Hararansa,Mom tayi tace"Kayi shiru Faruk, Hannun yasa ya kama laɓaɓɓansa still fuskarsa ɗauke da murmushi,Cikin fushi Daddy ya kalli Ummi da faɗin"Ahaka kike tunanin zaki ɗauki nauyin iyalanki baki ɗaya ahaka kike tunanin zaki iya kulawa dasu shin me kika tsaya yi har Abdulrahman yaje yayiwa kansa irin wannan illar!?".Cikin sauri Mom tace"Yaya be kamata kaga lefin Aunty acikin wannan maganar ba ko kamanta abinda RK ya shuka shiyake girba??taya ze cutar da marainiya wacce bataji bata gani ba wannan shine sakayyar ƙaryansa da kuma zaluncin da yayi babu lefin Aunty aciki!".Cikin wani irin fushi Daddy yace"Hajara kada ki manta irin sadaukarwan da Abdul yayi akan ɗanki Faruk ko ki manta abinda kika shirya aranan auren Faruk ne ganin kin ruguza wa Abdul farin ciki!??.Shiru tayi tare da ƙasa da kai.Cikin damuwa Uncle Jabeer da shigowan sa yace"Abdul me yasa meka?,kallonsa ya mayar kan Daddy dake tsaye yayi da faɗin"yaushe ka dawo,Ataƙaice yace"Yanzu...Ƙasa da kai Mom tayi tace"nayi hakan ne saboda in ƙara dan ƙon zumunci dake tsakanin mu sannan asake samun jituwa",cikin fushi Daddy yace"wani irin zumunta kike tunanin haɗawa ahaka?.
Harara ta maka masa kafin yace"Yaya kayi haƙuri amma koba komai yanzu Abdul ya samu yarinyar data dace da rayuwarsa yar mutunci anma ya yaudareta, Amaimakon ya riƙe ta da hannu biyu seya juya akalarsa zuwa ga wancan gantalalliyar yarinyar.
Afusace Uncle Jabeer yace"Hajara Shut up!,Wani banzan kallo ta watsa masa tare da ɗauke kanta agaresa,"Cike da mamaki Daddy yace"Me kike nufi?,Matsawa kusa dashi Mom tayi,cikin tashin hankali Ummi ta girgiza mata kai alamar kada tace"komai,Kusa da shi ta tsaya cikin kawar da kai gefe tace"Abdul yana soyayya da ƙanwar Sajnah wato Ainah.... Afusace Daddy yace"
Ki tsare kalamanki Hajara kisan irin kalmar da zaki dinga furtawa akan ɗana wannan maganar yasa takasa ƙarasa abinda ke ranta!,Itama cikin ihu tace"Idan har baka yadda dani ba ka tambayi ɗan ka!.
Wani irin kallo Daddy yayiwa Ummi cikin ihu ya e"Fatima ki faɗa min gaskiya nasan ɗana baze taɓa aikata irin haka ba!, Shiru Ummi tayi,Hannu Faruk ya buga da ƙarfi tare da hargitsa tulin sumar kansa yace"Oooo Nooo Ummi bata yi ƙaryaba kaine maƙaryaci,kai da ɗanka duk maƙaryata ne,ku mugayene kuma maha'inta kun fara ganin sakayya.Afusace Uncle Jabeer yace"Ya isheka Faruk idan kasake magana sena maka dukan tsiya"!.Kashe masa Ido Mom tayi alamar yayi shiru kafin ta maida kallonta kan Daddy tace"Yaya yanzu kabani amsa!. Afusace Uncle Jabeer ya nufeta yace"Hajara bance kada ki ƙara furta koda kalma ɗaya ba, Afusace ta kalleshi tace"A yau bazanyi shiru ba Sede ka fita acikin gidan,ta miƙe tare da ɗago Faruk tace"ka dubi yanda rayuwar ɗan mu ya kasance,ta maida kallonta kan Daddy tace"Yaya kanaso ka mayar da rayuwar ɗan ka kamar yanda ka mayar da rayuwar Faruk abisa kuskure iri ɗaya?ina jiran amsar ka?".Wani irin cukowa da ruwan hawaye idanun Ummi sukayi.Da ƙarfi Mom ta fin ciki hannun Faruk tace"Let's go inside Tunda bashi da abin faɗa,kuka Faruk ya fashe dashi yana turjewa.
Shigowa Dr yayi kallon Ummu yayi yace"yanzu jikinta yayi sauƙin dan haka mutum ɗaya ne ze zauna da ita kafin Ummu tace"Komai Granny tace"Ni Zan zauna da ita"Amma Mama, hannu Granny ta ɗaga mata da faɗin"nagama magana Murmushi Ummu tayi tace"badamuwa mama ku zauna Ummu ta faɗa tare da sumbatar goshin Sajnah tace"Allah yabaki lafiya daughter, Murmushi Sajnah ta mata hawaye na taruwa a Idanunta,kasa fita Ainah tayi,Ɗauke kai Sajnah tayi daga barin kallonta.Ahankali Ainah tace"take care of yourself Sister ta faɗa tare da ficewa, Lumshe idanu Sajnah tayi hawaye suka zubo...Ummu nashiga gida ta kalli Ƙawar Granny dake zaune tace"Mama bari na haɗa muku abinci,hannu ta ɗaga mata da faɗin"bana buƙata kallon Abbey tayi tace"Moh'd kawomin fura,Kai Abbey ya gyaɗa ita kuma ta shige, Ajiyar zuciya Ummu ta sauƙe tace"Abbeyn Sajnah Ina so na kawai Mama abinci anma nasan kona kai baza taciba,"Murmushi yayi da faɗin"Kar ki damu zan haɗa mata,kai ta gyaɗa tace"muje ina tayaka.Hannu Ainah tasa a aljihun wandonta tare da ciro wayarta dake ruri baƙon Number ta gani Picking tayi tare da kaiwa kunnenta.Daga ɗaya ɓangaren dariya me sauti Faruk ya fashe dashi yace"Oooo Ya kusa mutu!wa,Kinyi ƙoƙari RK ya kusa mutuwa!. Ahankali tace"Waye kai?",Ido Faruk ya kashewa Mom da sauri Mom tace"Meyesa ka kirata bayan ita Sede tasa abu yayi tsanani bazata iya gyarawa ba kana gani zatayi sanadiyyar ɗan uwanka,"lCikin yanayin maganarsa yace"Oooo But Mom RK is die ya faɗa tare da katse kiran.Daga ciki Ummu ta ƙwalawa Ainah kira tuno irin yanda RK ke dukan kansa tayi aruɗe ta fice da gudu da faɗin"Ummuna ina zuwa...
Ɗago kan Sajnah Granny tayi tare da bata ruwa, Ahankali tasa hannunta ta ɗauki wayarta,ajiye glsscup Granny tayi tare da kallon Sajnah tace"me zakiyi da waya?!,Murmushi tayi cikin yanayin sanyin muryanta daya haɗu da rashin lafiya tace"Abbey zan kira ina son sha madara,kanta Granny ta shafa tace"Sajnah ina so muyi magana dake akan Ainah da sauri Sajnah ta kalleta,Zama Granny tayi tare da riƙe hannunta tace"Nasan bakya sauran kowa akan Ainah da mahaifiyarta amma yanzu ya kamata ki fahimci komai tunda Mahaifinki ya auro wancan gantalalliyar matar muka rasa farin ciki,gashi yarinyar da kika ɗauki yadda da amana kika bata ta yaudareki Idanunta nakan soyayyar ki seda taga tarusa miki farin cikin ki baza ki taɓa kasancewa da RK amatsayin mijiba kuma kinsan hakan ya faru adalilin Ainah ce.Kawar da kai gefe Sajnah tayi tana tuna lokacin da Ainah bata da lafiya irin yanayin tashin hankali data ga RK aciki da kuma yanda yake rawan jiki,cikin kuka Granny tace"kiyi tunani me kyau uwa da 'ya sun ruguza miki rayuwa kiyi tunani duk me ƙaunarka baze maka haka ba Ainah maƙiyiyar kice ataƙaice ita ba 'yar uwar ki bace,da wani irin sauri Sajnah ta kalli Granny tana jiran ƙarin bayani...Cikin ƙasa da murya Ainah tace"Please Faruk bari zan koma,kai ya girgiza yace"Oooo babu inda zakije se kinga halin da RK yake ciki kafin tace"wani abu ya fin ciki hannunta da gudu suka nufi cikin gidan ta ƙofar baya suka shiga yanda babu me ganinsu duk yanda Ainah taso ƙwace hannunta daga riƙon da Faruk ya mata kasawa tayi.Kallo ɗaya zaka musu kasancewa suna cikin yanayin tashin hankali da ɗimuwa,Sannu Ahankali RK yafara buɗe idanunsa da yaji sunyi masa mugun nauyi akan Ummi dake daf dashi ya sauƙe Sanyayyar Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe fuskarta ɗauke da Murmushi tace"Abdul ka tashi?,Kai ya gyaɗa mata yana Murmushin ƙarfin hali,Kallonsa ya mayar kan Daddy dake facing ɗinsa yace"Daddy Kaine agida a irin wannan lokacin?.Kafin Daddy yace"komai Ummi tace"Abdul shiya kawo ka ai,Kai ya gyaɗa yace"Ummi ya jikin Sajnah?,"Nayi magana da Dr yace"da sauƙi.Wani shegen kallo Ainah dake ƙofan baya tare da Faruk ta watsa masa!.Miƙewa Daddy yayi yace"Abdulrahman ina son magana da kai akan Ainah.Wani daɗi ne ya mamaye zuciyar Mom da Faruk alokaci ɗaya,cikin sanyin murya Ummi tace"Daddy kayi haƙuri yanzu fa yatashi,idan anjima za kuyi magana.
Hannu Daddy ya ɗaga mata batare da yace komai ba.Murmushi RK yayi yace"Don't worry Ummi, kallonsa ya mayar kan Daddy yace"Daddy zaka iya tambayata komai,"Cikin ɗaure fuska yace"Ina son sanin shin gaskiya shin dagaske kaida Ainah kuna son juna!?.Wani irin bugawa zuciyar Ainah da RK yayi alokaci ɗaya...Kai RK ya girgiza da faɗin"A'a Daddy,Zare ido Mom tayi tare da kallon Ummi tace"Aunty kiga RK baya kunyar ƙarya agaban mahaifinsa,Kallonta RK yayi yace"Ba ƙarya nake ba Mom,harara ta watsa mai tare da ɗauke kanta jin rainin hankalin da yake.Anutse yace"Daddy ayanzu banaso in sake karya zuciyar kowa inaso in faɗa muku duk kan gaskiyar dake tare dani,wani irin kallo Ainah dake tsaye take binsa dashi me cike da tsana.Cikin rashin fahimta Daddy yace"Me kakeson cewa?, Ahankali ya yunƙura ze miƙe,cikin sauri Ummi ta tallafa masa,Cikin gaskiya da gaskiya yace"Daddy I nason Ainah kuma zan cigaba da sonta acikin raina...
*AYI SHEARING SABODA ALLAH*
*Ya Allah Ubangijin kajiƙan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunubansa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajiƙan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani...*
*ESHAA CE*🤙🏻