Page 46
by @sadisakhna
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......
DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER
Wattpad:SAKHNA03
🏵🏵🏵
...46....
A falo suka samu hajjya mama da carbi a hannujta da alama sallah tayi
Yah mu'azzam ne ya cire hukar kansa tareda wurgata kan kujera,shikuwa Ahmad a bakim kofah ya tsayah kansa a sunkuye,da alamar kunyah.
Itadai hajiya mama daga kallo daya bata sake kallonsu ba,ta cigaba da jan carbinta,abin duniya ya isheta.
Abbah ne ya dawo daga masallaci da farouq a rike a hannunsa suna ta dan zance,duk da rabin zancen yaronne yakeyi,abbah saidai ya bishi da toh.
Da su yah mu'azzam yaci karo a falon,ganin halin da suke ciki yace,
"Lafiya kuwa,koh wani abune ya samu maryam din?"
"Ahah abbah babu abinda yafaru,maryam ce ta tashi dazu,nan take fadamana gaskiyar abinda yah fari,kan cewar kujera ce taja zaninta ta fadi,lokacin data fadi ma sumayyah ta bar gidan"
Saurin tashi hajiyah mama tayi tareda cewa "alhamdulillah yanxu kai mu'azzam saika fito da itah daga cell din ai koh"
"Ahah mama Bata can din,munje aka ce wata mata tayimata beli tuj da safe,kuma wanda yasan matar wai baya nan,kuma wayarsa bata shiga"
"Wacece ta fitar da itah to,mata kuma wace iri,amma duk inda take ma yakamata zuwa yanxu ai tadawo gida,wato bata yarda da abinda na fada mata a baya ba,kamcewa komai kunci karta bar gida ba,shine tabi wata mata daban"
"Babu wata mata da tabi,hasalima da safen tazo gidannan tana tambayarki,akan cewa na barta ta ganki ko sau dayah,sannan tana cemin bata aikata abinda ake tuhumarta ba,amma naki yarda da itah,na koreta nace mata kota hanyar gidannan karta sake biyowa,daga haka na shigo gida bansan ina tayi na yanxu"
Kallonsa hajiya mama take da takaici a fuskarta,kana gani kasan bacin rai ne ya cita.
"Ka koreta fah kace?,mai y'ar nan tayimaka da zafine ka tsaneta alhaji,da ina bin maza saina ce ba y'ar ka bace,meyasa bazaka iya sauraron uzurinta ba ne a Koyaushe,laifi daya tayi maka amma tundaga sannan kare ma yafita a wajenka,abin yana cutar dani yanda kake mata,amma haka nake dannewa danyi maka biyyah,saidai kai baka gani na kula,saida ka turata duniya kaji dadi,duk yadda na gargadeta karta bar gidannna duk rintsi taji magana ta amma kaikuma ka koreta,ka shigarmin da Y'a ta kudan jinina duniyah,taya kuma yanzu zakaga farinciki da walwala a fuskata.
Kullum zancen ta bar maka gidanka,gidan mazajenta bataji dadiba gidan ubanta ma bataji dadi ba,taya kake zaton bazata karbi duniya ba idan taji da dadi,hmmmmm kuma nima barin gidan zanyi bazan zauna ba,wlh kaida y'ay'an ka maza da kuma mijinta ku ne momin ya ta inba haka ba bazan tana yafemuku ba duniya da lahira.
Zan tafi idan kun samota saiku nemoni sannan na dawo,amma indai ba haka ba kar wanda yanemeni bare ya kulani"
Tana maganar hawaye yana bin kuncinta,
Hanyar dakinta tayi ta dauko akwatinta,har sannan suna tsaye kaman kungina,ka tashin hankalin batan sumayyah ga kuma borin da hajiya mama ta fara.
Har tazo fita yah mu'azzam ya rike mata akwati,a bakin kofah suka ci karo da salma wanda zuwanta kenan garin take samun labarin mai yafaru,shine ta iyo gidan su sumayyan ko tana nan,saidai ta gama jin abinda suke fada tasss.
Kallon su mu'azzam din take cikin bacin rai kafin ta koma kan Ahmad din ma.
"Abinda nakeji gaskiya ne,sumayyah ta bata dagaske,yanxu duk abinda ta shiga saida aka rabata da gida,tun ba kai ba yah mu'azzam matanku su suka hada wasu abubuwan"
Kowa kallonta yake har abban shima,ita kuwa ko a jikinta tafara magana,tundaga abinda taji suna fada ran auren sumayyah da kuma zigon da sukeyiwa maryam.
"Bazaku san sanjawar sumayyah ba sai kunga yanda take takura kanta da saka kamta a kunci a gidan Ahmad duk dan kuyi farin ciki abbah.
Su antu Maimuna da humairah sun sha zuwa gidan su cimata mutunci son ransu,sannan su jigaku ku hau ku zauna,komai suka fadamuku tayi sai ku hau ku zauna ku ga masu mata,idan nayi kokarin zuwa na fadawa hajiya mama sai tace ranki zai baci.
To Bayan tafiyata ma nasan abubuwa sun faru da dama,wln ancuci baiwar allah,abu daya tayi aka mata miliyan,tunda abinnna yafaru babu wanda ya taba tunanin yar adam ce tana bukatar abubuwan rayuwa,wani lokacin ni take roka kudi idan ya kure mata,idan kuma naga takasa roka na bata,wani lokacin kuwa sai tacemin babu abinda take bukata,kuma nasan dan karta tambayeni ne lokacin da take gidan Ahmad din ma mai yataba yimata a gidan,mijina ne ya biya mata kudin makarantar ta na farko,na biyu kuwa kin fadamin tayi ashe kayan dakinta ta siyar ta biya kidin,sannan ta shiga sana'a da sauran kudin,abinda ko wamda baku sanshi ba zaku iya masa,amma haka abubuwa da dama sukafi karfinta a rayuwar nan, saida aka bari ta samu sana'a ta fara dogaro da kanta yanxu kuma an dora mata sharri an jefata duniyah,wannna wace irin rayuwa bace allah yasa ma zuciyarta bata buga ba ta mutu,waya san yanzu wane hali take ciki"
Cikin masifah ta rufe ido take zazzago masifarta son ranta,ko girmansu a lokacim bata ganiba,bacin raine yake cinta sosai,saida tagama kafin ta fashe da kuka ta bar gidan tana fadin,
"In allah ya yadda zan bincika duniya inshaallah saina nemo sumayyah,rayuwarku kuwa tafita ma yanda kuke so din"
Da sauri tabar gidan tana gunjin kuka ta shiga motar ta tareda figarta da karfi,ikon allah ne kadai ya kaita gidansu.
Yanzu dakin yayi shuru ihun hajiyah mama ne kadai tana a fito mata da yar ta,dan dataji abinda bata saniba wanda yar ta take ciki bakaramim harzuka ta yayi ba,kara rike akwatin yah mu'azzam yayi,dan shi yake ganin tashin hankali.
"Ka shikamin akwatina bazan kwana a gidannan ba,ku masu mata sun rabaku da yar uwarku,saiku zauna dasu yanzu hankalimku ya kwanta,sun maidaku gararori,su haka sukeyiwa yan uwansu,ku a ganinku wato sun fi sonku fuyeda yar uwarku koh,abu kadan zatayi ku tunzura ubanku yana jigaku ku yi mata dari,toh wlh kar wanda ya nemeni in ba samota kukayi ba,matannaku kuma zakuga yanda zaku kare dasu"
Fisge akwatinta tayi tabar gidan da sauri,sakawa tayi a cikin motar tareda cewa ya kaita gidansu,abin mamaki ya bashi saida tasake magana.
"Ka kaini zariya gidanmu nace,ko baka jine?"
Shiga motar tayi suka ja sai tafiya.
Bin bayan motar yah mu'azzam yayi da kallo tareda sauke ajiyar zuciya,ko ta kan abbah dayake tsaye bai bi ba da kuma Ahmad wamda shima yazama mutun mutumi,motarsa ya dauka shima yabar gidan.........
A kwance take da wata riga a jikinta yar doguwa mai kalar sky blue,da alama ta asibiti ce.
A kan wani gado take duk kanta wayoyine wanda suke jinkin na'urah.
Daga ganin kayan aikin wajen da yanda fararen fata suke jirga jirga kasan wajen ba kasarmu bace ta hausawa.
Wata matace a gefenta fara mai yar kiba,amma kalar fatar mu ta yan Nigeria,magana suke da wani mai fararen kaya inda yake fada mata yau zasu daga ta daga kan na'urar,abin bashida worse sosai dam haka sati daya ma ya isa.
Wani daki aka tura sumayyan,har sannan bata farka ba,amma yanxu babu wayoyin akan ta.
Wasu gwaje gwaje suka mata daga nan suka fita akan barta ta hajiya munawwarah .
Bayan wasu a wanni idanuwanta suka fara motsi,inda ta saukesi akan cilin din dakin,motsin mutum datajine yasa ta juyawa tana kallon hajiya munawwaratun,murmushi tayi mata amma bata mayar mata ba,sai juyawa datayi daya gefen.
Zuwa sukayi aka kara yimata wasu gwaje gawajen,suka ce normal ne amma tarasa wani bangare na memorynta,a rubuce suka bata matsalolin,har da buccal cavity dinta yasamu matsala,saboda akwoa negetive massage din da brain dinta ta tura,wanda yahanata yim magana kwata kwata,saidai nuni da hannu.
Washagarin ranar hajiya munawwarah suka tafi gidan,idan kaga sumayyah bazaka ce bata magana ba sai an fada maka,amma silent din ta ya Karu.
Gidane katafare na alfarma mai ji da tsari da kuma imganci.
"Sumayyah Sunan ki koh"
Daga mata kai tayi alamar hakane.
"Nice name,toh sumayyah nan ne gidana,nasan kinsan labarina,inason zama dake idan na damuwa,akwai yar kanwata dana rike bata kaiki ba zata dawo daga makaranta,sannan mijina a nan yake aiki,shiyasa muka dawo nan,kamfanin daya saka gasar dakikayi nasara a abuja nawane wato "G&L decorations",hakika na yaba da basirarki da kuma jajircewarki,duk da banji dadin rasa muryarki ba,saidai ina so kisam cewa hakan bashine matakim faduwarki ba,saima ki maidashi matakim nasararki,saboda fasahar kirkira dakuma zane badaga murya yake ba,sometimes ma anfison dama mutum yayi shuru kafin yayi"
Matsowa kusada ita sumayyah tayi ta rungumeta,saboda batada bakim cewa komai yanzu,dan ita bata tuna abinda yasa ta daina maganaba,hasalima ita abinda tasani shine sunyi maganar akan cewa zatazo wajen hajiyah munawwarah,amma batasan har lokacin yayi ba haka.
Itama rungume sumayyan tayi tana dariya tareda cewa,
"Karki damu muje na nuna miki dakinki,duk wani abu dakike bukata an tanadar a ciki,inyaso gobe sai muje wajen aiki dake kawai,dama kwanaki dr Al'hassan(ogan hajiya Aisha) ya tiromin tarkadunki nagama miki komai anan,nima yanxu zanyi alfahari na kawo yar kasata kuma kamar yah a waje na inda nake aiki.
Muhadu mu basu kunya mu nuna musu basirarmu kinji dear?"
Daga kai sumayyah tayi tana dariya harda guntun hawayenta na farinciki
Tsayawa sumayyah tayi a dakin tana kalllon yanda aka tsarashi,babbane sosai,akwai wajen da gado yake,akwai wajen motsa jiki sannan kuma akwai wajenda aka saka system da kuma abubuwan decorations da littafai kala Kala is just like mini library.
Rufe baki tayi tana karewa dakim kallon saboda haduwarsa,(irin wanda kuke gani a film dinsu dai).
Wata kofa ta gani tayi zaton bandakine,tana shiga taga ashe dressing room ne karami,iyah kayane a wajen dakuma wajen saka kayan.
Fitowa tayi tashiga daya kofar wacce take bath room din ,nan ma kallo yana inda yake.
A takaice dai waje yayi bala'in haduwa.
Kwanciya tayi bayan tayi sallah taci abinci,sai hutu.
Washagari kuwa suka tafi wajen aiki da hajiya munawwarah tana ta nuna mata abubuwa sosai a wajen.
A bangaren masu zuwa decoration din wurare hajiya munawwarah tasaka ta inda zatayi aiki da mutum biyu,daya na miji daya mace,ling-lang dakuma namiji shin-xian,
Hannu bibbiyu suka karbi sumayyan dan sunsan hajiya munawwarah sosai.
A dan takure sumayyah take musamma ma da bata saba da rayuwar wajen ba data mutanen,amma tasan soon zata saba,dan ling-lang sai zanta take da surutu ta turanci wai tayi mata hausa,saida hajiyah munawwarah ta fada musu disorder ta kafin suke nuna mata da hannu.
Saukinta kenan basai tayi shishishi bah.
Bayan sati guda kuwa su abbah sun sami address din hajiya aisha kam cewa ita tayi belin sumayyan,da farko ta amsa tayi belinta amma saitace data kaita gidan antyn ta ta koreta saita kaita gidan su .
Daga nan ta tafi tabarta bata san mai ya faru ba.
Zasu sake magana hajiyah Aisha ta kawo kuka ta rusa akan zasuyi mata sshirri.
Ganin hakanne yasa suka fita daga office din .
Suna fita kuwa ta mirtsike idonta tareda cigaba da aikinta.
Kuma fah sannan tagama wayah da hajiya munawwarah kan cewa sumayyah ta tashi.
.........see you next chapter......
🏵*sadi-sakhna ce*🏵