Page 48
by @sadisakhna
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......
DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER
Wattpad:SAKHNA03
🏵🏵🏵
...48....
Ranar sadakar bakwai na rasuwar maryam aka radawa yaron suna MUHAMMAD yaci sunnan kakansa mahaifin ubansa,ana kiransa Abeeh.
A wajen mahaifiyar maryam aka bar yaron,dan yanzu babu inda yafi masa nan din.
Saida akayi sadakar bakwai din lafin Ahmad ya koma gidansa,tun daga bakim kofar gidan memory na abubuwan da suka faru gidan suka fara dawo masa.
Da su ukune a gidan,amma yanxu sauran shikadai.
Daga wacce ta rasu ta barshi da marayan dan sa,sai wacce ta bata a cikin duniyar bai ma san inda take ba,taya za'a tsammaci kwanciyar hankali a zuciyarsa.
Dauke ruwan hawayen daya fara zuba a kan fuskarsa yayi tareda tunkarar cikin gidan.
Dakinsa yafara nufah ya tattara kayansa daya san zayyi amfani dasu,dan bashida karfin zuciyar zaman gidan a lokacin
Dakin maryam ya shiga ya kalli kayanta da komai nata,kafin azo a debesu in anjima.
Shikenan fah rayuwar,kayan da'akayin fah sun gama aiki kenan,sannan koda da tsinin allura bazasu tana amfanarta ba yanzu,aikinta na garine kawai zai bita kabarinta.
Inkayi mai kyau mai kyau zaka gani,haka akasinsa ma,duk dukiyar da mutum ya tara,da cutar da kansa da yayi domin wanda miji ko kuma fadawa halakar bata daga kan turbar daidai,haka fah zaki muti ki barshi,in baki barshi ba dole shi sai ya barki,in babu saki yar iwa akwai mutuwa,wacce take tsinke igiyar alaka.
Allah ya hanemu fadawa tarkon shaidan ameen.
Har yazo fita daga gidan saikuma ya hango hanyar dakin sumayyah,karkata kafarsa yayi ta daukeshi zuwa dakin sumayyan.
Tura kofar yayi ya shiga,yana nan yanda ta fita ta barshi lokacin da ta dauki file,sai kura dayayi alamar ba'ashiga.
Har zai fita ya hango wani littafi a kan madubinta,dauka yayi ya bude inda ta kashe yin gaisuwa cin abinci dasu da kuma wasu abubuwan.
Murmushi yayi tareda shafa rubutun yace
"Inason wannan bangaren na halinki sumayyah,akwai ki ta fadar abinda bai mikiba,duk da shiya zefani a halinda na shiga daga farko amma bazan daina sonki da kuma halinki ba sumayyah,yanxu ke kadaice bangaren hasken dayayimin saura a rayuwata da wani,idan ban ganki ba bansan yanda zan komaba,bansan zuwa wane lokaci zan kasa daurewa ba zuciyata ta buga saboda halin datake ciki.
Ki waigeni a rayuwarki ki dawo,kodah tsanta ce zata dawo dake,ina farinciki da hakan,da ace na daina ganinki a duniyata sumayyah"
Haka Ahmad yagama sambatunsa tareda daukar littafin ya tafi dashi.
Dakinsa na gidansu ya share yasaka kayansa,suma su inna ramma basuce komai ba dan sunsan yana bukatar hakan,suma kuma zasu dunga ganin mai yake a kusada dasu.
Wasa wasa rasuwar maryam da batan sumayyah anyi kusan shekara guda.
Mutumin daya san a Ahmad a da idam ya ganshi yanzu sai ya tausaya masa,kuma yayi Mamakin yanda ya koma,ya rame ya tara gashin fuska.
Kullum idan inna ramma da iyah suka tambayeshi sai ya cemusu kalau yake babu abinda yake damunsa.
Yau ma tafiyah a hanya ya dawo daga ziyarar daya kaiwa abeeh,yaron yayi wayo sosai,yana yawo ko ina kaman ba dan shekara daya ba,kamar su daya da Ahmad amma idonsa ta kalar fatarsa na maryam ne.
Tuki yake a mota zai koma gida,dan yanxu zuwansa aiki ma ba sosai ba,ko yaushe yana gida a daki.
Su kansu masu kamfanin dasuka ga sai suka bukaci ya sayar musu da share dinsa,har yace a'a daga baya ya amince kawai,dan yanzu bata wani dukiya yakeba,neman account yayi yasaka kudin yabawa inna ramma pin din.
Itadai idan yana wani abu mamaki yake bsta,dan cewa yayi koda mutuwa yayi a ajiye idan sumayyah ta dawo a bata ta kulamasa da dansa da ita kanta,inkuma bata dawo ba a yi wani aiki da sunnan ta a cikin kudin sannna kuma a bawa abeeh dukiyar.,to kawai tace tareda neman wajen ta adana kudin.
Saurin komawa gefen titi yayi ya faka motar tareda kifah kansa a jikin motar yana rikeda kirjinsa,wayarsa ya zaro hannunsa na rawa yah kira doctor din sa wanda yake gani,
"H....elllo doctor please inkana asibiti gani nan zuwa"
Baijira mai zaice ba ya ja motar da kyar zuwa asibitin,ko gama faka ta baiyi ba ya fito ya nufi office din dr Suraj din.
Tashi yayi tsaye yana kallon shigowar Ahmad din tareda nuna masa gadon dayake office dinnasa
Kwamciya yayi yana maida numfashi shikuma yana dubashi,yunkuri yayi kaman zayyi amai saiga jini ya fito daga bakinsa,kallonsa dr suraj yayi cikin tausayawa bayan ya gama yi masa allurar kafin ya koma kujerarsa ya zauna.
"A gaskiya Ahmad gangancinka yayi yawa,matakin heart attack dinka yana haurawa,na fadamaka ka rage damuwa amma abin ya gagara,inaga zan fadawa familinka halin da'ake ciki"
KO ka fadamusu ma ba abinda zasu iya min,sai damuwa ma dazasu saka kansu a ciki,idan allurar tafara aiki zan iya tafiya?,allah ya kaimu kuma wani satin"
Yazo fitane daga office din sukayi karo da wata mace tana dauke da wani abu a hannunta,sake juyawa tayi ta kalli Ahmad din tareda shiga office din.
"Dr suraj wannan ba Ahmad bane mijin sumayyah,me kuma yake a nan"
"Kin faye surutu mufeedah,patient dina ne,tun batan matarsa da kuma rasuwar dayar yake zuwa ina dubashi,yaki bari yan uwansa su sani,gashi kuma shi yaki daukar mataki,kullum cewa yake bazai iya daina damuwa ba,yana bani tausayi sosai"
Shiru Mufeedah tayi daga haka,ta ajiye wa dr suraj dim abincinsa,ranar koh hira sosai basuyi ba ta tafi.
A ranta tana cewa,tabbas shine mijin sumayyah,dan sun zo wajen aiki neman hajiya aisha,kuma shine dai wanda aka ce mijinta ne,anya kuwa toh hajiyah Aisha tasan mai yake fariwa?"
Daga nan wajen aikinsu ta wuce,ko block dinsu bata tsayaba sai wajen hajiya aisha.
System ce a gabanta suna video call da ta cikinta,sumayyah ce saikuma wata mata babba suna ta dariya.
Lekawa Mufeedah tayi domin share tantama,dan ta kula da hajiya aisha batasan ta shigo ba.
Saurin rufe system din zatayi amma Mufeedah ta dakatar da itah tareda cewa,
"Hajiyah dan allah minti daya,inaso sumayyah taji mai zance itama,gaskiya haka bai daceba,kinsan inda take amma kiyi shuru,yanxu nan naje wajen yayana na likitan zuciyane na hadu da Ahmad yaje checkup,tsawon shekara guda kenan yana fama da ciwon zuciya saboda damuwa datayi masa yawa na batan matarsa da kuma na rasuwar dayar.
Wlh hajiya in bakuyi wani abu akaiba kuma zakuyi danasani,dam idan ya mutu akan haka Allah bazai barku ba,ku kanku kunsan yana son ta,baya sati bai zo wajennan ba akan ko munji labarinta,amma sai kuyi shuru ,karku manta fah ita matar aurece,kuma shi mijintane,yafiku hakki akanta"
Zagewa Mufeedah tayi tana magana ta kallon sumayyah,saidai ga mamakin ta babu abinda ya sanja daga yanayin sumayyan,saima kallon bata fahimceta ba take.
Kashe system din hajiya aisha tayi,amma daga gani jikinta yayi sanyi sosai,
"Bakomai inshaallah zamuyi magana akan hakan,hakika yakamata mu bar wannan boye boyen"
Da safe hajiya mama tana sakawa kanwar farouq kaya,yar gidan anty Maimuna,wai tayi yaji yah naseer ya fison amaryarsa akan ts.
Sallama taji Wanda hakan yasakata daga kai takalli matar.
"Ahh hajiyah aisha koh?"
"Eh wlh nice"
"Bismillah ga waje zauna"
Tashi hajiya mama tayi zata dauko mata ruwa,su ladidi sunyi aure.
Dakatar da ita hajiya aisha tayi tareda tambayar mai gidan.
Kiransa hajiyah mama tayi,har sannan kanta a kulle yake,mai yasa take nemansa oho.
"Uhm alhaji ina fatan ka shaida ni,nice hajiyah Aisha wacce tayi belin sumayyah"
"Eh na Shaida ki baiwar allah,lafiya dai koh"
"Eh to lafiya din dai,alhaji kayi hakuri da abinda na aikata idan kaji menene,maganar gaskiya nasan inda sumayyah take tsawon shekara guda,yanxu haka tana china,hasalima nice nayi sanadiyyar zuwanta can,amma gobe inshaallah zata dawo"
Dakatar da itah abbah yayi tareda mikewa tsaye.
"Tsawon lokaci kinsam inda take,menene dalilinki na boyeta"
"Ban boy eta ba,nice na kawota gidannan ranar danayi belinta na kaita wajen yar uwarta ta koreta,na kawota nan ka koreta,ba godiya zakayimin ba dana dauketa lokacin danaga ta fadi kaikuma kayi shigewarka cikin gidaba,magani nakai sumayyah china saboda ceton rayuwarta,nizan tafi,idan ta dawo gobe zam kawota wajen iyayenta,ruwanta ta zauna daku ruwanta tace bazata zauna ba"
Tana gama fadar haka hajiya Aisha taja bujenta tabar gidan.
Shiru dukkansu sukayi babu mai cewa komai tsakanin hajiya mama da abbah.
Itace ma tayi karfin halin daukar wayah tafara fada wa kowa abinda yake faruwa.
Ahmed yana daki yaga kiran yah mu'azzam,daukar wayar yayi yasaka kunne yai shuru,dam sannan yasha maganinsa yana jiran yabi jikinsa yayi bacci.
"Ahmad kana jina kuwa"
"Eh ina jinka mu'azzam mai ya faru"
"D'azu hajiya Aisha taje gida tana cewa wai tasan inda sumayyah take tsawon wannna lokacin"
Saurin mikewa Ahmad yayi tareda cews,
"Mu'azzam mai nakeji yana fitowa daga bakinka haka,tana ina to a ina ta boyeta"
"Ka kwantar da hankalinka,tana kasar china wai,amma tace gobe zata mayar da itah gidan"
"To miyasa sumayyah taje china kuma,tsawon lokacinnan bata je gida bs"
"Babu wanda yasan wannan amsar sai gobe kawai"
Bayan sun gama wayar zullumi Ahmad ya shiga na zaman summayn a kasar china,amma duk iyah tunaninsa bai gano daliliba.
Haka ya barwa allah ya komai tareda fatan allah ya kaimu goben.
Washagari tun da safe yan uwa aka fara taruwa domin ganin ta inda sumayyan zata bullo,su kansu masu aiki zama sukayu a gida dan ayi komai a gaban idonsu.
Ahmad kuwa tun karfe bakwai yazo gidan dan yaga ta inda sumayyan zata bullo.
Around 2:30 motoci guda biyu suka nufo kofar gidan,daya tana gaba ja saikuma wata wacce take binta a baya baka mai adon golden.
Hajiya munawwarah ce da hajiya aisha a cikin ta farkon,dukkansu sun sha kaya na alfarma.
D'aya bakar motar itace aka budeta daga baya.
Wata yarinya ce fara sol ta fito daga bangaren zaman banxa na gaban motar.
Daga baya ne mai tukin motar shima ya bayyana,.
Wowwwww even if you know her,it's difficult to recognize her.
Irin kayan jinkin yarijyar ne ita ma a jikinta,doguwar riga mai shegen ado,dayar nata kalar pink,yayinda ita kuma sumayyah tasaka baka mai adon golden,ta yi rolling shikuma Golden,golden girl kenan.
Kama hannu sukayi itada daya budurwar suka karisa inda hajiya munawwarah take.
A tsakiya suka sakata zuwa cikin gidan,dam sumayyah duk a zaton ta sunzo wani wajene daban,dan jiya a gidan su hajiyah munawwarah suka kwana a abuja.
Suna shiga gidan ta kara makalewa a bayan hajiyah,danji take gidan yana mata wani iri.
Kallon tarin mutanen dake falon tayi da kuma yanda suka kura mata ido,dan tsuke fuska tayi tareda juyawa ta daina kallonsu dan ta tsani kallo.
Ganin abinda sumayyan tayine yasa hajiya munawwarah cewa,
"Kuyi hakuri alhaji,sakamakon matsalar data samu yasa ta manta duk wani abu daya shafi gidannan,sannan kuma tunda ta tashi bata magana,danni ma ban taba jin maganar ta ba,har yanzu akwai matsala dan gane da kwakwalwarta,tunda harshen ta Kalau yake"
Toh fah .........