KAICO NAH

Page 50

by @sadisakhna


 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵


       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......



DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER


Wattpad:SAKHNA03


🏵🏵🏵

...50....








Tashi sumayyah tayi ta tafi abinta bayan abbah ya sallameta,a ranta tana salle walle kuma,kowa yakama gabansa,dui da yanda nake jinka a raina bazan iya kunsar bakinciki ba yanzu,da din ma wlh dama ka samu banda yanzu kuma.

Bayan sati dayah da kiran da abbah ya mata dakuma takardarta da Ahmad zai bata,bataji komai daga gareshiba,itama kuma bata nemeshi ba,a nufinta duk sanda yagama wanata ya bata takardar.

Komawa ma'aikatar hajiya aisha tayi tana rikemata wasu Abubuwa kafin ginin nata ya kammala,dan program ma taje ya kusan guda uku daga dawowarta kasar,musamman da aka san matsayinta yanxu na kwarewa a design din cikin gida company da kuma event.

Shigar kayah kuwa kala kala,gata da iyah wanka design din ya ratsata sosai,ko ina sunan golden girl yasake karadewa a karo na biyu,saidai wanann golden girl din mai takama da nata daukakarne bana ubanta ba.

Ranar taje wajen aiki suna zaune suna hira da abokanan aikinta Mufeedah tace,

"Dan Allah anty sumayyah idan bazaki damuba inaso mudan ja gefe zan miki magana"

"Okay ba matsala"

Tafiya suka dan yi har zuwa wani waje a can gefe inda aka saka kujeru,wani tagani a zaune a wajen da alama su yake jirax

 Kallon Mufeedah tayi tareda tsayawa tana bukatar karin bayani.

"Karki damu likintan Ahmad ne dr suraj kuma yayana,magana zakuyi mai muhimmanci shine ya nemi ganinki"

Karisawa wajen sumayyah tayi yayinda Mufeedah kuma tatafi abinta.

"Barkanki da aiki malama sumayyah"

"Yawwa barka ina jinka"

"Eh nima sauri nake,maganar data kawoni wajen ki akan rashin lafiyar Ahmad ne,wanda ya boyewa danginsa,sannan kuma yayi sign akan bai yadda kowa yasani ba,saidai ganin abun yanayin worse yasa na yanke shawarar fadamiki,a matsayinki na matarsa"

"Wace irin rashin lafiya kuma"

"Yana dauke da cutar heart attack sanadiyyar shiga damuwa daya dungayi a lokuta daban daban.

Na farko yayu ne tun rasaki a karon farko kika auri wani,wanda sannan ma akan magani yake,na biyun kuma yafi worse,saboda ya hada masa da rashinki dayayi na karo na biyu kin bata da kuma rashin matarsa dayayi sanadiyyar haihuwa.

Koyaushe idan nace ya fadawa yan uwansa sai yaki,duk sanda abin yatashi masa yakan zo ya karbi allura,to yanzu kam ma duk sati sai anyi masa,gashi tana da matsala sosai,kullum zancensa shine bazai iya daina tunanin abinda yayi miki ba,sanann burinsa shine sakaki a idonsa a karo na uku."

"To inda gaskene meyasa ina gidansa amma ko magana bayamin"

"Yanajin takaicin abinda wanda kika aura yayimiki,sannan kuma da tsananin kishin hakan,yana bukatar zamanki kusada shi a lokacin,amma ganinki a matsayin bashine wanda ya aureki da farko ba,wani kikeso daban bashiba shiyasa shi cituwa da zamanki kusada shi.

Sannan shareki dayake yana tsorom karya kara fadawa tarkon sonki kizo ki kara bayyana masa bakya sonsa shine yasashi haka.

Wanda kuma hakan ya tabbata da bama so,domin wancan satin dakyar yaje asibiti yana rikeda kirjinsa,nan yake fadamin wai kince ya baki takardarki.

Nayi kokarij kwantar masa da hankali amma abin ya gagara,ya shiga shock sosai,ko allurar bai gama tsayawa ta lafaba ya bar asibitin,har yau nayita kiran number sa amma shuru.

Nazo na fadamiki halin da ake cikine saboda karya mutu Allah yakamni da laifij yin shuri,yanzu aiki yarage naki"

"Tsaya dr yana ina yanxu haka toh"

"Yana gidansu a yanda ya fadamin"

Tun kafin yagama fada sumayyah tabar wajen da sauri ta nufi motarta,ko hajiya Aisha batayiwa sallamaba.

Gudu take sosai har ta isa gidan su Ahmad din.

Inna Ramma ce kawai a tsakar gidan iyah tana bacci a dakinta.

Gaisawa sukayi da inna ramman sama sama,tun kafin tace wani abu inna ramma ta kama hannunta tareda cewa,

"Sumayyah Ahmad yazo wancan satin cikin tashin hankali yana fadamin wai kimce ya baki takardarki,bazan tursasaki ba akan lamarin aurenku,saboda saidaga baya mukejin abinda Ahmad din yayi miki,nikai na naji haushin hakan,musamman damune muka hada auren,amma kuma rabuwar itama a yanxu batada masalhaa,kamata yayi ku fahimci juna,ni na tabbatar yanxu yana sonki baxai cutar dake ba,dan tun batanki yaketa ramewa ya daina walwala,yaki fadamana mai yake faruwa amma nasan bazai wuce rashinkiba dakuma abinda yayi miki.

Sumayyah ina rokonki badan a matsayin mahaifiyarsa ba saidan a matsayin uwa wacce baxata jure ganin wahalar dan ta ba ki daure ki fahimceshi ki gano mana damuwarsa dan......."

Saurin rike hannun inna ramman sumayyah tayi tareda cewa,

"Inna Ahmad din,dama shinazo nema"

Ya koma gidansa tun wancan satin da dayace zaki dawo"

Da sauri sumayyah ta juya ta fita a gidan tareda nufar motarta,sake tukawa tayi zuwa gidam Ahmad din.

A bakin kofar gidan ta ajiye motar bata shiga da ita cikiba.

Had'a ido sukayi da mai gadin su data shigo gidan,saurin sunkuyar da Kansas yayi,ita kuwa ko takansa bata biba

Tun a bakin falon dakalli yanda gidan ya sanja kamanni,karar amai din mutum taji a dakim Ahmad din,da alama mutum yana cikin halin ciwo.

Afkawa dakin tayi da sauri,zaro ido tayi ganin yanda zanin gadon ya baci da jini,sannan kuma ga inda akayi ta aman jinnin wani kuma ya bushe.

Bandakin ta nufah inda Ahmad ya juya bayansa ga kofar yana tofar da sauram wanda ya taru a bakinsa.

Hannayensa kuma ya daddafe sink din dasu sunata rawa alamar babu karfi jikinsa

Hannun daya sakalo ta bayansa ya doru akan kirjinsa na hagun inda zuciyarsa take ya kallah,kobai juyoba yasan na waye,lumshe ido yayi dajin saukar hannun jikinsa saidai baice komai ba

Karisa manna jikinta tayi da bayan tareda cewa,

"So kake ka kashe kanka koh,kasa inna ramma tarasa dan ta kwaya da ya aduniyah iya tarasa jikinta,sannan abeeeh yarasa uban da dama shiya saura masa,nikuma kasakani takaba koh,yayi maka kyau toh.

Ina nanne yake ciwon koh,toh ka fada masa an dawo za'a kuladashi ya tafi ciwon bama bukatarsa"

Duk maganar datake cikin serious take dakuma damuwa a dauke akan mauyarta,hannunta kuma har sanann yana kan kirjinsa tanajin bugun zuciyarsa.

Juyowa yayi da ita gabansa yana kallon idonta da nasa idanuwan wanda suke lumshewa kansu,hannunsa ya dora a gefen fuskarta kafin yace,

"Dolensa ma yanzu ya daina ciwo,dama maganin yaketa jira,tunda gashi yazo dolensa ya sallama ai"

Murmushi na karfin hali tareda cewa a hankali,

"Kayi hakuri da kasancewata mai kawo wahala a rayuwarka,duk naji abinda yake faruwa dakai,daga wajen inna nake ,ta damu matuka akan ka,yakamata ka tsayah haka kodan wanda suka damu dakai Ahmad,kuma bai kamata dama ka boyemusu ba"

"Banason su shiga damuwane,na fison na jure abun iya nikadai,banason kowa ya sani"

"Shikenan daga nan babu wanda zai sani zamu magance shi da kanmu,karka kara irin wannan gangancin a gaba,dan bazan dauka ba promise?"

Tafada tana mikomasa yatsanta,Murmushi yayi tareda dungure mata goshi kana ya jawota ya jikinsa ya kankameta kaman za'a rabashi da ita.

Komawa sukayi dakin ya zauna kafin ta koma bandakin tagyarashi tsaff ta hada masa ruwan wanka mai dan dumi.

Bayan ya shiga wankan kuma tacire duk wani abu daya baci a dakin ta fita dashi tayi mopping din kasan.

Kayansa ta bude taga su a gyare suke tsaff basu bukatar sakewa.

Riga da wando ta fitar masa dasu masu karamin hannu wamda taga yana yawan saka irinsu a gida.

Fita tayi falon tana kallon kurar dayayi,rike kumkumi tayi ganin akwai aiki sosai.

Farawa tayi dayimasa dan abinda zai iyah ci tukunna,mai sauri sauri.

Lokacin daya fito yaga yanda ta gyara dakin da kuma kayan data fitar bai san lokacin daya saki murmushi ba, a fili yace.

"Inason ki sumayyah,allah yayi miki albarka,allah yabani ikon kyautata miki tsawon rayuwata"

Lokacin data kawo abincin yana sallhar azahar,dan haka itama alwalar ta iyo tayi tata.

Abincin ta bude tasaka masa a gabansa bayan sunyi sallahr.

"Nizanci dakaina ai"

"Eh mana "

"Anya kuwa jinyar kika zoyi dagaske,naga kince.....tun kafim ya gama ta matso tareda diban abincin takai bakinsa,karbar cokalin yayi shima ya diba yakai nata bakin,har taki karba ya tsike fuska,dariyah tayi bayan ta hadiye tareda cewa,

"Au ka ramaa koh,lallai ka fara warkewa"

"Tun sanda kika shigo gidannan dama nafara wanrkewa ai.

Bayan sun gama cin abincin maganinsa ta bashi,wanda da yaki ballar ko guda daya daga ciki.

Kwanciya yayi dama ta gyara gadon,yayinda ita kuma ta koma ta fara gyara falon da kitchen din.

Dakin maryam da shiga wanda yake a da,an sanja dakin komai golden da baki,hatta kayan dakin ma bana kasar nan bane,wardrobe dinma an cikashi da kaya size dim ta da kuma size din abeeh,abin mamaki yabata amma ta mayar ta rufe,tasandai kam kayantane daga gani kenan.

Duk da batason zaman gidan saboda tuna maryam,amma wani bangaren batason barin gidam,saboda ya rike mata memory da dama na rayuwarta.

Sai kusan magriba tagama gyaran gidan tsaff,lokacin Ahmad ya tashi daga baccin dayayi.

Zaro ido yayi yana kallon ta yana kallon falon,hatta zaman wasu abubuwan saida ta sanjashi,dayake komai sabine a falon ma,hatta fentin gidan.

"Yaushe kikayi duk wannan aiki haka"

"Kana bacci nayi su dukka,barina zo na tafi magriba tayi tunda naga ka samu sauki"

Tazo wucewa ta gefensa zata dauko gyalenta da jakarta yayi saurin riketa ta baya.

"Please don't don't leave me again,idan kika sake tafiya zuciyata bazata iya jurewa ba sumayyah,kece hasken daya saura Wanda zai haska a cikinta,da sonki aka halliceni sumayyah,babu ransr dazan iya dainawa,bazan iya rubuta miki sakin da kika bukata yanzu ba,ki taimaki rayuwata karki barni,ki zauna dani,nayi alkawarin yimiki duk abinda kike so indai bazaki barnj nikadai ba,kiyafemin abinda nayi miki.

Kaman yanda kika fada zanyi nadama tabbas nayi nadama sumayya"

"Waye yacemaka zan barka Ahmad,tabbas ina sonka,ina tsoron kacigaba da shareni shiyasa nace ka sakeni amma badan na tsaneka ba,inna tafi ai zan dawo,dole na tafi tunda ba'asani a gidab........"

"Waye zai kamaki dankin zauna a gidan mijinki,kokuma bikin dawowar allha ne yace,please nafi bukatarki fiyeda da wannan bikin,kayanki sai muje ki dakko kawai zuwa jibi,amma yanzu kam i need you beside me my wife"

"Amma mai zance wa su .........abinda kunya Ahmad"

"Kice musu banida lafiyane shiyasa kika zauna,dan Allah kidaina maganar zaki saka kafa kibar gidannan kibarni ni kadai kinji"

Yafada yana karyar da kai,kallon idonsa sumayyah tayi wanda baxata iya cemusu a'a ba,dan haka dole bata da zabi ta daga masa kai alamar zata zauna.

Cikin murna Ahmad ya dagata cakk tareda wucewa dakin da ita.

Sai mita take wai duk nauyinta amma ya daga ta,dama ya warke wayo yake mata.

Bayan sun yi sallah hanata yin wani abincin yayi data ce zatayi,order yayi musu aka kawo har gida.

Suna zaune suna kallon wani labarai a tashar news

Ahmad ya makaleta a jkinsa kaman wanda idan baya gani zata gudu ta barshi.

Ita abinma har dariya bata,gashi dazu haka ya sakata ta kira hajiya mama ta fada mata bazata dawo ba.

Wajen karfe goma ta fara hamma,kallonta Ahmad yayi tareda cewa,

"Bacci zaiyi?"

Daga masa kai tayi kawai batareda da tace komai ba"

Tashi yayi ta kashe kallon da wutar wajen tareda kama hannunta suka nufi dakinsa.

Tsayawa tayi tareda cewa,

"Uhm Ko na shiga dakin can na kwanta kai,tunda naga an gyarashi ai"

"Nasan Har yanzu hankalinki bai kwanta da zama a kusa daniba,inaso kisani soyayyar danake miki bazata bari na cutar dake ba sumayyah,bakisan yanda nakeji a raina bane idan kikayi yunkurin yin nesa dani,ina ganin kaman ina cutar....,....

"Ya isa haka Ahmad,naga kaman kagyara dakin dannine,shiyasa nace naje na kwanta a can,banyi da wata manufah ba,nasan baxaka taba cutar daniba,Allah yabani ikon nima yin biyyah a gareka"

Daga haka yaja hannunta suka shiga dakinnasa cikin jin dadi da yardar datayi masa.

Hawa gadon tayi ta kwanta,shikuma saida ya shiga bandaki ya fito tukunna.

Kwanciya yayi a gabanta yana kallon inda take,itama kallonsa take yanda fuskarsa ta dam rame,yayinda shikuma yake ganin yanda tayi mada kyau sosai.

Hannunsa yasa yana shafa fuskarta har juwa kan wuyanta.

"Ke kyakykyawa ce sosai sumayyah,nagode Allah dana san haka kuma banason nayi wasa da damar dana samu dinnan"

Murmushi sumayyah kawai tayi tareda dora hannunta akan hannunsa dayake kam wuyanta.

"Nagode da yabonka gareni"

"Sumayyah banajin zuciya ta zata iya hakuri da ke a yau,can we become one please?"

"Yes why not"

Murmushi yayi mai kayatarwa tareda kashe dimm light din data dan haska dakin.

A ranta tana godiya ga allah daya kawo mata sanji na mijin aure,da wanda ya maidata tamkar tunkiya da kuma wanda a yanxu yake ganin ta tamkar dawisu mai adon zinariyah...



  To mubar masoya haka koh.....


 









🏵*sadi-sakhna ce*🏵