22
by @bilynabdul
da asuba ya tashi yay alwala, ya tafi masallaci, baitada Munneerah ba tunda yasan tana fashin sallah.
Ko da yadawo b'an garansa yanufa yay kwanciyarsa.
" Munneerah tatashi, itama sannan gari ya waye, tai wanka sannana ta nufi kichin ta had'a break,harda su ikileema.
Takoma d'aki tagyara ko ina taturare da k'amshi, tasake shiga wanka.
"Dady ya tashi yay wanka, ya shirya cikin purple d'in shadda, d'ikin rigar daka d'an ya wuce d'uwawunsa, akagyara suma fas, azuciyata nace kai gay d'innan yanaji da sumarnan kamar ta kayan kud'i, bayan ya gama yakwashi wayoyinsa, da jakar aikinsa, ya nufi b'angaren Munneerah.
Bata palo dan haka ya ajiye kayan hannunsa yanufi bedroom d'inta, tana zaune kan kujera ta baje kayan 'yan kunnanata akan tebir d'in gaban kujerar, tana neman d'an kunnan dazata saka.
"Ya shigo d'akin da sallama, ta d'ago tana amsawa, tazame k'asa tana gaishesa.
Ya amsa fuskarsa ba yabo babu fallasa,
"Lafiyar ki kika baje kaya haka???
"Tad'an turo baki gaba irinna shagwa6a6u,d'an kunne nake nema kuma nak'i ganinsa, tafad'a ido nacika da hawaye"
Shi dariyama tabashi, k'uruciya tatashi kenan ya fad'a azuciyarsa, yay d'an murmushi, sannan ya gintse fuska to kuma gashi ance dole sai shi zaki saka yau????
"Ta kuma turo baki gaba, nishi nakeson sawa wlh,
"To yikuka yafad'a yana dariya ciki ciki, dole dai dariyar ta fito"
Ta kallesa hawaye na shatata afuska, ya k'araso ya zauna kusa da ita, to 'yar shagwab'a bar kuka, ya sa hannu yana share mata hawaye, bari nataya ki dubawa ko, ya fad'a yana fara duba 'yan kunnan, wana iri kike nema, ta mik'a masa d'ayan data gani..
cikin minti biyu yagano d'ankunnan, ya d'ago yana murmushi to gashi zona saka miki, ta mik'a masa kunne yasaka mata, tajuyo d'ayan yasaka mata.
"Iye kaga 'yan matan baffa kinyi kyau fa sosai, amma da za'ayimini shagwa6a, tasa hannu tarufe fuska tana dariya 🙈.
"Ya mik'e tashi muje kibani break na wuce nakusa makara wajan duba d'an kunne.
Tace kai yaya duka minti nawa kayi kana dubawa??
"Oh hakama zaki ce"
"Da sauri tace a'a yi hakuri"
Suka iso wajana cin abincin, ta zuba masa komai, ta mik'e.
Yace sai ina ?
Zan kira au anty ikilimane muyi break d'in.
Nan take ya gimtse fuska,
Itama kanta saida ta tsorata taga yana k'ok'arin tashi.
Da sauri tace dan ALLAH yaya yi hak'uri na fasa.
Ya harareta kinsan ALLAH idan kika k'ara yimini zancensu saina 6ata miki rai.
Ta dur kusa agabansa kayi hak'uri bazan sakeba.
"Ki kiyaye"
Yau baimaci abincin kirkiba ya tashi ya fice, haka ta daure taraka shi, tana masa addu'a kamar yanda tasa ba.
Aciki ya amsa, yaja mota ya tafi.
Munneerah ta dafe kai, yaya matsala kamar bashine ya gama dariya ba yanzun.
Ta koma cikin gida ta had'a break d'in su ikileema a k'aton tire tanufi 6an garen husna tunda shine kusa da ita, ta tura kofar falon ta shiga ba kowa dan haka taje ta ajiye kan tebir ta fita.
"Su asannan ma sunacan suna kwasar barci abinsu..
yana zuwa office ya fara duba marasa lafiya, kamar yanda yasaba.
"Bayan yatashi yanufi gidansu
Ya tura k'ofar palon, yashiga da sallamarsa bakowa palon, sai TV daketa 6a6atu, yanufi d'akin mom, nanma batana sai kawai ya haye saman dad, danyana tunanin tanacan.
"Ilaikuwa suna tare da dad, dad ya washe baki oyoyo babana kaine agidan yau.
Yazauna yana fad'in dad nine wlh, ya tsugunna ya gaida su.
"Mom tace babammu daga ina haka??
Mom daga asibiti nake nace bara na gaidaku.
To sannu ya aikin??
"Alhamdulillah mom"
Ya rage fara'a
Dad yace dadyna ya akayi ne??
Sunsan tun yana yaro idan yanason abu saboda miskilanci bazaiyi magana ba saidai fuskarsa ta nuna, dan haka sukan gano damuwarsa da wuri ta wannan hanyar.
Yaja ajiyar zuciya dad yarannan ne suka dawo jiya"
Dad yace su husna?
"Ya gyad'a kai batare da yayi maganaba"
To ai.shikenan babana saika had'asu ka rik'e da adalci kaji, kar kuma nasake naji wata fitina ta taso, kazama namiji a gidanka, miye kazama namiji, karka yarda wata ta cutar dawata acikinsu, su duka 'yan uwankane, bana son tasanadin aurennan zumincinmu yay rawa ko kad'an.
Dady yace amma dad kasan fitinar yarannan, muna zaune abummu lafiya, yanxu sun dawo zasu 6atama mutane zama.
Kayi hak'uri nida kaina zan tsawatar musu kasami lokaci koda daddarene ka d'akkosu kuzo kajiko.
"To dad zanyi k'ok'ari"
Mom.ina 'yan biyu??
"Suna makaranta dady, yanzu zaka gansu nan tunda sunce darasi d'aya garesu yau.
To ALLAH yadawo dasu lafiya.
"Amin"
"Ya mik'e to bari nawuce gida"
To babana kagaishe da iyalinnaka.
"To zasuji, insu 'yan biyu sun dawo ina gaidasu, tunda sunk'i zuwa, Munneerah tanata so suzo.
"Mom tace makaranta ke hanasu sakewa wallahi. Tayi hak'uri zasuzo"
"To sai suzo.
Bayan tafiyarsa dad ya kalli mom, bilkisu kinga babana saiwani kyawu yakeyi, gawani tashen k'iba dayakeyi.
Mom tai dariya, dad'in mace tagari kenan alhaji, da yana ta wani shi bayaso,
Dad yay dariya aikinga yanzu kinjishi shiru ko.
ALLAH ya k'ara basu zaman lafiya dai.
To amin..
husna tatashi abarci tafito falo tana mik'ar tashi da hammar yunwa, karaf idonta akan tiren abincin da Munneerah ta ajiye, ta k'arasa da sauri wajan tana bubbud'e kwanikan abinci wani k'amshi mai dad'i yadaki hanacinta, tace "wow" waya ajiye abincinnan??
Tanana tsaye ikileema ta shigo, ta k'araso da sauri husna a'ina kika samu abinci??
"Kedai bari wallahi nima yanzu nake jajen wanda ya ajiye"
Munnerah ta shigo da sallama, suduka suka bita da kallo a wulak'ance, tace ina kwanan ku??
Ba wadda ta amsa mata saima tsaki da ikileema taja, husna tace to 'yar shishahigi miya kawoki b'angarena??
"Munneerah ta raunana murya kiyi jakuri anty husna dama cazan muku ga abincinan"
"Gabad'ayansu sai jikinsu yay sanyi, amma dan karta ganosu sai husna tace to munji ga hanya nan, tafad'a tana nuna hanyar fita👉🏻🏡.
Munnerah tafito tana murmushi, nace baiwar ALLAH kenan.
Muta nan naku kuwa sai suka zauna suna kwasar gara suna santi dayaba girki ko dad'in abincinne yasasu mance wacece ta dafa.
Darana takuma dafa wani lafiyayan abincin akakaiwa dady office, bata yi zuciyaba ta kaimaau ikileema suma.
~~~~~~~~~~
Dady yay hon maigadi ya bud'e masa k'aton get d'in ya shigo saida suka gaisa da mai gadi sannan ya ida shigowa.
6an garensa yanufa, yarage kayan jikinsa, kamar yanda tasaba yauma ta had'a masa ruwan wanka daketa tashin k'amshi, yashiga yay wanka yana maijin dad'in ruwa, yaudai koda ya shirya sai yanufi masallaci dan yaji anakiran sallah.
Saida akai isha'i yadawo gida, 6angaren Munneerah ya wuce, su husna dake zaune suna jirnsa afalon Munneerah, bayan sun gama zaginta da cimata mutunci, tanata kuka amma tanaji sallamar dady cikin dabara ta goge hawayen, lokaci d'aya suka mik'e, ita tana masa sannu dazuwa, sukuma suna aikin kallonsa.
Ya kuma tamke fuska kamar bai ta6a dariya ba, ya nufi bedroom d'in Munneerah, batare daya tanka suba, husna takalli ikileema. 'Yar uwa mubishi, suma suka nufi bedroom d'in,
"Yana kwance akan gadon k'afafunsa nak'asa idanuwansa alumshe,suka zauna agefensa, sun sakashi tsakkiya kenan.
Har asannan bai bud'e idanun saba, ikileema ta shafa sajensa my love!! ko motsi baiyiba' ikileema tace dan ALLAH dan ANNABI kayi hak'uri, kayafe mana.
"Ya bud'e ido yana kallonta aini bakuyi mini komaiba.
A'a my sweet. Wlh mun maka laifi tunda kak'i saurarenmu, amma dan ALLAH kayafe mana, munmaka alk'awari bazamu sakeba.
In kuma kun sake nai muku mi?
"Duk abinda kai niya"
Ikileema tace in sha ALLAHU bazamu sakeba"
Munneerah tashigo tace musu ga abinci fa, saidai zuciyarta tayi zafi daganin su ikileema sunsa mata miji tsakkiya, duk suka mik'e, suka nufi falon.
Munneerah tazubama dady, sukuma suka zuba da kansu, tazuba kad'an tanaci, dady yakalleta wannan shine abincin??
Ta d'aga kai, alamar eh.
"Shiyasa gakinan kamar tsinke"
"Batace komaiba, sai murmushi...........✍️