KAICO NAH

Page 42

by @sadisakhna

🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵


       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......



DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER


Wattpad:SAKHNA03


🏵🏵🏵

...42....






Bayan dawowar su maryam shiru ana jira a ga wani sanji amma babu,tun suna saka rai har suka sallama wa Allah ikonsa.

Yanzu abin yayi sumayyah sauki,dan bata zuwa makaranta saidai idan aikinta zata kai dr hunu ya duba mata,ko yaushe tana wajen aikinsu,idan ta dawo kuma in an bata wani aikin tayi,idan kuma babu ta bincika abin karatunta.

Yanzu ta kara busy sosai,abinda hajiya Aisha take sonta dashi na jajircewa yafara fitowa,dan ji take da ita kaman tsoka daya a miya.

Hankalin ta kwance take sakata aiki yanda ya dace.

Wata rana taje aiki da safe,riga da wandone a jikinta na Pakistan sai gyalen daya yafa shima a kanta.

Mai napep ne ya sauketa a kofar wajen tashiga da kafarta.

Dayake tayi dan sabo da mutanen wajen,kusan wata uku kenan da zuwanta.

Office din hajiya aisha ta shiga kafin ta wuce nasu na ma'aikata,a zaune ta sameta tana duba wani abu a takarda.

"Sumayyah kece,an fito kenan?"

"Eh hajiyah ya aiki"

"Lafiya Kalau,dama akwai abinda nakeso nafadamiki,munyi da director mu na abuja akan cewa zan turaki ki kara koyon aikinki sosai,dan sun bude sabon samfuri wanda bamuda shi a nan,ko ya kikace,amma sai sanda kika shirya"

"Eh Toh Idan har za'a jira mai laifin nabari saina gama da makaranta tukunna,inyaso sai nayi service a can,ina zuwa wajen koyon"

"Eh to kin kawo shawara hakanma,inaga hakan za'ayi kam,Allah yabada sa'a ki gama din"

"Nagode da taimakon dakike min hajiya"

"Lah karki damu ba komai,nasan idan kin koyo din zamu bunkasa abinmu sosai,koya kikace,ni fah harkar samu bana raina ta ko kadan"

Dariya sumayyah tasaka kafin ta bar office din.


Lokacin da su sumayyah suka karbo takardarsu kuwa ta service,murna kaman ta nutse.

Da gudu ta shigo gidan da yamma,dan tun sake suke can ana ta bikin samun nasarar gamawa.

Wayah ta daga ta kira salma.

"Hello aminyah ya kike,nasamu nasarar karbar takardata a yau,ki shirya zuwana abuja dan dama can cika kuma nasamu"

"Dan allah kicemin dagaske,kai amma naji dadi,a gidana zaki zauna kuwa ina koh"

"Inshaallah kuwa,ki kawantar da hankalin ki ina nan xuwa,naso cika garinmu ma dan bazasu bani bane banida hanya,da badan haka ba kinsan bazanzo gidanki na dade ba.

"Karki ce komai tinda zakizo din shikenan"

Da daddare su ahmad na zaune shikadai a falo da waya a hannunsa sumayyah taje gefensa ta zauna.

"Barka da dare"

Batayi tsammanin zai amsa ba saikuma taji yace mata barka.

"Uhm dama na karbo takardata tayin service yau,zanyi ne a garin abuja can akayi posting dina"

"Yayi kyau allah ya taimaka,yaushe zaki tafi?"

"Wani satinne"

"Allah yakaimu"

"Ameen"

Daga haka sumayyah ta karbi takardar tata dake wajensa tada bashi ya gani ta nufi dakinta.


Washagari taje gida tayi musu sallama,shikansa abbah yaji ance takoma makaranta,bai dauka dagaske bane saida tace masa zata tafi service.

Fat an alkhairi yayi mata harda kudi tayi gujiri.

Shiryen tafiyar sumayyah take tayi,itama hajiya Aisha tayi mata ihsani sosai,harda kuma takardar dazata nemi ma'aikatar shugabannata daya bukaci sumayyan taje.

Shima Ahmad kudi mai yawa yabata ranar dazata tafi,ya kaita tashar shiga mota tareda yi mata fatan alkhairi.

Duk da bada magana amma kuma rabuwa da gidan dazatayi saida taji babu dadi,musamman ma maryam dasuke zama wani lokacin suyi hira.

Da mamakin dan sauyawar Ahmad din tabar garin,Koyaushe sai ya dunga abinda batayi tsammani ba.





......Bayan shekara daya......




Abubuwa da dama sun faru,sumayyah tagama service dinta harta karibi certificate na shaidar gamawa,farincikin da taji da kuma jinjinawa kanta kar a so a Tona.

Sannan kuma tadawo da nan ma shaidarta na kara koyon ilimin design,na zamani wanda ake yayi. Hajiya Aisha bakaramin ji da ita take ba.

Salma ta haihu danta na miji,dan sumayyah tana can ma ta haihu,haka humairah ma matar yah mu'azzam itama ta haifi yar ta mace(zainab ana cemata yusrah) mai sunan hajiya mama.

Anty Maimuna kuma mijinta yakara mata kishiyah,kullum yanzu cikin masifah suke.

Ita kuma Muhibba tukunna,amma tsohon cikine da ita itama.

Kowanne gida ya cigaba,iyah nasu Ahmad aka sakawa ido,dan yanzu mutane har sun fara zargin ko haihuwar daga shine,dan idan ita maryam bata haihu ba to sumayyah fah(babu wanda yasan dawar garin)

Allah bai bashi da ba amma kuma aikin kasuwancinsa ya bunkasa,dan yanzu har company ya shiga na hadin gwiwa shida yan kasuwa.

Amma haihuwa kam shuru,kullum maryam har ma da sauran dangi abinda suke jira kenan.

Uwar gayyar kuwa babu abinda ya dameta da daga hankali. Ba laifi yanzu ta shiga dutyn abinci,amma shiri kam har yanxu yar gidan jiyace.

Da alama kowa yagane matsayin kowa a zuciyarsa,amma kuma yarda da hakan shine yazama abin matsala.


Sumayyah ceh a zaune a katifarta daga ita sai vest da kuma zani,sai aiki danna system take tana shan coke.

Duk wani abu na gayu da amfani tasiya kayanta,ta sayi dan karamin fridge da kuma kayan makulashe daga sun kare zata siyo ta cika fridge din.

Banda decoration datayiwa dakin abin sha'awa kamar na (Disney).

Kwankwasa kofar akayi,dan kamar wata munafuka kofar daki kullum a kulle,

"Uhm water?"

"Keda suwaye a gidan?"

"Uhm mu ukune waye daga cikin biyun?"

"Ke banason rainin hankali ki bude dakinnan sauri nake zan fita"

Tashi tayi kaman anyi mata dole ta bude dakin,Ahmad ne a taye cikin wani farin yadi mai aiki.

Dauke kansa yayi dayaga daga ita sai vest da kuma zani,shidinma sai kokarin sincewa yake.

Magana yake kasa kasa yana satar kallon jikinta amma batajim mai yake cewa.

Sake fitowa tayi tareda cewa,

"Uhm mekacene ban jiba,ka kirani naji kayi shiru,aiki nake fah a ciki"

"Sannu sarkin aiki,ki ajiye aikin kizo kiyi abinci,mai girkawa ta baki yau batajin dadi,gashi iyah ma tace zatazo gidan,tunda ku kunki zuwa"

"Lahh kardai tayi fushi,zancen a bani abinci ina zaune kuma ku kukaso hakan ai,an bani girkine nakiyi,ku kuka ga zaku iyah shiyasa kukeyi.

Barina shiryah na fito to,saika dawo,kayi kyau"

Daga haka tashige dakin da sauri tareda bugo kofar da sauri.

Murmushi yayi ganin tafita da gudu kaman yarinya,ya danyi minti kaman biyu yana kallon kafin yah jijjiga kai yabar wajen.

Ita kuwa tana shiga dakin jingina tayi da bakin kofar tana maida numfashi,marin fuskarta tayi tana murmushi tareda cewa,

"Kai mai yasameni tun sanda nadawo ne,saina dunga takalar Ahmad da zolaya"

Wata zuciyar tace mata dan shima yana biyemikine,fuska kika gani,da kiyi mana.

"Eh da kuma hakan,bari na shiryah naje tarar tsohuwar can da abinci mai dan laushi"

Shaff shaff tafara aikin tagama,dan yanzu kwata kwata batasan wani abu waishi son jikiba,kullum cikin wani abu take.

Har take bakin kofar dakin maryam din zata shiga saikuma ta dawo,dan takula kwannanan maryam din sai a hankali,kullum ciin bata rai take,abu kadan zata daikeshi fada,shiyasa take kokarin rage shiga sabgarta.

Tana cikin kwashe abincin taji sallamar iyah Ahmad ya kawota,tundaga bakin kofar take mita.

"Sallama dai ina yan gidan suke,da baku nemeni ba nina nemeku,kuma ba'a banza ba dan bana barin kota kwana"

"Sannu tajuwa mai ran karfe,zamu biyaki da goro kuwa farare masu laushi dadai hakoranki"

Zama sukayi aka fara gaisawa,bakin iyah bai mutuba sam.

Lekawa tayu bataga maryam ba hakan yasa tace,

"Inakuwa meramu dason bangantaba,koh jikin da tsananine kai"

"Ahah iyah barina dubota nace mata kinzo"

Ahmad ne yatashi da sauri ya nufi dakin maryam din,aka daga iyah sai sumayyah a zaune.

"Iyah ina inna ramma bata biyoki kunzo ba"

Kasa da muryah iyah tayi a dole zatayi gulma tace,

"Hmm tazota ita a dole gidan dan fari,kuma fah tana son zuwan,kozata ga gari,amma taki tayi zamanta,ita tasani ai nikam nafito shan iska"

Dariyah sumayyah tayi tareda cewa,

"Aikuwa kinfito shan iska kam,iska kuwa zaki shata,bari rana tayi sanyi muzagaya gidan koh"

"Wlh kuwa yar nan,musha iska"

Dariya sumayyah tacigaba tayi mata musamman idan tace iska,itakuwa bata kulaba sai fada takeyi.

Suna cikin zancensu maryam tafito itada Ahmad yana gabanta tana binsa a baya.

Fuskar nan a daure tazo ta zauna,ciki ciki babu sakin fuska kaman anyi mata mutuwa ta gaida iyah ,sumayyah kuwa bata kalli inda take ba,itama bata kulata.

Sama sama idan akayi magana take saka baki,gashi idan aka tambayeta sai tace babu komai,kowa dai kallonta yake,badai lafiya ba kam.

Wajen cin abinci suka nufah harfa maryam din,sai anyi magana takalli mai yin maganar kawai,ko kuma idan an tambayeta ta bada amsa,daga ganin fuskarta kasan haushin wanda suke kusada itan takeyi.

Sakwara da miyah sumayyan ta bude tana kallom iiyah,dama dan ita tayi tasan tana son ta sosai.

"Iyah surprise kalli mai aka dafa kafin kizo"

Dariya iya tayi tareda cewa,

"Kai wannna yah kinmin sauka kam,ni inaga na barmiki mijinnawa ma na hakura,gaskiya bazan iya ci akan bencinnan ba indai tuwon doya ne,bari na koma kasa ki kawomin nawa"

Hhhhh to shikenan iyah bari na zuba miki toh"

Daga maryam har Ahmad zubawa iyah da sumayyah ido sukayi suna kallonsu,daga ganinsu kasan sun dade da sanin juna.

Kallonta Ahmad yake da yanda take dariya da kuma yanda dabi'unta suke a kwannan sai yamzu yake ganin ainihin sumayyan daya fada sosayya ta ita akan fuskarta,karamar sumayyah mai saukin kai da fara'ah,ba sumayyah yar jami'ah budurwa data kasa masa ayah a hannu ba.

Kuma abin mamaki duk kala ukun itace,rayuwa mai juyi juyi.

Zuba abincinta take suna magana da iyah,bata ma kulada kallon da Ahmad yake mata ba har saida ta mika masa nasa abincin,saurin dauke kansa yayi yana wayancewa,amma ya makara ta ganshi sarai,itama kuma tasani sai tayi gyaran muryah kawai

Duk abinda yake faruwa a wajen akan idon maryam yake wanzuwa,dan mayar dasu tayi tamkar Tv.

Sai sanda sumayyah ta mika mata nata abincin tukunna tayi mata yar godiya kadan kafin taza shi gabanta.

Cokalin ta dauka ta yanki sakwarar takai bakinta,tun kafin ta hadiye takejin wani tashin zuciya

Saboda bata saba kuma tasan ba rashin lafiya take ba,sai kawai ta basar ta hadiye abincin.

Ai kuwa take yace bai san zama ba sai ya fita.

Kokarin aman da maryam takene yasa dukkansu hankalin su yakoma kanta.

Tashi tayi da gudu tana rufe baki tayi hanyar dakimta da gudu.

Bandaki ta nufah tafara kela amai,bayan lomar abincin tada jubar harda wanda taci ma da safe,amma har sannan bata daina aman ba,kan kaceme ta galabaita jikinta yah shika sharaff.

 

Guess what makaranta,😂 hmmmm cakwakiya fah tana gaba fah,kudai karkuyi miss ku cigaba da bibiyah.





   







🏵*sadi-sakhna ce*🏵