Page 22
by @babyluv
*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_
2️⃣2️⃣
*Not edited*
_babyluv_
*****
Kallon Sabrine farouk yayi a Zuciye ya jawo hannunta ta dawo kusa dashi , sannan ya nuna Adnan da yatsa ya fara fad'in “harkai waye d'in , this is family issue don't involve ana magana ne ta family ”
Kallon fuskar Sabrine Adnan yayi da alama jin zafin rikon da farouk yayi Mata take , cikin hawaye Sabrine ta ri'ke hannun farouk daidai inda ya ri'ke Mata hannu tace“yaya farouk you are hurting me wallahi da zafi ka ri'ke ni”hawaye ya Kara zubo Mata, kallan ta farouk yayi Yana jin zafin abinda Tai masa yasa“i will continue hurting you Sabrine inda har zaki avoiding d'ina akansa”
Ran Adnan ne ya baci dan shi harga Allah beyi niyyar kula farouk Amma yanzu kam Dole sai yayi masa magana hakan yasa ya dubi farouk yace“abokina take it easy mana , and you just said something akan family issue right”sai kuma yayi shiru Yana duban face d'in Sabrine sannan ya matsa inda Sabrine ke tsaye farouk ya damke hannun ta sannan ya dora da fad'in “hakika a soyayya babu duben family ita soyayyya guda d'aya ce kuma ni idan na rantse maka bazan kaffara ba wannan soyayyar ni Sabrine take yiwa ita kuma nasan ni take so , so stop talking about hurting my Sabrine hurts me instead”yakai karshan maganar Yana raba hannun Sabrine da farouk ya ri'ke Mata shi kamar zai balla
Kasan control d'in anger d'insa yayi farouk , tabbas yasan inya Kara ko minti daya to tabbas zaiyi abinda Granny zata iya fitowa shiyasa cikin fushi ya nuna Sabrine da yatsa sannan ya jinjina Kai kawai yabar gurin
Dawani mugun karfi ya ja motar sa , ganin hakan da gudu me gadi ya bud'e masa gate ya fice
Zamewa Sabrine Tai ta zauna akan kujerar gurin tana kuka, sosai kukanta ke sosa masa hakan yasan gently ya jawo kujerar sosai kusa data Sabrine sannan ya zauna Yana dubanta dayananyin kayan da yake jikinta Dan wallahi wannan kayan tsaf zasu sashi zaucewa
Cikin magana 'kasa kasa wadda Sabrine kad'ai dake kusa dashi zata iya ji , magana me cike da lallashi Adnan yafara fad'in “sabrine Dan Allah stop crying muyi magana please kinji”tsayar da kukan Tai batare data d'ago kanta ba, ganin tabar kukan yasashi dorawa da fad'in “sabrine nayi zaton problem d'inki Is between me and my Dad and bayin zuwa na Nan saina ga wani problem d'in daban ”
D'agowa Sabrine Tai ta dubi Adnan sosai , jin yadda kirjinta ya buga yasa da sauri ta janye idonta daga kallonsa tare da fad'in “adnan please what brings you here ? I told you ka rabu Dani Dan Allah , kada ta sanadiyya ta familyn ya samu problem but please ka kyaleni dan”
“wallahi Sabrine bazan barki ba , impact idan dad zai ban nai choosing between you and him I will choose you”
Zaro ido Sabrine Tai jin abinda yace, da sauri ta Mi'ke, tana ja baya ahankali tana fad'in “stop saying such things adnan , nidai katafi pls don't come back Dan Allah”kawai ta juyawa Tai gida da gudu, bin bayanta Adnan yayi da kallo wani abu yaji ya tokare masa kirji dasaida yadan dafa kirjinsa, but abinda yayi noticing aduk maganar da Sabrine batace Bata sanshi ba , kenan tanason shine?
And ko Dad d'insa haryanzu beji tace bataso ba kenan what does that mean, badai Sabrine can't choose between him and Dad
“ya Allah help me, I'm hepless here”ya furta a fili Yana dafe kansa , wallahi dazai iya da tabbas saiya bar Sabrine for sure Amma Ina kaddara tariga fata, a yadda yakeji he will surely sacrifice anything for Sabrine, why can't did the same thing to Dad? Why can't i sacrifice my love to my darling Dad? , why why,
Yana Nan zaune Zuciyarsa nakara masa zafi, ahalin yanzu kwanyar kansa ta tsaya besan meyamata yayi ba , d'ago kansa yayi yaga me gadi, da hannu yayi masa alamar yazo, aikuwa da hanzari me gadi ya taso yazo ya rusuna sosai , kallonsa Adnan yayi sannan cikin shakakkiyar muryarsa wadda dakyar take iya fita yace “please I want to speak to Sabrine's mom or even dad d'inta please”gani yayi megadin yazuba masa ido , daganan ya fuskanci Ashe da turanci yayi masa magana, Dan dukan kansa yayi sannan yace“sorry please Ina nufin inaso nayi magana da mahaifiyar Sabrine ko mahaifinta right now please”
Murmushi me gadin yayi alamar ya fahimta sannan ya Dan risunar da kansa kasa alamar biyayya yace“ranka ya dad'e Sabrine Bata da mahaifiya Dan ta rasu”da sauri Adnan ya kalli me gadin Dan wallahi betaba tunanin Sabrine's mother is dead ba, kallonsa yayi tare da fad'in “you mean Sabrine marainiyace”daga masa Kai me gadin yayi alamar Haka yake nufi, jiyayi ya Kara kaunar Sabrine Dan aduniya yana tausayin maraya,
“okay koma dai wane inaso Naga wani nata please”rusunar da kansa kasa yayi me gadin had'e da fad'in “to yallabai inshallah yanzu zanje na fad'a wa hajiya”
“okay”was abinda Adnan yace , Yana kara jinjina kansa , da sauri mekama da gudu megadin yanufi cikin gidan
Ita dai Granny tananan zaune taga hucewar Sabrine da gudu tana kuka , abin ya daure Mata Kai Dan taga da walwala ta fita amma ta dawo da kuka, tana Shirin kuma tashi taje taga meke damunta taji abinda ya faru taji sallamar me gadi , da mamaki ta dube shi Dan taji meke tafe dashi
Taga 'Dan nesa da inda Granny take ya d'urkusa cike da ladabi yace“barka da wannan lokacin hajiya”
D'aga Kai tayi tare da kosawa taji me zaice , ganin Haka yasa megadin yace“hajiya anyi bako ne shine yace nazo nai masa iso”
“bako”granny ta furta a fili, da sauri yace “eh hajiya wani Dan matashin yaro ne haka , Amma da alama gurin hajiya karama yazo”
“tooo kana nufin gurin Sabrine”eh hajiya ya furta da sauri, jinjina Kai tayi sannan tace “jeka jeka shigo dashi”da sauri ya tashi tare da fad'in angama hajiya, Yana fita Granny ta d'au hijabi take kusa da ita sannan ta zura, waiting for Adnan to come Dan taga waye Wanda yazo gurin jikallen ta
Komawa yayi hargun Adnan ya taho dashi , har cikin parlor d'in ya kaishi Yana fad'in “ranka ya dad'e bisimillah” sannan ya kalli Granny cikin rusunawa yace hajiya gashi,
D'aga masa Kai Tai sannan taiwa Adnan nuni da kujera dake cen nesa da ita alamar ya zauna , Shima me gadin tace ya koma bakin aikinsa sannan yayi godiya ya juya ya fita,
Sam Adnan kasa zama yayi a kujerar sai kawai yayi zaman sa a carpet d'in Wanda yake da laushi sosai kamar Cushing ,
Dubansa Granny Tai had'e da fad'in “sannu da zuwa”sosai Adnan yayi kasa da kansa cikin ladabi da biyayya ya gaishe da Granny Dan jiyayi Yana matukar jin nauyin ta, sosai Granny ta amsa cikin fara'a Dan wallahi ita tunkan su gaisa taji yaron ya birgeta sosai yana da tarbiyya da alama, shiru Adnan yayi ya kasa cewa komi Banda hannunsa da yake murza azurfa
Ta fiskanci nauyin ta yakeji yasa tace“kaine aka cemin ka zo gurin Sabrine”
Kara sunkuyar dakai yayi sannan cikin nutsuwa yace“eh hajiya nine ”
“to Masha Allah kaga kasan me zai faru Bari na tashi na d'ebo kayan kwalliya ta nima na matso kyau d'ina ka kyale Sabrine d'innan”dariya Adnan yasaki , jiyayi ya saki jiki da Granny hakan yasa ya dubeta ganin tana niyyar tashi yace“a' a hajiya Yi zamanki kibari a fara da guda daya itama kuma wahala take ban”abinda Granny takeson ji kenan Dan taga yaki sakin jiki da ita shiyasa tace masa hakan because she wants him to feel comfortable taji meke tafe dashi, jin ya furta Sabrine na wahalar dashi hakan yasa Granny tace shikenam kaga tunda ita bataso ni inaso saika kyaleta, dariya sosai Adnan yayi sannan Granny ta kalle shi with serious face tace“tom Ina jinka Kai d'an inane and did you know Sabrine” babu kojin nauyin Granny Adnan ya dubeta had'e fad'in
“Ni sunana ADNAN ni mazaunin kano and I'm a doctor , I seriously love Sabrine but I don't know what to do now”
Girgida Kai Granny Tai azuciyarta tana tunanin abinda ya hana Sabrine son wannan yaron tunda tace batason farouk
“to naji na fahimceka abinda nake bukata give Sabrine some time dakake ganinta Nan yarinyace but inshallah komi zaiyi daidai kaji, I want you to go back home”daga Mata Adnan yayi yanaso ya fad'a Mata dalilin daya gifta tsakaninsa da Sabrine Wanda ya kawo Mata rudani Amma Yana jin tsoro Kar Granny tace ya hakura shiyasa kawai yayi shiru ,
Yanaso ya Kara ganin Sabrine Sabrine Amma yanajin nauyi , Kamar Granny tasan abinda yake tunani tace“ko saina turo ma ita ne, kaga kasaki jikinka nan Kamar gidankune kaji duk meson Sabrine tabbas ni yaso saboda Ina santa sosai kaganta Nan mahaifiyarta tun lokacin haihuwar Sabrine Allah ya kar'bi rayuwarta, Yan uwa da abokan arziki sunyi sunyi na bada ita Amma bazan iya ba Dan gani nake kamar mahaifiyar Sabrine nake gani”jinjina kai Adnan yayi dajin dadin maganarta Dan ta karasa bashi confidence akan Sabrine yanzu shi ko hango Daddy baya Yi kawai soyayyar Sabrine yake kara rayawa azuciyarsa, Granny ce ta katseshi da da fad'in “to ni yanzu likita ya hanani hawa bene bare naje na koro maka ita ”ganin tana kokarin tashi yasa Adnan saurin fad'in “no Granny kiyi zaman ki , ni zanje da kaina”jinjina Kai Granny tayi sannan tace “to ai shikenam ga dakinta can a sama ni zan koma ciki ka gaida gida kaji ”tana fad'ar hakan ta tashi ta nufi wani part Wanda da alama shine nata, Saida ya tabbatar Granny ta bar gurin sannan ya d'aga kansa sama Yana kallon upstairs d'in , Yana tunanin ko wanne dakin Sabrine d'in oho, tashi yayi ahankali yasa takalminsa sannan ya nufi Benin, yadda yaga dakin farko hakannan jikinsa be bashi dakin Sabrine bane hakan yasa kawai ya nufi wani dakin dayake facing d'insa Wanda ya tabbatar zata iya yiwuwa na tane
Sabrine kam takasa zaune takasa tsaye ban sintiri a dakinta babu abinda take , Dan taga shigarsa gurin Granny data leka ta window , fatanta azuciyarta Allah yasa Granny ta Kore shi tace anmata miji koya gyaleta ta huta, tananan tsaye tana jiran taga fitowarsa daka gun Granny Dan tana tsaye a window taji an turo kofar, tayi zaton Granny nice yasa kawai ta taho da gudu as usual Dan indai taji Granny ta hawo sama saita rungumeta Dan likita ya hana ta hawa saman Amma ita Sabrine gani take kwara Granny ta dinga hawowa hakan kaman training ne, ita Granny beyewa Sabrine take tana hawa saman
Jinta ajikin mutum gakuma wani mahaukacin kamshi dake tashi ajikinta , yasa zuciyar Sabrine bugawa da sauri sauri, da sauri ta d'ago da kanta zata bar jikin Adnan Amma besan meya shiga cikin Zuciyarsa ba kawai yariketa sosai , rikon da bazata iya tashi tabar jikinsa ba, yadda yaji kirjin Sabrine a kirjinsa da yadda yakejin tudunsu jiyayi gaba d'aya wani abu na daban ya ziyarci jikinsa, sunkuyowa Adnan yayi daidai saitin kunnan Sabrine da muryarsa wadda Bata iya fita sosai yace “where are you going Sabrine? Why are you doing this to my innocent heart Sabrine why? ”karayin kasa sosai Adnan yayi da muryarsa tare da fad'in “narantse da Allah sabrine Ina sonki wallahi nafi dad d'ina bukatarki please accept me mana Sabrine please”yawani jaa please d'in dawani huci Wanda har Saida Sabrine taji saukarsa a wuyanta,
Da sauri Sabrine tayi baya had'e da kwace jikinta d'aga na Adnan tana yin baya idonta na cikin na Adnan kamar yadda Shima kallonta take, binta yayi ahankali tana matsawa baya Ahaka har Saida sukaje jikin bango, saurin kautar da kanta Sabrine Tai tana rintse ido had'e da fad'in “no Adnan stop please leave my room, please”jaa baya kadan Adnan yayi Yana kallonta , yasan abinda yake bekamata ba Amma to ya ya'iya indai Sabrine zata dinga gudunsa kamar haka to tabbas Zuciyarsa zata iya bugawa
Dan sunkuyo da kansa Adnan yayi“feel free Sabrine I will not do anything to you until you get married and you know what Granny ta banike ”da sauri Sabrine ta d'ago kanta ta kalleshi had'e da fad'in “what Granny ta baka ni , why Granny will did this to me”baya Adnan yayi Yana d'aga kafad'a had'e da fad'in “yess because she likes me”
Hakannan Sabrine ta tsinci kanta dayiwa Adnan karya da fad'in “may be she told you saboda ta kwantar ma hankali but let me told you that man daka ganmu dashi awaje she's my husband Tobe munsamu missed understanding ne shiyasa kaji nace i didn't love him but I love him and I will get married to him ”
“and I will kill him ”yayi saurin katseta , zaro ido Sabrine Tai da mamakin abinda yace, d'aga Mata gira yayi Yana kara fad'in “yess I will kill him, and Bari kiji Sabrine not only him koma waye yayi trying aurenki because you are my life and anyone try to took away my life from me you can't imagine what I will did to him, ”yana fad'ar hakan ya bud'e kofar zai fita juyowa yayi ya dubi Sabrine da ta saki small mouth d'inta tanajin abinda yake fad'a
“i repeat it you are my life Sabrine and I love you, make sure you come back to school or else wallahi kullum Ina hanyar kaduna Mark my words”daga Nan kawai ya fice beko juyowa ba, Granny Bata parlon Dan haka kawai ya fice , yana zuwa yayi wa megadi alama da hannu yazo aikuwa da gudu ya taso , yana zuwa ya durkusa had'e da fad'in barka da fitowa ranka ya Dade
Bud'e masa bayan motarsa Adnan yayi yace yashigarwa da Sabrine kayannan, ledojine irin manya manyannan dayatsaya wani babban super market yayiwa Sabrine wani mahaukatan siyayya dashi kanshi baze iya tuna meya siyo ba, sannan ya d'auko kud'i meyawa ya bawa me gadin Wanda yaji dad'i sosai yashiga yiwa Adnan adduar Allah ya bashi Sabrine aikam Adnan yaji dad'i sosai da wannan me gadi ya bud'e masa gate ya fita da farin ciki fal ransa na yadda Granny ta karbe shi hannu biyu ,da wannan farin cikin yashiga kano…
*Share and comments*