LUBABATU

04

by @rahmakabir13

LUBABATU


04

Freepage.


Rahma kabir Mrs MG.

Wattpad@rahmakabir



*Ranar asabar*

Rahima ta gama shiryawa zuwan Hashim, sai rawar kai take yi da zumudi, duk kan mutanen gidan babu wanda bai san da zuwansa ba hatta Abba Ummi ta sanar masa. Rahima ta shirya masa hadden abinci sakwara miyar agushi da farfesun kayan ciki sai juice din kankana, ta kai dakin baki kana ta zuba wanka ta sanya Riga da siket yar kanti ta yane kanta da farin gyale, ta yi kyau Masha Allah sai zuba kamshi take. Karfe Sha biyu da minti goma dai dai mai mashin na sauke Hashim a kofar gidansu Rahima, da yake Alh. Lukman Giwa sananne ne sosai shiyasa gidansa baida wahalar ganewa Kuma sunan layin da Giwa street aka sanya masa, ya sallami Mai mashin ya isa bakin gate ya buga, Mai gadi ya bude ya kare masa kallo dan bai wayeshi ba.


Wa kake Nima?


Wajen Rahima nazo, in banyi batan hanya ba nan ne gidan Alh. Lukman Giwa ko?


Eh Nan ne bari na isar da sakonka


Saiya rufe gate din ya wuce cikin gida, ya samu Rahima zaune a falo da hajiya Babba suna hira ya isar da sako ta ce tana zuwa sai ya wuce. Rahima ta mike ta kalli kanta da kyau.


Mami na hadu kuwa?


Rahima ai fade batawa, kinyi matukar haduwa sai kiyi maza ki tafi ki kaishi masauki.


Nagode Mami, in Ummi ta fito ki sanar mata da zuwan bakona, in yaci abinci Zan shigo dashi ku gaisa.


To ba damuwa Allah dai ya tabbatar da Alkhairin dake tsakaninku.


Ta amsa da Amin ta wuce, tana isa gate ta fita waje ta ganshi tsaye ya sanya duka hannunsa a aljihun wando yana kallon titi, ta tsaya tana kare masa kallo bata yi zaton zata ganshi a kafa ba saboda yadda yake nuna mata shi dan mai hannu da shuni ne, sallama ta yi ya juyo fuskarsa cike da mirmushi jajayen hakorarsa suka bayyana, dam kirjin Rahima ya buga ganinsa cikin munin kama domin yadda yake nuna mata kansa a waya gaba daya yasha bamban da wannan sai ta bayar ba shi bane bai rika yazo ba, cikin sanyin jiki ta soma magana.


Malam kaine me nima na?


Ya dage gira sama yana murmushi.


Nine, ko kina nufin baki gane Hashim ba.


Rahima ta waro ido waje tare da sakin baki cike da tsantsar mamaki.


Kana nufin kaine Hashim? Amma ya akayi kamanninka yasha bamban da yadda nake ganinka a hoto?


Wancen camera ne wannan kuma zahiri ne.


Tafdijam ta fada sai ta gyara tsayuwa ta rungume hannu a kirji gaba daya guiwarta ta sale da kuzarinta. Hashim ya matsa kusa da ita da sauri taja baya domin wani irin wari da kamshin turaren da yasa ya hade ya daki hancinta, ta toshe hanci tare da tsirtar da miyau. Rahima ta kasa danne kunci da bakin cikin da zuciyarta ke ciki saboda tsawon lokaci data dauka tana batawa akansa ba tare da tasan cewa shine Hashim ba a zahiri, ta hana idonta barci ta hana zuciyarta sukuni kullun cikin son ganinsa take a zahiri, tayi chart da shi na batsa sosai wanda take imagination dinsa tamkar a zahiri, kuka ne ya kubuce mata ta soma zubda hawaye kamar an bude famfo, ta kalleshi cikin tsana ta soma magana tare da zayyano masa duk kalmar data zo bakinta.


Wallahi da nasan haka kake a zahiri da ban bata lokacina ba akanka, Allah ya isa ban yafe ba, har abada bazan taba sonka ba wawa kawai kazami, ashe duk hotunan daka turo min ba Kai bane a jiki, kayi amfani da sune ka yaudareni, to Allah sai ya saka min macuci kawai, kuma ka bar kofar gidan nan tun kafin nasa a sakar maka karnika.


Ta juya a fusace zata koma gida, Hashim ya dakatar da ita cikin tsawa, ta tsaya ta juyo tana kallonta cike da tsantsar tsana mafi muni.


Ni zaki wulakanta har haka? To bari kiji wlh sai kinyi dana sanin abinda kika aikata min, wawuya mara tarbiyya, kila bata hanyar sunna aka haifeki ba shiyasa kike watsewa a waya kamar karuwa. Kuma kisa a ranki ko bajima ko ba dade sai kinyi nadamar abinda kika min.


Duk abinda ka isa kayi insha Allah babu abinda zan gani sai alkhairi, nafi karfinka domin wutsiyar rakumi ya yi nesa da kasa.


Ta kare maganar cikin dogon harara ta juya a fusace ta shige gida da gudu, har tana bangaje Umar da zai fito waje, Umar da Hashim suka yi kallon kallo ba wanda yacewa wani, Hashim ne ya yi kwafa kana ya wuce ya samu napep ya juya da shi inda ya fito. Umar ya dage kafada irin ko a jikinsa ya juya gida dan tambayar Rahima abinda yasa ta shiga gida da gudu.


Yana isa babban falo ya samu, Mami, Ummi, Sara, a kan Rahima dake kuka kashirban kamar wanda aka yiwa mutuwa, sun tsaya suna tambayarta dalilin kukan taki saurarensu sai gunjin kuka take harda birgima, yau dai autancin nata ya motsa, da kyar ta saisaita kukanta ta basu labarin abinda ya wakana tsakaninta da Hashim, Umar ya zauna dirshen a kasan tiles ya tintsire da dariya har yana rike ciki, sai da Ummi ta kwabeshi kafin ya sassauta ya mike tsaye ya soma rawa yana cewa.


Anzo gurin, kai kai kai kai anzo wajen, din din din din, anzo gurin. 


Sai ya kuma tintsirewa da dariya Yana cewa cikin sauti.


Anty Sara kun ganshi kuwa? Irin bagidajen kauye ne wanda hajilci ke naso a fuskarsa, ba arabi ba boko, wlh Rahima kinyi faduwar bakar tasa da Kika bata tsawon lokaci kina hira da shi a waya, na tausaya miki tare da Allah ya kara.


A fusace ta wawuri takalmi ta wurga masa tana hawaye, da sauri ya kauce yana dariyar mugunta. Ta kara fashewa da kuka.


Allah in baka bari ba saina tona maka asiri ai kasan a hannuna kake ka cigaba.


Da sauri Umar ya kunshe dariyarsa ya hade hannunsa biyu.


Na tuba bazan sake ba kin ga tafiyata Allah ya huci ran kanwata.


Ba shiri ya wuce suf-suf kamar munafiki dan gudun kar ta baro masa gari. Ummi ta dangware mata kai.


Maganinki kenan, saida naja miki kunne akan yaye yayen social media Amma kinki ji wannan shine na uku da kika gayyato yazo gidan nan, to gobe ma ki Kara.


Haba Hajiya karama rabu da ita taji da zafi daya mana, kinsan lallashi take bukata yanzu.


Cewar Mami tana murmushi cikin ba'a, Cikin gatsali Ummi ta mayar Mata da martani.


Nifa Yaya Babba bana son shisshigi, 'yarki ko tawa? to ki kama kanki ehe.


Allah ya baki hakuri bani nakar zomon ba rataya aka bani.


Cewar Mami ta mike cikin sanyin jiki ta basu waje, cikin bacin rai Sarah ta soma magana.


Gaskiya Ummi abinda kikewa Mami yayi yawa, ya kamata ki daina tunda baiwar Allah nan bata takura miki ba, duk kinbi kin tsangwama mata bayan itace gaba dake.


Allah ko rasa kunya beran tanka? to sa bulala ki dakeni shine nasan kin huce fushinki akan abinda nakewa sirikarki. Wato kin samu guri har kin fara mance matsayi na a gunki ko, toni yayar uwarki ce ko kinki ko kinso in kuma naso farraka aurenki da Ubaidun ina da yadda zanyi cikin kifta ido ki bar gidan nan, ki bini a hankali fa don kin fara shiga min hanci da kudundune.


Allah ya baki hakuri, daga gyara kayanka ai bai Zama sauke mu raba ba.


Sai ta wuce fiii kamar guguwa tana kunkuni. Ummi tayi kwafa ta maida kallonta ga Rahima.


Sai ki tashi ki je ki kwaso abincin da kika dafa mun samu na rana, dan shi zanci ma, gobe ma ki kara yayibo wani shashasha.


Rahima ta goge kwallarta ta mike tana zummburo baki.


Kedai Ummi kowa sai kin yi masa fada Allah babu kyau abinda kike yi.


Ummi ta kai mata duka Rahima ta kauce ta ruga tana murmushi harta fara mance bakin cikin da Hashim yasa mata.


Zanci ubanki Rahima, ashe na zama abokiyar wasanki ko, to zaki zo niman wani abu a gurina


Tayi kwafa zata wuce daki Rahima ta bude murya tana cewa.


Ummi kiyi hakuri bazan sake ba kinsan kece kadai uwata me sharen hawaye, Amaryar Abbanmu ko ba fosta dole abi ki sauda kafa a zauna lafiya.


Ummi ta juyo tana dariya.


Allah ya shirya min ke.


Shikenan ta sauko don Ummi macece mai mugun son fadanci, da ranta ya baci aka zubo mata kalamai nan take zata huce. Rahima tana shiga daki ta zauna dirshen a gefen gado ta shiga blocking number Hashim da duk wani kafa na social media da zai hada ta da shi, kana ta sauke ajiyar zuciya ta kira kawarta Aliya ta labarta Mata abinda ya faru, Aliya tasha dariya sosai daga bisani ta bata shawara akan ta guji yaye yayen samarin social media saboda da yawansu wasu ba Alkhairi a tare dasu.


Hashim kuwa ya koma zaria Soba LG, cike da kuncin abinda Rahima tayi masa tare da tunanin shirya mugayen kuduri akanta.


******    ****    ****** 


Yola


Bayan mako biyu.


Haruna ya Kuma dawowa rigarmu ya siya nono mai yawa tare da yiwa Baffa alkhairi, hakan yasa ya Kuma samun shiga sosai a zuciyarsa. A hankali Haruna ya saba da rigarmu aka dauki kimanin wata biyu yana zarya, sannan soyayya mai karfi ya kullu a tsakaninsa da Adda Jidda, Baffa ya nuna matukar amincewarsa akai sabanin ni da Ummanmu da muka nuna rashin amincewa saboda shi Haruna badan rigarmu bane hasalima bamu san daga inda ya fito ba, amma da yake ya gama siye imanin Baffanmu da kudi kwata kwata baya ganin aibin haka, Jidda kuwa har fushi tayi damu musamman ni akan nuna rashin amincewar aurenta da Haruna, ganin tayi nisa bata jin Kira yasa muka saduda tare da yi mata fatan alkhairi.


_____


Bayan wata biyu.


Aka sanya bikinsu sati biyu, Haruna ya turo iyayensa wanda yace daga Kano suke aka sanya biki zuwa sati biyu mai zuwa. A wannan lokacin ne ciwo na ya yi tsanani sosai, sai dai a tayar akwantar hakan yasa duk hankalinsu ya tashi da tunanin mutuwa zanyi, Baffa ko nuna farin cikinsa karara yayi yana tunanin zan mutu ya huta da wahala, da yake ina da sauran shan ruwa a gaba, a wani zuwa da Haruna yayi ya samu labarin rashin lafiyata shi ne yayi ruwa yayi tsaki akan lamarin ya dauki nauyin kaini asibitin birni, Wanda inda a son Baffa ne baiso haka ba a cewarsa kar yayi asarar kudinsa a banza dan ba warkewa zanyi ba, yaki saurarensa muka tafi asibitin birni tare da Umma Adda Jidda tayi mana rakiya. 


Nasha gwaje gwaje kama daga na jini har fitsari da hotuna dan a bincika komai a jikina a gano cutar data ke damuna. A ranar basu barmu mun dawo gida ba suka bani gado na cigaba da jinya har sai da naji sauki sosai, sai da na kwana biyu kafin sakamakon gwaji na ya fito, wanda ya tabbatar da ina dauke da cutar suckler, aka daurani bisa kan magani tare da karin jini wanda nasha har leda uku, ga bayanin likita da yayi mama.


SICKLE CELL DISEASE: (Amosanin jini) ita wata ciwo ce mai kama jajayen kwayoyin halitta na jini( Red blood cell). Ba kwayar cuta bace take kawo shi gadar ta ake daga wajen iyaye wadanda ke dauke da wannan ciwon.


Kwayar halittar jajayen jinin tana fitowa ne da siffar sabon wata ko lauje maimakon a kewaye kamar yadda ya dace hakan zai sa ta hana kwayoyin hallittar jikin dan Adam samun wadatatacciyar iska (oxygen).


wannan ciwon mafi yawa tana fara nuna alamomi ne a yaro mai dauke da ita idan yakai watanni biyar zuwa sama, ga kadan daga cikin alamomin :


- Ciwon jiki

- Rashin Jini

- Kumburin Jiki

- Yawan rashin lafiya

- Hajijiya

- Rashin karfin jiki

- Rashin girma da wuri

- Gani dishi dishi

- Ciwon kirji


Ana iya tabbatar da mutum na dauke da wannan ciwon ta amosanin jinin ta hanyar gojin jini (Heamoglobin Genotype Test).


Ga Nauyukan Jinin kamar haka :


- AA ( Lafiya)

- AS ( Akoi Rabin Ciwon)

- SS ( Akoi Ciwon gabaki daya)


1- Idan mai Kwayar sinadarin AA ya auri mai AA dukkan yaran da za su haifa lafiyayyu ne, babu maganar wannan ciwon.


2- Idan mai AA ya auri mai AS shima ba matsala bace sosai acikin yaransu za a samu masu AA da masu AS.


3- Idan mai AA ya auri mai SS shima dai ba matsala bace sosai sabida dukkan yaran su za su zama AS.


4- Idan Mai AS ya auri mai SS shima akoi matsala sabida za su iya haifan masu SS da Kuma AS ( Babu Aure tsakanin su)


5- Idan mai AS ya auri mai AS akoi matsala sabida rabin yaransu lafiyayyu ne rabi kuma za su gaji SS (akoi matsala shima Babu aure tsakanin su)


5- Idan Mai SS ya auri mai SS dukka yaransu za su gaji SS. Sabida haka akoi matsala. (Babu aure tsakanin su(


Idan akasamu mutum na dauke da wannan ciwon yana bukatar kulawa ta musamman :


1- A dinga bawa mara lafiya maganin karin jini (folic acid) kullum daddaya.


2- Yana dakyau abawa mai dauke da wannan ciwon maganin kariya daga zazzabin cizon sauro (proguanil) shima kullum.


3- Yana dakyu mai wannan ciwon yadinga shan ruwa sosai sabida rashin ruwan jiki na tayar musu da ciwo.


4- Masu dauke da wannan ciwon basa son sanyi sosai haka Kuma basa bukatar zafi.


5- Masu dauke da wannan ciwon idan suka zabi shan tabar sigari rayuwar su zai shiga cikin hatsari.


6- Bada maganin rage radadi ga masu dauke da wannan ciwon kafin zuwa asibiti ba laifi bane.


Dayawa mutane suna tambaya shin ana warkewa daga wannan ciwon:


Babu wani bincike da ya nuna na cewa akwai maganin wannan ciwon sai dai ana iya yin aiki a canzawa mai dauke da wannan ciwon b'argon sa wanda ake kira da bone marrow transplant.


A lokacin da likita ya gama yi mana wannan bayanin ciwon a gaskiya na yankewa kaina kaunar zan rayu, domin mun shiga cikin damuwa sosai musamanin ni da nake ganin gaba daya zuwata duniya jarabawa ce wanda nake fatan Allah yasa na samu lahirata tayi kyau. Sati na guda aka sallamo ni kuma cikin ikon Allah naji sauki sosai har kumari nayi saboda ruwa da jinin dana sha. A lokacin saura sati guda bikin adda Jidda aka cigaba da shirye shirye kafin zuwan ranar saboda ana daura aure zai dauketa su tafi, a Yola yace zasu fara zama kafin ya kaita ainahin gidansa dake Kaduna kamar yadda ya fada.


----


Ranar daurin Aure

Anyi shagali irin namu na fulani, aka daura auren ba wata hayaniya kowa ya shaida Adda Jidda ta auri babban mutum d'an birni mai kumbar susa, saboda irin shagalin da aka yi sai kace yar sarkin garinmu. Washe gari da misalin karfe sha biyu na rana muka rakata gidanta da yake cikin birnin Yola, a gaskiya mun gigice da susucewa irin tagomashin arzikin da aka zuba a gidan, tun da muke bamu taba zuwa cikin yola ba balle musa ran zamu ga irin wannan gida aljannar duniya. Haka muka kwana guda muka barota muna santin wannan daula da Adda Jidda ta samu kanta a ciki. Mun sha kuka sosai kafin muka rabu da ita muka dawo rigarmu cike da jimamin rabuwa da ita, a Bakina Umma ta samu labarin irin arzikin da muka baro Jidda a ciki, tayi murna sosai tare da yi mata fatan alkhairi, ta bangaren Baffa kuwa ya samu kansa da matsanancin farin ciki wanda ya kasa rike murnansa harda kukan dadi.


Kwanan Jidda biyar a wannan gidan suka zo gida, a yadda fatarta ta sauya cikin kankanin lokaci ba karamin mamaki muka yiba, ta murje tayi kyau har dan kiba tayi hakan ya tabbatar mana da ta samu kwanciyar hankali sosai. A zuwansu ne Haruna ya dauki Baffa zuwa cikin Baihari ya nuna masa wani gida mai kyau ba laifi domin anyi masa gyara, daki ciki uku da bayi da kicin sai rijiya daga gefe, ya dankawa Baffa key yace ya bashi halak malak, Baffa harda kuka dan murna yayi masa godiya kamar zai durkusa masa, haka suka dawo ya dauki Jidda suka tafi da nufin kwana biyu zasu dawo. Baffa ya labarwa Umma kyautar da Haruna yayi masa ta yi murna sosai, kana Baffa yace zaisa yan haya a gidan saboda bazai iya rabuwa da rigarmu ba duba ga iyaye da kakanni duk nan suka kwanta dama, baya jin zai iya rabuwa da mahaifarsa.


Jidda suna komawa washe gari suka wuce Abuja, satin su biyu ya tarkatota zuwa gidansa dake kaduna, babu wanda yasan inda take daga ita sai shi suka fara sabon rayuwa. Abu na farko data fara fuskanta shine kulle yaki bari ta saba da kowa hatta ma'aikatan gidan bai yarda suyi magana mai tsawo ba, sannan bata komai ci da Sha sai dai a kawo Mata, jin dadin rayuwa babu wanda bata samu, fita kuwa sai da daddare suke fita suyi yawo a mota zuwa manyan wajen shakatawa da restaurant, a hankali ta fahimci Mijinta mutum ne mai son jin dadi kuma yana matukar sonta wanda yasa ta sakankance cewar tayi dace da gidan aure.


----


Bayan wani lokaci 


Kusan wata biyar kenan da bikin basu sake zuwa ba, Umma ta aikeni ya kai sau biyar zuwa gidanta na Yola a kulle nake samu basa nan, daga karshe dole yasa muka hakura kullun muna zuba idon zuwansu. Wannan shurun da suka yi yasa ni cikin damuwa tare da Umma, Baffa kuwa bai damu ba bai Kuma hango matsalar haka ba a cewarsa in anji shuru to lafiya ce tasa haka.


A hankali mutanan gari suka soma yada gulmar Baffa ya saida Adda Jidda, saboda irin yadda mutane suka bayar da labarin gidanta, gashi kuma wata da watanni ba amo ba labarinta, tun ana yin zancen a boye har aka soma yi a gabanmu ana zund'armu wai Baffa ya saida lafiyayyar 'yarsa ya bar nakassasshiya. Abin yayi matukar damunmu, ya zamana mutane karara suke gudunmu basa yarda mu rabesu, hakan yasa muka takura sosai bama iya fita sai kwakkwaran dalili, shiko Baffa gaba daya ya natsu guri guda baya fita sai in zaije kiwo ko masallaci, hakan yasa ganin halin da muke ciki muka bar rigarmu muka koma Baihari gidan da Haruna ya siyawa Baffa, muka tarkata komai namu hatta shanunmu dasu muka yada zango, tare da kafa sabon rayuwa, da yake kanin Baffanmu yana garin da iyalinsa sai muka cigaba da zumuncinmu muka hakura da rigarmu.


#Rahmace

#MamanSultan

#share

#comments

#vote


     _______________

*Talla*


*HERBAL BREAST ENHANCEMENTS*


-Yana ciko breast suyi kyau.

-In sun fadi zasu ciko su tashi.

-Ga mace me yaye zai gyaru su ciko ba ruwanta da zubewar Breast.

-Ga mata masu rama, in sun sha zasu ciko suyi kumari.

-And finally yana karin ni'ima sosai.


Kawata kin gwada magunguna basu miki aiki ba? to yar uwa kiyi kokarin yin amfani da wannan Breast enhancer din insha Allah kafin sati biyu zaki ga biyan bukata. 100% tested and trusted.


Siyan daya ko sari, muna turawa ko ina. Delivery is not free


Price:N4,000

Location: Kaduna State

WhatsApp: ***.


UMMU SULTAN

100% NATURAL HERBS.